Sashe 11
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Mama ta shi ki ƙarasa suyar nan...”
“Wallahi Umma ba zan iya ba, ga Saratu nan, sai ki sa ta ta soya”
“Eh kuma haka ne, Saratu, tun da kin tashi ita me suyar, ke sai ki ƙarasa”
Saratu ba ta ce mata komai ba, ta girgiza kanta tana takaicin halin mahaifiyar tasu da ƙanwarta, ta zauna ta ci gaba da suyar.
“Na yi zaton ba za ki fito ɗin ba ai...”
Sassanyar muryar Yaya ta faɗi, yayin da yake kallon fuskar Rabi'a.
Ta ɗan yi murmushi kaɗan tana sinnekai.
“Umma ce ta sa ni aiki, shi yasa”
Ya langwaɓe kai gefe yana faɗin.
“Allah ya bani kuɗin da zan aureki Rabi'ata, dan na gaji da ganinki kina wahala a banza, Gwara na aureki ki je can gidana ki yi bautar me lada!...”
Ƙwalla ta taru a idon Rabi'a, amma sai ta shanyeta, don ko kaɗan bata so ta zubo.
“Gobe sallah, me kika tana da min ?”
Ta ƙara sunkuyar da kanta.
Warin wannan bolar na cika hancinta, don Allah ya sani bata san zama a ƙofar gidansu.
“Babu komai”
“Na sani ai, shi yasa ni na samu na ɗan ɗinka miki kala ɗaya da hijabi, ki yi haƙuri ba yawa Honeyna!”
Abubuwa biyu ne suka karya zuciyar Rabi'a lokaci guda, ɗinkin da yace ya mata, da kuma sunan Honeynsa da ya kirata da shi, wannan ƙwallar da take ta ƙoƙarin riƙeta ta sauƙo mata.
Ta ɗago da kanta ta kalli fuskar Yayan, sannan ta kalli kedar da yake miƙa mata.
*
Tsabar murnar samun sabon kayan da take ranar kasa bacci ta yi, daga ta ɗan jima a kwance sai ta miƙe zaune ta janyo ledar kayan ta duba su, ta kuma mayar wa.
Allah ne kaɗai yasan yanda ta yi farin cikin samun kayan, shi yasa a har kullum take taya Yayyan da addu'a kan Allah ya buɗa masa, har ya samu kuɗin da zai kawo a aura masa ita.
Duk lalacewr auren yafi zaman gidansu.
“Ka zo?!...”
Kamar daga sama ta ji muryar Mama, hakan yasa ta buɗe idonta dake a lumshe, ta cikin net ɗinta ta hangi fuskar Maman, wadda ta yi kwalliya a cikin daren Allah ta ala.
Wasu tsukakkun riga da wando ne a jikinta, ga kitson attachment ɗin da takanas ta tashi ta je aka mata shi, ta zube shi a bayanta, ta caɓa wata uw*r kwalliaya, kamar me shirin zuwa gidan bikin, gidan bikin ma irin na kece rainin nan.
“Ka ɗan ƙara matsawa gaba... kasan ni bana san sa ido, kar ka ga dare ya tsala, akwai munafukai masu bacci da ido ɗaya”
Ta kuma faɗi ta cikin wayar da take.
“Ok to bari na fito...”
Kuma daga haka Maman ta sauƙe wayar da ke riƙe a hannunta, ta gyagyyara jikinta, sannan ta kashe wutar ɗakin ta fita.
Rabi ta ƙara dunƙuƙunewa a cikin bargonta, don bata ma so Maman ta san cewa ta farka.
Abin da ake zarginta da shi, shi ne 'yar mai zargin nata ke yi.
*No.181, Guzape, Abuja....*
*10:00pm*
KULIYA POV.
A hankali ƙafafunsa suka taka cikin falon gidan.
Abu na farko da ya yi shi ne kunna wutar gidan gaba ɗaya.
Kafin ya ƙaraso cikin falon, ya sauƙe ledojin da ya shigo da sua kan sofa.
Sabbin kayan da ya siya zai saka idan zai je idi.
