Sashe 22
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta yi zaton zata ce mata tana da wa na miji, amma ba ta ji hakan ba.
Kuma rashin jin hakan ne yasa ta ɗora ayar tambaya kan lamarin, duk yanda aka yi Adawiyya ta haɗa jini da abokin yayanta.
Dan kamar ta wuce kama haka kawai.
Sai mamakin son sanin abin da ya kawo shi wurin ya kamata, me yake a nan ɗin?, sannan me yasa yanayinsa ya sauya ?, duk da a sanda ta ganshi yana cikin halin jinya, hakan bai hanata ganin buɗar idonsa ba.
Sai dai yau kuma idon nasa kusan a lumshe suka.
Ko dai ba dhi da lafiya ?.
Da saƙe-saƙen nan a ranta har suka bar layin suka hau kan titi.
Rabi na fita daga gate ɗin makarantar idanuwanta suka hango mata shi tsaye daga can tsalleka, ya jingina da jikin bango, sanye yake cikin wata orange T-shirt, da farin chinos trouser.
Hannaynesa duka biyu sanye cikin aljihun wandonsa.
Waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallonta ƙasa-ƙasa.
Kusan kullum a kwanakin nan sai ta ganshi tsaye a wurin, ba ta san me yake ba, amma kamar jikinta na bata cewar bibiyarta yake, ko kuma yana tsayawa ne a wurin kawai dan ta fito ya ganta.
Kanta ta ɗauke, tare da gyarawa ledar hannunta riƙo.
Ba tare da ta sake kallonsa ba, ta kama hanyar da ta saba bi.
Sai da Raja ya gama ƙare mata kallo, zuciyarsa na faɗa masa abubuwa da dama a kanta, kafin ya ga ta kama hanya tana tafiya.
Wani abu daga can ƙasan zuciyarsa yace masa kawai ya bita.
Bai yi wata-wata ba wurin bin umarnin, ƙafafuwansa suka soma takawa cike da nutsuwa.
Har ya kai kusa da ita, a yayin da suka ci gaba da tafiya tare.
Rabi ta yi saurin juyowa ta kalle shi, jin an tsaya kusa da ita, wannan fuskarce dai, mamallakin fuskar ne ke biye da ita.
Sai dai ba ita yake kallo ba, hanya yake kalla, kuma har zuwa lokacin hannayensa cikin aljihu.
“Sannu Ammata!”
Wannan salihar muryar tasa ta furta ya na ci gaba da kallon hanya, sai da gaban Rabi ya faɗi, saboda yanda amon muryar tasa ya kunna wata jiniya a cikin kanta.
Ta haɗiye wani abu sannan tace.
“Sunana Rabi'a...”
“Na sani ai, Ammata!”
Ya yi hanzarin katseta.
Rabi ta ɗauke kai tana kallon hanyar ita ma.
“Daga ina kike zuwa nan ?”
Ya tambaya yana ɗaga kafaɗarsa ta dama, tare da zaro hannunsa na dama daga cikin aljihu, ya kaishi bayan wuyansa, saitin inda tatto ɗin kan zaki yake, yana sosawa.
Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, sannan ta amsa da.
“Unguwar Madallah, Suleja!”
Ta lura da yanda ya ɗan tsaya da tafiyar da yake, kafin kuma ya ci gaba, sai a yanzu ya kalleta tun bayan da ya tsaya kusa da ita.
“Kusan tafiyar muntuna arba'in fa kenan ?”
“Umhum”
Ta amsa da ɗan sakewa, ba kamar yanda suka fara hirar ba.
“Amma me yasa kike zuwa nan ?”
Rabi'a ta ɗan sunkuyar da kanta ta kalli yatsun ƙafarta, sannan tace.
“Aikin shara da goge-goge nake”
“Ba kya zuwa makaranta ?”
Ya kuma tambaya.
Sai ta gyaɗa kanta.
“Eh, ba na zuwa..”
Ta ba shi ahi amsa a dai-dai lokacin da suka iso bakin titi, sai ya dakata, hakan yasa Rabin ma dakatawa.
Shiru ya ratsa tsakaninsu na 'yan wa6sy muntuna...
