Sashe 5
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma yau ɗin ba kallonsu take ba, tunanine fal kanta, tunani take kan abinda ya faru ɗazu a makarantar da take aiki, abinda ya faru ɗazu tsakanin Malamar nan da yarinyar da ta kira kanta da Mishal.
Yanda yarinyar ta haƙiƙance kan ba za ta kwashe sharar ba, ita da ta mata magana, sai ta ganta a matsayin me sauƙin kai, ashe ba haka ba ne.
Dan da ƙyar ta samu ta tausheta, sannan ta haƙura ta tafi, kafin ita Rabin ta dawo kan malamar ta bata haƙuri, kana ta ci gaba da sharar da ta fara.
“Ni ban ga Abba ba”
Cewar Saratu, kuma maganar tata ce ta dawo da Rabi zahiri.
Habiba ta yi tsaki tana taɓe baki.
“Yana can yawon gantalinsa mana”
“Gaskiya Umma bakya kyautawa Wallahi, kullum ina faɗa miki cewar abinda kike bai dace ba....”
Cewar Saratu, kuma tun kafin ta ƙarashe Mama ta tari numfashinta.
“Eh, me u*a, an taɓo mata ƙahon zuciyarta, yau ni Allah na tuba har na kalli wannan abun na ce shine ub*na?!....”
“Mama ya isheki haka....
Da kike rena shi a yanda yake, gwara shi sau dubu da iyayen wasu, kuma ub*n mutun ko a bola yake kwana indai har shi ne ya haifi mutum ro ub*nsa ne, ko miji bai isa ya amsa sunan uba ba....
Kuma ki sani cewar; da ub*a ake ado.....”
Kuma Saratun na kaiwa nan ta miƙe daga kan tabarmar ta faɗa ɗakinsu har tana ƙoƙadin bangaje Rabi.
“Aikin banza....
Umma mi ye na faɗa ba dai-dai ba ?”
Mama ta tambaya tana tauna doyar bakinta, dan bisa ga dukkan alamu ma ba ta yi azumin ba yau”
“Wallahi baki da laifi, me ake da Ɗan Lami a rayuwa?!, ita ma in ta gaji da abinda ake masa ne a gidan nan,ta yi zuciya ta nemi mijin aure....”
Ita dai Rabi sai ido, dan bata isa ko tari ta yi ba, bata da wani kataɓus a gidan, yau wanda ya kawota ya aje ma bashi da iko da gidan bare ita karan kaɗa miya.
“Umma babu ruwan sanyi fa...”
Habiba ta kalli Fatima, sannan ta kalli ruwan dake aje a can baranda.
“Yanzu ke dan baƙin hali kinsan babu ruwan sanyi a gidan shi ne kika yi shiru, yanzu da an kira sallah fa?”
Ta kawar da kanta.
Habiba ta yi ƙwafa tana cince ƙullin dake gefen zaninta, ta fito da nera ɗari biyu, sannan ta cillawa Rabi.
“Karfa, uw*r 'yan baƙin hali, tashi ki je ki siyo mana ruwan sanyi leda ɗaya, kuma idan kin so ki zauna a can kin ji ?”
Rabi ba tace komai ba, ta miƙe tsaye, sannan ta shiga ɗakinsu ta ɗauki hijabinta, ta fita.
Mama ta bi bayanta da harara.
“Wallahi na tsani yarinyar nan, dan Allah Umma ki koreta ta koma inda ta fito”
Habiba ta yi dariya.
“Baki da hankali Mama, ai idan na barta haka ban amsa sunan Habiba ba, so nake sai ta tagayyara tukunna, ba na so ta koma wurin dangin uwarta ta ji daɗi, dan kinsan ai 'yan uwan uwar tata suna da kuɗi, so nake sai ta gama lalacewa, so samu ma ta haɗa da cikin she*e, sannan zan sa Ɗan Lami ya koreta daga gidanan, tunda dama ni ce na saka shi ya kawota!”
