← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 80

Sashe 61

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda soyyayar da iyayenku ke wa juna ya sa ita mahaifiyar Rabin ta wa Mamarku me suna, ashe da rabon za ku haɗa kanku har alaƙarku ta kai ga aure”
“Yanzu ita wannan ita ce yarinyar da mamarta ta riƙeka?”
Kawu Munzali ya tambaya ya na kallon Rhoda dake gefe tana nata hawayen, dan ita ma ta tuna nata dangin.

Raja ya gyaɗa kansa.

“Eh ita ce, sunanta Rhoda”
“Iko sai Allah, har yanzu ba ta musulunta ba kenan?”
Ɗaya daga cikin iyayen me sunan Mamman ya tambaya.

“Eh...

Amma za ta musulunta nan ba da jimawa ba”
“Zo nan 'yata, kema ai kin zama 'yar gida”
RABI'A POV.

Kamar kullum suna zaune a falon Hajiya suna hira, yayin da ita take gefe tana daddana sabuwar wayar da kawu Abdullahi ya mata kyautar ta yau ɗin nan da safe, duka 'yan matan na nan, sai hayaniyarsu suke, kuma bayan su ɗin ma har da yayunsu, waɗanda suka girme musu.

“Kai jama'a, kun ji labarin abun da yake faruwa a waje kuwa?”
Gaba ɗayansu suka zubawa Hafiza ido, wadda ta shigo tana ta wannan batu, ita Hafizan ba sa'ar su Rabi ba ce, don ta ma girmewa Baby, ƙawar su Shafa yayar Nafisa ce, kuma ita ce BBCn gidan, ko wani sabon labari a bakinta za ka tsince shi.

“Faɗa mana mu ji ta gidana”
Shafa wadda ke kishingiɗe a kan kujera ta faɗi tana miƙewa zaune.

“Wai ɗan gidan Gwaggon mu ne ya zo!”
Cike da rashin fahimta kowa yake kallonta.

“Wata gwaggon namu?”
Momi ta tambaya.

“Ke Rabi 'yan biyun Mamanku, me sunanki nake nufi”
Ba shiri Rabi ta miƙe zaune tana kallonta, ɗan gidan me sunanta?, Zaid ne ya zo?, ko de ɗayan ne ya zo?, amma ta ina suka san nan ɗin?, kuma wata ƙila ma Raja ne ya biyo ta?...

Kuma tunanin nata bai yi wani nisa ba, zarginta ya tabbata, a sanda Hafizan tace.

“Kuma ma ni a yanda na ji, haka aka ce wai saurayinta ne, tsabar abu irin na yarinyar nan wai ba ta san ɗan uwanta ba ne, kuma fa an ce kamarsu ɗaya da ita”
Dammm!, gaban Rabi ya buga, saurayinta kuma?, haka yace kenan?, duk yadda aka yi ma Raja ne?, Wai shi me ya sa ba zai barta ta hutawa rayuwarta ba ne?.

“A'a fa yaya Hafiza, yaran da aka bamu labarin sun mutu”
Hafiza ta wurgawa Jidda harara.

“Ƙarya zan muku?, kuma ai da aka bamu labarin cewa aka yi sun ɓata, ba sun mutu ba...”
A dai-dai lokacin Hajiya ta fito daga ɗakinta, duk abun da suka faɗi babu wanda ba ta ji ba.

“Me...

Me kuka ce...

Ɗan Rabi ne ya zo?”
Ko kafin Hafizan da ta buɗe baki ta bata amsa, suka ji sallamar Kawu Abdullahi a ƙofar falon.

Miƙewa suka yi a tsaye cikin girmamawa.

Bin su ya yi da kallo kafin yace.

“Duka ku bamu wuri, Hajiya tana da baƙo”
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga ɓacewa suna silalewa zuwa ɗakin Hajiyan, har zuwa lokacin Hajiya na tsaye tana kallon Kawu Abdullahi.

Isowa ya yi gabanta ya na zaunar da ita.

“Ina zuwa Hajiya”
Ya faɗi yana fita waje.

Jim kaɗan sai ga shi ya dawo, bayansa biye da Alhaji Ali da kuma ƙannen Kawu Abdullahin guda biyu, sai kuma wani saurayi guda ɗaya biye da su, wani saurayi me kama da 'ya'yanta 'yan biyu, wani saurayi me kaka da jikarta ɗaya.

