← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 80

Sashe 15

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sani cewa ko cikin 'yan uwanta na haɗejia babu mai kaka da wannan, duk da ba za'a rasa ba, amma dai wannan ba daga can yake ba, to kenan waye shi ?, daga ina yake ?, me yake a nan ?, kuma me yasa yake kama da Ummansu ?, don sai dai ta dangana kamar tasa da ta Ummansu ba tata ba.

Mafarin komai kenan😎.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.

“Aliyu, this will be your next assignment, ina so ka yi ƙoƙarin yinsa cikin taka tsan-tsan da kula, ka sani kuma nima na sani, a halin yanzu akwai masu farautar rayuwarka...

Dan haka ka kula, coz this was the most dengerous assignment ever.

Dan haka sai ka kula....”
Chidera Kinsily ke koro masa wannan jawabin, yayin da yake miƙa masa wani file.

Hannu bibbiyu yasa ya karɓi file ɗin.

File ɗin da zai kai rayuwarsa zuwa wani mataki, file ɗin da zai sauya rayuwarsa, file ɗin dake ɗauke da matakin farko na sauyawar ƙaddararsa.

Ƙaddarar da za ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu lamuran.

Chidera ya ci gaba da faɗin.

“Case ne a kan wasu manya-manyan 'yan ta'adda da suka yi wa garin Abuja tsinke a yau ɗin nan...

Ba ma so abun ya tafi da nisa, wannan file ɗin ɗauke yake da bayanin kowannensu, don haka kasan abun yi...

Sannan idan kana so za ka iya neman temakon abokin Abubakar”
Kuskure mafi girma kenan da ya zama sanadiyyar faruwar wannan ƙaddarar.

Wata ƙaddara mai cike da tarin abubuwa, masu daɗi da akasinsu.

A hankali Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ce.

“Zan san abun yi sir”
Kuskure na biyu kenan, wani babban kuskure da zai yi nadamarsa da farko, sannan daga baya ya dawo ya yi farin cikin ɗaukarsa.
*
“Shigo!”
Muryar Abubakar ta faɗi daga cikin office ɗin.

Bayan da aka buga ƙofar office ɗin nasa.

Kuliya ya murɗa ƙofar office ɗin, sannan ya shiga ciki.

A hankali Abubakar ya ɗago da kansa ya kalle shi.

Kamar kullum sanye yake cikin baƙar suit, sai dai babu suit ɗin, waist coat ce kawai a saman baƙar oxford shirt ɗin dake jikinsa.

Hannunsa na dama riƙe da file ɗin dake ɗauke da ƙaddararsu.

Ƙaddarar da za ta sauya LABARINSU.

“Sabon assignment ne, idan babu abun da za ka yi, sai ka taya ni...”
Wannan dakkakiyar Muryar tasa ta faɗa.

Kuskure na uku kenan.

Abubakar ya yi murmushi yana aje ipad ɗin hannunsa.

“Babu damuwa Dude, ai duk assignment ɗinka nawa ne... akan miye ?”
Kuskure na huɗu kenan.

“Ban sani ba, dan ban duba ba”
Ya amsa shi a taƙaice, duk kuwa da yasani ɗin.

MISHAL POV.

Shekaran jiya suka dawo daga Maiduguri.

Kuma a jiya ne Abubakar ya kaita aka cire mata braces ɗin dake haƙwaranta.

Ba ƙaramin daɗi ta ji ba a sanda aka rabata da su, don Allah ya sani, ba ta san su, ga shi dai ita ta ce a saka mata su, amma daga baya sai suka gundureta.

Zaune take a comound ɗin gidan, suna hira ita da Shatu, yayin da Daala ke zaune a gabanta.

Akasarinta hirar tasu a kan Maiduguri ne.

Daga can saman benin gidan kuwa, Hajjara ce ke leƙowa ta window tana kallon Mishal ɗin.

Cike da tsana da kuma alwashi.

Ta ɗaukawa kanta alƙawarin ganin bayan Mishal, ba za ta huta ba sai ta ga tabbatuwar hakan.

