Sashe 73
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kitchen ya nufa, dan ya san ba za ta wuce can ba.
Damm, zuciyarsa ta harba bindiga, lokacin da ya saka ƙafarsa a cikin kitchen ɗin, abu na farko da ya fara arba da shi shi ne, Wutar gas a kunne tana ci.
Irin waɗanan dalilan ya sa baya san shiga kitchen, ko da magana yake san yi da Rhoda idan har tana kitchen sai de ya haƙura.
Ba shiri ya ji kansa na juyawa, duniyar ta fara masa duhu, numfashinsa ya shiga kokawar ɗaukewa.
Rabi dake wanke nama a sink ta juyo da sauri jin fitar wani kalar numfashi.
“Ga ruwa”
Cewar Rabi tana miƙa masa ruwa a cikin wani glass cup, Zaid da ke zaune kan kujera a falo ya ɗago da kansa ya kalleta.
Kafaɗarsa ya daga ya na miƙa hannunsa tare da karɓar glass ɗin.
Rabi ta zauna a gefensa tana shafa kafaɗarsa a sanda yake shan ruwan.
Ita ta karɓi cup ɗin ta aje, bayan da ya kammala shan ruwan.
Gefen fuskarsa take kallo cike da damuwa.
Har zuwa lokacin tana shafa kafaɗarsa a hankali.
“Na zubo maka abinci?”
Zaid da ya cilla duniyar tunani ya girgiza mata kai, ya na jingina da bayan kujera, hakan ya sa Rabi ta ɗauke hannunta daga bayansa, ta dawo da shi ƙirjinsa tana masa tausa.
Ganin har zuwa lokacin be dawo dai-dai ba ya sa tace.
“Me yake damunka wai?”
Kallon fuskarta ya yi na wasu 'yan sakkani, sai kuma ya kama hannunta dake kan ƙirjinsa, ya kwantar da ita akan ƙirjin nasa, ta yanda har tana iya jiyo sautin bugun zuciyarsa dake shirin ɓalla allon ƙirjinsa ta fito.
“Na san komai a kanki, ya kamata a ce kema kin san komai akaina!...”
Tun kafin ya kai ƙarshen labarin nasa Rabi ta fara hawaye, tunawa da ta yi cewar ɗan uwansa da yake so, kuma yake tunani ya mace yana raye.
“Zaid!”
Ta kira sunansa tana sharar ƙwalla.
Kanta Zaid ya shafa yana amsawa.
“Aliyu ya na raye!”
Wani irin bugu da ta ji zuciyarsa ta yi ya sa ta yi saurin tashi daga jikinsa, dan a tunaninta ko zuciyar tasa ta buga ne gaba ɗaya.
Amma kuma sai taga har lokacin yana da rai, sai de kuma kamar ya mace, dan kallonta kawai yake, amma jikinsa a ƙame.
Wai me take faɗi ne?, Aliyu yana raye?, Aliyunsa bai mutu ba?.
A'a, wata ƙila dai kunnensa ne ke haihuwa, ko kuma Rabi'a tana faɗin hakkan ne dan ta kwantar masa da hankali.
Aliyu na raye?.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*26*
~~~
*You ware using your ear to hear, and i am using my heart...*
***
*No.181, Guzape, Abuja...*
*10:11pm*
KULIYA POV.
_🎶I lost my way, somewhere in another galaxy_
_Too much to take, these memories end in tragedy_
_And all of these pleces , all of these faces, I didn't wanna let you down_
_And all these mistakes of mine I can't replace it, i gotta move on somehow 🎶..._
Waƙar dake tashi kenan a falon gidan.
Daga can ɓangaren da kujerun gidan kuma suke, Kuliya ne durƙushe a gaban Mishal, wadda ke zaune a kan kujera, ya kama ƙafarta ta dama yabna saka mata safa, saboda sanyin da ake a gari.
Safar ya gama saka mata, sannan ya kai hannunsa ya janyo hular sanyita dake gefen kujera, ya miƙe tsaye yana saka mata a kanta.
