Sashe 25
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na san kaf duniya, babu wanda...
Zai...
Zai iya riƙe Mishal in...
Ba shi ba...
Don haka shi ne mijin nata!...”
Sakan ɗaya...
Biyu...
Uku.
RAJA POV.
A karo na uku ya ƙara jan akwatin dake hannun mutumin da suka zo karɓar kaya a wurinsa, kuma shi ma mutumin kamar ɗazu yaƙi ya saki akwatin.
Raja ya ɗaga kansa sama, sannan ya sauƙe.
“Ka cika gardama, ni kuma ba na san gardama, ka fahimta ?”
“Kuɗin da kuka bamu bai cika ba, don haka sai kun ciko za mu baku kaya”
Mutumin ya faɗi yana kallon idon Raja.
A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa kansa, tare da sakarwa mutumin akwatin.
“Na fahimta”
Ya faɗi yana neman bindigarsa a aljihun wandonsa na baya, kuma yana kamo bindigar, ya fiddo da ita, sannan ya saitata a kan mutumin, bai yi wata-wata ba, ya matsa kunamar.
Ƙaran harbin bindigar ya karaɗe wurin.
Mutum ukun da suka zo tare da wanda aka harba suka yi ƙoƙarin guduwa, amma sai Rhoda da Zuzu dake tare da Raja suka buɗe musu wuta.
A nitse Raja ya sukunya saitin gawar mutumin dake yashe a ƙasa, ya kai hannunsa sannan ya finciki akwatin.
“Kun yi wa kanku, babu kuɗi, sannan babu kaya...
Ko dan ga ta rai ma ai kun yi!”
Daga haka ya miƙe ya juya, Rhoda da Zuzu na take masa baya.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
_“Kamar yanda na maka bayani tun daga farko...
Ina son na fito takarar sanata ne...
Don haka ina buƙatar wasu 'yan kuɗaɗe masu yawa...
Wanda zan yi amfani da su wurin yin campaign, kasan yanda mutanen Nigeria suke!, Kaji ne, sai da tsaba, idan ba su ganka da wani abun duniya ba, ba za su ko kalleka ba, bare su zaɓeka...
Don haka na ce ka dawo kusa da ni....
Don ku min aikin da ya fi wanda kuke yimin shi a garin kano!...”_
Tar muryar Alhaji Bala ke fitowa daga cikin laptop ɗin dake gaban Raja, zaune yake a kan kujerar falo, Rhoda na zaune a gefensa.
Waɗanan su ne ire-iren maganganun da suka yi da shi a ranar da suka tattauna da shi a ganawarsu ta farko.
Ba tare da sanin shi Alhji Balan ba, Raja ya naɗi komai ta cikin wata na'urar ɗaukar hoto da magana, wadda ya saƙala a gaban rigarsa a waccan ranar.
Rhoda ta ɗaga hannunta, tare da bubbuga kafaɗarsa.
“Mun yi aiki me kyau Raja...
Ina tunanin wannan hujjar ma kaɗai ta ishe mu...
Ba ma buƙatar wata...”
Bisa ga mamakinta sai ta ga ya girgiza kansa, ya na jingina da jikin kujera.
“Basu isa ba Rhoda, muna buƙatar wasu”
Cike da mamaki take kallonsa, wata hujja za su buƙata bayan wannan ?, 'yar wannan maganar tasa da suka naɗa wadda ba ta wuce mintuna biyu ba, ita ce ta shigo da su wannan rayuwar da ba ta su ba.
A ganinya wannan kaɗai ta isa ta hutar da su aikin bautar da suka sha tsawon shekaru huɗu.
“Rhoda, ba ni da ke kaɗai Alhaji Bala ya zalinta ba, ya zalinci mutu ne da dama...
Kuma ba shi kaɗai ne yake zalincin ba, har da ɗansa Usman...
Kin san yara nawa Usman ya yiwa fyaɗe ?”
Cike da ƙunar zuciya Rhoda ta girgiza masa kai, dan kuwa maganarsa ta tuna mata da bayanta, rayuwarta ta baya da mahaifiyarta.