Kafin Raja ya ɗaga hannunsa ya tsayar wani mai mota, sannan ya buɗe mata gidan baya.
“Zo ki shiga 'yan mata!”
Rabi ta kalleshi,sannan ta kalli motar.
“Akwai bus...”
“Ammata ba'a mun musu, just enter, kin fahimta ?!”
Rabi'a ta haɗiye wani abu, dan ya yi maganara ne yana kallonta da ƙwayar idonsa da take gray color.
Ta tara yaɗonta gu ɗaya, sannanta shiga bayan motar, ciniki suka yi da mai motar, ya zaro kuɗin ya biya, har da haɗa shi da gargaɗin kada ya ɗauki wani bayan ita, sannan kada ya yi gudu da ita.
“Sai gobe 'Yan mata”
Ya faɗi sunan in full, saɓanin da da yake faɗarsa a wata sigar.
Rabi'a ba ta iya ce masa komai ba, sai hannun da ta ɗaga masa.
Motar ta fara tafiya, zuciyarta na ƙara cika damamaki da tunanika iri-iri.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
Tsaye suke a ɗakin tattaunawa na headquartern, yayin da ya buɗe musu map ɗin wurin da za su wa dirar mikiya a yau ɗin nan, don a yau aka basu damar kamo 'yan ta'addan da suke bincike a kansu.
Sharon, Kamis, Sani, Mubarak, Symon da kuma shi kansa, su ne tsaye, kana kewaye da teburin da taswirar ke kai.
“Wannan ita ce hanyar shiga gudan...
Ta nan za mu shiga, akwai ƙofa ta baya, dan haka za su iya guduwa idan suka gane cewa muna cikin gidan...
Dan haka Ab...”
Bai ko ƙarasa furta sunan Abubakar ɗin ba, Abubakar ya turo ƙofar ya shigo, a tare suka ɗaga kai suka kalleshi.
A gurguje ya ƙaraso ya tsaya a jikin teburin shi ma.
“I'm so sorry guys, cinkoson ababen abun hawa ne ya makarar da ni”
Kuliya ya haɗiye wani abu, a sanda ya ɗora idonsa a kansa, kammaninta suka faɗo masa a rai.
Yarinyar nan ta rakurawa tunaninsa, ya gaji!, me yasa wai take damunsa ne ?.
Sai ya ɗaga kafaɗarsa, sannan ya juya ya ci gaba da kallon taswirar.
“Abubakar kai da Symon za ku tsaya ta nan, ni da Sharon, Kamis da Sani, za mu shiga...”
Bai ƙarasa ba Abubakar ya dakatar da shi, ta hanyar furta abun da zai zama sanadiyyar faruwar ƙaddarar da Allah ya hukunta a wannan ranar.
“Me zai hana ni da kai, Sharon, Kamis da Sani, mu shiga cikin gidan, Symon da Mubarak sai su tsaya a ƙofar baya!...”
Cike da gamsuwa Kuliya ya gyaɗa kansa.
“Well, hakan ma ya yi, Good to go guys!”
“Yes Sir!”
Suka amsa kusan a tare, sannan suka yi azamar fitar.
*Abacha Road, Abuja...*
Motoci ne guda biyu suka yi parking a ƙofar wani madai-daicin gida, cikin gaggawa ƙofofin motocin biyu suka buɗe a tare.
Kuliya, Mubarak, Sharon, Kamis, Symon, Sani da Abubakar suka fito, kowannensu sanye da baƙaƙen kaya irin na aikinsu, jikin bullet proof jacket ɗin kowanne daga cikinsu an rubuta 'DSS' da farin rubutu.
Kowanne a cikinsu hannunsa riƙe da bindiga, Kuliya ne ya yi wa Symon da Mubarak alama da su zaga ya ta bayan gidan, cikin sassarfa suka bi umarninsa.
Shi da sauran kuma suka nufi cikin gidan.
Shi ne kan gaba, su kuma biye da shi.
Daga cikin gidan kuma, mutum biyar ne zaune kan kujeru, baje a gabansu kayan maye ne kala-kala, mace ɗaya ce a cikinsu, yayin da sauran suka kasance maza.
“Chizoba, wai ka biya me tifar nan da ya kaɗe Kuliya ?”