Mama ta tintsire da dariya, Fatima na na tayata.
Rabi na fita kai tsaye bakin titi ta nufa, a hanya ta tsaya tana kallon wasu yara dake buga wasan ƙwallo.
Ba yau ta saba ganinsu suna ƙwallon ba, kusan kullum a lokaci irin wannan suna buga ƙwallo, a wasu lokutan ma ba su ne suke yi ba, manya ne ke yi a filin, kasancewar ana azumi shi yasa manyan basa bugawa.
Tsaiwarta ta gyara tana ci gaba da kallonsu, ƙwallo na ɗaya daga cikin burukanta na duniya, ƙwallo mafarkin rayuwarta ce, a da bata da wani fata sai na ta zama shahararriyar 'yar ƙwallo.
Sanda Ummanta na raye burin nata ya ɗauko hanyar cika, dan akwai wata football academy da Umman nata ta sakata, kuma kullum tana zuwa yin training, sai dai bayan rasuwar Umman tata komai ya sauya.
Komai ya ruguje, ciki kuwa harda burinta na zama 'yar wasan ball, dan a nan gidan makaranta ma ba'a barta ta je ba, ta ina za'a barta ta wani samu damar tarining.
A gidan kakaninta kuwa cewa suke ai ƙwallo ba wasan mata ba ce, dan haka ita ƙwallo ba ta dace da ita ba, ko a sanda Umman na raye babu yanda ba'a kai ruwa rana ba a kan wannan ball ɗin.
Ganin tsaiwar ba zata kaita ba hasa ta kwashi ƙafafunta ta yi gaba.
*FHA 2 lugbe, abuja*
*11:00am*
Wasu baƙaƙen motoci ne har guda biyu suka yi parking a gaban wani gida cikin layin.
Yanayin gudun motocin ne kaɗai zai tabbatar maka da ba lafiya ba.
Ƙofar gaba ta ɗaya daga cikin motocin ta buɗe, wani matashi ya fito a fusace, yanayin yanda yake fitar da iska daga hancinsa ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar a fusace yake.
Sauran ƙofofin suka buɗe, sannan ɗaya bayan ɗaya mutanen ciki suka firfito, yanayin shigarsu ne kaɗai zai shaida maka matsayinsu.
Duka sanye suke da baƙaƙen kaya, sannan a jikin kowannensu akwai bullet proof jacket, wadda a jikinta aka rubuta DSS.
Na farkon da ya fito ne kaɗai babu bullet proof jacket ɗin a jikinsa.
Kuma shi ne a kan gaba wajen shiga cikin gidan, a harabar gidan suka tsaya.
Matashin sai safa a marwa yake, kamar wanda aka ɗorawa maganar duniya.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya taho kusa da shi, hannunsa riƙe da bullet proof jacket, a tsorace yace.
“Sir baka saka wannan ba...”
Wani irin kallo da ya masa ne yasa bai ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa ba.
Hakan yasa jami'in ja da baya, ya matsa kusa da mace ɗayan dake cikinsu, dan kaf wurin maza ne, ita kaɗai ce mace.
“Ki masa magana”
Kanta ta gyaɗa, sannan ta sofare bingarta ƙirar pistol a aljihun wandonta na baya.
Ta sa hannu ta karɓi rigar, ta matsa kusa da shi.
“KULIYA kana buƙatar wannan......”
Sai da ya fitar da wani huci na takaici, sannan ya miƙo hannunsa ya fisgi rigar ba tare da ya kalleta ba, rigar ya saka yana ta hura hanci.
Sannan ya yi alama da kawo masa abun magana.
“Ta ko ina gidanan a kewaye yake da jami'an tsaro, zai fi muku da ku miƙa wuyan ku cikin ruwan sanyi, idan kuma ba haka ba!.......”