Dama abun da ya zamo sanadiyyar rabuwarsu da mahaifiyar tata.
“Kusan yara mata goma ya yi wa fyaɗe!...”
Idonta ta rintse tana kawar da kai.
Raja ya zauna da kyau, sannan ya kamo hannaunta.
“Kada ki damu, za mu ga ƙarshen komai, za su kwashi kashinsu da hannayensu, sai an ƙwatawa kowa hakkinsa...
Ba ni...
Da ke kawai ba...
Kowa Rhoda, i mean each and every body da suka taɓa zalinta”
A hankali wata ƙwalla ta sauƙo daga idon Rhoda, ta kwantar da kanta a kafaɗar Rajan, shi kuma ya shiga bubbuga bayanta, alamun rarrashi.
A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cikin faɗin.
“Wannan hujjar ta yi kaɗan mu kai babban mutum irin Alhaji Bala ƙasa, muna buƙatar hujjojji masu tarin yawa, waɗan da ba wai ƙasa kawai za su kai shi ba, rugu-rugu za su yi da shi...
Za mu kai masa wannan kayan, kuma kin san daga haka zai ƙara yarda da mu, mu kuma daga haka za mu ƙara ƙaimi wurin kai shi ƙasa!”
Rhoda ta share hawaye, tana yarda da maganar ɗan uwanta ɗaya tilo da ya rage mata a duniya, tun da har ya faɗi tasan zai cika, zai aikata duk abun da yace...
A idanunsa kawai take hango irin faɗi tashin da ya riƙa yi a rayuwarsa don kawai ya ga ta samu gobe me kyau.
“Lokacin sallah ya yi, zan je masallaci”
Ya faɗi yana miƙewa, sannan ya dafa kanta, ya fice daga falon.
A balcony ya haɗu da su Zuzu.
Suna zaune sai zuƙe-zuƙensu suke.
Wutar da ya hango a jikin tabar Jagwado ce ta sa hayyacinsa ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinsa.
Suma kuma sai a lokacin suka lura da shi, don haka suka yi saurin kashe wutar dukansu, dan sun san matsalarsa da wuta.
Sun san halin da yake ciki, shi yasa ba sa shaye-shaye a kusa da shi.
Saboda suna sonsa, suna sonsa Saboda yanda ya temaki rayuwar kowannensu.
Sai da Raja ya dafe bango, sannan ya dawo hayyacinsa, da ƙyar ya kallesu.
“Lokacin sallah ya yi, ku tashi muje ku yi...”
“Ai kasan ba ma je gaban Ubangiji muna warin wuwu ba ko...
Oga Raja ka bari sai mun ɗan eh yi wanka...
Ka gane ko?...”
Cewar Alandi yana miƙewa.
Yanda yake magana kawai ya tabbatarwa da Raja cewa sun bugu, ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarasa, ya sauya komai a tare da su, wannan shaye-shayen ne ya kasa hanasu yi.
Amma ya ƙudircewa ransa cewar, suna gama wannan aikin zai sada kowannensu da Rehab.
Agogo ya duba, ya ga lokacin tashin ɗaliban makarantar nan ya kusa, dan haka a gurguje ya ƙarasa masallacin estate ɗin.
Ya yi sallah, sannan ya fita ya tsaya a inda ya saba tsayawa don ganinta.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja..*
MISHAL POV.
Tsaye take a tsakiyar abokan koyan faɗanta na Kungu fu.
Sanye take cikin uniform 🥋 ɗin koyar da wasan kungu fu ɗin, ta ɗau matsayarta.
Yayin da hannunta na dama ke dunƙule ta seta yarinyar da aka haɗasu faɗan, ɗayan ma a dunƙule yake amma a ƙasa.
Ɗaya yarinyar ce ta kawo mata duka, hakan yasa cikin salon faɗan na kungu fu ta ware hannunta na dama, ta kama hannun yarinyar, tare da banƙara shi, ta rataya hannun yarinyar a kafaɗartsa, sannan ta kaiwa yarinyar bugu a gefen ciki da hannunta na hagu.
Tini yafinyar ta shiga ɗaga hannunta, alamun saduda.