Ko da za ta ƙarar da duka abun da ta mallaka ne sai ta aikata hakan.

Abun da ba ta sani ba shi ne; ƙaddarar da Allah ya hukunta faruwarta ta kusa afkuwa, kuma tun kafin abun da ta tsara ya kai ga gaci komai yake wargajewa.
*Unguwar Rafin Cinnaka, Suleja, Niger state*
“Yanzu miye abun yi ?”
Muryar Habiba ta tambaya, yayin da take zaune a falon gidan yayarta hajiya Inno.

Hajjiya Inno ta yi murmushi.

“Yanzu abun da ya kamata shi ne kawai ki kawo wani abun, a kai masa a matsayin kafin alƙalami...

A fara aiki a kan Saratun, na faɗa miki aikinsa ba ƙaramin ci yake ba...

Da zarar ya yi aikin ina mai tabbatar miki da ko sati ba za'a yi ba za ki ga samari sun fara sintiri a ƙofar gidanki...”
Habiba ta ɗan yi dariya.

“Haka nake san ji, dan Wallahi har ga Allah na gaji da ganinta a gidan nan haka...

Ita ma idan ta ɗan samu ta yi auren nan ai yafi ko?”
“Hakane”
“To sai batun Mama, yarinyar nan so take ta fara fin ƙarfina, wai rannan dan na mata magana kan ta ɗan yafita min wani abu sai ta hauni da faɗa?!”
“Mtswwww!, Wallahi kuwa Habiba da kin bada mata, har ita ta isa dan ub*nta ?, Idon ki za ki murje ki nuna nata cewar ke ce uw*rta, ba ita ta haifeki ba!”
Habiba tace“Hummm!” cikin taɓe baki.

“Gaakiya ba zan iya takurata ba, dan baki san yanda nake san Mama ba ne, sam ba na so ranta ya ɓaci Wallahi, ke dai kawai kawo wata shawarar”
Cike da mamaki Inno take kallonta.

Can kuma sai ta taɓe baki tace.

“To ai ita ma nata lamarin mai sauƙi ne, sai amata na kasuwar samarin, alhajan nan na abuja su yi ta kai kawo a kanta, sannan a rufe mata baki, duk sanda za ki mata maganar kuɗi ta miƙo miki kawai...”
Habiba ta saka dariya har da shewa, tana jin wani abu na washewa daga ranta.

“Wallahi Yaya Inno abun ne da yawa, kin ga na Zainab ma abun yaƙi daɗi, kar ki ga yanda bawan Allahn nan ke gasa mata aya a hannu”
Inno ta kuma yin dariya.

“Shi ma nata mai sauƙi ne...

Habiba idan fa da kuɗin ki shikenan, duk wata matsala taki ta kau, in dai za ki bada shikenan...”
Ta sauƙe ajiyar zuciya.

“Sai kuma na wannan sheg*yar yarinyar, kinbga fa duk dan na tagayyara rayuwarta na sa Ɗan Lami ya dawo da ita nan garin, toh!, ta taggayar ɗin, amma ni ba haka na so ba....Na fi so ta ƙare da cikin sh*ge, shi ne fa yasa ma na aikata akatau, amma dai har yanzu shiru ki ke ji...”
Dariyar da Inno ta saka ce ta sata yin shiru.

“Wai ni Habiba yaushe kika yi sanyi ne ?, ina Habibar da na sani ta da ?, wai duk kin yi sanyi kin zubar da makaman yaƙinki ?, yo in ba haka ba ai wannan ba wata matsala ba ce, ke dai zo ki ji”
Ta ƙarashe tana matsawa kusa da Habiban, Habiba ta miƙa mata kunne.

A take Habiba ta saka shewa tana tafa hannu, bayan da ta gama sauraron abinda Innon ta raɗa mata.

“Ai kuwa ko miliyan nawa zan sadaukar a kan wannan aikin, in dai har...

Zan ga bayan jinin Maryam a duniyar nan!”
______________
_Wai Siyama ce take san Kuliya😂...