Binsa kawai take da kallo, tana shawara da zuciyarta, kan ta yadda za ta ɓullo masa da maganar da suka yi da Adawiyya a yau.
Zama ya yi a gafenta ya na cewa.
“Shikenan?”
Kanta ta gyaɗa masa tana gyara zamanta.
Kallon da suke suka ci gaba da yi, kafin Kuliyan ya miƙe ya shiga kitchen ya aje plates ɗin da suka ci abinci.
Har ya kamo hanya zai fito, sai kuma ya fasa ya koma dan ɗaukar ruwa.
Babban kuskuren da ya tafka kenan a ranar.
Dan a sa'ilin da ya rufe murfin fridge ɗin, asa'ilin wani ɗan ƙarami, kuma mulmullallen ƙarfe, ya fito daga cikin bindigar da aka harba da ƙarfin tsiya, kuma bai tashi sauƙa a ko ina ba, sai a damtsen Kuliya na dama.
Wani irin shiga harbin ya masa, hakan ya sa shi sakin gorar ruwan dake hannunsa da sauri, sannan ya yi luuu zuwa baya ya na shirin faɗu, cikin dauriya da zafin nama ya kai hannunsa ya dafa island.
Da ƙyar ya tsaya a kan ƙafafunsa ya na layi.
Wani irin zugin azaba hannun nasa yake masa, hakan ya sa ya kalli hannun, bai tabbatar da abun da yake gani ba, sai da ya kai hannunsa ya kawar da ɗan guntun hannun T-shirt ɗin jikinsa, ya ga ramin da harbin da aka masa ya yi.
Ji ya yi jini na ɗibansa, tunawa da ya yi da Mishal dake falo ya sa shi cije leɓensa na ƙasa.
Ya kai hannunsa na hagu ya riƙe damtsen nasa dake ta zubar jini, da ƙyar ya ja ƙafarsa zuwa falon, dan ya san ko ma su waye suka zo gidan dan shi suka zo, kuma idan aka jima kaɗan za su iya shigowa cikin gidan, wata ƙila su cutar masa da ita.
“Ab...
Abu...
Abu Aswad...
La... lafiya...”
Mishal ta faɗi tana miƙewa tsayi, ganinsa cikin wani hali ba ƙaramin ruɗata ya yi ba, kamar an kunna famfo, haka hawaye ya shiga mata zuba, da sauri ta nufi inda yake tana kiran sunansa, duk ta birkice, ta rasa abin yi.
“Zo...
Zo mu je ka zauna!”
Ta faɗi tana jan hannunsa na hagu dake kan damtsensa na dama.
Da sauri ya riƙe nata hannun ya na girgiza mata kai cike da dauri, leɓensa ya ƙara datsewa.
A sanda ya fara jan hannunta zuwa ɗakinsa.
Kamar raƙumi da akala haka ta riƙa binsa har zuwa ɗakin nasa, duk kuwa da shi ɗin ba ya tafiya da kyau, ta lura ma da layi yake.
Wani abu da ya bata mamaki shi ne, ganin ya nufi closet ɗinsa da ita.
Mamaki bai gama cinyeta ba har sai sanda ta ga ya danna wani switch da duk shigowarta wurin ba ta taɓa lura da shi ba.
Ba tare da ɓata lokaci ba, lokar kayan dake wurin ta zuge zuwa gefe sannan ƙofa ta bayyana a gabansu.
Hannunsa na hagu wanda ya yi kaca-kaca da jini ya kai ya tura ƙofar ta yi baya, sannan ya tura Mishal ɗin ciki, shi ma ya shiga.
Ya na shiga ya rufo ƙofar, ya danna wani switch dake kusa da ƙofar, nan take lokar nan da ta yi gefe ta koma mazauninta na ainahi, kamar ma ba'a taɓa motsa ta ba.
Mishal ta ci gaba da bin wurin da kallo, ganin cewar ɗaki ne, har da gado a ciki, ga kuma wani work table dake ɗauke da computers da kuma tardu.