Kuma kafin ya taho gidan nasa sai da ya biya ta gidan Anna, ya kai mata nata kayan idin.
Sai ledar da Annan ta saka masa abinci a ciki, don haka tace yana buƙatar ya riƙa cin abincin gida, ba na kanti ba.
Kuma haka ɗin ne, bayan farin ruwan sanyi da ya sha a office lokacin da aka yi buɗa baki bai saka komai a cikinsa ba.
Dan shi ba iya girka abinci ya yi ba, idan har ba gidan Annan ya je ba to sai dai ya yi order a wani restaurant da ya saba siyan abinci.
Idan kuma aiki ya sha masa kaibama ya samun damar cin abincin.
Dan bai damu da shi ba, shi yasa ulcer tai masa kamun kazar kuku.
“Ayra!, Ayra!....”
Muryarsa ta shiga kiran sunan a hankali, kamar ba shi ba, yana yi yana dudduba ƙasan kujeru.
Da gudu kuliyar tasa ta fito daga ƙasan wata kujera, sannan ta iyo kansa.
Wata hallita ɗaya a duniya bayan Anna da take iya ganin farin haƙorinsa cikin murmushi ko dariya.
Shi kansa yaan cewa ba kasafai yake murmushi ba ma balle a je ga dariya.
Murmushin ma baya yi sai idan ya yi nasara a aikinsa.
A ƙasa ya zauna, sannan ya kamo kuliyar tasa yana shafa kanta.
“Kina jin yinwa ko ?”
Ya tambaya kamar yana magana da mutum, don shi ɗaukarta yake kamar ƙawa, saboda bayan me gadin gidan, sai wata tsohuwa dake zuwa tana masa shara a gidan duk sati, babu wani abu mai rai dake rayuwa a gidan sai ita.
Ledar da Annan ta saka masa abinci ya janyo, sannan ya fiddo da abincin da Annan ta zuba masa.
Ya buɗe flask ɗin, ya zubawa Kuliyarq a murfin flask ɗin, ya tura mata gabanta, nan take ta hau ci.
Shi ma gefe ya koma ya zauna ya fara cin nasa abincin.
Yana tunanin yanda ayyuka za su masa yawa a satin nan, dan abokinsa kuma abokin aikinsa ya ɗauki hutun bikin sallah.
Saboda haka duka ayyukan Abubakar ɗin shi ne zai ƙarasa.
A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
Yana kai lomar abincin bakinsa, idonsa a kan Ayra, yadda take ta famar cin abincin ne kaɗai zai nuna maka cewar a matse take da abincin.
Bayan sun gama cin abincin, ya ɗauki Ayra tare da ɗorata a kan kafaɗarsa, sannan ya ɗauki sauran kayan nasa na ledar, ya shiga ɗakinsa.
A kan gado ya zube ledojin, kafin ya aje Ayra kusa da ledojin, Ya juya zuwa walk-in closet ɗinsa.
Bayan ɗan wani lokaci ya fito, ya shiga banɗaki.
Wanka ya yi, ya fito bayan ya sauya kaya.
Daga suit ɗin da ya shigo da ita zuwa wasu baƙaƙen shirt da wando na pyjams.
Ya dawo ya zauna a kan gadon yana fitar da kayan idin nasa.
Kamar yanda ya saba duk shekara, baƙar shaddace guda ɗaya, sai wani baƙin voil, hulunan ma baƙaƙe ne babu ratsin wata kala ko guda a jikinsu.
Haka takalman ma baƙaƙe ne guda biyu, dan shi ba wasu manyan kaya yake sawa ba, sai lokaci irin wannan idan ya zo, hatta da sallar juma'a ba da manyan kaya yake zuwa ba.
Miƙewa ya yi ya koma closet ɗin.
Wani abun mamaki shi ne, gaba ɗaya kayan cikin closet ɗin baƙaƙe ne, kamar na mai shirin zuwa jana'iza.
A rayuwarsa ba ya saka wani kaya mai kala, duka kayansa a duniya baƙi ne, motarsa baƙa, kayan sakawarsa baƙaƙe, hatta da case ɗin wayarsa baƙi ne.
