Sashe 66
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Who are you Zaid”
Raja ga haɗiye wani kakkauran miyau me ɗaci, sannan ya lumshe idonsa ya buɗesu a kanta, kana ya amsa mata da:
“Zaid Aliyu...
Department of state service (DSS) officer!”
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
“Yaushe za mu je gidan Anna?”
Ta tambaya ta na saka kayan Kuliya da ta wanke yau da safe a cikin loka.
Kuliya dake zaune a bakin gado yan danna waya ya kalleta.
“Me ya faru?”
Ya tambaya.
Mishal ta girgiza kai ta na saka wata rigar cikin lokar.
“Kawai de ina kewarta ne?”
Sai ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai.
“Nanbda sati ɗaya ne fa Teddy Bear,saurin me kike?”
Ta juya ta na ci gaba da aikinta tare da faɗin.
“Na gaji da zuwa school ne...
Kuma mun kusa mu fara exams”
Lokar ta rufe, sannan ta juyo ta iso gareshi.
“Next term za ku fara Neco da Waec right”
“Ummm!”
Ta amsa masa tana karɓar wayar hannunsa.
“Lokacin danna waya ya ƙare, let's fall asleep”
Murmushi ya yi ya ja kamo hannunta, tare da zaunar da ita akan gadon.
Wayarsa dake haannunta ya karɓa ya na ajeta kan side drawer.
Kwantar da ita ya yi a kan gadon, ya juya ya kashe wutar ɗakin, sannan shi ma ya kwanta ya na karata da jikinsa.
“Abu Aswad?”
Mishal ta kira sunan bayan wani lokaci.
“Ummm!”
Muryar Kuliya ta amsa ƙasa-ƙasa, alamun kamar ma ya fara bacci.
“Yaya batun Anti Adawiyya?”
Tar Kuliya ya buɗe idonsa cikin duhun ɗakin.
Jin ta ambato masa sunanta, bayan da ya gama bincike ya gano komai a kanta, ciki kuwa har da fyaɗen da aka mata, sai de kuma baya so ya faɗa mata komai, dan baya so hankalinta ya tashi, shi ya sa bar wa cikinsa maganar, ba tare da ya faɗa mata komai ba.
“Sharon tace zuwa gobe za a iya samo address ɗin gidansu, ki kwantar da hankalinki!”
Ya faɗa mata dan ta kwantar da hankalinta, wata ƙwalla ce ta taru a idon Mishal, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta silalo.
Sai jin damshi Kuliya ya yi a gaban rigarsa, kasancewar kanta na kan ƙirjinsa ne.
Iska ya furzar daga bakinsa ya na ƙara ƙanƙameta.
“Hafsat?”
“Na'am!”
Ta amsa a raunane.
“Ni fa da kaina na ce miki zan gano miki inda take, babu abun da zai sameta”
Hawayen ta goge da kanta tana gyaɗa kai.
“Umhumm!”
“I love you, maza ki yi baccin ki.....”
“I hate you”
Ta faɗi tana lumshe idonta.
*No.86, Garki 2, Abuja...*
*10:20 PM.*
RABI'A POV.
Tsaye take daga jikin dressing mirrorn ɗakinta, a hankali ta aje wayarta dake riƙe a hannunta, bayan da suka gama waya da Jidda.
Juyowar da za ta yi ta ji an buɗe ƙofar ɗakin.
Ba shiri zuciyarta ta doka tsallen albarka a ƙirjinta har sau biyu.
Dan kuwa ko ba'a faɗa ba, ko ba ta kalla ba, ta san waye, hakan ya sa ba tare da ta ko kalli side ɗin ƙofar ba, ta juya ta ƙara fuskantar mirronrn.
Allah ya sani, sam bata son su haɗu, ba ta son wani abu ya haɗasu, ta na jin kunyarsa da kuma kunyar kanta da ta yi masa mummunar fahimta, tana ta zarginsa game da abun da sam bai aikata ba, me ya sa zuciyarta ta yarda da abun da idanuwanta suka gani?, me ya sa har take zaton shi zai iya aikata wannan mummunar ta'asar?, kaiconta da ta kasance mace me matuƙar san kai.
