← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 80

Sashe 49

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da safe da ta tashi ayyukanta ta shiga yi cikin gaggawa, don so take ta yi sauri ta kammala abun da za ta yi don ta bar gidan kafin ya fito, hakan da ta tuna ne ya sa ta zabura za ta bar kitchen ɗin, sai dai kuma fatan ta bai cika ba, don a dai-dai lokacin ƙofar kitchen ɗin ta iyo ciki, Kuliya ya shigo, kamar kullum sanye cikin baƙaƙen kaya.

Kallonta yake cikin wata iriyar siga da Mishal ba ta san ta inda za ta mata fasarra ba, hancinta ta ja, sakamakon murar da ta kamata a jiya, ta haɗiyi yawu da ƙyar.

Numfashinta ya kusa ɗaukewa a sanda ya tsaya a gabanta.

“Har kin shirya?”
Ya tambaya ya na kallon hancinta da ya yi jajir, da alama dai mura take.

“Eh”
Ta amsa masa cikin muryar me mura.

“Ba ki da lafiya?”
Ya tambaya ya na duban yanayinta, da sauri ta girgiza masa kai, sai kuma ta gyaɗa kan nata tana shaƙar ƙamshin turarensa da duk murar da take ba ta hanata jinsa ba.

Wani sauti ta ji me kama da na murmushi, hakan ya sa ta kalli fuskarsa da sauri, kuma sai ta ga da gaske ne, Kuliya ne yake mata murmushi, wani abu sabo, wani abu da za ta cewa ba ta taɓa ganinsa a zahiri ba.

Kuma murmushin da ya yi sai ya ƙara bayyana mata kamarsa da Adawiyya, haka zalika murmushin nasa ya ƙara bayyana kamar da suke da ɗan uwansa...

Tunaninta ya katse a sanda ta ji sauƙar tafin hannunsa a kan fatar wuyanta, wannan sanyin ya shiga bi ta jijiyon jikinta, hakan ya sa ta ɗan ɗauke numfashinta na wasu sakkani, kafin ta dawo da shi ta na jansa da sauri-sauri.

“Har da zazzaɓi kenan?”
Ya tambaya ya na dawo da hannun nasa goshinta.

“Zan bawa Ibrahim (Drivernta) maganin mura ya kawo miki”
Da sauri ta gyaɗa masa kai tana jan hanci.

“Ban manta ba...

Mecece amsata?”
Ta kalli fuskarsa, amma sai ta kasa cewa komai, bakinta ya mata nauyi, kamar wanda ta haɗiyi dutse.

A hankali Kuliya ya ƙara matsawa kusa da ita, sannan ya saka hannunsa na dama ya kewaye ƙuginta, ya haɗeta da jikinsa ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, hakan ya sa Mishal rintse ido tana kawar da kanta, hannunsa na hagu ya sa ya kamo haɓatar ya juyo da fuskarta.

“Look at me!”
Sai ta buɗe idon nata tana kallon fuskarsa.

“Did you love me?”
Saboda abun da Mishal take ji ba ta san sanda ta shiga gyaɗa masa kanta da sauri ba kuma ta gyaɗa ya fi sau biyar.

“Kin tabbatar?”
“E...

Eh!”
Kalaman sun yi wa Kuliya daɗi, hakan ya sa ya yi wani irin murmushi da sai da ya bayyana haƙoransa, kafin ta ɗauke hannunsa daga kan haɓarta, ya dawo da shi gefen fuskarta, yana shafawa a hankali.

“I love you Teddy Bear!”
Ya na kaiwa ƙarshen maganar, ya raba leɓensa biyu, sannan ya sa nata na ƙasa a tsakiya, kafin ya haɗe bakinsa da nata gaba ɗaya.

Abun da ya yi ya sa Mishal ɗaga ƙafarta sama, sannan ta dunƙule hannayenta a kan ƙirjinsa.

