← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 80

Sashe 34

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma a lokacin ne na samu cikinku!...”_
Kalaman mahaifiyarsu kenan garesu, a ranar da Zaid ya tambayeta labarin mahafinsu, kuma tun bayan lokacin ya tsani wannan kalmar ta fyaɗe, a duk sanda zai jita, sai ya ji kamar an watsa masa maɗaci a kan zuciyarsa, ko da wasa ba ya son sauraron kalmar.

Don shi ko aiki aka ba shi wanda ya danganci fyaɗe hukuncin da yakewa me laifin ma da ban ne.

A hankali ya gyaɗa kansa ya ba buɗe file ɗin.
*
Sharon, Kamis, Sani, Mubarak da Symon su ne zaune kan kujeru, yayin da suka kasa kunne suna sauraronsa.

“...Gaba ɗaya akwai tarin bayanai game da kisan, akwai hujjojin da 'yan sanda suka samo a wurin da aka yi kisan.

Na farko, wuƙar da aka yi amfani da ita wurin kisan.

Wuƙar na ɗauke da jinin victim ɗin, sannan akwai shatin yatsun me lefin a jiki.

Hujja ta biyu kuma ita ce; autopsy report, bayanan da likitan da ya bincika gawar ya bayar sune; farko sai da aka mata...”
Kamar kullum, yau ma sai da ya tauna maganar kafin ya faɗeta, kallonsu ya yi gaba ɗaya, amma su ba shi suke kallo ba, ko wanne a cikinsu da takardar da yake dubawa, wadda ta ƙunshi bayanan case ɗin, hakan ya ba shi damar yin gyaran murya, ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.

“...Fyaɗe, kafin ya kasheta, kamar yanda na faɗa muku tun farko, ya yi amfani da wuƙa ne wurin yanka wuyanta, sannan kuma rahoton ya bayyana cewa makashin ba hagume ne, ma'ana yana amfani da hannun hagu!”
“Amma ni sai nake ganin...

Kamar waɗanan hujjojjin ba su isa susa mu gano wanda ake zargi ba, muna buƙatar ƙarin wasu hujjojjin”
Cewar Sani, bayan da Kuliyan ya gam zayyano musu kaf bayanan cikin file ɗin.

A hankali Kuliya ya gyaɗa kansa ya na kurɓar coffen dake hannunsa.

“Kai ma ka ce wani abu”
“So what are we gonna do next?”
Sharon ta tambaya.

“Zan yi magan da Ram, sannan zan yi magan da ɗansandan da ya kula da case ɗin kafin ya zo nan, na san za'a iya samun wasu bayanan”
Kuliya ya bata amsa.

“Amma ya kamata mu yi magana da iyayen yarinyar” Cewar Kamis yana aje takardar hannunsa.

“Ƙwarai wannan ma babbar makamace, wata ƙila za su iya bamu wani hint”
“But babu wani wanda zargi ya hau kansa?, i mean ko da ɗaya daga cikin mutanen gidansu ita yarinyar ne?”
Cewar Symon.

“A bayanan cikin file ɗin dai babu, amma idan muka nitsa cikin binciken ba za mu rasa ba”
Kuliya ya amsa masa yana sosa kansa.

“Gaskiya makashin nan ba shi da imani, kalli yanda aka yanka wuyan yarinyar, kuma a profile ɗin yarinyar na ga ba ta wuci 18 years ba” Cewar Mubarak, sanda yake kallon hotunan da aka wa gawar.

Sai da Kuliya ya ɗan yi jim, tunowa da ita da ya yi, ita ɗin da a yanzu zai iya kira da matarsa, ita ɗin da zai iya cewa zuciyarsa ta raurawa a kanta, ita ɗin da ta zama sanadiyyar haɗuwarsa da wata wanda yake ganin kamar ta jiɓanci rayuwarsa ta baya.

