Sashe 32
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau na ga wata me kama da Mommana, me kama da Zaid ɗina, kuma me kama da ni!”
Wani irin shiru ne ya ratsa falon, yayin da babu ƙarar abun da ke tashi sai na tv dake a kunne, sai kuma ƙarar acn dake fita a hankali, kuma da a ce Kuliya ya kasa kunne sosai, da ya ji sautin bugun zuciyar Anna, yanda take kallonsa kawai shi ne zai shaida masa kalar tashin hankali da mamakin da take ciki.
Siyama dake kitchen ta ɗora hannunta a kan bakinta, yayin da zuciyarta ke tambayarta; shin da ma Kuliya na da wasu 'yan uwan bayan Anna?, ita dai haka ta taso ta ganshi a gidan Anna, kuma ce mata aka yi maraya ne da Annan ta samoshi a tsohon gidan marayun da ta taɓa aiki.
*Shekarata 2000*
Aliyu ne zaune kan wani benci da ke Garden ɗin gidan marayun da aka kaishi, matar da ya saba da ita cikin kwana uku kacal me suna Rahama na aikin share garden ɗin, jifa-jifa Rahaman da tace ya riƙa kiranta da Annan ke masa hira.
Sai dai shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ba ya kanta, hankalinsa ya karkarta kan ɗan uwansa da ya shafe kwana uku ba tare da shi ba.
Babu kowa a garden ɗin, daga Annan sai shi, saboda gaba ɗaya yaran gidan na ajin ɗaukar karatun Alkur'ani.
Wata iriyar ƙara da ta cika wurin ce ta sa Anna da Aliyu firgita, a kiɗime suka dubi ginin wurin.
Wanda ke taci da wuta.
Wata kalar ƙara haɗe da salati Anna ta saki, tunawar da ta yi kowa na gidan na cikin ginin, babu kowa a waje sai ita da.
Wannan ɗan marayan Allahn.
A dugunzume ta ja hannun yaron suka yi waje, sannan ta shiga neman ɗauke, har aka samu wanda ya kira 'yan kwana-kwana, aka zo aka kashe wutar, amma babu wanda ya tsira a cikin gidan, tun daga kan yaran gidan har ma'aikatan.
Ba Anna kaɗai ba, hatta da Aliyu da bai jima da zuwa gidan ba sai da abun ya taɓashi, haka gwamnati da sauran masu faɗa a ji suka riƙa sintiri a gidan marayun, kafin daga bisani aka rufe shi.
Tun bayan faruwar lamarin Anna ta ɗauki Aliyu suka koma gidan wata ƙawarta a nan garin Kano, kasancewar da ma da ta zo garin a nan ta sauƙa.
Bayan da ta gama haɗa kuɗaɗenta na mota ta ɗauki Aliyu suka koma mahaifarta Abuja, inda mijinta da 'yan uwanta suke.
Da ma can nemawa mijinta kuɗin da za'a masa tiyata ne ya sa ta zo garin kano neman aiki, har Allah yasa ta samu a wannan gidan marayun.
Kai tsaye gidan mijinta ta wuce da Aliyu, kuma da isarsu ta zauna ta masa bayanin inda ta samu Aliyu, be musa mata ba, haka ya amince da zaman Aliyun tare da su, ya tiƙe Aliyu kamar ɗan da ya haifa, kasancewar Allah bai taɓa basu haihuwa ba.
Haka Aliyu ya ci gaba da zama a gidan Anna.
Wadda ita ce ke kula da kaf nauyin gidan nata, kasantuwar shi mijin nata ba shi da lafiya, har makaranta ta saka shi, bayan da ta samu aikin dafa abinci a wani restaurant, da albashin da suke bata take kula da kaf matsalosalun gidanta.
Anna ita ce wadda ta ƙarawa Aliyu sunan Bhici a gaban sunansa na makaranta, kasacewar mijinta hifaffen garin Bhicin jahar Kano ne.
