← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 80

Sashe 69

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ni ne ban da kunyar?”
“To kunyar ce da kai?”
“Allah kuwa Ammata ina da kunya sosai, kowa yana darajanta ni, kowa yana bani kima, ina da kwarjini a idon mutane.

Kuma duk da haka sai ke ki ce ba ni da kunya?”
“To idan baka so ina faɗa maka haka ka dena min irin waɗana zantuttukan”
“Wasu zantuttuka ke nan?”
Ya tambaya cikin ɗage gira, har da mata alama da hannu, Rabi ta ja tsaki, dan ta lura da yau 'yan neman tsokanar ne a kusa, gwara ta rabu da shi ta yi tafiyarta.

“Kin ɗau ba shi, idan muka koma gida sai na fanshe da...”
Wani dukan ta ƙara kaiwa bakinsa amma sai ya dafe bakin nasa yana dariya.

“Yi haƙuri damisar Raja, takawarki lafiya uwar gidan Zaid, maman Aliyu da Maryam!”
Baki sake Rabi'a take kallonsa, wato ita nan har an gama zaɓa mata sunan 'ya'yan da zata haifa?.

Kuma maganar tasa sai ta tuno mata da shi, Aliyu, mijin Mishal, ɗan uwansa.

Ya kamata ace zuwa yanzu ta san meke faruwa a tsakaninsu, amma ba komai za ta tambaya.

Motar ta buɗe ta fita, har ta shige lungunsu Zaid na mata dariya, nan duniya babu abun da ke sashi mishaɗi face zolayarta, in dai zai zolayeta sai ta yi fushi, shi kuma fushin nata me ke mugun aika shi duniyar nishaɗi.

Motar tasa ya tayar ya yi gaba, dan masallacin da za'a ɗaura auren a gaba yake.

Bayan an ɗaura aure, ya yi wa Abba da Fu'ad barka, ya basu uzurin akwai aikin dake jirans, sannan ya samu ya sulale ya gudu.

Gida ya koma ya je ya shirya cikin suit, kai tsaye daga nan ya nufi DSS headquarter.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja.*
“Sun yi bayani?”
Muryar Zaid ta tambaya, yayin da yake tsaye ya na kallon Usman da abokansu huɗu dake cikin ɗakin horo.

Duk sun fita hayyacinsu, dan ba ƙaramin duka suka sha ba.

Matemakinsa ya amsa masa da.

“A'a Sir, sun ƙi yin magana”
Ya juyo ya ɗauke idonsa daga kan glashin da yake iya kallon su Usman ta ciki, ya kalli matemakin nasa me suna Marcus.

Sannan ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a ɗayan gefen nasa.

“Shi kuma Alhaji Balan fa?”
Rhoda ta amsa masa da.

“Ya magantu, bugu ɗaya ya ji ya saki baki ya shiga koro bayanai”
Kannsa ya gyaɗa yana ci gaba da kallon su Usman, hannayensa rungume a ƙirjinsa.

“Ina Joseph?”
Ya tambaya ba tare da ya kalli ɗaya daga cikinsu ba, Marcus ne ya amsa masa da.

“Sun fita wani aiki...”
Bai jira Marcus ɗin ya gama rufe bakinsa ba, ya fara takawa zuwa ƙofar shiga cikin ɗakin horon.

Rhoda ta girgiza kanta, dan ta san ba zai ragawa su Usman ba.

Ilai kuwa, ya na shiga ya bi ɗakin da kallo, zaratan mazan dake tsaye a ɗakin hannayensu riƙe da sandunan duka suka sara masa.

Ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba ya kalli sandar dukan hannun guda daga cikinsu.

“Da wannan kuka dake su?”
Ya tambaya yana raba idonsa a kansu.

Ɗaya daga ciki ya amsa masa da.

“Yes sir”
Hannun rigarsa ya shiga tattarewa ya na faɗin.

“Ina kwa za su yi magana.

Wannan ai ba duka suka sha ba...

Marcus!”
Ya ƙarashe yana ƙwalawa Marcus dake tsaye a waje kira.

Da hanzari Marcus ya shiga ɗakin yana amsa kiran.
”A kawo min lantarki!”
Cike da iko isa da jzza ya yi maganar, ta yanda babu wanda ya isa ya tanka masa a cikinsu.

Marcus ya ammsa yana fita.

Shi kuma Zaid ya ja ɗaya daga cikin kujerun ɗakin ya zauna a yana facing su Usman, waɗanda suka jigata sosai, dan ko ɗan yatsa babu wanda ya isa ya ɗaga a cikinsu.

Jim kaɗan Marcus ya dawo da wata na'ura, shi da kansa ya jonata a ɗakin, sannan ya miƙawa Zaid wasu abubuwa guda biyu, masu suffar biro, waɗanda ke jone jikin wannan na'urar da ya jona.

Yana kallon Usman ya miƙa hannunsa ya karɓa.

