← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 80

Sashe 28

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shaida mata da; babu wani abun da ya tanada, kawai a je a ɗauko amaryar, koma miye daga baya sai a yi, ba ta ƙara cewa komai ba, dan wata ƙila a ganinsa hakan ya masa, a irin halin da yake ciki ba ta jin za ta iya tirsasashi kan wani abu da baya so ba.

Daga can gidan Anti Karima, Siyama dake kan danning ta nufota a razane, jin ta ambaci aure da kuma suna Kuliyanta.

“Anti Karima wai menene?”
Cike da baƙin ciki da ƙunar zuci Anti Karima ta kalleta tace.

“Wai Kuliya aka ɗaurawa aure!”
Wani irin duka gaban Siyama ya yi, har ta ji kamar an daki zuciyarta da ƙarfin da aka saka a wuta, kamar da Anti Karuma ta watsa mata barkwano, zuciyarta ta shiga mata ɗaci, wanda ya zagayo har zuwa bakinta.

Kuliyanta ?, Kuliya ya yi aure?, wai me Anti Karima ke faɗi ne?, anya ma kuwa tana cikin hayyacinta?

Inna!

Ba za ta saɓu ba, wannan zancen ƙarya ne, Kuliya na ta ne ita kaɗai, wata mace ba ta isa ta rabata da shi ba, babu wanda ya isa ya shiga tsakaminta da shi.

Ba ta san ta fara hawaye ba, sai da Anti Karima ta dafata.

“Kada ki damu Siyama, ko wace sh*giya ya aura za mu raba shi da ita, Kuliya naki ne ke kaɗai, dan haka ke kaɗai za ki same shi”
Kamar wadda ta bada ajiyar hankalinta haka ta kalli Anti Karima, hawaye na mata zuba.

“Anti Karima Wallahi ina sansa...

Na rantse miki da Allah ina san Kuliya, na shiga uku ni Siyama!

Yanzu wai Aliyuna ne ya yi aure?, Wayyo Allahna, Anti Karima...

Anti Karima Ina sansa, I love him Anti Karima...

I can't live without him, I can't, i can't...”
Gaba ɗaya ta fita hayyacinta, sambatu kawai take tana ƙarawa.

Anti Karima ta rungumeta tana bubbuga bayanta.

“Ba za mu rabu a su ba, dole sai mun rabasu!...”.

Haka Siyama ta ƙarar da yinin ranar kamar mara lafiya, kuka kam ta yi har ta gode Allah.

Sai da yamma Anti Karima ta shirya dan zuwa gidan Anna, amma sai wayar Annan ta risketa kan ta yi zamanta ba sai ta zo ba, Kuliya yace zai je ya ɗauko matarsa da kansa.

Tun daga lokacin ta riga ta tabbatarwa da kanta ba zata bar wannan auren ya ɗaure ba, sai ta ga bayan wannan auren, ta ko ta halin ƙa-ƙa.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
MISHAL POV.

“A gidan Ub*n wa aka ɗaurawa jikar tawa aure?...

Tukunna ma ub*n waye ya aurar da ita?!”
Jadda kakarsu ce ke magana cike da masifa, a sa'ilin da Ammu Musa ke sannar musu da batun ɗaurin auren Mishal da aka yi, tare da faɗin wai ga mijinta nan ya zo ɗaukanta su tafi.

Yau kwana takwas kenan da rasuwa Abubakar, gaba ɗaya ahalinsu na Maiduguri babu wanda bai zo gidan ba, haka aka yi zaman makoki aka share a jiya, sannan kowa ya koma Maidugurin, ban da Jaddan da ta ce ba za ta koma yanzu ba, sai Nimra wadda gidanta ke cikin garin Abuja.

To yau ma ita da yaranta gaba ɗaya suna gidan.

Mishal dake kwance a kan doguwar kujera ta miƙe zaune, ta na jin wani zance da ba shi da ƙafa bare kai, aure ?, wa aka yi wa auren wai ?, wai ita?, ita akawa aure?, ta na cikin sallalamin rasuwar ɗan uwanta za'a wani zo mata da batun aure?.

