← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Muje Gumalti, daga can sai mu wuce gidan zoo”
Kwaisen ta faɗa tana kallon Arman dake zare wani zare daga kan Narjis, 'yar iqra ƙanwarsa dake zaune kan cinyarsa.

“Shikenan, yarinya sai ta tanadi kuɗin da za ta kashe, an jima za mu fita!...”
Arman ya faɗa da ɗan ƙarfi, dan sauran 'yan uwan nasa su ji.

“Ni dai ba wani kuɗi da zan fitar, ina aljihunka”
Cewar Iqra.

“Alƙur'an ba ki isa ba, ga mijinki ai, sai ya biya miki”
Iqra ta juya ta kalli mijinta Adam da suke cin abinci tare.

“Rabu da shi Babe, sai mun kashe sama da abun da zai kashe”
Adam ɗin ya faɗi cikin sigar zolaya.

“Aki, za mu tsaya a hanya na sai fara ”
Cewar Ijaz, yayin da yake cusa abinci a bakinsa.

“Hello!

Ban da ni za'a je?!”
Wannan muryar ta faɗi daga bakin ƙofar falon, gaban Mishal ya yi tsalle ya hau kan mountain ever rest sannan ya diro ƙasa.

Kallon fuskarsa kawai babban tashin hankalinta ne a duniya, kasancewar a duk sanda za ta kalli fuskarsa ma sai wannan lokacin ya haska a cikin kanta.

Bata da tsoro, amma shi tana tsoronsa, ba ma shi kaɗai ba, duk wani abu da ya dangance shi tsoro yake bata.

Ta zabura za ta miƙe tun kan ma ya ƙarasa shigowa cikin falon, Arman ya yi sauri ya riƙe hannunta yana mayar da ita ta zauna.

Sannan ya juya ya kalli Yazid ɗin da ya shigo falon.

“Yazid fita!”
Arman ɗin ya furta a dake...

Cikin kakkausan amonsa irin nasu na sojoji, babu alamun wasa ko kaɗan a fuskarsa, ya dake ya koma ainahinsa na soja.

Sai da kowa ya jiyo ya kalli Arman ɗin, sannan kuma suka kalli Mishal da jikinta ke ɓari, sai ɓuya take a bayan Arman.

“Ai ba.....”
“Ka juya na ce!”
Arman ɗin ya faɗi ya na aje Narjis kusa da Mishal ɗin da numfashinta ya fara yin sama.

“Ok...”
Ya faɗa yana juyawa, babu wani alamun nadama ko kunya a tare da shi, dan ya ci bulis, duk da bai mata komai ba a lokacin, kuma a ganinsa ko da ya mata wani abun babu abinda zai faru, tun da shi na gida ne.

“Ki nustu Mishal, ya tafi, ba ya nan...”
Adam ke faɗi yana san kwantar da ciwon nata, kasancewarsa likita.

Idanuwanta sun fara yin sama, ga yanda numfashinta ke fita wani iri.

Abubakar da Arman na gefenta suna mata fifita.

A hankali-a hanakli hayyacinta ya dawo jikinta, sai sauƙe ajiyar zuciya take a kai-akai.

“Kin sha maganinki yau ?”
Arman ya tambaya.

Kanta ta girgiza masa, shi kuma sai ya gyaɗa mata kai, tare da juyawa ya kalli Kwaise.

“Duba ɗakinta ki ɗauko min jakarta...”
Kwaise ta miƙe tana faɗin to.

Hanin Mishal ɗin ta dawo hayyacinta yasa kowa ya koma ya zauna, Mushal ta cure gu ɗaya tana saka babban ɗan yatsanta na dama a baki, tare da fara shan hannun a sace.

Dan bata san wani ya gani.

Ko Abubakkar da sha hanata shan hannun, amma ba ta iya denawa, duk da takan jima bata sha ɗin ba, amma duk sanda zai faɗo mata a rai sai ta sha.

