← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 80

Sashe 29

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma masu kayan suna da matuƙar haɗari, bai ɗauka cewar su Rajan za su iya ƙwato kayan cikin sauƙi kamar haka ba, wannan aikin da suka masa yasa ya ƙara basu matsayi me girma a cikin zuciyarsa, tare da ɗaura niyyar ɗorasu a kan sauran harkokinsa, zai buɗe musu cikinsa, ya faɗa musu sauran ayyukansa da ya saba yi, don su taya shi ya tara kuɗin da yake buƙata, wajen yin campaign ɗin takararsa.

“Da kyau Zaki, aikinki na kyau!

Na ji daɗin wannan aikin, Dan haka zan ƙara baku wani aikin!”
Kusan a tare Raja da Rhoda suka kalli juna, a cikin idon Raja roda ta hango 'Ba na faɗa miki ba?', ita ma ta idon nata ta mayar masa da 'Na gani'.

Sai kuma suka juya dubansu kan Alhaji Bala dake ta washe baki.

Raja ya ɗaga kafaɗa yana faɗin.

“Wani aiki ne wannan ?”
“Safarar makamai!”
RABI'A POV.

Zaune suke ita da Zara a tsakar gida, yayin da Habiba da Mama ke ɗaki suna ƙus-ƙus ɗin da suka san na miye, wai yau suke faɗin Maman za ta yi tafiyar, kuma tun safe suke ta shirye-shirye.

Anti Saratu kuma na banɗaki tana wanka, Fatima da Mahmud kuma basa ma gidan.

Fitowar Mama da Habiban ce tasa su dakatawa da hirar da suke, a tare suka kallesu.

“Allah ya tsare Mamana, Allah kare min ke gabanki da bayanki, Allah ya kauda idon maƙiya a kanki!...”
Haka Habiba ke ta faɗi har Maman ta sa kai za ta fita.

A lokacin Saratu ta fito daga banɗaki, kallonsa kawai ta yi, ta kama hanyar ɗaki cike da takaici.

Daga Mama har Habiba bin bayanta suka yi da harara.

Har waje Habiba ta bi Mama tana ta mata addu'a.

Kuma kafin ta dawo ne Anti Saratu dake ɗaki ta ƙwallawa Rabi kira.

“Gani Anti Saratu!...”
Rabin ta faɗi a sanda ta shiga ɗakin , ta iske Anti Saratu zaune a bakin gado tana shafa mai.

“Awara za ki siyomin”
“To kawo...

Ki ban ɗari biyar a cikin kuɗina sai na ƙaro mana da kifi”
“To”
Anti Saratu ta amsa tana miƙewa, tare da nufar jakarta inda take aje kuɗi, kuɗin ta shiga lalubowa, kuma kafin ta gama lalubo kuɗin, wani yaro ya rangaɗa sallama daga bakin ƙofa, Zara dake tsakar gida ce ta amsa masa, abinda ya fito daga bakin yaron ne ya sanya duniyar Anti Saratu da ta Rabi girgiza, don abu ne da ba su taɓa zato na, wani abu da kaf tsawon zaman Rabi a gidan ba ta taɓa gani ko jinsa ba.

“Wai saratu ta zo in ji Fu'ad!”
Abun kamar mafarki, abun kamar wasa, wai yau wani ne ke sallama da Anti Saratu, wani abu sabo, wani abu da bai taɓa faruwa a tarihinta ba, ko da wasa ba ta taɓa yin saurayi ba, tun tasowarta babu wanda ya taɓa cewa yana sonta da soyyaya.

Ko dan Allah maji roƙon bayinsa ne, kuma ma an ce wai haƙuri me tadda rabo.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.

Zaune take a bakin gadon da a yanzu yake amsa sunan nata.

Ita fa har yanzu ba ta ganewa komai, ta kasa ganewa halin da take ciki, gani take kamar mafarki ne, kamar ba gaskiya ba ne, babu abun da ta yi kewa a gidansu sai Daala da kuma su Mama Ladi.