Duk da ba wani sosai take shiri da yayan nata ba, amma tasan da cewa ya na santa, kuma yana yin duk wata hidima da za ta faranta mata, ba ta yi kuka ba a rasuwar tasa, amma ta shiga cikin ƙinci mara misaltuwa, don ko makaranta ba ta zuwa.

Ammu Musa ya sunkuyar fa kansa a gaban matar kawunsu, sannan yace.

“Aure Jadda, Abubakar da kansa ya bayar da auren Hafsat ga abokinsa Aliyu!

Kuma wannan ɗaurin auren shi ne abu na ƙarshe da Abubakar ɗin ya nema kafin Allah ya amshi ransa!”
Ba Jadda kawai ba, hatta da Nimra da kuma Hajjara sai da suka yi mamaki, amma me yasa babu wanda suka faɗawa batun auren har tsawon kwana takwas?.

Tun da bakin Ammu Musa ya ambaci sunan Aliyu, zuciyar Mishal ta hasko mata fuskarsa, wannan fuskar me kama da ta Adawiyya, kazalika irin wannan fuskar da take ganin mamallakinta na yawan tsayawa a tsallaken makarantarsu, kenan shi aka aura mata ?, wai tsaya ma, ita Mishal akai wa aure ?, wai har nawa ma take ?, da za'a mata aure, aure fa?.

“To Wallahi ba Abubakar ba, ko Muhammad ub*n Abubakar ne zai dawo duniya yau ba ku isa ba, nawa ma yarinyar take ?, duka-duka fa bata fi shekaru 16 ba, shi ne za ku cuci rayuwarta ku mata aure?”
Anna ta faɗi tana miƙewa, kamar ta kaiwa Ammu musa bugu haka take ji.

“A'a Anna, kin san dai Ammu ba zai miki ƙarya ba, dan haka batun auren nan an riga an ɗaura, kawai dai mu yi wa Mushal fatan alkari, tare da danƙata a hamnun mijinta, kinsan dai Abubakar ba zai taɓa aurawa Mishal mijin da bai dace ba”
Cewar Nimar ta na miƙewa tsaye, Jadda ta juyo ta kalleta tare da wurga mata harara.

“Ba ke ba, ko Fatima kakarki ba ta isa ta faɗa min haka ba!

Kar ki ga ina sakar miki fuska, ki ɗuka cewar za ki iya kawo min raini Falmata, Wallahi ina iya ɓatawa da ub*n kowa a kan jikokina!...”
Daga nan Jadda ta shiga buɗe musu wutar bala'i, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, masifa kwando-kwando haka ta riƙa sauƙewa.

Sai da Nimra ta kira escort ɗinta, waɗanda gomnati ta bata dan kariya, a matsayinta na general, kasancewar a waje suke suna jiranta ba ɓata lokaci suka shigo, cikin su har da yaranta biyu, Ijaz da Arman.

Su suka saka bakin Jaddan yin shiru, ba dan ta na so ba a gaban idonta Nimra da 'yarta Iqra suka shiga ɗakin Mishal suka haɗo mata kayanta kaf.

Sai da suka so shiryata ma, amma da suka duba kayan nata suka ga babu na arziƙi sai suka barta haka, dan Mishal ba atamfa ko leshi take sawa ba, ita dai barta da ƙanun kaya.

Ita kuwa Mishal tun da aka fara wannan dambaruwa ta rasa gane kanta, ba ta ma fahimtar zancen da ake, dan zantukan nasu sun wa ƙwaƙwalwarta girma, wai yau ita aka yiwa aure, ita ɗin da take cewa ko da candy ta yi, ba za ta yi aure ba sai ta fara aiki, ga shi tun ba'a je ko ina ba har zancen ya warware.

KULIYA POV.