Duk da tana cikin halin ruɗu, bai hanata jin mamaki na jan ƙafarta zuwa ƙasa ba, to shi wannan ɗakin ta wani ɓangare yake a gidan?, dan ita ko da wasa ba ta taɓa sanin cewa akwai wasu ɗakuna bayan waɗanan ukun da ta sani a gidan ba.
Jin abu ya faɗi yaraf a bayanta ya sa da sauri ta waigo.
Idonta ya sauƙa a kan Kuliya dake yashe a ƙasa, hannunsa na hagu dafe da damtsensa na dama, wanda yake ta ɓuɓullar da jini.
Da gudu ta isa kansa tana kiran sunansa, a hankali ta kama kansa tana shirin zaunar da shi.
Da ɗan sauran kuzarin da ya rage masa ya miƙe zaunen ya na jingina da bango.
Mishal sai duba jikinsa take, kamar wadda aka cewa akwai wani switch da za ta danna a jikin nasa, wanda zai hana zubar jinin da yake.
Gaba ɗaya ya haɗa gumi sharkaf, kasancewar babu wata isashiyyar iska a ɗakin, dan ita ba ta ga windo ko wata ƙofa bayan wadda suka shigo ba.
Hular kanta ta cire ta na faɗin.
“Tsaya na saka maka wannan a wurin, may be zai hana jinin zuba”
Da ƙyar Kuliya ya iya sauƙe hannunsa na hagu daga kan raunin, sannan cikin sauri Mishal ta cikukuye hukarta pink color tana danawwa a wurin.
Jin ya yi wani irin nishi ne ya sa ta fashe da kuka me sauti tana kallon fuskarsa, idanuwansa har sama suke, alamun dai ya na gaf da rufesu gaba ɗaya.
“Na shiga uku ni Hafsat, Abu Aswad kar ka mutu, dan Allah kar ka mutu ka barni, Abu Aswad ka min alƙawarin kasancewa tare da ni fa, kuma na san Anna ta faɗa maka cewar karya alƙawari ba kyau, kar ka karya alƙawari, Abu Aswad ka kasance tare da ni, Abu Aswad ɗina dan Allah!...”
Sambatu take tana ƙarawa, ita kanta ba ta jin ma tana cikin hayyacinta, hular kanta da ta cire ce tasa gashin kanta barbajewa a bayanta, ta koma kamarwata wadda sanyi ya taɓawa ƙwaƙwalwa.
“Kana ji ko?!”
Ta tambaya tana mammarin gefen fuskarsa, idonsa da ya lumshe ya buɗe a kanta.
“Kar ka mutu baka haɗu da Zaid ba!...”
Kuliya ya ja wani kalar numfashi yana buɗe idonsa da ƙyar, cikin wani irin sauti yace.
“A...
Ina...
Ki...
Ki ka san...
Za...
Zaid?”
Ba dan babu sautin komai a ɗakin ba, da balalle ta ji abun da yake faɗi ba.
“Yau Anti Adawiyya ta zo makaranta ta same ni, shi ne take faɗamin cewar Zaid ne mijinta, kuma...
Kuma da ma ina ganinsa a layin makaranta”
Kansa ya kawar gefe yana ƙoƙarin ƙwato numfashinsa da ya nufi wata duniyar.
“Zaid ya gudu...
Gu...
Guduwa aka ce ya y... yi”
Da sauri Mishal ta share hawayenta, hakan ya sa gefen fuskarta ɓaci da jinsa.
Ta gyara zama ta shiga ba shi labarin da ta sani a kan Zaid ɗin.
Duk kuwa da ba ta da tabbacin yana fahimta.
Sai de kuma yana fahimtar, dan babu abu ɗaya da ta faɗa wanda bai samu mukkulin kansa ya buɗe ƙofa ya shiga ba, ya ji komai, kuma ya haddace komai.
Kallonta yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa gaba ɗaya.
“Hafsat!
Ballale...
Na...
Na kai gobe ba...
Amma idan...
Idan kin haɗu...
Haɗu da Zaid, ki ce...
Ki ce masa ina kewarsa...
Sa...
Sannan...
Sannan kuma ba duk tswon wannan lokacin, ban manta da shi ba...
Ki kuma faɗa masa cewar...