Ogansu dake zaune kan kujera ya tamabaya cikin harshen igbo.
Chizoba ya amsa masa da:
“Eh mana, dubu talatin na bashi”
Ogan ya yi dariya, yana hango nasarasu a cikin idanuwansa, a sanda suka sauƙa a garin sai da aka sanar musu da cewar wani wai shi Kuliya zai kawo musu cikas.
Kuma da suka bincika sai suka samu cewa ma a kansu yake bincike, hakan yasa suka saka wani me tifa ya daki motarsa, a sanda ya tashi daga wurin aiki.
Yanda suka ga motarsa ta yi raga-raga ne yasa suka ɗauka cewar ya mutu.
Babu wani mai basu matsala kan aikin da ya kawo su garin Abuja.
A tunaninsu kenan, sai dai cikin abin da bai fi muntuna uku ba, komai ya sauya.
Gidan ya karaɗe da ƙarar harbe-harbe.
Daga waje babu abin da ke tashi sai ƙarar musayar wutar da ake tsakaninsu da su Kuliya.
Kuma a cikin musayar wutar ne, ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya aikowa da Kuliya harbi, kasancewar shi bai lura ba, yansa harbin bai same shi ba, Abubakar da ya ankara ne ya hankaɗashi gefe.
Shi kuma harbin ya same shi a ciki!.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
RABI'A POV.
_🎶Bari ki ji, ki zauna_
_Batun so na zana_
_in zanyi batun ƙauna, za ki shigo labarina_
_Na zaga duniya_
_Ko wacce nahiya, na zamma jan wuya, amma kin saita ni da ƙauna🎶..._
Waƙar Idan babu ke, wadda Umar Mb ya rera ce ke tashi ta cikin wayar Anti Saratu, wadda ke kwance ta na sauraren waƙar, yayin da take daddana wayarta.
Daga can gefe kuma Rabi ce ke gogewa kayanta, Fatima kuma na daga ɗayan ɓarin tana tsifar kai, daga cikin ɗakin Habiba kuma, Mahmud ne kwance yana bacci, yayin da ita kuma Habiban ke bakin ƙofar ɗakin, ta na kaɗa wani abu a cikin kofi.
Ɗaya daga cikin magungunan da Malamin yayarta ya bata ne, kuma yace a haɗa da madara, ta sa an siyo mata madarar, shi ne yanzu take haɗawa, zuciyarta cike da fatan kasancewar abin da take fata.
“Anti Saratu Yaya yace min jiya an yi wasa” Cewar Rabi, tana motsa iron a kan kayanta.
Daga kan katifa, Anti Saratu ta ɗan kallota sannan tace.
“Ko na baki ki je ki turo ?”
Da sauri ta gyaɗa mata kai.
Anti Saratu na murmushi ta miƙe zaune, sannan ta kashe waƙar ta miƙa mata wayar.
“Dan Allah ki ce masa nima ya saka min sabbabin fina-finan indian hausa guda uku...
Nawa zan bada ?”
Rabi'a na saka hijabi ta yi dariya.
Kullum idan za ta je turi shagon Yaya Sai Anti Saratu tace za ta biya kuɗi, shi kuma baya fasa cewa ba zai karɓa ba.
Ta karɓi wayar tana faɗin.
“Ni na gaji da garan bawul ɗin da kuke da ni, nasan cewa zai yi an yafe miki, dan haka ki bar kayanki”
Anti Saratu ta yi murmushi tana kwanciya.
“An ji asara dai, daga bin maza sai kallon wasan maza, mtswww!”
Cewar Fatima tana makowa Rabi harara, Rabi'a ta juyo ta kalleta, du-du-du a shekaru Fatiman ba za ta wuce 14 ba, amma yanda take mata rashin kunya kai kace sa'arta ce.
“Fatima!
Ba na hanaki yin wannan rashin kunyar ba?
Ko Rabi'a sa'arki ce?...”
Rabi'a ba ta tsaya ta gama jin faɗan da Antu Saratu ta fara ba ta kaɗa kanta ta fita.
Tana saka takalmi suka haɗa ido da Habiba.
Ba tare da sanin daliliba ta ji gabanta ya faɗi.