Tsaye yake a harabar gidan Abubakar, ya jingina da jikin motarsa, tunanika iri-iri na kai kawo a cikin kwanyarsa, shi kansa ba zai ce lafiyarsa ƙalau ba, dan yasan ba shi da lafiyar a irin halin da yake ciki.

Kuma ba ya jin akwai maganin damuwarsa, komai ya masa duhu, ya kasa gane ainahin kan lamarinsa, shin farin ciki yake don ya samu wadda zuciyarsa ta gama tabbatar masa da sonta yake ?, ko kuma yana alhinin mutuwar amininsa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ceton tasa rayuwar?.

Ya kasa ganewa, ya kasa gane dai-dai da akasinta, ya kasa gane duhu da haske, ya kasa gane sarƙaƙiya da warwara.

Ba ya fahimtar komai, ya na jin kamar rayuwarsa ce ke tangal-tangal a cikin kwale-kwalen katako, wanda ke tsakiyar tekun dake ambaliya...

Tunaninsa ya katse, a sanda ya hangi mutane na fitowa daga cikin gidan, sojoji ne guda huɗu a kan gaba, kowannensu riƙe da akwati, sai mata uku daga baya, sun saka ɗaya tsakiyarsa, wadda yake da tabbacin ita ce Mushal ɗin, duk da fuskarta a rufe take da gyale.

Har suka ƙaraso inda yake ya na kallonsu, ɗaya daga cikin sojojin ne yace ya buɗe musu booth, bai musa ba ya buɗe, suka saka akwatunan a ciki.

Dai-dai da lokacin da mata nan biyu suka saka Mushal a cikin motar tasa a seat ɗin gaba.

Ɗaya daga cikin matan ce ya fusaknci cewa babbace, don ga shekarunta nan sun bayyana hakan, kuma sai yake ga kamar ma yasan fuskarta.

Gaishe da ita ya yi cike da girmamawa.

“Kai ne Aliyu right? ”
Sai ya gyaɗa mata kai idonsa a ƙasa.

“Ba ka gane ni ba ko?”
Sai ya gyaɗa kansa yana ɗaga kafaɗa, don ya kasa ganotan.

“Mun taɓa haɗuwa sau ɗaya, General Adamu Nimra Arab”
Take fuskarta a ranar da suka fara haɗuwa ta dawo masa, tabbas ita ce, ita ce matar da ta babshi award a wani taron karramawa da ya taɓa zuwa.

“Ni uwa ce, kuma yaya a wurin Mishal, ba sai na zauna na maka dogon bayani ba, nasan ka mallaki hankalin kanka, ka kuma san hakkin mata a kan mijinta, na kuma san da ka san hakkin Maraya, don haka sai ka kiyaye!”
Maganganun nata ba su da yawa, amma baƙaramin taɓa shi suka yi ba, shi kuwa ya san maraici, ai yana jin babu wanda zai bada labarin maraici sama da shi...

RAJA POV.

Zane yake a kan kujerar dake facing Alhaji Bala, wanda ya buɗe akwatin dake cike da hodar ibilis, wadda su Rajan suka ƙwato masa a hannun waɗanda sukai haɗa kasuwanci da su. da ma haka Alhaji Bala ya saba saka su aiwatarwa tun suna garin kano.

Sai ya yi yarjejeniya da dilolin cocaine, kan yana so a kawo masa zai biya kuɗin, sai kuma ya tura 'yan daba karɓar kayan, idan waɗanda aka aiko da kayan ba su yi gardamar hana kayan ba, 'yan dabar Alhaji Bala za su karɓi kayan salin alin, idan kuma waɗanda aka aiko da kayan sun yi gardama, 'yan dabar Alhaji Bala za su kashesu su ƙwaci kayan.

Fuskar Alhaji Balan, ɗauke take da wani irin yanayi, wanda yake cakuɗee da farin ciki da kuma mamaki, tun da ya fara safarar hodar ibilis, bai taɓa yin wadda ta kai wannan yawa ba.
Chapter 28 · 0% Book details