Sashe 40
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uchechi ta fashe da matsanincin kuka tana cin kwalar Raja, dai-dai da isowar su Rhoda da suke binsu a baya ita da Alandi, dom cewa suka yi bari su je gulma, sai kuma Allah ya sa suka ci karo da wannan faɗan.
“Ke sakar shi!...”
Rhoda ta faɗi tana yin kan Uchechi, Raja ya ɗaga mata hannu alamun ta dakata.
“Ni za ka ci amana Raja?, Ni?, Ni Raja?, Idan ka isa Yesu ya kwashe min albarka!, A kan wannan ƙazamar za ka gujeni?...”
Tass!, ka ke ji, Raja ya wanke fuskar Uchechi da mari, hakan yasa ba shiri ta sake shi tana dafe fuskarta setin inda ya mara, hawaye wani na bin wani a kan fuskarta, ta ɗago da idanuwanta ta kalleshi.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba, ganin idanuwan Raja buɗe a kanta, wani abu da za ta iya cewa tsawon zamanta da shi ba ta taɓa gani ba, a ko da yaushe idanuwansa kusan a lumshe suke, amma yau ga su buɗe a kanta, sun yi jajawur, jikinsa har karkarwa yake dan ɓacin rai, mutanen dake wucewa har sun ɗan fara tsayawa tagumi, duk da layin babu mutane sosai.
”Don't you hare what i just said?, I said that she is my wife to be!, You better respect her before i injured you!”
Kuka sosai Uchechi ke yi, haka ta juya da gudu ta shige motar da ta fito daga ciki, ba ɓata lokaci motar ta bar wurin, ba ta taɓa tabbatar da cewa Raja ba ya santa ba sai yau, ta gaji da abun da ya ke mata, don haka za ta sakar masa mara ya yi fitsari, babu ita babu shi, za ta jurewa komai da zai mata amma banda cin zarafi.
Ta haƙura da shi har duniya ta naɗe.
Da sauri Raja yake sauƙe nufashi, ya ɗaga hannunsa ya dafe goshinsa, zuciyarsa na bugawa da sauri, be so ya bayyanawa Rabi ta ji wannan sirrin zuciyar tasa a yau ba, ba yau ya kamata ta sani ba, ba a irin wannan lokacin ya kamata ta sani ba, ko wani kallo za ta masa bayan wannan abun da ya faru?, Oho.
Rhoda dake cikin farin ciki da ɓacin rai a lokaci guda ta dafa kafaɗarsa.
Ta na cikin farin ciki jin yau Raja ya rabu da Uchechi, ya kuma bayyana sirrin zuciyarsa kan abun da yake ji game da Rabi'a, ranta kuma ya ɓaci ne saboda nasa ran ya ɓaci.
A hankali ya sauƙe hannunsa daga kan fuskarsa, sannan ya juya bayansa da sauri, ya kalli Rabi dake a sanƙare a wurin, kamar wata mutum-mutumi, kamar wadda aka manne mata ƙafafunta da glue me ƙarfi, kuma kamar wadda ta cillar da hankalinta a hanya, haka take jin kanta, duniyar ta mata shiru, babu abun da take ji sai muryar Raja cikin faɗin “She is my wife to be!”, anya kuwa tana cikin hayyacinta?, kamar fa ta haukace ma, yau in ba wadda ta yi hauka ba, waye yake jin abunbda babu shi a zahiri, ko kuma dai iskokai ne suka shiga jikin Rajan?, Oho, a'a abun zai fi kyau ace jikinta suka shiga ba nasa ba.
Kanta ta ɗaga ta kalli fuskarsa, jin yana kiran sunanta.
Kallonta kawai yake, ya kasa cewa komai, don ya ma rasa abun da zai faɗa mata, sai kawai ya juya ya tsayar mata da mota, sannan ya kamo hannunta ya sakata a cikin motar, don ya ga kamar bata cikin hayyacinta.