“Wai ke Baby har yanzu baki san cewa kin girama ba?...

Da ma har yanzu kina shan hannu ?”.

Da sauri ta cire hannun na ta ta na turo baki, tare da juyawa Arman ɗin kai.

Arman ya yi dariya.

“Abubakar me yasa baka kaita an cire mata wannan braces ɗin ba ?” Cewar Arman ɗin ya na duban Abubakar.

Abubakar da ke magana da Adam a kan ciwon Mishal ya ɗago ya kalle shi.

“Sai mun koma za mu je a cire mata, dan na ga gap ɗin sun haɗe...”
“Na kwaise kuwa har yanzu ba su haɗe ba”
Cewar Ijaz.

“Ai ba'a wani jima da saka mata ba shi ya sa, na Mishal ɗin fa ya kai shekara biyar, kawaise kuwa ai ko shekara uku bai yi ba”
Arman ya ba shi amsa.

Haka hirarrakinsu suka ci gaba da wanzuwa, har zuwa sanda Kwaise ta dawo riƙe da jakar maganin Mishal, Arman da kansa ya bata.

Sannan suka ci gaba da hirar, har zuwa yamma, kowa ya sake kwalliya suka fita zaga gari da yawon gidan 'yan uwa.

RABI'A POV.

A yau ne aka dawo makaranta, don haka ita ma ta shirya da wuri, ta kama hanyar makarantar, Kuma bayan ta je ta gama aikinta, sai ta shiga shawagin duba Mishal, amma haka ta gama shawagin nata ba tare da ta ganta ba.

Wata ƙila ba ta dawo ba, haka ta faɗawa kanta tana juyawa da ga tsayuwar da ta yi a ƙofar ajin su Mishal ɗin.

Daga nan kuma ta wuce ɓangaren ta wuce ɓangaren sport na makarantar, ta tsaya a wurin da ake buga ball.

Tana kallon yaran da ke cikin raga suna ta buga ball ɗin.

Ƙafarta har ƙai-ƙai take mata, dan ji take kamar ta shiga cikinsu su buga tare da ita.

Gani take kamar ba dai-dai suke wasan ba.

Kamar idan ta shiga cikinsu za ta iya yin abinda ya fi wanda su suke yi.
_“Yaya Baby, ba haka ake ba.....ki tsaya na nuna miki yanda ake...”_
Tunawa ta yi da wani lokaci da ya wuce a can baya, lokacin da suke buga ball ita da Baby a garden ɗin gidansu na da.

Gidan da rannan Habiba ke sanar mata da cewa Babansu ya siyar da shi.

Don wasu daga cikin kadarorin mahaifiyarta da aka raba gado aka bata, 'yan uwan mahaifyarta suka danƙa su a hannun Ɗan Lami, sauran kuma suna wurin dangin nata.

“Ke!, me ki ke a nan ?!

Bar nan dallah!”
Muryar ɗaya daga cikin masu gadin makarantar ta katseta a tsawace.

Shikenan kuma, da ma ta jima da sanin cewa shi talaka ba a bakin komai yake ba.

Ba shi da wata kima ko dajara a idon mutane.

Ba ta ce masa komai ba, ta juya ta fara tafiya.

Ko jikin store ɗin da ta sabba zama ba ta kai ba aka kaɗa ƙararrawar tashi.

Hakan yasa ta fasa zuwa store ɗin, kai tsaye ta yi hanyar fita daga makaranatar.

Tun da an tashi to ita ma babu abun da za ta zauna ta yi.

Tana tafiya ta na kwatanta yanda wasan da Yaya ya bata labarin za'ayi zai kasance, yace mata yau akwai wasa tsakanin arsenal da fc Barcelona.

Shi yasa take ta kwatanta yanda wasan zai kansace.

Ba tare da ta an kara ba wani me mota ya iyo kanta, ƙiris ya rage bai kaɗeta ba, amma duk da haka sai da ta faɗi.

