← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 80

Sashe 46

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya bar Brickhall kai tsaye gidan Annan ya nufo.

“Na sani Anna.

Na san ba za ki aikasu su yi wa matata haka ba, amma ina son na sanar da ke da ki jawa kowaccensu kunne, kan kada su ƙara taka ƙafarsu cikin gidana, jiya ma girmanki da darajarki suka ci, ba dan haka ba Wallahi ba zan barsu ba”
Anna ta share hawaye.

“Ba komai Aliyu, tashi ka tafi aikinka, zuwa yanzu na san ka makara, ka je kawai, ni na san matakin da zan ɗauka!”
Ya karkatar da kansa gefe.

“Ba za ki dena kukan ba?”
Anna ta ɗan yi murmushi tana share wani hawayen.

“Na dena, ka je kawai”
“Shikenan”
Ya faɗi ya na miƙewa, har ya fice Anna na kallonsa, ta san abun da za ta yi.

Don ta zubawa su Karima ido suna ta haukansu ba wai don ba za ta iya taka musu birki ba ne, ba ta san cewa haukar tasu ta ƙamari ba, amma ba komai, Allah ya kaimu gobe, za ta yinwa tufkar hanci.
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.*
Da gudu wata nurse ta fito daga wani ɗaki da aka kwantar da wata mara lafiya da ta baƙunci asibitin nasu a safiyar yau, hannunta na dama ɗore a bakinta, a ƙoƙarinta na tare kukan dake son cin ƙarfinta, ta jingina da jikin bango tana kallon ƙofar ɗakin, a hankali ta zame zuwa ƙasa, kukan da take ta yunƙurin riƙewa ya fito da ƙarfinsa.

Tun da uwarta ta kawota duniya ba ta taɓa ganin tashin hankali irin wanda ta gani yau ba, ta na jin labarin fyaɗe, amma ba ta taɓa ganin wanda aka yi wa fyaɗe ba sai yau, an ce mata idan ta fara aiki sai ta gamu da abun da zai sa ta kuka, a wancan lokacin da aka faɗa mata dariya ta yi, don ita ba ta hango yiyuwar hakan ba, sai a yau ta yarda da abun da aka faɗa mata, kuka take sosai har ta na dafe ƙirjinta.

Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, likitan da suka shiga tare da shi ya fito ya na sharar ƙwalla, kafin ya kalli nurse ɗin, shi kansa da ya kwashi tsawon shekaru ya na aikin bai taɓa ganin abu makamancin wanda ya gani yau ba, bare ita da ta ke sabuwa a aikin.

“Ke Sakina! lafiyar ki kuwa?”
Wata ƙawarta ta tamabaya, a sanda ta biyo corridorn ta ga ƙawar tata zaune a ƙasa tana kuka kamar wadda aka yi wa mutuwa, juyawa ta yi ta kalli likitan, shi ma duk jikinsa ya yi sanyi, kansa a ƙasa kamar da aka ce shi ne ya aikata fyaɗen.

Hannunta ta kai ta kamo ƙawar tata tana miƙarta, tare da share mata hawaye, amma Sakinan sai ta ƙwace fuskarta ta na komawa gefe.

“Dan Allah Kausar ki bar ni na yi kuka.

Bar ni na koka da abin da na gani.

Kausar wasu mazan ba su da adalci, ba su da tausayi!”
Ta ɗaga hannunta tana nuna mata ƙofar ɗakin.

“Shi ga ki ga abun da suka yi wa wata yarinya.

A shekaru dai na san yarinyar ba za ta wuce 19 ba, amma ki je ki duba ki ga yanda suka mata fyaɗe cike da rashin imani, mutum biyar Kausar, mutum biyar ko sama da haka ne suka haike mata!.Kuma ba su barta da wannan tambon ba, sai da suka ƙara mata da wasu raunuka a jikinta, gefen fuskarta da kuma kanta duk sun fasa mata, yanzu haka yarinyar ta shiga doguwar suma!”
Ita kanta Kausar ɗin sai da gabanta ya buga da mugun ƙarfi, don za ta iya cewa wannan ɗin sabo abu ne da ya shigo asibitin nasu.

“Me ya sa Kausar?.

Me ya sa mu ba mu da 'yanci?, Kowa sai ya taka mu ya wuce yanda yake so.

Me ya sa wasu mazan ba sa ganin mata da kimi?.

Me yasa?...

Sai zuwa yaushe ne za mu tsira?, sai zuwa yaushe?!”.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
RAJA POV.

Zaune yake a ɗakinsa, ya yi tagumi da duka hannayensa biyu, abun duniya ya bi ya isheshi, musamman yau da ya ga Rabi'a ba ta zo ba, abun ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, shi fa burinsa shi ne ya samu ya ganta don ya mata bayani, zai gabatar mata da kansa a ainahin yanda yake, zai faɗa mata gaskiyar komai a kansa, amma yau haka ya ƙaraci tsayuwarsa a ƙofar gate ɗin ba tare da ya ga gilmawarta ba.

Ƙofar ɗakin aka buɗe, sannan Rhoda ta shigo hannunta tiƙe da wayarsa.

Kansa kawai ya ɗaga ya kalleta ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama.

“Alhaji Bala ne yake ta waya.

Yace ya na buƙatar kayansa cikin gaggawa”
“Mtswwww!”
Ya ja tsakin ya na kawar da kansa, shi ba ta Alhaji Bala yake ba, don matsalar Alhaji Bala sifili ce a wurinsa, babba kuma shirgegiyar matsla gareshi ita ce RABI'A!.