A kan idonsa motar da ya sakata ta bar wurin, sannan ya dafe kansa cikin neman sauƙi, a bisa tsautsayi idonsa ya sauƙa kan wata rumfar me ƙosai, wutar da ya yi arba da ita tana ci a cikin murhunta ta tuno masa ƙiyayyarsa da wuta.
*2008.*
*Gidan Maman Rhoda, Kano...*
*08:30 PM.*
“Zaid miƙo min kwanon can!”
Cewar Maman Rhoda tana nunawa Zaid kwanon dake ɗauke da farfesun kifi, Zaid ya ɗauki kwanon sannan ya miƙa mata, zaune suke a kan carpet ɗin dake falo, Rhoda na daga gefen Zaid, yayin da Maman Rhodan ke facing ɗinsu, girkin ranar da suka yi ne zube a gabansu, yayin da suna shirin cin abincin dare.
“Mom ni kifin nake so kawai”
Cewar Rhoda tana shagwaɓe fuska, Maman Rhoda ta wurga mata harara.
“An ƙi a baki kifin, da ci kike ?, Kifi na Zaid ne kawai”
Zaid ya kunshe dauriyarsa ya na shafa kanta, kasancewar ta jingina da shi, Maman Rhoda ta zubewa Zaid gaba ɗaya kifin, sannan ta bawa Rhoda tata shinkafar babu kifi sai miyar kawai.
Rhoda ta turo baki tana ture abincin, sannan ta miƙe ta bar falon da hawaye.
Nan da nan Zaid ya shiga damuwa, don Allah ya sani ba ya son ɓacin ran 'yar ƙanwar tasa, don haka ya miƙe, hannunsa riƙe da kwanon abincin nasa.
“Zaid ina za ka?”
Ba tare da ya juyo ba ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan yace.
“Abincin zan je mu ci”
“Da ka rabu da ita kawai”
“Ba zan iya cin abincin ba tare da ita ba!”
Ya amsa mata a lokacin da ya ke ƙarsa fita daga cikin falon, Maman Rhoda ta girgiza kanta tana murmushi, soyyayar Zaid da Rhoda sai kallo, ko ka shiga tsakaninsu kai ne za ka ji kunya.
“I'm sorry Cuzie”
Zaid ya faɗi a karo na biyu ya na kallon Rhoda, wadda ta cunkune tana wani kawar da kai, wai ita a dole an ɓata mata rai, tana zaune a bakin gadonta, yayin da Zaid ɗin ke zaune kusa da ita.
Ya na murmushi ya aje kwanon abincin a kan cinyarsa yana buɗe kifin, ya guntsuro tsoka ya haɗa da lomar shinkafar, sannan ya kai mata saitin bakinta, kamar ba za ta karɓa ba, sai kuma ta buɗe bakin ya saka mata.
“Story time!...”
Sai ta juyo tana kallonsa da kyau, ta harɗe ƙafafunta a kan gadon, tana buɗe duka kunnuwanta dan ta ji labarin da zai bata.
Ta san labaran Zaid, babu na yarwa.
“Wani Gayene ya zo Wajen Budurwarsa.
Saiya Kira Yaro Yace mai; Kai je Gidannan Kace Sani Striker Na Kiran Hassana.
Yaro Ya Antaya,yace wai Ana kiran Hassana.
Babanta Yace waye Ke Kiranta?
Yaro Yace Sani Striker.
Sai Babanta Yace; Je Kace Isah Defender Yace Bata Zuwa” (Labaran musha dariya).
Yana ba ta labarin yana kai mata lomar abincin haɗi da kifin, yana kaiwa ƙarshen labarin Rhoda ta tintsire da dariya.
Abincin ya ci gaba da bata ya na bata wasu labaran, sai da ta ga ta kusa cinyewa, sannan ta karbi kwanon, ita ma ta shiga ba shi a baki.
Kamar daga sama suka ji an banko ƙofar falonsu, hakan yasa ba shiri suka miƙe suka bazama zuwa cikin falon.
Abun da suka gani ya bala'in gigita duniyar ko wannensu.