Haka dai suka yi ta tattaunawa a kan case ɗin, kafin kowa ya tashi ya fita, ya rage daga Kuliya sai Sharon, wadda suke ƙara tattaunawa kan yanda za su ɓullowa batun.

“Ya kwanan amarya?”
Sharon ɗin ta faɗi tana harhaɗa kan papers ɗin da suka barbaza, sai da Kuliya ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da.

“Tana lafiya”
Sharon ta ɗan yi murmushi tana rufe file ɗin dabta gama haɗawa.

“Na san yarinyar, ba ta da wasu shekaru masu yawa, na san ba lalle ma a ce tasan menene ɗaukar nauyin miji da na gida ba...

Amma idan ka daure, ka yi haƙuri komai zai zo maka da sauƙi, ka yi ta ɗorata a kan hanya, za ta dawo dai-dai. hmmm?”
Sai ya aje mug ɗin hannunsa ya na gyaɗa mata kai, kaf abokansa ita ce mutum ta biyu da yake iya sauraron maganarta.

“Thanks for the advice”
“Not at all”
Ta faɗi da wani guntun murmushi a kan fuskarta, ta haɗa abin da za ta haɗa ta fice daga office ɗin.

Kuliya ya shafo kansa yana fitar da iska daga bakisa.

Da alama wannan assignment ɗin zafin kai kawai zai ƙara masa, bayan wani ɗumin da kan nasa ya ɗauka.
*Unguwar Madalla, Suleja, Niger state*
RABI'A POV.

“To yanzu Rabi gurin wa zan tura su?”
Cewar Antu Saratu, bayan da saurayinta Fu'ad ya zo zance ya shaida mata da ya kamata ta sa masa ranar da zai turo magabatansa.

Yayin da suke zaune ne a ɗakinsu, kan katifar Anti Saratun.

Rabi ta ɗan yi shiru tana nazari, can kuma tace.

“To me zai hana ki turasu wurin kawu Habu, ki ga shi ne kawai wanda za'a iya nemar aurenki a wurinsa”
“Kuma fa haka ne, kai amma na ji daɗin shawarar nan taki Rabi...

Sam ni tunanin hakan bai zo cikin raina ba”
Rabi ta ɗan yi murmushi.

Ta na so ta ga an yi wannan auren, ko ita ba ta fita daga rayuwar ƙuncin gidansu ba, wata ƙila ita anti saratun za ta fita daga rayuwar ƙuncin gudan.

Kusan sati biyu kenan da tafiyar Mama, duk wanda ya tambayesu ina Mama sai Habiba ta yi wuff ta ce wai ta tafi ziyara.

Hira suka ɗan yi kafin Rabi'an ta fara jin bacci, hakan yasa ta yiwa Anti Saratu sallama ta koma kan tata katifar ta shimfiɗe, sai dai kafin ta gama addu'ar baccin da ta saba yi, waɗanan fuskokin guda biyu masu kama da tata da kuma ta Umma suka gifta ta cikin idonta.

Hakan yasa ta buɗe idon nata, tana shafa addu'ar da ta ida, ba ta san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce mata ba, tunawa da ta yi da shi, wannan innocent voice ɗin, waɗanan drunken eyes ɗin, wannan nitsataiyar tafiyar da ma yanda yake ɗaga kafaɗarsa bayan shuɗewar duk wani ƙaramin lokaci.

Wai me kike shirin yi ne Rabi?, kar fa ki zarme da yawa, don ya na kama da ke ya sa kar ya sa ki dauka cewar shi sa'an ki ne!, Raj sam ba sa'an ki ba ne, kamar da kuke ba ita za ta sa ku dace ba, dacewa da ban kamanni ma da ban!.

Yayan da kika samu shi ne dai-dai ke, kar kuma ki shiga shirin ɓallowa kanki ruwa!.

Wani yanki na zuciyarta ya ba ta wannan shawarar, kuma ta yarda da shi ɗari bisa ɗari, don da alama zuciyar tata na shirin sakata ɗaukar dala ba gammo, don kuwa sam babu haɗin zuma da maɗaci, Raja ba sa'anta ba ne ita ma ta sani.

