Sashe 67
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cak, kansa da yake gyaɗawa ya tsaya a iska, sakamakon Rabi'a da ya ga ta fito daga cikin gidan, kasancewar ya na facing kofar entrance ne, sanye take cikin wata atamfa koriya da ratsin milk, ba zai iya faɗar kalar ɗinki da aka mata ba saboda milk ɗin hijabin da ta ɗora a saman kayan, fuskarta babu komai, amma kuma tar yake ganin zanen fuskarta ta cikin hasken ranar da yake haska duniya, kanta a ƙasa take takowa, har ta iso gabansa.
“Ina zuwa Rhoda”
Ba tare da ya jira cewar Rhodan ba ya sauƙe wayar.
Hannunsa ya sa yana janyowa Rabi, ta faɗo jikinsa, ba shiri Rabi ta kalli idonsa ta saman glasses ɗin da ya saka, wani kalar kallo yake mata wanda ba za ta iya cewa ga irinsa ba, jikinta ya shiga rawa, a lokaci guda tsigar jikinta ta tashi, ita kam wai yaushe za ta saba?.
Da sauri ta juyar da kanta side ɗin me gadi, sai ta ga ba ya ma wurin, su kaɗai ne a tsakar gidan kenan?.
“Irin wannan kyau haka?”
Murmushi ta yi tana sunkuyar da kanta ƙasa.
“You look out of this world 'Yan matana!”
“Na gode...
Amma ina za muje?”
Ta tambaya, dan wannan ita ce tambayar da ta yi wa kanta a sanda ya leƙo ya faɗa mata ta shirya.
“Wani wuri...
Ko akwai inda kike san zuwa?”
Sai ta gyaɗa kanta.
“Ina san zuwa na ga Anti Saratu, sai kuma Brickhall school, don akwai yarinyar da muke zumunci da ita sosai”
Zaid ya yi murmushi.
“Ƙanwarki righ?”
Sai ta gyaɗa masa kai ta na mamakin yanda be manta ba.
“Yau de kam ba za mu samu damar zuwa Brickhall ba, sai de Sulejan, amma next fitar da za mu yi sai na kaiki”
Rabi'a ta gyaɗa masa kai.
Kuma daga haka suka shiga motar ya tayar suka bar gidan.
Jifa-jifa yake mata 'yar hira, amma ita kuma ba ta amsa masa sosai.
Don burinta ɗaya, shi ne ta ga inda yace za su je.
Kuma sai burin nata ya cika, a sanda ta gansu a Vinca Hospital.
“Ki bita ku je Ammata!”
Umarnin ya biyo baya, lokacin da Zaid ya fito daga office ɗin Huzaifa, bayansa biye da wata nurse, cike da mamaki ta dube shi.
“Ina?”
Ta tambaya, don ita bata gane ba, da shigowarsu asibitin ya zaunar da ita a reception, shi ya sa ba ta san ma me suka tattauna da Dr.n ba,don haka take buƙatar ƙarin bayani.
“Wasu 'yan gwaje-gwaje ne za a miki...
Kada ki damu, ki bita kawai!”
Ba dan ta gamsu ba, ta bi bayan nurse ɗin data fara tafiya.
“Babu wata damuwa...
Za ta iya buga ball, amma Zaid wajen mu'amalar aure ka riƙa ɗaga mata ƙafa, dan har yanzu da sauranta, ba ta gama warkewa duka ba, amma nan da wani lokaci za ta dawo normal”
Kalaman Huzaifa kenan gareshi, bayan da aka gama mata gwaje-gwajen da ita har zuwa yanzu ba ta san dalilin yinsu ba, don be ce da ita komai akan hakan ba, duk kuwa da ta tambayeshi.
Ɗaukin san ganin Anti Saratu ya sa ta ture wata maganar gwaji zuwa bayan ƙwaƙwalwarta, saboda ta ga sanda suka hau titin zuwa Suleja.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger Satate.*
“Zauna”
Cewar Zainab, babbar yayar su Anti Saratu wadda aka mata aure.