Ya kai ƙarshen maganar yana haɗe haƙwaran sama da na ƙasa cikin fusata, sai da ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.
“Idan ba ku miƙa kanku ba, sai na binne kowannenku da ransa, idan kuma kun musa, kada wanda ya fito a cikinku!....”
Wani irin shiru ya ratsa wurin tsawon muntuna biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan.
“Wallahi wannan mara mutuncin ne!....”
Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki.
A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji.
Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace.
“Wai wa kake nufi?”
“KULIYA!”
Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna ɗaya da yake firgita duk wani me laifi a garin abuja da kewatenta.
Sunansa kawai kan sa cikin mai laifi ya ɗuri ruwa, KULIYA wani irin bahagwan mutum ne, wanda ba'a gane gabansa bare bayansa, ga saurin fushi da fusata, bashi da imani ko kaɗan.
A razane suka miƙe tsaye gaba ɗaya, kuma ɗaya bayan ɗaya suka shiga leƙa windown dan tabbatar da abinda ɗayan nasu ya faɗa.
“Yanzu miye abun yi ?”
Ɗaya daga ciki ya tambaya, fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali.
“Kawai mu miƙa wuya”
“Kai baka da hankali, mu miƙa wuya fa?”
“To mu ci gaba da zama har ya shigo ya harbe mu”
Daga harabar gidan, Kuliya ya fiddo da bindigarsa wadda ke saƙale a bayansa, sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan gadan-gadan.
“Kuliya!, what are you trying to do ?”
Wannan macen cikin nasu ta faɗi tana bin baya sa.
“Sharon, kar ki takuramin!”
“Ba'a bamu umarni ba, dole sai mun jira umarni.....”
Sharon bata rufe bakinta ba, Kuliya ya raɓata ya wuce cikin gidan.
Cike da takaicinsa ta ɗaga kanta sama tana girgiza shi, har abada Aliyu ba zai taɓa sauyawa ba.
Matasan nan na tsaye a cikin ɗakin, suna ta nemawa kansu mafita.
Basu ankara ba suka ji an banko ƙofar ɗakin, kuma a cikin ƙasa da sakan sittin.
Ƙarar harbin bindigar Kuliya ya cika gidan.
Kafin aka samu wani harbin da ya fito ba daga bindigar tasa ba!.
*Kano....*
*11:30pm*
Motoci biyu ne parker a wani filin Allah, wurin ba gida gaba da baya.
Duka fitilun motocin a kunne suke, kasancewar babu wani haske a wurin bayan na motocin.
Motocin na kallon juna ne, yayin da wasu mutane shida ke tsaye a tsakiyarsu.
“Ku bamu saƙon”
Muryar macen cikinsu ta faɗa, wasu gardayen maza ne guda uku a bayanta, alamun dai tare suke.
Yayin da take fuskantar wani matashi, wanda shi kuma mutum ɗaya ne tsaye a bayansa.
Matashin ya yi murmushi.
“Ku bamu kuɗi tukunna....”
Ya faɗi cikin rainin wayo.
Sai macen ta yi murmushi, tana kawar da kitson kalabar attachment ɗin da ya sauƙo mata kan fuska.
“Ka...bamu saƙon!”
Ta maimaita masa abinda ta faɗi tun farko, sai ya kuma yin murmushi.
“Ku kira ogan naku ya zo ya karɓa muku....”
Daga cikin motar dake bayan su macen, mutum ɗaya ne zaune a gidan gaba, kansa a sama, yayin da bayansa ke jingine da jikin kujera.
Waƙar lonely at the top dake tashi a cikin motar yake biyawa, yayin da idanuwansa ke a lumshe.
“Zuwan RAJA nan ba zai mana daɗi ba, dan haka ka bamu saƙon, mu juya....”
A wannan karon fushi ne kwance a fuskar matashin.
“Waye shi ?, kira mana shi ya zo ya ƙwata da ƙarfinsa”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga budurwar tana murmushi.