Bayan ya aje kayan, ya fito ya zauna a kan work table ɗinsa, ya shiga yin sauran aikin da ya dawo gida da shi.
*Dambuwa road, Maiduguri...*
MISHAL POV.
Zaune take a ɗakin da yake a matsayin nata.
Don ba yau suka saba zuwa Maidugurin ba, hasalima suna zuwa akai-akai.
Kuma idan sun zo ɗin a babban family house ɗinsu suke sauƙa.
Duk da kasancewar gobe sallah, amma gidan har yanzu be rabu da zuwan baƙi ba.
Tun daga hayaniyar dake tashi a gidan za ka gane hakan.
Ba su dameta ba, Don Kullum ba ta fita, tana ɗaki, bata san ta fita su haɗu da Yazid.
Yazid?, wani mutum da ya so lalata mata rayuwa, wannan mutumin da duk duniya bata tsani wani mahaliƙu kamarsa ba.
Shi ne wannan mutumin da a sanadiyyarsa ta gamu da ciwon hysterian da take da shi a yanzu.
Kuma dan abun a family ya faru, haka aka rabu da shi ya ci gaba da yawonsa.
Yana shiga cikin 'yan uwa kansa ɗage a sama, kamar bai aikata komai ba.
Ita kuma da aka yi ƙoƙarin cutarwa ita ce ke ɓuya, ita ce ke ɓoye kanta da barin shiga dangi, har yanzu gani take kamar idan ta idan ta shiga cikinsu suna ganin wannan tabon a jikinta ne.
Duk da Allah bai sa ya haike matan ba, amma tana jin zafin abinda ya mata a ranta.
A duk sa'ar da za ta ganshi ji take kamar ta fasa ihu, a wasu lokutan ma ganin nasa kawai shi ne ke tada mata ciwonta.
Ta ɗan ja gutun tsaki tana ci gaba da buɗe littattafanta.
Ita ta tsani aikin makaranata, dan de ba ta san ɗan uwanta ya yi asarar kuɗin da yake kashewa a kan makarantar ta a banza, amma da ba za ta na maida hankali ba.
Gashi dai hutun sati ɗaya a ka bayar, saboda ba ƙarshen term ba ne, a tsakiyar term aka basu hutun, amma sai da suka haɗo su da holiday project.
Kuma tun barowarsu Abuja abun da take ta ƙoƙarin yi kenan.
Amma har yanzu ta kasa gamawa.
Ta kuma jan wani tsakin tana ture littatafan, duk aikin ya gundureta, fita take san yi, bata san zaman gidan gaba ɗaya.
To amma ta fita ta je ina ?, ta san in ma fitar ce ba za'a barta ta fita ita ɗaya ba, dole za'a haɗata da wani.
“Baby!”
Kamar daga sama ta ji muryarsa yana kiran sunanta, sunan da kaf duniya babu me kiranta da shi sai 'yan gidansu.
Tasan da cewa za su zo, amma ba ta san cewa yau za su zo ɗin ba.
Da sauri ta miƙe ta fita daga ɗakin, a falo ta same shi yana ta nemanta.
Yana ganinta ya sakar mata wani kyakkyawan murmushin.
Da gudu ta ƙarasa kusa da shi, kuma tana zuwa jikinsa ta ɗale shi, duk tsayinsa amma saida ta riƙe masa wuya.
“Tun sanda muka zo nake ta nemanki”
Wannan dakakiyar muryar tasa ta faɗi.
Ta yi kewarsa da ma duk wani ɗan gidansu, dan za ta iya cewa duk familynsu babu wanda take so kamar 'yan gidansu, duk da su ma a Abuja suke da zama,amma bata gajiya da ganinsu.
Sunansa Arman, ɗa ne a wurin cousin ɗinta Nimra, wadda ta kasance soja me riƙe da muƙamin general na nigeri.
Yaranta uku Arman, Iqra sai Ijaz, kuma gaba ɗaya yaran nata sojoji ne.