Mama da ake bawa umarnin ta zauna da ƙyar, don ba ƙaramar azaba take ciki ba.
Alhajin da san zuciyarta ya sa ta bi har england shi ne ya haɗata da jafa'ai kala-kala, a da idan zai sadu da ita ta gaba yake saduwa da ita kawai, amma bayan zuwansu england sai ya lakaɗa mata ɗan bazan duka, sannan ya sadu da ita ta baya, a cewarsa wai bokansa ne ya ba shi wannan laƙanin.
Haka ya yi ta azabtar da ita na tsawon wannan wattanin da ta yi a wurinsa.
Bayan da ya gama da ita, ya sa aka hankaɗota Nigeria, bayan da ya haɗata da ciki, ga kuma cuta me karya garkuwar jiki da ya bar mata tukuci.
Yanzu haka dawowarsu kenan daga asibiti, sun je an ɗorata akan magunguna, zuwa yanzu ta gane cewa Allah ɗaya ne, kuma hanyar shiriya ɗaya ce, duk wanda ya bi Allah ya dace ya kuma tsira, wanda kuwa yace ba haka ba shi zai jawa kansa asara tun a duniya.
“Sannu Mama”
Cewar Saratu cike da tausayawa, Mama babu bakin magana sai alama ta mata da kai, Anti Zainab ta zauna a gefenta ita ma tana ta jera mata sannun, Habiba na daga kan kujera tana matsar ƙwalla, koma me ya samu Mama ita ce wadda ta jawo mata, ita ta nuna mata hanyar bin maza, har ta kaisu ga wannan hali, kaiconta, kaicon rayuwa irin tata!.
Ɗan Lami ne ya fito daga ɗakinsa yana kallonsu su duka.
Kansa ya girgiza cike da nadama, a sanda ya kalli Mama, ya tabbatar da koma miye ya samu 'ya'yansa shi ma akwai nasa sa hannun a ciki, shi ma ya bada gudunmawa ta musamman a lalacewar tarbiyyar yaran gidansa.
A matsayinsa na uba, kamata ya yi a ce yana saka ido akan ko wace harka dake kai kawo a cikin gidansa, ya kamata ace shi ne tsaye a kan ko wata harka ta gidan, sannan nauyin ci, sha da suturarsu duka ya rataya a wuyansa ne, amma sai ya yi burus da su, ya kama wata hanya da ba ta haifar masa da ɗa ne ido ba.
Zuwa yanzu ya yi nadamar abubuwa da dama da ya aikata a rayuwarsa, kuma hakan ya biyo baya ne, sakamakon nasihar da wannan matashin me kama da matarsa da kuma 'yarsa ya masa.
Sosai matashin ya ja hankalinsa kan abubuwan da yake basu da kyau, kamata ya yi ace ya kama sana'a yana kula da gidansa da kansa, ba wai tsinduma cikin harkar caca da bin matan banza ba.
Kuma matashin be sallame shi ba sai da ya danƙa masa jari me tsoka, ya shawarce shi da ya kama sana'a, sannan abun da yake ƙoƙarin yi kenan, don hatta da wannan ɗawainiyar asibitin na Mama shi ne a kai.
Ya kuma hana habiba saida wannan finiason da take, duka nauyin gidan ya dawo kansa.
“Sannu kin ji Mama!”
Ya faɗi yana jan kujera tare da zama, shi ma kai ta gyaɗa tana kallonsa.
Kamar daga sama suka ji sallamar wata murya me kama da ta Rabi'a.
Cikin sauri su duka suka kalli ƙofar soron gidan.
Ilai kuwa, Rabin suka gani ta shigo cikin gidan.
Farin cikin ganin Rabi ya sa Saratu miƙewa da gudu ta yi kanta suka rungume juna.
Tun daga Habiba, Mama, Ɗan Lami har da Zainab kallon sabuwar Rabin suke, ba wai ƙiba ta yi ba, don idan aka dangana da jikinta na da sai de ace ta rame, amma ta yi wani irin fari, ta ƙara haske, yanayin fatarta kawai zai sheda maka da irin sauyin rayuwar da ta samu.