Har matashin ya shigo ya zauna kusa da ita idonta a kansa.

“Kin ga ikon Allah ko Hajiya?”
Ta juyo ta kalli Kawu Abdullahi kafin ta ƙara juyowa ta kalli matashin, kuma a lokacin ne Rhoda ta shigo ta zauna daga can nesa da su.

Hawaye ya zubo daga idon Hajiya, hannunta na karkarwa ta kai ta kama fuskarsa.

“Ji...

Jikana!”
Ta ƙarashe tana rungume shi, tare da sakin kuka me sauti.

Kafin ta sake shi tana ta dudduba jikinsa.

A hankali Rabi ta saki labulen ɗakin Hajiya, bayan da ta ɗaga shi ta ga jikan Hajiyan da ya zo, a gaskiya ta yi babban kuskure, ta yi kuskure da ta zama sanadiyyar shigowar makashi ahalinsu, amma kuma ba za ta ce ba ta farin cikin ganinsa ba, kuma ba za ta ce ta na ɓaƙin cikin zuwansa ba, kawai dai halinsa ne yake ba ta tsoro.

“Kun ga tabbaci, Wallahi haka yace shi saurayinta ne”
Hafiza ta ƙara faɗi tana kallon bayan Rabi, Rabi ta juyo ta kallesu, su ma kuma su duka ita suke kallo.

“Wai da gaske ne Rabi?” Cewar Kairiyya.

Ta kasa cewa a'a, ta kuma kasa cewa eh, kawai ta ci gaba da tsayuwa a wurin, hannunta riƙe da wayarta.

“Ni bari ma na leƙa na ganshi”
Cewar Hafizan ta na miƙewa, leƙawar ta yi, Allah ya sa ta ga fuskarsa kuwa.

“Ikon Allah, wai kin ga kamar da yake da ita kuwa?”
Haka suka riƙa tasowa ɗaya bayan ɗaya suna leƙawa, sai mamaki suke ta yi, yayin da Rabi ta koma gefe tana karanta wasiƙar jaki.

Kawu Abdullahi ne ya lura da su, hakan ta sa ya yi gyaran murya, bayan da ya gama bawa Hajiya labarin da Zaid ɗin ya basu.

“Leƙen kuma na miye, ai za ku iya fitowa ku ganshi”
Da gudu Fati da Kairiyya suka koma ɗakin cike da jin kunya.

“Ko ba ku ji ba ne?!.

Ku fito ku gaisa da yayan ku!”
Ɗaya bayan ɗaya suka shiga fito suna gaisawa da Zaid, amma fur Rabi ta ƙi fitowa.

Ba za ta iya fitowa ta haɗa ido da shi ba, gwara ta zauna a ɗakin zai fi mata sauƙi.

Ta na cikin saƙe-saƙen nata ne Rhoda ta buɗo ƙofar ɗakin ta shigo, kanta ta ɗaga suka haɗa ido, da sauri ta miƙe ta isa gaban Rhoda suka rungume juna, duk yanda za ta kai da fushi da Raja ba za ta yi da Rhoda ba, don kuwa ita ba ta taɓa ganin aibunta ba.

“Ya kike Rabi'a?”
Cewar Rhidan ta na sakin Rabi, Rabi ta gyaɗa kanta cikin faɗin.

“Ina cikin ƙoshin Lafiya”
“Ashe ma kun san juna?”
Jidda da ta biyo bayan Rhoda ta faɗa ta na dubansu.

Rabi ta gyaɗa kai.

“To kawu yace tare za mu kwana da ita, su sun fice, sai ki zo mu koma ɓangarenmu, dan su fati sun wuce”
Ba tace komai ba ta kama hannun Rhodan suka raɓa Jidda suka fice.
*
“Ga su nan, suma 'yan uwanka ne, sai ku kwana tare zuwa gobe...”
Cewar Kawu Abdullahi, a lokacin da yake sada Zaid da samarin gidan waɗanda ba su yi aure ba, su huɗu ne cas, Muhammad, Sani, Auwal da Zakar.

Raja ya kallesu ya na gyaɗa kansa.

