Sashe 58
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsoho Alhaji Ali ya ji ƙwalla ta cika idonsa.
“Irin cin amanar da Ɗan Lami zai mana kenan?, Bayin Allah a nan a gabanku fa nake tura masa kuɗi duk sallah na ce a yi wa Rabu ɗinkin sallah, amma kun ji, rabonta da sabin kaya tun wanɗanda ta bar gidan nan da su”
Cewar kawu Abdullahi, babban ɗa a wurin Alhji Ali, haka kuma babban wa a wurin su Maryam.
“Ni ai ba wannan ne ya bani mamaki ba, kadarorin Maryam ɗin da ya ɗaga ya siyar su ne suka ba ni mamaki”
Cewar Kawu Hassan, ƙani a wurin kawu Abdullahi.
Haka dai suka ci gaba da maida zance, har da masu cewa ƙarar Ɗan Lami ɗin ya kamata a yi, Rabi kuwa jinsu kawai take, dan ita kaf duniya yanzu ba wannan ne a gabanta ba, farin cikinta ɗaya, da danginta suka karɓeta, suka nuna mata ƙauna kamar yanda suka saba.
Sai kuma matsalarta; Raja!.
Har yanzu tunaninsa bai bar cikin kanta ba, har yanzu ta na iya hango fuskarsa a cikin kanta, har yanzu ta na iya hango kanta a tsakanin hannayensa, har yanzu akwai sansa a cikin zuciyarta, amma ko ta ƙi ko ta so dole ta cire wannan son, don ba zai amfaneta da komai ba, face ya wagalar da ita, aure tsakaninta da makashi ɗan daba ba abu ne me iyuwa ba, wai ita ya aka yi ma ta yarda da shi har haka?, ina hankalinta ya shiga da har ta bari zuciyarta ta yarda da shi, ta inda har ta kasa tambayarsa wani aiki yake.
Me ya sa idonta ya rufe ta kasa ganin gaskiya?.
Wani abun farin cikin ma shi ne; da bata faɗa masa cewar shi ɗan uwanta ba ne, wannan shi ne kaɗai arziƙin da aka yi.
Ta raya hakan a ranta, don ita ta manta da maganar da ta faɗa masa a sibiti.
Haka suka yi kiɗansu suka yi rawarsu, amma ba ta ƙara cewa kanzil ba, har suka babbata haƙuri, kawu Abdullahi ne yace ta shirya zuwa gobe zai kaita a mata gwaje-gwaje, sai a lokacin ta yi magana, ta sanar masa da cewar duk wasu gwaje-gwaje da suka dace babu wanda ba a mata ba, amma yace shi bai yarda ba, kawai ta shirya zai kaita a sake mata wasu, ba ta ƙara masa musu ba tace to, sannan ta miƙe ta koma cikin gidan.
Kai tsaye ɓaangaren kakarsu ta yi, inda ta san 'yan matan gidan suna tare a can, dan a dai-dai lokaci irin wannan a can suke taruwa.
Kuma kamar yanda ta ayyana a ran nata sun taru a can ɗin.
'Yan mata shida ne sa'o'inta a gidan, Momi, Nafisa, Fati, Jidda, Kulsum da Kairiyya, su na ganinta su ka yi shiru, kowa ya zuba mata ido ya na kallo, dan kaf cikinsu babu wanda ya san da zuwanta, a sanda ta shigo garin ma suna islamiyya.
Gaba ki ɗayansu so suke su ganeta, kammaninta na musu kama da na wata da suka sani, kallon ƙurillar da ta ga suna mata ya sa tace.
“Ya da kallo haka 'yanmatan Waliki family?”
Kusan a tare suka fashe da dariya suka iyo kanta.
A dai-dai wannan lokacin kakarsu ta fito daga ɗakinta ta na ɗingisa ƙafa, kujera ta samu zauna ta na kallonsu.
“Rabi'a?, wai yaushe ma kika zo garin?”
Cewar Kulsum ta na dariya.
Rabi ta zauna a kujera ta na faɗin.