Ba ta san ma me yake faruwa ba, ba ta san me ake yi a duniyar ba, ba ta san me yake wakana a kitchen ɗin ba, abu ɗaya ta sani, shi ne ita ce riƙe a hannun Kuliya, yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da gefen fuskartsa na dama, bakinsa kuma cikin nata, ya na aika mata da wani laffiyayyen kiss.

A lokacin ne aka ƙwanƙwasa ƙofar falon ta can compound, sannan muryar Ibrahim ta biyo baya.

“Ranki ya daɗe lokaci na ƙurewa, ki fito kar mu makara!”.😁
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*17*
~~~
*Time moves slower when you miss somebody.*
***
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja*
RAJA POV.

Yau zaune yake a tsakar gidan, ya na kallon yanda iska ke busawa ta na kaɗa bishiyoyin farfajiyar gidan, a zahiri kenan, amma a baɗini sam ba su yake kallo ba, tunaninsa na can wata uwa duniya, yayin da shi kuma yake wannan duniyar, sati uku kenan rabonsa da farin ciki, sati uku kenan rabonsa da walwala, sati uku kenan rabon da wani abu na fara'a ya gifta a fuskarsa, sati uku kenan da shigar yaruwarsa cikin yanayin tashin hankali da zullumi, sati uku kenan da komai na rayuwarsa ya yi juyin waina a tanda, kuma a cikin wannan satin ukun ne rayuwarsa ta shiga kwale-kwalen katako, wanda ke tangal-tangal a cikin kogin da ke cike da yunwatattun kadogi, a cikin sati ukun nan komai ya cakuɗe masa.

Kuma duk hakan ya samo asali ne ta sana diyyar ɓatan Rabi'a, don zuwa yanzu ya na da tabbacin Rabi'ar ba kawai makarantar ta dena zuwa ba, ɓata ta yi, amma abun tambayar a nan shi ne, ina ta je?, ta na ina ?, shin ta na hannu na gari?, ko a'a, idan ya yi zurfi a tunani irin wannan sai kansa ya kulle, kamar wata ƙofar da aka garƙame da makulli.

“Raja!”
Ya ji muryar Jagwado na kiran sunansa, amma sai ya ƙi juyawa bare ya amsa.

“Raja!”
A wannan karon muryar Alandi ce ta yi kiran, kuma a yanzun ma bai amsa ba.

Kusan a tare suka zauna a kusa da shi, Zuzu a ɓangaren dama, Alandi a kusa da Zuzu ɗin, Rhoda ta zauna a gefensa na hagu, yayin da Jagwado ya zauna a ƙasa ya na kallonsa, kai kace me shirin ɗaukan karatu ne, kansa ya juyo ya kallesu gaba ɗaya, sannan ya ɗauke kai ya ci gaba da kallon bishiyoyin.

“Ka da ka damu Raj.

Ka gane ko?.

Rhoda ta ce eh...

Za ta gano maka 'yar shilarka.

Dan haka kawai ka share”
Kalon Alandin dake wannan batun kawai ya yi, ya kuma ɗauke kai, shi da za su tashi su bar shi shi ɗaya ma da abun zai fi masa sauƙi, dan duniyar ma kanta ji yake kamar babu kowa sai shi kaɗai, kamar a duniyar babu wanda ya kai shi kaɗaici, kamar ma kwanakin ba sa sauri, gani yake kamar a jiya ne Rabi ta ganshi ya na harbin wannan mutumin.

“Zaid!”
Juyowa ya yi ya kalli Rhoda da ta kira sunansa.

“Na ƙara tsananta bincike, ka roƙi Allah ya temakemu mu samota”