A sanda ko wannensu yake gabatar masa da kansa, ɗaya bayan ya ya basu hannu suka gaisa, kafin suka nuna masa shimfiɗa in da zai kwanta, bai kwanta ɗin ba sai kawai ya zauna ya na saƙe-saƙe kala-kala a ransa.
*
“Rabi!”
Rabi ta juya ta kalli Jidda da ta kira sunanta, ta na zaune ne a bakin gadonta, lokacin kusan ƙarfe sha ɗaya, amma Rabin bata samu rintsawa ba, tunani ya hanata ta yi bacci.

Jidda ta taso daga kan nata gadon ta dawo ta zauna a bakin gadon Rabi ta na dubanta.

“Me yake damunki?”
Rabi ta kawar da kanta tana furzar da iska.

“Babu komai”
“A'a Rabi, duk yadda aka yi da komai. babu komai ba za ki zauna kina tunani ba.

Kuma na lura da tun zuwan wannan Zaid ɗin yanayin ki ya sauya”
Rabi ta sunkuyar da kanta tana kallon yatsun hannunta, amma ba ta ce komai ba.

“Menene yake faruwa?.

Ko bakya sonsa kamar yanda Hafiza tace?”
Rabi ta yi saurin girgiza kanta tana faɗin.

“A'a, ba haka ba ne.

Ina sonsa, kawai de wata matsalar ce da ban”
Jidda ta gyaɗa kanta tana dafa kafaɗarta.

“Na gane, to Allah ya kawo miki mafita, ke de kawai ki yi addu'a...

Kin ji?”
Sai ta gyaɗa kanta kawai.

Jidda ta ƙara dafa kafaɗarta, sannan ta miƙe ta koma gadonta.

Rhoda dake kwance a gefen gadon Rabi ta yi murmushi ta na gyara kwanciyarta.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriter's
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*22*
~~~
*Keep on letting your love shine...*
***
RAJA POV.

Zaune yake a falon kakansu wanda mutanen gidan ke kiransa da Baba, Baba Munzali da kuma Kawu Abdullahi ne tare da Baban.

Kawu Abdullahi ne ya masa tambayoyi kan yanayin yanda rayuwarsa take a can garin Abuja da ya faɗa musu ya na da zama, sun masa tambayoyi sosai, kafin suka tambayeshi alaƙarsu da Rabi'a.

“Na gamu da ita ne a hanyar makarantar da take zuwa aikatau, kuma daga haka ne muka soma soyyaya, har muka fahimci juna, giftawar wannan iftila'in ne ya kawo mana tsaiku”
Kawu Abdullahi ya gyaɗa kansa a sanda Zaid ɗin ya kai ƙarshe a maganganunsa.

“Ke nan ka san abun da ya faru da ita?”
Kansa a ƙasa ya gyaɗa shi.

“Na sani Kawu, dan ni ne ma da kaina na yi jinyarta a asibitin da aka kwanatar da ita”
Baba Munzali ne yace.

“Kuma kai yanzu kana santa a hakan?”
“Sosai ma kuwa Baba, ina san aurenta a yanda take, abun da ya faru da ita ƙaddara ce,wadda ta wuce fata, kuma san aurenta da nake ne ya sa na biyota har nan...”
Ko kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai, wayar Zaid ɗin ta yi ringing alamun shigowar kira.

“A min afuwa...”
“Ba damuwa za ka iya ɗaga kiranka”
Kawu Abdullahi ya amsa masa.

Kansa ya gyaɗa ya na ɗaga kiran.

“Ok”
Kawai yace sannan ya katse kiran, cikin WhatsApp ya shiga, ya buɗe chat ɗin wani contact, a inda aka turo masa wani vedio, buɗe vedion ya yi, kafin a hankali ya matsa ya miƙawa Kawu Abdullahi wayar.

“Ka duba ka ga”
Kawu Abdullahi ya karɓa cike da mamaki, kafin ya danna play, vedion ya buɗe, sannan hoton Habiba dake garƙame a cell ɗin 'yan sanda ya bayyana, fuskarta ta ji duka ba na wasa ba, muryarta ce ta shiga fitowa raɗau daga cikin wayar.

Hakan ya sa Kawu ya karkata fuskar waya zuwa ga su Baba dan su ma su gani.
Chapter 61 · 0% Book details