“Ɗazu da yamma, kuna islamiyya lokacin”
“Wayyo Allah, wallahi na ji daɗin zuwanki, kusan shekara biyar fa rabonmu da ke”
Cewar Fati ta na matsawa kusa da ita.
“Ke Allah ya yi da ke kina nan za ayi bikin Nafisa”
Kairiyya ta faɗa, baki buɗe cike da mamaki Rabi ta kalli Nafisan da ta kawar da kanta, saboda Hajiya kakarsu dake wurin.
“Wai dan Allah?”
“Wallahi kuwa, nan da wata ɗaya da sati ɗaya” Jidda ta amsa mata.
“Ke Rabi a ina kika ji wannan raunin na fuskarki?”
Momi ta tambayeta, Rabi ta kai hannu ta shafa gefen fuskarta na hagu, sai da ta haɗiye wani abu sannan tace.
“Haɗari ne...
Kai ni yanzu ku ba ni labari, ya ake ciki ?”
Daga haka suka shiga hira a kan batun bikin, suna bawa Rabin labarin yanda suka tsara bikin, da yanda zai kasance, har kusan ƙarfe goma suna can, dan abincin dare ma tare suka ci.
Kasancewar 'yan matan su duka ɗakinsu ɗaya, ya sa ita ma ta kwana a cikinau, dan dana tun can tare auke kwana, gadon Rabin ma na da yana nan, kuma yanzun ma a kansa ta kwana.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
RAJA POV.
_🎶It was just two lovers..._
_Sitting in the car, listening to blonde_
_Falling for each other_
_Pink and orange sky_
_Feeling super childish_
_No donald glover🎶..._
Waƙar dake tashi kenan a cikin sifukun gidan, wanda Raja ya ƙure volume.
Tsaye yake daga gaban mirror, ya na taje sumar kansa, sanye yake cikin wata ash shadda, a hankali bakinsa ya ci gaba da biya waƙar Golden hour ɗin dake tashi a falo.
“I was all alone...
With the love of my life...
She's got glitter for skin...
My radiant beam in the night...
I don't need no light to see you...
Shine...
It's your golden hour...”
Sai kuma ya yi shiru ya na kallon kansa a mirror, yayin da ya aje matajin hannunsa, bayan wani lokaci me tsayi yau shi ne sanye da manyan kaya, ya daga kafaɗarsa ya na murmushi, ya gyara wuyan rigar jikinsa, ya ƙara fesa turare a jikinsa, sannan ya finciki hularsa ya fito.
“Huh?!
Dude?
Yau ina zuwa?”
Cewar Rhoda kenan, yayin da ta fito daga kitchen, hannunta na dama riƙe da plate, Raja ya kama kumatunanta ya na ja.
“Zance zan je”
Rhoda ta shafa kumatunta da ya saki da hannunta na hagu.
“Guys, ku shigo ku ga ikon God!”
Kiran da ta ƙwalawa su Jagwado ne ya sa suka afko cikin gidan babu shiri.
Kallon Rajan su ma suka tsaya suna yi, a karo na farko tun bayan saninsu da Rajan da kuma Rhoda, ba su taɓa ganinsu da mabanbantan kaya ba, a ko da yaushe kaya kala ya suke sawa, sai yau.
“Allah de ya biya oga Raja, ina za ka fasa haka?” Alandi ya tambaya.
“Zance zan je”
“Kutumar dumadu, Kaga Oga Raja namu, Allah ya biya, gayu, oga fa ya rufta ramin ƙauna Allah Wallahi”
Cewar Zuzu ya na wani ɗaɗɗaga hannu.
Raja ya yi murmushi ya na girgiza kansa.
“Wai Zuzu ban hanaku magana irin haka ba?”
Zuzu ya shafa kansa ya na kallon ƙasa.
“Sabo ne oga Raja, amma za mu dena da yardar me duka” ya faɗi muryarsa babu wani banbanci da ta ɗazun.
“Ku fa?”
Raja ya tambaya yana kallon sauran.
“Aah, ai muma hakan take oga, ko ya kuka ce gayu?”