RAJA POV.

A yau suka sauƙa a garin Abuja, bayan duk wasu maganganu da suka yi da Garuje, sai yau Allah ya hukunta tahowar tasu.

Duk da ba shi kaɗai ya taho ba, ya taho ne tare da duka yaransa, Rhoda, Alandi, Zuzu da Jagwado.

Dan su ɗin na amana ne, ba zai iya zuwa ko ina ba tare da su ba.
_🎶.....It's something that i never, ever, ever had _
_I have never needed somebody🎶_
_But i wannan spend sleepless nights, and sleepy days with you.._
_With you, with you, you make me speechless...🎶_
A hankali waƙar sleepless nights ta Armaan Malik ke tashi a cikin motar tasa ƙirar Jeep.

Raja ne ke tuƙa motar, yayin da Rhoda ke zaune a gefensa, Alandi, Zuzu da Jagwado na gidan baya.

Rajan na sanye cikin wani blue jeans, da farar shirt dake ƙasan baƙar denim jacket ɗin da ya ɗora a saman rigar.

Kuma sak kalar kayan dake jikin Rhoda ne.

Don ita ce ta zame masa kamar abokiyar tagwaitakar tasa, abu ne mawuyaci su saka kaya da ban da ban.

Kaya kala ɗaya suke sakawa, size ne kawai ke banbanta.

Shi da Rhodan ne ke bin waƙar, Raja na yi yana murmushi, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.

Kuma a lokacin abun ya faru.

A lokacin ƙaddarar da ke jiransa a garin Abuja ta auku, wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura.

Kan motar ya juya dan shiga layin gidan da ya kama a KAURA DISTRICT.Wata yarinya ce tafe a gefen hanya, ba ya ce ya iya ganin fuskarta ba.

Sai ganin wucewar wata baƙar mota ya yi da gudu, wadda ta so ta kaɗe yarinyar, duk da bata kaɗetan ba, sai ta kaɗata gefen hanya.

Ba shiri ya taka birki.

A firgice ya fice da ga motar, su Rhoda suka bishi da kallo su ma suna fitowar.

Da gudu ya yi inda yarinyar take, sannan ba tare da jiran komai ba, ya kama hannun yarinyar ya ɗaga ta.

“Sannu kin ji”
Ya faɗa yana san kallon fuskarta, kuma sai aka yi sa'a ta ɗago da fuskar tata ta kalleshi.

A lokaci guda zuciyarsa ta yi wani irin tsalle a ma'ajinta.

Kamar zata fito daga bakinsa.

Ba komai ne ya jawo hakan ba, face wata fuska da ya gani, fuskar sak irin ta mahaifiyarsa, fuskar sak irin ta ƙaninsa Aliyu, sannan fuskar sak irinta ce a tare da shi.

Amma ta ya hakan za ta faru ?, ya aka yi yarinyar ke kama da su ?, wacece yarinyar ma ?, daga ina take ?.

Kusan ƙamewar muntuna shida Rabi ta yi, a sanda ta kalli fuskar matashin da ya temaka ya ɗago da ita bayan kifawar da ta yi.

Mamaki ne bayyane a fuskarta ita ma, kamar yanda yake kwance a tasa fuskar.

Za ta iya rantsewa da Allah ta ga gilmawar mamakin a cikin idanuwansa.

Ba ƙaramar kaɗuwa ba ta yi ita ma, ba dan kada ta yiwa kanta ƙarya ba, da sai ta ce wannan ya fi kama da mahaifiyarta fiye da ita.

Dan ya fita farin fata, saboda ita ba wata fara ba ce sosai, ta ɗan kwaso baƙin Abbansu.

Amma Ummansu fara ce sosai, kuma farinta sak irin na wannan bawan Allan ne, kusan rabin idanuwansa a lumshe suke, sannan ya kafeta da ƙwayarsu wadda ta kasance gray color.
Chapter 14 · 0% Book details