Ganin hakan ya sa Rhoda zama kusa da shi, sannan ta dafa ƙafaɗarsa.

“Na san halin damuwa da kake ciki, amma ya kamata ace ka sameta ku yi magana, ka faɗa mata gaskiya, wata ƙila ta saurare ka”
Fuskarsa ya shafa da hannayensa.

“Yau ba ta zo ba fa” Ya faɗi cikin wata murya me sanyi.

“Wata ƙila ta zo, ta ɓoye ne kawai dan kada ka ganta”
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleta, ƙwarai, hakan za ta iya kasancewa, amma me ya sa shi bai yi tunanin hakan ba?.

“Ki na ga zan iya shiga cikin makarantar?”
“Me zai hana?”
Sai ya gyaɗa kansa, ya na hangowa kansa mafita a cikin kalaman Rhoda.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*07:00 PM.*
MISHAL POV.

Tsaye take a kitchen tana juya stew ɗin da take dafawa, duk da yau girkin a makare take yinsa, saboda makarar da ta yi wurin dawowa gida.

Ba tare da ta san lokacin da ya shigo ba, ta ji muryarsa a bayanta.

“Ana san magana da ke!”
Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya na tsaye daga bakin ƙofa, kallonsa da ta yi a yanzu shi ya tuna mata da shirman da ta yi masa yau da safe a school ɗinsu, don haka ta yi ta nuna shi a wurin 'yan makarantarsu tana faɗin ga mijinta nan.

“Waye yake san maganar da ni”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, dai-dai da lokacin da Mishal ta ɗaga tata kafaɗar ta dama, don kawai neman tsokana, ita ta rasa me yake ji a wannan ɗaga kafaɗar, mutum ya yi ta wani ɗaga kafaɗa?, shi ba tsuntsun ba, kuma ta lura da wancan ɗan uwan nasa ma ya na ɗaga kafaɗar.

Cike da mamaki Kuliya yake kallon Mishal, wato shi take kwaikwayo?, don ta na ga ya na ɗaga kafaɗa shi ne ita ma za ta yi?.

Kuma ita ma ta lura da kamar fushi yake shirin yi, don haka ta yi saurin cewa.

“Waye yake son maganar da ni?”
Maganar tata ta tuna masa da batun da ya zo mata, sai ya share batun ɗaga kafaɗa yace.

“Yayarki Nimra”
Sai ta juya ta kashe wutar gas ɗin, sannan ta juyo ta kalle shi.

“Wayar tana ina ?”
Da hannunsa ya nuna mata falo, don shi gajiya yake da wannan surutan, ita ma kuma ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta raɓa shi ta fice tana dariya ƙasa-ƙasa.

Ƙamshin da stew ɗin ke yi ya ci gaba da shiga hancin Kuliya, don haka ya cewa kansa de yau ya kamata ace ya ɗanɗana abincin nata, sai ya shiga bubbuɗa pots ɗin da ta yi girkin da su, farar shinkafa ce sai wannan stew ɗin dake ta tashin ƙamshi, ga kuma coslow a gefe.

Tsakani da Allah abincin ya burgeshi kamar sauran abincinta, ga kuma yunwar da yake ji, saboda rabonsa da abinci tun safe, ya kai hannu ya ɗauki plate, ya zuba abincin iya yanda ya san zai iya cinyewa.

Sannan ya fara ci, bai taɓa zaton ƙaramar yarinya kamar Mishal za ta iya yin girki haka ba, a da duk ɗaukan zancen girkin nata yake a matsayin shirme, amma yanzu da ya ɗan-ɗana sai ya ji kamar irin wannan abincin yake buƙata a kullum domin ci.

Mishal na fita ta hangi wayar tasa aje a kan coffe table, da sauri ta ƙarasa wurin ta ɗauki wayar, gaisawa suka yi, kafin Nimran ta tambayeta yanayin zaman nasu, kana ta ƙara mata da nasiha, ita kuma Mishal ɗin babu abun da ta tambayeta sama da Daala, don ita kaɗai ta yi kewa.

Sai da suka gama wayar, sannan ta tashi ta nufi kitchen ɗin, zuciyarta ɗaya ta tura ƙofar kitchen ɗin, kuma abu na farko da idonta ya fara gane mata shi ne.

Kuliya tsaye a kusa da stove, hannunsa na hagu riƙe da plate, wanda yake cike da shinkafa da miyar da ta dafa, harda coslow a gefe, hannunsa na dama kuma riƙe da cokali, ya kai shi setin bakinsa ya na shirin kai loma.

Ba ƙaramar dariya ya bata ba, mutumin da a kullum yake gudun cin abincinta, yau shi ne ta kama ya na cin abincinta a ɓoye, amma sai ta riƙe dariyar, ba tare da ta ce masa komai ba, ta tsaya a kusa da shi, ta sauƙe tukunyar stew ɗin daga kan stove.

Kuliya ya ci gaba da binta da kallo, ya zaci za ta ce wani abun, amma sai ya ji ta yi shiru, har ta gama kwashe abincin duka, ta zubawa Ayra, sannan ta ɗauki nata ta zauna a kan kujerar island.

Ganin ya kasa ƙarasa cinye abincin nasa ya sa Mishal faɗin.

“Ka zauna ka ƙarasa ci”
Kuliya ya ɗan sosa ƙeyarsa, sannan ido ba kunya ya ƙaraso ya zauna a tsallakenta ya na ci gaba da cin abincin.
Chapter 46 · 0% Book details