Alandi ya faɗi ya na kallon su.
“Haka ne”
Jagwado ya amsa.
“Na zo na raka ka?”
Rhoda ta faɗi ta na aje plate ɗin hannunta, wanda ke ɗuke da alale.
Raja ya maka mata harara.
“Wa za ki bi?...
Kama hanyar ki can joo!”.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.*
Da gudu Fatima ta shigo gidan har tana bangaje Saratu da ta fito daga banɗaki.
“Ke Fatima mi ye hakan?”
Inaa, sam ba ta tsaya ba sai da ta dangana da ɗakin Habiba.
“Ke dallah mi ye hakan za ki faɗo kaina?”
Habiba ta tambaya ta na miƙewa.
Fatima ta dafe ƙirji ta na zaro ido, hannunta ta ɗaga tana nunawa Habiban ƙofar ɗakin.
“Wa...
Wani na... na ga a waje...
Kamarsu ɗaya da...
Da Rabi!”
Wani irin juyi kayan cikin Habiba suka yi, don a sanda fatiman ta ambaci kamar mutumin da ta gani da Rabi, ƙwaƙwalwarta ta hasko mata 'yan uwan Maryam na Haɗejia.
To ko su ne suka zo kamata ?, wata ƙila Rabi ta sanar musu da duk irin abubuwan da ta mata, shi ne suka zo dan su kamata.
Muƙut!, ta haɗiye yawu, tunawa da ta yi da labarin irin kuɗin baban Maryam ɗin da aka bata.
Ba shiri gumi ya shiga tsatsafo mata, cikinta har wani ƙugi yake.
Sallamar da Saratu ta ji a waje ya sa ta leƙa, kasancewar akwai hijabi a jikinta.
Ita kanta sai da ta firgita, ganin wani mutum sak Rabi, tsaye a soron gidan nasu, amma sai ta ɓoye tsoronta ta amsa sallamar tasa.
Ba tare da ta tambayeshi wa yake nema ba, ta masa lamini da ya shigo cikin gidan.
Wata kujerar roba ta bashi, tace ya zauna a kai.
Ya na zama a kan kujerar Habiba ta bankaɗo labulai ta fito, Fatima na biye da ita.
Curko-curko suka yi daga bakin ƙofar ɗakin Habiban suna kallon ikon Allah.
Saratu ce ta kawo masa ruwa, sannan ta zauna suka gaisa.
“Am...
Rabi'a nake nema”
Wani irin ƙara cikin Habiba ya saki, da saida ta saki wata siriyar tusa, shikenan, wata ƙila tata ta ƙare, kenan da Rabin ta bar gidan Abubakar ba can ta yi ba, tun da ga shi su ma nemanta suke, amma garin yaya har aikin nan ya karye?, don kuwa ita ta san ta sa a yiwa 'yan uwan Maryam aikin da duk tsawon shekarun da Rabi za ta yi a gidan ba za su taɓa neman ganinta ba.
“Amma waye kai bawan Allah, ko daga Haɗejia kake ?”
Raja ya sosa kansa ya na faɗin.
“Sunana Zaid, kuma ba daga haɗejia nake ba”
“Laaa!, da ma kai ne Zaid ɗin, ai ko Rabi ta na yawan bani labarinka, sai dai ko da wasa ba ta taɓa faɗa min cewar kuna kama ba”
Raja ya ɗaga kafaɗarsa ya na faɗin.
“Allah sarki”
“To Rabi dai ba ta gidan nan, satin da ya wuce Umma ta koreta, ita kuma sai ta koma gidan kawu Habu, gidan na ɗan gaba da mu”
Da farko har hankalin Habiba ya kwanta, jin shi wannan bawan Allahn ba daga haɗejia yake ba, amma kalaman Saratu su ne suka dawo da tsoron sabo.
Kuma cikinta bai ƙara rikicewa ba, sai da Raja ya juya ya kalli side ɗinta.
Hatta da idanuwansa irin nata ne, banbancin kawai shi ne na sa a lumshe suke, kuma ƙwayar cikinsu kalar ruwan toka ce.