Sashe 53
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma gashin kanta da ya lura da kamar sun rage masa tsayi, duk da shi bai taɓa ganin gashinta ba, amma ya yana da yaƙinin cewa gashin kan nata ba haka yake ba, kuma ya fahimci kamar saboda raunukan dake kanta aka rage yawan gashin.
Idanuwanta a rufe, fatar bakinta ta yi fari sol, a kallo ɗaya idan ka mata sai ka ce maccacciya ce, shi kansa ba don Huzaifa ya tabbatar masa da tana raye ba da ba zai yarda da tana da ran ba.
Jikinta sanye yake da rigar asibitin, wadda take blue colour, sai farin bargon asibitin da aka rufa mata a rabin jikinta.
Ya tuna yanayin murmushinta, ya tuna sanyin maganarta, ya tuna nutsuwarta, ya tuna hankalinta, ya tuna yanda take kallonsa da idanuwanta masu kama da na Aliyu, ya tuna komai a kanta, hatta da ranar da ya fara ganinta sai da ya tuna.
Idonsa ya rintse a sanda hoton file ɗinta da ya buɗe a ɗazu ya dawo masa cikin tunani, wai mutum biyar ko sama da haka ne suka mata fyaɗe, sannan bayan haka ma harda raunikan a jikinta, ga kuma dukan kanta da aka yi, wanda shi ne maƙasudin shigarta doguwar suma.
A hankali ya buɗe idanunsa nasa, wanda ya yi ja kamar sabon barkwano.
A dai-dai lokacin Rhoda da ya aika ta shigo ɗakin, juyawa ya yi ya kalleta, a sanda ta ke ƙarasowa ciki.
Sai kuma ya ɗauke kansa ya na dawowa da dubansa kan Rabi'a.
Ya ɗaga kafaɗarsa kafin yace.
“Me kika gano?”
Ya tambaya cikin wata murya me ɗaci, Rhoda ta haɗiye yawu sannan tace.
“Na yi magana da waɗanda suka tsince ta a lokacin, kuma su ne suka kawota wannan asibitin, amma su... sun ce a gefen hanya suka ganta, nannaɗe cikin bargo, ko...
Ko...
Tufafi...
Ba...
Babu a jikin... jikinta!...”
Raja ya rintse idonsa, jikinsa har karkarwa yake, ga kuma hannun Rabin da ya ƙara damƙewa cikin nasa, Allah ne kaɗai ya san yanda zuciyarsa ke tafarfasa, shi kansa ya na mamakin yanda yake iya riƙe kansa a wannan lokacin, amma shi ya riga da ya san kansa, ba ya iya ɗaukar ɓacin rai, ya kan jima ransa bai ɓaci ba, don ba komai ne ke ɓata masa rai ba, amma idam har ransa ya ɓaci to na kowa ma kan iya ɓaci.
“Bargo?”
Ya tambaya ya na ɗan juyowa da kansa ya kalleta.
“Eh bargo, kuma sun ce wata ƙila ma a kan bargon aka haike mata...
Saboda sun... sun ga...”
Yanzu kam miƙewa ya yi tsaye, kuma ba tare da ya damu ba ya nufi kan wata chest drawer, ya kai hannunsa ya yi fatali da kayan kai, ƙaran abubuwan da suka fashe sai da suka razana Rhoda.
Da gudu ta yi kansa ta na riƙeshi.
“Zaid!, Zaid!
Ka nutsu, ka nutsu ka ji”
Ta faɗi hawaye na mata zuba, yayin da take bubbuga kafaɗarsa.
Ƙofar ɗakin aka turo, wata nurse ta leƙo da kanta.
“Lafiya kuwa?”
Rhoda ta juya ta kalleta.
“Lafiya, mun gode, za ki iya tafiya”
Nurse ɗin ta taɓe baki ta na jan ƙofar, da ma wucewa ta zo yi ta ji ƙara, shi ya sa gulmarta ta motsa, har ta kaita ga leƙowa don ganin meke going.
“Ka nustu ka ji?”