Mishal ta saketa, hakan yasa hall ɗin koyon wasan nasu ya karaɗe da tafi, ita ce ta yi nasara kamar kullum.
Cike da girmamawa ta miƙawa malamin kungu fu ɗin nasu gaisuwa, sannan ta ja baya.
Malamin nasu ya ɗan musu wasu jawabai a kan wasan, sannan aka sallami kowa.
Ita ta koma jikin lokarta inda ta saba aje kayanta ta sauya kayan, sannan ta damƙawa Angelica riƙon jakarta, suka fito a tare.
Sai da ta je wurin Adawiyya suka yi sallama, sannan ta karɓi jakarta a wurin Angelica, tare da sallamarta, ta shige mota, Baba Ali ya tayar, suka fita daga makarantar.
Kamar jiya yau ma sai da ta ga Kuliya tsaye a jikin gate ɗin estate ɗin nan, to wai shi wannan me yake zuwa yi nan ?, ta tambaya kanta.
Sai kuma ta share, tare da faɗawa kanta cewar; to wai ina ruwanta ma?.
Har suka kai gida tana shan hannu.
Fita ta yi daga motar, a sanda suka iso gidan, ta shiga cikin gidan, Daala ta samu ita da Mama Ladi suna wasa a falo, kai tsaye sama ta wuce, ta shiga ɗakinta.
Abu na farko da ta fara yi shi ne, aje jakarta a kan work table ɗinta, sannan ta shiga wanka ta fito, ta sauya kaya zuwa wata yaluluwar shift dress, rigar bata sauƙa har ƙasa ba, bakinta kan singalinta.
Ta nannaɗe gashin kanta cikin bun, tare da saƙala wani hair pin ɗinta me shape ɗin bow.
Da saurinta sauƙo zuwa ƙasa, sannan ta faɗa kitchen dan ta samawa kanta abun da za ta ci, duk da ta ga abinci a kitchen ɗin, amma alƙawari ne ta ɗaukawa kanta cewar ko yunwa za ta kasheta ba za ta ci abincin da Hajjara ta girka ba.
Jallof ɗin rice stick ta shiga yi, babu jimawa ta gama, sannan ta dawo ta zauna kusa da su Daala ta soma ci.
Loma ta uku kawai ta yi, wayar landline ɗin dake falon ta yi ringing, hakan ya sa ta aje bowl ɗin hannunta, ta miƙe tsaye ta na ɗaukan wayar.
“Hello!”
Ta faɗi a sanda ta kara wayar a kunneta, muryar kawu Musa ce ta doki dodon kunnuwanta, cikin kuka da shessheƙa.
“Hafsat ke ce ?”
Gabanta ya faɗi, amma sai ta dake tace.
“Eh Ammu(Kawu)...
Ni ce”
“Ina Hajjara?...”
Sai ta kalli falon, kamar me neman Hajjaran a falon, sannan ta kalli danning area tana amsa ma sa da:
“Ba ta kusa”
“To ki sanar mata da ku yi maza-maza ku taho International Hospital, Abubakar ba lafiya!...”
Duk rashin hankalinta, da ƙarancin shekarunta a duniya ta san cewa jinya kawai ba za ta saka babban mutum kamar Ammunsu kuka ba, dole akwai wani abu dake faruwa da yayanta mara kyau, kk mutuwa ya yi ?!.
RABI'A POV.
Kamar yanda ta saba ganinsa jingine jikin gate ɗin estate ɗin nan, yana kallonta da lumsassun idanuwansa.
Yau ma haka ɗin ne.
A memakwan kullum da ta saba wucewa ba tare da ta masa magana ba, yau sai ta ɗago masa hannu, sannan ta yafito shi.
Sai da gaban Raja ya faɗi, ganin yanda ta kira shin, amma sai ya dake, ya fara takawa zuwa gabanta.
A lokacin da ita kuma ta hau hanya ta fara tafiya, kamar jiya sai ya fara binta a gefe.
“A can kake da zama?”
Bayan ɗan wani lokaci ya ji ta tambaya.
Sai ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan ya amsa mata da.