A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya, kafin a hankali wani damshi ya sauƙo daga idonsa har zuwa ƙasan kuncinsa, wani abu ruwa, wani abu da ba zai iya tuna rabon da su fito daga idonsa ba, amma yau sai ga su a idonsa, yau shi ne yake hawaye saboda wani ɗan adam da ba Rhoda ba, a da ya ɗauka cewa duniyarsa ta mutu gaba ɗaya, bayan Rhoda ba shi da wani abun damuwa, ba shi da wani wanda yake damuwa da shi bayan ita, ba shi da wanda zai bawa kula sai ita, amma yau a kan Rabi sai ga shi ya na hawaye, hawayen da yake san ya yi su tsawon lokaci, amma ya na dannewa.

Gaba ɗayansu suka ci gaba da kallonsa cike da tausayawa, don har wata rama ya yi, ga ɗan duhu da faratrsa ta yi, tsabar tashin hankali, saboda shi gani yake koma miye ya samu Rabi'a shi ne sila.

Rhoda ta dafa shi, kuma kafin ta faɗi abun da ke bakinta ya kwanta a jikinta ya na rungumarta, tare da sakin kuka a hankali, kuka yake sosai, amma kuma ba sauti, sai jijjigar da jikinsa ke yi tare da na Rhoda da ya runguma.

Rhoda da jikinta ya yi sanyi, ta shafa kansa ita ma hawayen na sauƙo mata, tun suna yara sun riga da sun saba da ko kuka tare suke yi, hakan ya sa za ta taya shi jimamin halin da yake ciki.

Su Alandi ma gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi ƙalau, kamar wanda suka kwana a cikin fridge.

“Rhoda ki temaka ki nemota....

Rhoda ba zan iya ɗaukar wannan ciwon ba, ba zan iya ba!”
Cikin muryar kuka ya yi furicin kuma a lokaci guda ya na sakin Rhodan, Rhoda ta shafa sumar kansa ta na girgiza masa kai.

“Na maka alƙawarin samo maka ita, ko ina ta shiga a garin Abuja, ka yarda da ƙanwarka ko?”
Ya gyaɗa mata kai.

“To ƙanwarka ba za ta barka ka faɗi ƙasa ba.

Zan tabbatar da na nemo maka ita a ko ina take kuwa”
Ƙara rungumarta ya yi ya na sakin wani kukan.

“Rhoda Ina san Ammata, ina santa...

Ina santa.....

I na...

I na....

Santa!”
Rhoda ta shafa bayansa tana gyaɗa masa kai.

“Na sani, na san ka na santa, kuma za ka aureta, da yardar yesu zaka aureta!”
*No.181, Guzape, Abuja*
*10:04pm*
KULIYA POV.

A hankali hannunsa ya tura ƙofar shiga falon gidan zuwa ciki, sai da ƙofar ta buɗe gaba ɗaya, sannan ya saka ƙafafunsa ciki, shiga ya yi ya na baza idanuwansa a falon a yunkurinsa na neman ta inda zai hangota, idan ma ta na falon kenan.

A kan kujera 3 seeter ya hangota, ta yi rashe-rashe ta na bacci, ganinta kawai da ya yi a yanzu ya tuna masa da safiyar yau, a lokacinda ya tsinci kansa cikin duniyarta, yanda ya sumbaceta a yau da safe ba ƙaramin saka shi cikin nishaɗi ya yi ba.

Sai tunanin abun da ya katse masa nishaɗin safiyar ya dawo masa.

Wannan maganar ta Ibrahim ce ta sa ya saki bakinta a hankali, sai dai kuma bai raba fuskarsa da tata ba, ya na kallon murfin idonta da ta lumshe, a hankali ya janye hannunsa dake kan ƙugunta ya kama fuskarta, sannan ya sumbaci gaban goshinta, kuma sumbatar ce ta sa ta buɗe idonta.

“Ki je Ibrahim ya na jiranki”
Ya furta mata a hankali, kuma ita ma sai ta gyaɗa masa kai kawai, ta na fita daga hannayensa, ta ɗauki lunchbox ɗinta za ta fiti ya kamo hannunta, sannan ya rungumeta sosai a jikinsa, yana jin yanda jikinta ya yi karkarwa a lokacin.

Kafin ya saketa ya bata damar tafiya.
Chapter 49 · 0% Book details