Cewar Rhoda ta na shafa ƙirjin Raja, wanda yake huci kamar wani zakin da ya je farauta bai samo komai ba.
Hannunsa ta kama ta zaunar da shi a kan kujera, tana shafa kansa.
Idonsa ƙir a kan Rabi, wani abu me ɗaci yana kai kawo daga maƙogwaronsa zuwa bakinsa, ga wani ɗaci da zafi da ransa ke masa, ji yake kamar wuta ce kr ci a ƙirjin nasa, kamar da aka tsire zuciyarsa a tukubar tsire.
“Ga shi...
Karɓi ka sha”
Kansa ya ɗan ɗaga ya kalli Rhoda dake miƙa masa cup ɗauke da ruwa.
Karɓa ya yi ya sha, a lokacin da ita kuma Rhodan take zama a kusa da shi, hannunta ta kai ta share hawayenta.
“Wannan ba shi ne mafita ba Zaid, kamata ya yi a ce ka yi tunanin mafita ba wai fusata ba, akwai ranar da za mu huce haushinmu a kan wanda suka aikatawa Ammata haka”
Ya juyo ya kalleta ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, mafita?
Tabbasa ta na da gaskiya, haka ya kamata ace ya kasance, kamata ya yi ace ya nemo wata mafitar da za su iya kama masu lefin, dan a nan me lefin ba ɗaya ko biyu ba ne, mutum biyar ake zargi, wata ƙila ma sama da haka.
Hannunsa na dama ya dunƙule ya ɗora a kan bakinsa, sannan ya rufe idonsa dan samun nutsuwa, ta yanda zai yi tunani me kyau.
Kusan shuɗewar mintuna goma, sannan ya buɗe idonsa.
“Shin kin tambayesu da bargon suka kawota nan?”
Rhoda ta ɗan kalleshi.
“Idan ba da bargon ba to da ne za su kawota nan ɗin?”
“Correct, makamar mu ta farko kenan, ki tambaya mana Huzaifa, shin har yanzu wannan bargon ya na nan?, In har ya na nan, to wannan bargon shi ne madafarmu, ta hanyarsa za mu iya kama masu lefin”
“Ok”
Raja ya juya ya ƙara meda idonsa kan Rabi'a.
“Wallahi!, Wallahi!, Wallahi!
Rhoda idan har...
Na kama me laifin nan, ba zan sassauta masa ba, sai na tabbatar da na gana masa azabar da tun da uw*rsa ta kawo shi duniya ba'a taɓa masa ba, sai na tabbatar da ya yi wata ɗaya ba tare da ya ga hasken rana ba, sai na tabbatar da ya kwana a cikin fitsarinsa, sai na tabbatar da bai ƙara ko da kusantar macen da ba ta hallata gareshi ba, sai na ɗai-ɗaita rayuwarsa, wannan alƙawarina ne!”.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
Tana zaune a bakin gadonta, yayin da take cire sliders ɗin ƙafarta, ƙafafun nata ta ɗauke daga ƙasa, ta ɗorasu a kan gado, tana jan bargo dan rufe ƙafafunta nata, aka turo ƙofar ɗakin.
Kallon ƙofar ta yi, a sanda Kuliya yake shigowa, ganinsa ya sa ta fasa kwanciya ta zauna, cike da mamaki take kallonsa.
“Me ya faru?”
Ta tambaya.
Ba tare da ya amsata ba, ya zagaya ta ɗayan ɓangaren gadon ya zauna, ya na cire takalman ƙafarsa.
Mamakin dake kan fuskar Mishal a yanzu ya ma fi na ɗazu, ido waje take kallonsa.
“Wai...
Wai me yake faru?...”
Ba ta ko ƙarasa faɗin kalaman ba, ya janyota jikinsa, tare da kwantar da ita.
Idanuwanta suka ƙara girma wajen kallonsa.
Wai me bawan Allahn nan yake nufi da ita ne?, me yake shirin yi haka?.