Shi kuma mijin nata shi ne yake kiran sa Kuliya, saboda yace halayensa kaf irin na wani ƙaninsa ne da ya rasu, kuma sunan kanin nasa Kuliya!.
Har zuwa lokacin Zaid na maƙale a ran Aliyu, sau tari yakan keɓe kansa ya sha ƙuncin kewar yayan nasa.
Da haka har ya kwashe shekaru biyar tare da su Anna, a cikin wannan shekaru biyar da suka shuɗe, Allah ya yi wa mijin Anna rasuwa, sakamakon jinyarsa ta ciwon ƙoda da ya kasa sakun sauƙinta.
Haka Anna ta ƙara rungumar Aliyu a matsayin wanda ya rage mata, ta manta da cewar shi ba ɗanta ba ne, ta manta da cewar ba ita ta haifeshi ba, ganin bayan mijinta da 'yar uwarta ba ta da kowa, kuma ga shi mijinta ya rasu, sai ƙanwar tata da kuma shi Aliyun.
Lura da Anna ta fara yi da yanayin damuwar da Kuliya ke ciki ne ya sa ta ritsa shi da tambayoyi, har ta samu nasara a kansa, ya bayyana mata abun da ke cin ransa.
Da haka ta masa alƙawarin za ta je har Kano tare da shi don su duba ɗan uwansa.
Sai de me?!.
A sanda suka isa Kano suka je gidansu Aliyu na da, basu iske kowa a cikin gidan ba, hakan ya sa Aliyu da kansa ya shiga gidansu Naufal ya tambayi Maman Naufal ɗin, shin ta san inda ɗan uwansa yake?, kuma Maman Naufal ɗin ce ta sanar masa da cewar ai rana ɗaya suka tashi suka ga babu Zaid ya gudu.
Jiki a saɓule cikin tashin hankali da sallalami Anna ta dawo Abuja da Aliyu, kuma tun daga lokacin yanayinsa na shiga ƙunci ya ƙaru fiye da da.
Babu yanda Annan ba ta yi da shi ba, kan ya dawo yanda yake amma ya ƙi.
Har ta haƙura ta zubawa sarataura Allah ido.
Bayan da Kuliya ya kammala secondary, Anna ta ƙuƙuta ta sa ma masa gurbin karatun diploma a wata makaranta dake cikin garin Abuja.
Bayan ya kammala diplomar ne ya shiga fafutukar neman aikin da suka taso cikin burin yinsa shi da ɗan uwasan, aikin da Momma ta ƙarfafa musu gwiwa a kai, tun suna ƙananu suka yi wa kansu alƙawarin yin aikin DSS!.
Sai da ya gama shan wahalar neman aikin, kafin Allah ya sa wani ɗan uwan mijin Anna ya kawo masa offern aikin DSS ɗin.
Da an ce mutum na da hannaye shida, da Kuliya ba zai yarda ba, amma a sanda aka ba shi offern zai iya cewa ya ga hannayensa sun nunku daga biyu zuwa shida wajen karɓar takardun, ya yi matuƙar farin ciki da samun aikin.
Kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga aiki gadan-gadan, bayan da aka musu training, ƙwarewarsa kan aikin da kuma gaskiya da maida hankali ne yasa shi samun nasarori da dama, tare da samun ƙarin girma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
*Present day...*
RAJA POV.
_🎶...We're not in love..._
_We share on stories_
_Just something in your eyes..._
_Dont be afraid..._
_The shadows know me_
_Let's leave the world behind...🎶_
Waƙar da yake saurare kenan, ta cikin headphones ɗin dake saƙale a kunnensa.
Jingine yake jikin gate, idonsa a kan ƙofar gate ɗin makarantar tasu.
Ya na kallon sanda ƙafafunta suka fito daga cikin gate ɗin, kuma zai iya rantsewa kan abu na farko da ta fara kalla daga fitowar tata shi ne.