Maman Rhoda ce yashe a ƙasa, Bala ya danne mata kai, ga sauran yaransa su Garuje tsaye a bayansa.
Bala wani me kuɗi ne a unguwar kusa da ta su Maman Rhoda, ya na bawa mutane bashin kuɗi, musamman ma mata, sannan ya kan ƙawarawa mutane da kuɗin ruwa me yawa, idan kika ka sa biyan bashin kuma sai ya nemi ya fanshe a kanki, ga shi da tara yara 'yan daba, kasancewarsa ɗan uwan sanata ya sa ake ɗaga masa ƙafa ya na cin karansa babu babbaka.
Lokacin da Maman Rhoda za ta biyawa Zaid kuɗin makaranta gaba ɗaya har zuwa lokacin da zai gama, kuɗaɗen hannunta ba su da yawa, hakan ya sa ta karɓi bashi a hannun Bala, suka yi da shi kan za ta riƙa biyansa da kaɗan-kaɗan.
Kwana nan kuma sai ya bijiro mata da maganar ta ba shi kanta kawai, ita kuma sai ta nuna ƙin amincewarta, harda marinsa a yammacin jiya.
Shi ne kuma yau ya iyo musu dirar mikiya a wannan daren.
A cikin wannan daren Bala ya yiwa Maman Rhoda fyaɗe a kan idon Zaid da Rhoda, waɗanda ke riƙe a hannun yaransa su Garuje, sai da Zaid ɗin ma ya yi ƙoƙarin kaiwa Balan farmaki amma Garuje ya riƙe shi tare da buga kansa a jikin bango, hakan ya haddasa masa jiri da fashewar goshi.
*
Sosai Maman Rhoda take kuka, Zaid da Rhoda rungume a jikinta, yayin da suke tsaye a harabar police station, bayan da ta kawo ƙara kan zalincin da aka mata, faɗar sunan wanda take ƙara ya sa 'yan sandan korarta har da haɗa mata da duka.
Babban tashin ha kalinta shi ne yanda Rhoda da Zaid ke cikin damuwa, ba za ta iya ɗaukan baƙin ciki irin wannan ba, hakan yasa ta fita wajen police station ɗin, ta siyo fetir da ashana, ta ture Zaid da Rhoda gefe, sannan a kan idon Zaid da Rhoda da kuma sauran jama'ar station ɗin.
Maman Rhoda ta ɗaga jarkar fetir ɗin nan ta tittila a jikinta, sannan ta kunnawa kanta wuta, Rhoda na kuka tana fisge hannunta daga ruƙon da Zaid ya mata, yayin da wannan wutar ke ci a kan idon Zaid, komai na cikin kansa ya taɓu, tsoron wuta ya kama shi, ya zamana ba shi da wata abokiyar gaba kamar wuta.
Don a lokacin suma ya yi, 'yan san dake da imani a wurin ne suka temaka musu, ita kam Maman Rhoda babu abun da ya yi saura a gawarta, ta ƙone ƙurmus, Zaid kuma ya suma, Rhoda kuma sai kuka take, ta rasa inda za ta sa ranta, ita a tunaninta shi mq Zaid ɗin mutuwa ya yi.
Kwanan Zaid ɗaya a aibiti kafin ya farfaɗo, kuma yabna farfaɗowar babu wanda ya samu kusa da shi sai Rhoda, haka ya ƙanƙameta suka rera kuka me isarsu, kafin ya ɗauketa suka dawo gidansu.
Haka suka ci gaba da rayuwa, sai dai ba kamar yanda suka saba a da ba, kamar yanda Maman Rhoda ta bar musu kuɗinta da kayan ƙosai da kokonta, haka suka ci gaba da yin sana'ar, kuma a ɓangare guda suna zuwa makaranta, Zaid ne ya ci gaba da riƙe su har zuwa lokacin da shi ya kammala makaranta.
Duk da Rhoda ce ke soya ƙosan, dan shi ya koma maƙiyin ganin wuta.
Amma kuma ba ya bafinta ita kaɗai, duk inda za ka ganta to shi ma za ka ganshi.