Satinsu ɗaya da aure, amma fur ba ta yarda su haɗu ko da wasa, kullum za ta yi girki ta aje masa nasa amma ko da kaɗan ba ta bari ya ganta.
Ba za ta iya haɗa ido da shi ba, ta kalli tsabar idonsa tace shi makashi ne, tace za ma ta iya kaksheshi, duk da ba da gaske take ba, amma ai ta faɗa.
Tunaninta ya katse a sanda ta ji tsayuwarsa a bayanta.
Hakan ya sa ta ɗaga idonta ta kalli fuskarsa ta cikin mudubin dake gabanta.
Zaid ya ci gaba da kallonta da lumsassun idanuwansa, tun bayan ranar da ya bayyana mata gaskiyar kasancewarsa ma'aikacin DSS suka shiga wasan 'yar ɓuya shi da ita, wata ƙila kunyarsa take ji, wata ƙila kuma ba ta yarda da abun da ya faɗa ba ne.
Ko ma de me take tunani a kai, shi de be damu ba, damuwarsa ita ce rashin ganinta, nisantarsa da take ya fi sosa masa rai, shi be ƙi a kullum ya kasance da ita ba, ko da kuwa za su ci gaba da zaman doya damanja ne, dole ne ta sama musu mafita, dan shi kam gaskiya ya gaji da wannan tazarar da suke bawa juna.
“Ammatan Raja!”
Rabi ta lumshe idonta sannan ta buɗe, ko a da ma ya ake ƙarewa idan ta ji sunan?, bare yanzu da sunan ya samu ƙari a gaba, ‘Ammatan Raja!’ haka yake kiranta.
Sai ta kasa amsawa, ta ci gaba da kallonsa ta cikin mirrorn.
Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe, ya yi taku ɗaya...
Biyu..
Wanda ya ƙara kusanta shi da ita, sannan ya ɗaga hannayensa tare da zurasu ta ƙugunta, suka kewayo zuwa cikinta, kafin ya jata baya zuwa jikinsa, ya sunkuyo da kansa zuwa wuyanta.
Ba shiri Rabi ta rintse idonta gam, wai me ya sa?, me ya sa duk yadda zai taɓa jikinta irin haka sai ta ji wani sauyi tare da ita,me ya sa?.
“Na yi lefi ne?...
Ko har yanzu ni makashi ne a idonki?”
Ya tambaya muryar ta sa na fita a hankali, Rabi'a za ta iya cewa sai da kalaman suka gama shawagi a kan fatar wuyanta kafin suka isa zuwa ga kunnuwanta, a lokaci guda kuma sai ta ji jikinta ya ɗauki wani irin ɗumi, kamar wata wadda aka kara a jikin kyandir, ko wata ƙofa ta gashi a jikinta ta buɗe.
Amma sai ta ture komai ta girgiza masa kai.
Zaid ya saka hannayensa ya na juyowa da ita, ta fuskanceshi, ya sunkuyar da kansa dan samun damar haɗa ido da ita amma fur ta ƙi barin hakan ta faru, don nata idanuwan kulle su ta yi gam.
“Idan de kika ci gaba da yin abun da kike ɗin nan zan ɗauka cewar har yanzu baki yarda da ni ba!”
Da sauri Rabi'a ta buɗe idonta, dan kuwa gwara ta sha kunya da ace ya ɗauka cewar bata yarda da shi ba ne, a yanzu tana jin wani irin girma da kamarsa na ƙara hauhawa a cikin ranta, wani irin kwarjini yake mata, wanda ba za ta iya kwantanta kalarsa ba.
“Trust me Diary...
Wallahi gaskiya na faɗa...”
Da sauri Rabi ta ɗago da hannunta ta rufe masa baki tana girgiza masa kai.
“I trust you Raj.
And I'm sorry”
Cikin hanzari Zaid ya kai hannunsa ya kamo nata dake kan bakinsa, ya riƙe hannun nata ya na kallon fuskarta da ta fara jiƙewa da hawaye.