A karo na barkatai ta ƙara kallon ɗakin, sannan ta ja guntun tsaki a ƙasan numfashinta, miƙewa tsaye ta yi a hankali, ita ba ta saba zaman ɗaki ba, dan haka ba za ta iya zama gu ɗaya ba.

Shi ma wanda ke amsa suna mijin nata bayan ya kawota gidan ya ajiye , ba ta ƙara ganinsa ba, ga shi har kusan ƙarfe tara na dare.

A ƙofar ɗakin nata ta tsaya, tana kallon corridorn dake ɗauke da ƙofofo uku, wanda take da tabbacin ɗakuna ne.

Ba ta damu da buɗe ko da ƙofa ɗaya ba, ta ci gaba da takawa zuwa cikin falon, kasancewar gidan bungalow ne.

A falo ta ci birki, ta shiga kalle-kalle, har idonta ya sauƙa a kan wata farar kyakkyawar mage, kwance a kan sofa.

Ba ta san sanda murmushi ya suɓuce mata.

Da sauri ta yi wurin magen ta na ɗaukarta, hakan ya sa magen ta farka, sosa jikin magen ta shiga yi ta na mata wasa kamar wadda ta samu ƙarimin yaro.

Jin ana buɗe ƙofar shigowa falon ya sa ta ɗora magen a kanta ta kalli ƙofar, dai-dai da shigowar Kuliya, sanye cikin baƙaƙen ƙananun kaya.

Kamar yanda take kallonsa haka shi ma yake kallonta.

Sanye take cikin wani short trouser, wanda bai rufe gwiwarta ba, sai wata half vase da bata rufe duka cikinta ba, ta ɗora falmaran ɗin wandon a saman half vase ɗin, wadda take da ɗan tsa yi, ƙafafunta sanye cikin wasu pink fluffy sliders, gashin kanta fake cikin ponytail.

Zuciyar Kuliya ta yi tsalle daga ma'ajiyarta, wani abu me kama da garwashi ya shiga bi ta kan zuciyarsa, yanda ta kafe shi da olive green eyes ɗinta kaɗai ya isa ya sa shi a uku.

Da ƙyar ya haɗiye wata iska, sannan ya fara takowa zuwa cikin falon.

Mishal ba ta san wa ta kunya ba, hakan ya sa ba ta ji komai ba dan ya ganta a cikin irin wannan shigar.

“Wannan kuliyar, take ce?”
Muryarta ta fito a sake, kamar ta san shi, kamar ta saba da shi, haka ta masa maganar tana shafa bayan kuliyar.

Ba tare da ya kalleta ba, ya aje ledar hannunsa a kan coffe table, ya ɗaga kafaɗarsa sannan ya ce.

“Ayra”
Mishal ta ƙyal-ƙyale da dariya, dan ta fahimci cewa sunan Kuliyar ne Ayran.

Ɗagowa ya yi ya kalleta, wai ita ba ta san rashin sabo ba ne?, ji yanda ta ke, kamar wanda suka saba tsawon shekaru.

“Wato saboda kada a kirata da irin suna ka, shi ne ka yiwa Ayra star takwara, tab ɗi jam, Ayra star go sue you oo!”
Kallonta ya ci gaba da yi, yanda take maganar a sake, da yanda take shafa jikin kuliyar, da kuma yanda take abu cike da yarinta ne ke nuna masa ƙarancin shekarunta.

Leda ɗaya ya miƙo mata, cikin ledojin da ya shigo da su.

“Ki ci!”
Mishal ta ɗan kalli ledar, wai shi ba ya doguwar magana ne ?.

Ba tare da tace masa komai ba, ta karɓi ledar, sannan ta ɗora Ayran a kanta, tana zama a kan sofa, tare da yunƙurin buɗe ledar.

Gadan-gadan Kuliya ya ga tana shirin fara cin abicin da hannunta ba tare da ta wanke hannun nata ba.

Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar faɗin.