Ya ga sanda ta yi wani siririn murmushi, shi ma kuma martanin murmushin ya mata, sannan ya miƙe a kan ƙafafunsa, ya fara takowa zuwa inda take tsaye, wato ƙofar makarantar.
Hannunsa ya kai ya tura headphones ɗin ƙeyarsa.
Tare da ɗan ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Mu je ba?”
Tana wannan sirirn murmushin ta fara tafiya, yayin da shi ma ya jera tare da ita, be san me ya sa ba, amma bayan son sanin asalinsa ta dalilinta, yana san samun kusanci da ita, sai dai ba ya jin abun kamar yanda Rhoda ke faɗi ne, da ta ce wai ya na santa ne, shi sam bai ga hakan ba, kawai dai ya na jin son wannan haɗuwar da suke, don idan weekend ya zo ba ya jin daɗi, shi da za'a bi ta tasa ma da an dena yin weekend ɗin.
Sai kuma ya yi wa kansa da kansa murmushi.
Da ya hango tarin ɗaliban da ba sa son zuwa makaranta, wasu ma ba su da lokacin hutu sai wannan weekend ɗin, wata ƙila idan suka ji wannan batun nasa sai sun naɗa masa na jaki.
“Yau ina Rhoda?”
Muryar Rabi'a ta faɗi bayan wani lokaci.
Kamar me neman Rhodan, sai da ya waiga bayansa ya kalli ƙofar Estate ɗinsu, sannan ya juyo da kansa yana kallon hanya.
“Yau ba ta zo tsurkun ba”
“Ku kaɗai kuke rayuwa a gidan naku ne?”
Sai da ya ɗan kalleta, sannan ya amsa mata da.
“Eh, amma akwai wasu abokai na guda uku, mu 'yan Kano ne, aiki ne ya kawo mu Abuja, kuma da zarar mun gama za mu koma”
Sai ta gyaɗa kanta.
A sanda take ƙara tabbatarwa da kanta duk yanda aka yi bai san da zaman mijin Mishal ba, amma sai dai idan matsala suka samu, har ta kaisu ga rabuwa, ko kuma dai sun rabu ne ba tare da sani ba, ma'ana ko ɗaya ne ya ɓacewa ɗaya.
To ita yanzu mamaki da ruɗanin sai suka zame mata biyu, tana san sanin wace alaƙace tsakaninta da su, tana kuma son sanin abinda ya raba waɗanan 'yan uwan biyu, amma ba ta san ta inda za ta fara ba.
Kawai sai ta tare shi tace masa ta ga ɗan uwansa?, to idan kuma da ma ya san da zaman ɗan uwan nasa fa?,ya kammata ta fara sanin abun da ke tsakaninsu tukkuna, ta na buƙatar sanin farkon LABARINSU, kafin ta san wani mataki ya kamata ta ɗauka a kan lamarin.
“Ke fa?, tare da wa kike rayuwa?”
Wannan innocent muryar tasa ta faɗa, a sanda suka tsaya a bakin titi, ta kalli hanya sannan tace.
“Ni da yayata da kuma Ummanmu, kafin Allah ya yi wa yayartawa rasuwa, daga bisani kuma Mamata ma ta rasu, sai kuma na dawo da zama a gidan babana, akwai matar babana da yaranta huɗu, Anti Saratu, Mama, Fatima da Mahmud...
Sai kuma shi baban nawa”
“Shi ne yasa kike aikatau a nan?”
Ya tambaya kansa tsaye, kuma ya lura da ta haɗiyewa wani abu, kafin wannan siriryar muryar tata tace.
“A'a, ba babana ba ne, matar babana ce”
Raja ya gyaɗa kansa ya na ƙara tabbatarwa kansa da abun da zuciyarsa ke zargi a kan yarinyar.
Ba tare da ya sake ce mata komai ba, ya tsayar mata mota kamar kullum, ta shiga sannan suka yi sallama.
Sai da suka yi nisa, sannan ya juya ya koma layinsu.