Sakata ya yi a tsakiyar hannayensa, ya kwantar da kanta a ƙirjinsa, ya matseta a jikinsa sosai, har wata ajiyar zuciya yake sauƙewa.
“Ab...
Abu Aswad”
Kafaɗarsa ta dama ya ɗafa yana ƙara kewaye hannunsa dake jikinta.
Alamun dai ya na jinta.
“Me ya faru?”
Ta tambaya ta na shaƙar ƙashin turarensa.
“Babu komai, kawai de ba zan iya ba ci ba tare da matata ba ne”
Muryarsa ta furta hakan a hankali cikin duhun daren.
Shiru ya ƙara rasta ɗakin, jin yanda yake sauƙe ajiyar zuciya, ya sa Mishal saka hannayenta ta kewaye shi ita ma.
“Abu Aswad”
“Ummm Teddy Bear”
“I hate you”
Tana jin sautin murmushinsa a kanta.
“And i love you”
“I hate you ”
“I said i love you”
Kusan a tare suka yi dariya.
“Gobe akwai school, ki kwanta ki yi bacci”
Kwanciyarta ta gyara a jikinsa tana lumshewa idonta.
*One hug fixes everything...*
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja.*
RABI'A POV.
_“Na roƙe ku da girman Allah da kada ku taɓamin mutuncina, dan Allah, dan Allah kada ku haikemin!...”_
_Irin magiyar da ta riƙa yi wa samarin nan da suka saceta kenan a waccan ranar, babu kalar magiyar da ba ta musu ba, amma haka suka shiga da ita cikin wani gida, suka danganata da ɗaki._
_Duk da tashin hankalin da take ciki a wancan lokacin, bai hanata gane fuskokinsu ba, su biyar ne cas, sannan ɗaya bayan ɗaya ta na da hoton kowannensu a cikin kanta.
Miƙewa ta yi kan gwiwoyinta a kan gadon da suka cillata, sannan ta haɗe hannayenta ta na binsu da kallo, hawaye na mata zuba._
_“Dan Allah, dan Allah, na roƙeku da Allah da kada ku aikata min haka...
Dan Allah kada ku keta min martabata, dan Allah, na haɗaku da Allah, Wallahi ba ni da kowa, ba ni da komai, yanzu haka rayuwata ta na cikin wani hali, dan Allah...”._
_Kalaman suka tsaya a maƙoshinta, sakamakon ganin da ta yi kowanne a cikinsu ya na cire tufafin jikinsa, basu damu da ko kallonta ba, ballantana su saurari abun da take faɗi. kukanta ta ƙarawa ƙarfi ta na rintse idonta._
_“Wai me ya sa mutane ba su san Allah ba?
An haɗasu da Allah amma sai ka ce da wani sheɗan aka haɗasu, me makon mutum ya bar abun da yake sai ma ya ƙarawa abun ƙaimi, dan Allah na roƙeku...”_
_Ta ci gaba da roƙonsu, a lokacin da Usee yace._
_“Kai duk ta bi ta cika mana kunne, dallah kusa ta yi shiru!”_
_Jaz ne ya ɗauko ƙarfen abun shisharsu me kauri, ba tare da Rabi ta ankara ba, saboda idanuwanta da suke a kulle, ta ji sauƙar yankan wani abu me kaifi a gefen fuskarta, hakan ya sa ta buɗe idonta da sauri, wani kalar raɗaɗin azaba ya ziyarci ƙwaƙwalwarta, nan take ta ƙwala wani uban salatin da sai da gidan ya amsa, gefen fuskar tata ya yanku ba kaɗan ba._
_“Kai dallah mahaukaci!
Cewa na yi ka sata ta yi shiru ba wai ta ƙara volume ba!”_
Cewar Usee ya na rarumar wata vase, sannan ya ɗaga ta sama, ya bugawa Rabi a tsakiyar kanta.
Nan take Rabi ta ji wani dimmm, kamar injinan da suke aiki a kanta sun dena, komai ya tsaya cak, babu wani abu dake aiki, kan kace me, jini ya wanke mata fuska.