“Ina sirikin nawa?”
Rabi ta yi murmushi tana sunkuyar da kanta.
“Yana waje”
“To shigo mana, bari shi ma na masa iso”
Sai a lokacin idon Rabi ya sauƙa a kansu sauran mutanen dake tsakar gidan, fuskar Ɗan Lami da ta kalla ce ta tuno mata da kashedinsa gareta, na kar ta ƙara dawowa gidansa, hakan ya sa fara'ar fuskarta ta ɗauke ɗip, sannan ta juya da sauri za ta bar gidan.
“Tsaya Rabi'a”
Tsayawar ta yi, saboda jin amon muryar mahaifinta, an ya kiwa yau ba mafarki take ido biyu ba?, to in ba haka ba, ita de tun tasowarta da mahaifinta, ba za ta iya cewa ga rana ɗaya da ta ji ya yi magana cikin nutsuwa kamar haka ba, an ya ma kuwa shi ne?.
A hankali ta juyo ta kallesu, zuwa lokacin su duka sun miƙe tsaye, sai a yanzu ma ta lura da Mama wadda ke zaune a kan tabarma, ita sam ba ya ma ganeta ba, yanzu wannan Mama ce ta zama haka?, oh!, rayuwa kenan.
Sai kuma Habiba, wadda ta rame, ga kuma tabbuna a jikinta ta ko ta ina.
“Ki dawo Rabi, nan ɗin gidankimu ne”
Zaune take a gefen Anti Saratu, yayin da Mama da Zainab ke zaune a kan tabarma, Habiba na kan kujera, haka ma Ɗan Lami, daga can gefe kan wata sabuwar sallaya kuma Zaid ne zaune, ya sunkuyar da kansa ƙasa.
Ɗan Lami kallonsa kawai yake yana ƙarawa, ashe de wannan matashin sirikinsa ne?, ashe shi ne yake auren 'yarsa Rabi?!, Ashe e kuma shi ne jinin Rabi 'yar uwar Maryam, me sunan Rabi 'yarsa?.
Allah kenan.
Rabi ta share wata ƙwallar da ta silalo daga idonta, wai yau ita ce Abbansu da Habiba suke neman yafiyarta, ita kuwa me za ta iya cewa?.
Ba ta da wani abun cewa face ta godewa Allah.
“Na yafe muku Abba, muma Allah ya yafe mana”
Ta furta muryarta a raunane.
Habiba ma ta share hawaye tana saka mata albarka, Mama ma kallonta kawai take, tana san tace ita ma Rabin ta yafe mata, amma babu hali.
*06:50 PM.*
Sai a lokacin suka samu damar dawowa gida, Rabi ce a kan gaba, yayin da shi kuma Zaid ke biye da ita, ita ta buɗe ƙofar falon ta shiga, sannan shi ma ya shigo, tsayawa ya yi kukkuna fitilun falon dan babu haske sosai.
Kuma fitilun ne suka haska masa ita tar, tsaye a tsakiyar falon tana dubansa, idanuwanta sun cika da ƙwalla.
A hankali ya aje jakar kayanta data karɓo a gidansu.
Kafin ya ƙara wani yinƙiro, Rabi'a ta tako ta rungime shi tana sakin kuka.
“Na gode Raj, Na gode da duk wani abu da ka san ka taɓa min”
Zaid ya yi murmushi yana shafa kanta.
“Ammatan Raja babu komai fa, babban surprise na tafe nan da next week nan”
Ba komai ta fahimta a kalaman nasa ba, amma ko ba komai sun mata daɗin sauraro, dan haka ta ƙara narkewa a jikinsa tana kukanta.
*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.*
MISHAL POV.
Zaune take a falon Annan suna hira.
Yau tun safe Kuliya ya kawota, tare da faɗa mata cewar bayan sallahr magrib zai dawo ya ɗauketa.