“You have to wash your hands first”
Sai ta dakata da shirin kai lomar da take, ta ɗago ta kalleshi, ya na tsaye a yanda yake, sai kuma ta aje take away ɗin, sannan ta sauƙe Ayran dake kanta.

Ta nufi ɗakinta dan ta wanke hannun nata.

Kuliya ya bi bayanta da kallo yana mamakin irin halin da yarinyar ke ciki, Abubakar ya sha ba shi labarin irin halayenta, bai taɓa yarda ba sai yau.

Lalle akwai aiki ja a gabansa, dole ne yasan yanda zai seta yarinyar nan, saboda sam ba ta san ma mecece rayuwa ba, rayuwarta take kanta tsaye.
*Washe gari...*
*07:30 AM.*
Kuliya na tsaye a falo yana fitar da abincin da ya siyo daga leda, wanda ya siyo a restaurant ɗin da ya saba siyan abinci.

Jin motsin buɗe ƙofa a corridor ne ya sa ya juya ya kalli ƙofar, kamar yanda ya sa ni, ita ɗin ce ta fito, sanye cikin kayan da ya fara ganinta da su, wato uniform.

Backpack ɗinta riƙe a hannunsa na dama, yayinda suit ɗin uniform ɗin ke riƙe a hannunta na hagu.

Ba tare da ta tambayashi ba har ta riga da ta yankewa kanta hukuncin cewa za ta je makaranta.

Da alama ma dai ita ba ta san hakkin aure ba, ba zai yi wa kansa ƙarya ba idan yace ba ta ma san miye auren ba, ba ta san cewa yanzu tana ƙarƙashin wani ba ne.

Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama a hankali, kana ya Juya, ya ci gaba da fitar da abincin.

Mishal ta aje backpack ɗinta a kan sofa, sannan ta ɗora suit ɗin nata a kan jakar.

Ta ɗan kalli inda yake, wai shi ba shi da aiki sai saka baƙaƙen kaya, ta faɗi a ranta tana kallon baƙar suit ɗin dake jikinsa, amma kuma ai kwana kin da take ganinsa a tsallaken makarantarsu ba baƙaƙen kaya ba ne.

Sai kuma ta taɓe bakinta kaɗan tana ƙarasawa kusa da shi.

“Ina kwana”
Ta gaida shi tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya amsa mata da:
“Ummm”
Wai shi ba ya magana ne?, sai kuma ta kawat da komai, ta yi masa tambayar dake ranta tun jiya da ta gama cin abincin da ya kawo mata.

“Babu kayan girki a gidan nan ne ?”
A hankali Kuliya ya juyo ya kalleta, kayan girki?, to me za ta yi da su?, ita nan ɗin wai har wani girki ta iya?, inaaa, shiriritar ta ce kawai, dan a haka idan ka kalleta kai ka ce babbace wadda take da tunani, sai ka yi magana da ita za ka ga tsantsar yarinta.

Ba tare da ya amsata ba ya ci gaba da abinda yake.

“Magana fa nake...”
Ya ƙi ko kallonta.

“To ni dai ba na iya cin abincin waje, ina san na yi girki da kaina!”
Still be kalleta ba har ya gama fitar da kayan, ya ware mata wasu robobi biyu, sannan ya tura mata.

“Ki ci ɗaya yanzu, and you can take the other one to school”
“Yanzu fa na ce maka ba na iya jurewa cin abincin waje...”
Ba tare da ya ko kulata ba ya ɗauki nasa, sannan ya yi corridor.
*
Tafe suke a motarsa, yayin da Kuliya ke tuƙa motar Sharon da ta ba ahi aro a kwanakin, dan har yanzu bai samu damar siyan wata motar ba, tasa kuwa da ma bai ƙara bi ta kanta ba.

Da yake yasan makarantar tasu, kansa tsaye can ya dosa, har cikin makatarantar ya shiga, sannan ya yi parking a harabar makarantar.
Chapter 29 · 0% Book details