Saboda haka duk wani abu da za ta bari ya shiga tsakaninsu yaudarar kanta za ta yi.

RAJA POV.

Cike da mamaki suke kallon ire-iren muggan makaman da mutumin da Alhaji Bala ya haɗusu da shi ya turo musu wai su zaɓi wanda suke so, daga Raja har Rhoda babu wanda bai saba riƙe makami ba, amma kalar waɗanan makaman ko jami'an tsaron Nigeria ba su da irinsu.

“Zaid this thing is getting worst!”
Rhoda ta faɗi, mamaki kwance a kan fuskarta.

Raja be iya amsa mata ba, kansa kawai yake girgiza wa.

Mamakin abun da yake gani ya hana shi cewa komai.

“Raja we have to do something about this”
Yanzunma kansa ya girgiza mata yana ɗaga kafaɗa, shi ji yake kamar an sakawa bak8nsa wani shirgegen kwaɗo an kulle.

Lalle Alhaji Bala ya wuce yanda suke tsammani, abun nasa ma ya wuce hankali, ko da wasa ba su taɓa tunanin cewa ya kai haka ƙarfi a harkar tasa ba.

Kallon hotunan kawai yake yana ƙarawa, ya rasa wanne daga cikin hotunan zai nazarta.

Ture ko wani tunani ya yi, dan yasan zuwa yanzu lokacin tashinsu ya kusa, hakan ta sa ya rufe laptop ɗin, dan ba ya so ko da wasa ya yi missing ganinta.

Rhoda ta bi shi da kallo a sanda ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa.

“Wait for me Abeg”
Rhodan ta faɗi tana miƙewa, tare da bin bayansa, dan so take ta je ta yi neman tsokanar da ta saba.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja.*
MISHAL POV.

A karo na barkatai, Rabi'a ta kuma ɗaga jerseyn da Mishal ta kawo mata, ta juya rigar a hannunta ya fi sau abun da ya fi.

Yau gaba ɗaya ba su haɗu ba sai yanzu, kasancewar yau ita Rabin har ɓangaren hostel ɗin mata ta je yin shara, kasantuwar makarantar a haɗe take da boding.

Wadda ta saba yi ma 'yan hostel ɗin shara ce ba ta nan, hakan yasa aka turata ta je ta yi.

Kuma ta na gama sharar hostel ɗin ta ɗora da ta makarantar, hakan ta sa ba su haɗu ba sai yanzu da aka tashi, ba wai iyaka jerseyn ta kawo mata ba, akwai wani baƙin baby hijab, da leggins, da kuma short ɗin jersyn, sai wani farin canvas.

Mishal ɗin ta faɗawa Rabi'a cewa Akinta ne ya siya mata mata kayan saboda da farko cewa ta yi ɓangaren ball za ta zaɓa a sport, amma bayan ta ga cewa ana koyar da kungu fu a makarantar sai ta sauya ra'ayi, hakan yasa ta aje kayan, yanzu kuma da ta ji cewar yayarta na son buga ball sai ta kawo mata su.

“Ki na ji ko?, gobe ki saka su, ina san na ga irin wasan da kike”
Cewar Mishal tana zuge zip ɗin jakarta, Rabi ta kalleta da mamaki.

“Na sa kuma?, da wa zan buga ball ɗin?”
Mishal ta yi dariya tana saɓa backpack ɗinta a baya.

“Akwai matan da suke buga ball a makarantar nan...

Da su nake so ku buga”
Ido waje Rabi take duban Mishal.

“Ni zan buga wasa da su?”
Ta tambaya tana hango waɗanan marasa mutuncin 'yan matan dake yawan buga ball a filin.

“Seesee kin iya ball ko ba ki iya ba?”
Mishal ta tambaya.

Rabi'a ta sunkuyar da kanta tana faɗin.
Chapter 34 · 0% Book details