“Babu buƙata Ammata, kuskuren fahimta ne”
Rabi ta ja hanci.
“Amma me ya sa to ni na kasa fahimtarka?.
Ya kamata ace na fahimceka Raj...
I'm sorry...
I'm really really sorry...”
Saurin rungumeta Zaid ya yi, hakan ya bata damar sakin kukan dake cin ranta, ta masa kuskure, abun da ta masa sam be kamataba, ta aikata babban kuskure.
“Ka yi haƙuri please!”
Kansa ya ci gaba da girgiza mata yana ƙara ƙanƙameta a cikin jikinsa.
“Wallahi sam ba ki min kuskure ba.
A ko da yaushe ni me miki uzuri ne ko da kin yi laifi, bare kuma ba ki aikata komai ba.
Ba dan komai ya sa na ɓoye miki ba sai dan yanayin aiki, ina kan wani assignment ne yanzu haka”
Rabi ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tana sakin wani kukan, ba ƙaramin ɗaɗi wannan shauƙin yake da ba, me yafi wannan daɗi a duniya?.
Ka kasance a tsakiyar hannun wanda ƙaunarsa ke daddatsa ruhinka a ko da yaushe, wanda shi ma taka ƙaunar ke kai kawo a cikin nasa ruhin.
Me ya fishi daɗi?.
Ta jima a jikinsa tana kuka, kafin ya ɗago da ita yana share mata hawaye, a lokacin ta samu damar kallon fuskarsa, dan haka ta ɗaga nata hannayen ita ma, tare da kamo fuskarsa.
“Ban taɓa faɗa maka wannan ba, amma yau zan faɗa.
I love you...
I love you Raj...”
Da sauri Zaid ya kara fuskarsa kan tata yana sauƙe tagwayan numfashi.
Rabi ta lumshe idonta hawaye wani na bin wani.
“You love me Adawiyya?”
Ya tambaya, dan ya kasa gaskata kunnuwansa, he can't believe, wai yau shi Ammata take cewa tana so?, abun is unbelievable.
Bakin Rabi tale cikin kuka, idonta a rufe ta gyaɗa masa kai, wanda hakan ya sa nasa kan ma motsawa tare da nata.
“I adore you, i love you...”
“Kwatankwacin yaya?”
“Like damn...
Damn much Raj!”
“Alhamdullilah!”
Ya furta yana ɗora lips ɗinsa a kan nata.
“Adawiyya!”
Idonta ta buɗe jikinta na tsuma, saboda yanda ya yi maganar lips ɗinsa na goguwa a kan nata.
“Can i kiss yah?...”
Bai ko ƙarashe ba, ita ta saka hannyenta ta kama fuskarsa, tare da haɗe bakinta da nasa.
Zaid ya saka hannayensa ta bayanta yana ƙara matseta a jikinsa.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*24*
~~~
*Handwriting love letters will never go out of style.*
***
*No.86, Garki 2 , Abuja...*
“Adawiyya!”
Raja ya kira sunan yana shiga ɗakinta, saurin juyowa ta yi, yayin da take fitowa daga bayi, kallonsa take kamar yanda shi ma ke kallonta.
Sanye take cikin wata green fitted wrap shirt, da wani pink capri pants, gashin kanta nannaɗe a tsakiyar kanta cikin bun.
“Ki shirya za mu fita, ina waje ina jiranki”
Ba tare da ya jira abun da za ta faɗi ba, ya juya ya fita.
“Ina jinki Rhoda”
Muryar Zaid ta faɗi a sanda ya ɗaga kiran Rhoda da ya shigo wayarsa, tsaye yake a compound ɗin gidan, ya jingina da jikin motarsa.
Sanye yake cikin wata milk shadda, kansa babu hula, ga wani sunglasses da ya saka a idonsa, ya kuma sauƙo da shi kan hancinsa.
A hankali yake gyaɗa kansa ya na saurarar bayanin Rhoda, don zuwa yanzu sun kusa kawo ƙarshe aikin da suke, saboda haka dole su bi a hankali.