Wani ya bata shawarar kada ta fara tafiyar dare ba maraki, ah to, kar ta ce ba mu gaya mata ba_
_Shin wata ƙaddara ce wannan ke shirin faruwa ?_
_Ya za ta kaya tsakanin RAJA da RABI'A ?_
_Kun ji alƙawarin Hajjara a kan MISHAL?_
_Sannan ga Habiba ma a nata ɓangaren, me kuke ganin tana shiryawa ?_
_Kamar fa an bawa Kuliya assignment ɗin da zai sauya rayuwarsa, sannan Chidera ya ce 'yan dabar yau suka sauƙa a garin abuja....Kada ku ce min su RAJA ne😨...._
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters
°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*06*
~~~
*The wrong one will find you in peace and leave you in pieces.

The right one will find you in pieces and lead you to peace.*
***
*Shekara ta 2000*
*Kano.....*
A hankali Zaid ya juya ya kalli ƙaninsa Aliyu, wanda har zuwa lokacin yake ta risgar kuka. awa biyar kenan da aka kashe wutar da ta kama a gidansu.

Wutar da ba ta bar musu komai ba, ciki kuwa harda mahaifiyarsu.

Kuma har zuwa lokacin, suna sanye da wannan uniform ɗin islamiyyar, yayin da ƙonnaniyar gawarbmahaifiyarsu ke rufe a gabansu.

Zaune suke a ɗakin da aka ajeta bayan da aka samu aka kawota asibiti, kuma tun kafin su kawo asibitin jama'ar da suka ɗaukota ke faɗin ai ta cika.

Shi ma kansa Zaid ɗin so yake ya yi kukan, amma ya kasa.

Bai san ina za su je ba, bai san ina za su koma ba, bai san kowa nasu ba, kuma Momman nasu ko ƙawa ba ta da ita, bare su ce za su je wurinta.

Hatta da asalinsu basu sani ba, bayan ce musu da ta yi ita 'yar haɗejia ce, ba ta ƙara ce musu komai a kan asalinsu ba.

“Aliyu....”
A hankali nitsataiyar muryarsa me cike da kamewa ta kira sunan, yayin da lumaassun idanuwasa masu ɗauke da gray ƙwaya suke kallon Aliyu.

Aliyun ya juyo ya kalli yayansa.

Kuma har a lokacin kuka yake.

Lokacin ƙarfe takwais na dare da ɗorariya, jama'ar da suka kawo su asibitin ma tafiyarsu suka yi bayan an tabbatar musu da rasuwarta.

“Ba mu yi sallar magrib ba...

Ga isha ta kawo kai”
Da ƙyar sautin muryar tasa ke fita, don mai sauraro ma zai iya tsintar ɗacin da muryar tasa ke ɗauke da shi, ba zai ce ya gama mallakar hankalinsa ba, amma ya san cewa duk wanda ya mutu ba ya dawowa.

Ya san cewa yanzu su da ganin Mommansu wata ƙila sai a lahira, sun zama marayu, yanzu su marayu ne waɗanda basu da kowa sai junansu.

Babu wanda zai taya su kukan rashin da suka yi.

Ba tare da Aliyun yace komai ba ya miƙe tsaye, shi ma Zaid ɗin miƙewar ya yi, ya dafa kafaɗarsa suka fara tafiya zuwa waje.

Kuma har lokacin Aliyun na kuka, shi kuma Zaid ɗin sai rarrashinsa yake.

A masallacin asibitin suka yi sallah.

Sannan suka fita wajen asibitin.

Dan Zaid ɗin ya tuna da ɗari biyun da Momman ta basu a yammacin ranar, tace da su; su siyi wani abun idan sun je islamiyya.

Awara ya sai musu da ita, sannan suka dawo cikin ɗakin da aka kwantar da ita.

Suna kallon gawar suna cin awarar.

Kuma bayan sun gama suka ci gaba da zama a ɗakin, har zuwa lokacin da dare ya tsala.
Chapter 15 · 0% Book details