Sannan ya karawa Usman saitin ƙirjinsa, wata zabura da Usman ɗin ya yi ce tasa sauran ma dawowa cikin hayyacinsu, karkarwa yake kamar wani me farfaɗiya, ga bakunansu a kulle, babu damar magana, ihun ma ba sosai ake jiyowa ba, babu ko ɗugon tausayi haka Zaid ya ci gaba da zona masa shocking ɗin nan a jikinsa, dan babu abun da yake hangowa a idonsa face Rabi'a, sanda ya sameta kwance a gadon asibiti, sai kuma hoton result ɗinta da Huzaifa ya danƙa masa.

Kan kace wani wani abu Usman ya suma kusan sau huɗu, sai da ya kusan aika ɗan mutane lahira kafin ya ƙyaleshi, ya dawo kan Jaz, dake kusa da kujerar Usman ɗin, haka ya yi ta gana masa tasa azabar.

Sauran tun kafin a zo kansu suka fara shan jinin jikinsu, J boy harda fitsari a wando.

Bai ƙyalesu ba saida ya ɗanɗanawa ko wannensu, sannan ya sa aka kawo masa kyakkyawan madoki, ya shiga dukansu yana ƙarawa, saboda gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe, ba ya jin ko ɗigon tausayinsu, don suma ba su ji tausayin Adawiyya ba sanda za su haike mata.

Ganin Zaid niyyar kashesu yake ya sa Rhoda saurin shigowa cikin ɗakin tare da faɗin:
“Ya isa haka Zaid...!”
Cak sandar da ha ɗaga dan bugawa Usman a ka ta tsaya a iska, dan niyyarsa ita ce ya masa wani kyakkyawan bugu a tsakiyar kansa, wanda zaisa ya tuno da auren uwarsa.

Dan duk cikinsu ya fi jin haushin Usman, saboda shi ya fi kowa irin wannan halin zalincin a cikinsu.

A fusace ya cillar da madokin yana huci, idanuwansa sun firfito waje, ya danne haƙwaransa na ƙasa da na saman, kallonsa kawai idan mutum ya yi sai ya bashi tsoro, dan shi sam bai iya fusta ba.

Kafaɗarsa ya ɗaga yana sharce gumi.

Baya ya juya musu baya yana maida numfashi.

Ganin kamar Usman na san magana ya sa Rhoda isa gareshi cikin hanzari, tare da buɗe masa bakinsa.

Idanuwansa ya lumshe yana buɗewa, dan sam baya cikin hayyacinsa, ya jikkata sosai ba kaɗan ba.

“Wallahi...

Mu...

Mu ne...

Mu...

Ne muka...

Muka mata f...

Fyaɗe!”
Wani irin duka Zaid ya kaiwa katangar dake gabansa kamar zai fasata, a fusace ya juyo zai kuma dawowa kansu, amma Rhoda ta yi saurin riƙe shi.

“Ya isa haka Zaid....

Ya isa, tun da sun riga da sun amsa lefukansu, ka ƙyalesu kawai!”
Leɓensa na ƙasa ya ciza ya na huci, ji yake kamar wuta ce ke ci a ƙirjinsa, kamar idan be daki bayin Allahn nan ba ba zai huce ba.

KULIYA POV.

“An ce yau Lion ya kawo ziyara fa!”
Da sauri ya ɗauke idonsa daga kan laptop ɗin gabansa ya kalli Symon dake wannan batu.

Symon ya gyaɗa masa kai.

“Da gaske nake, haka na ji ɗazu ana ƙus-ƙus ɗin zancen...

Amma an ce bai jima ba ya tafi, kuma ma wai na ji ana cewa ya kawo ƙarshen assignment ɗinsa ne”
Ba shiri Kuliya ya saki wani murmushi, dan kuwa burinsa na gab da cika, Chidera ya masa alƙawarin daga zarar Lion ya kammala assignment ɗinsa zai haɗasu.

Har ya tashi daga aikin ransa ƙal, haka ya nufi gida cikin farin ciki.

Da sallama a bakinsa ya tura ƙofar falon gidan nasa.

Mishal dake zaune a kan kujera tana rubutu ta aje rubutun ta iyo kansa da gudu, shi ma yana dariya ya buɗe mata hannyensa ta shige jikinsa, harda ɗagata sama, dan tsabar farin cikin da yake ciki.

“Wannan farin cikin fa?...

Na menene?”
Mishal ta tambaya a sanda ya sauƙeta.

Hancinta ya ɗan ja yana murmushi.

“Kin tuna da labarin wani lion da na baki?”
Ta ɗan yi shiru tana san tunawa, can kuma sai tace.

“Haaaa!

Na tuna...

Ko ba labarin wannan zakin da yake cinye 'ya'yan wata barewa ba?...

Wannan wanda ka karanta min a cikin littafin stories ɗin nan?.”
Kuliya ya dunguri kanta yana faɗin.

“Silly girl, ba shi ba, wannan role model ɗin nawa da na taɓa baki labari, ki tuna”
“Eh yanzu na gano...

Kun haɗu ne?”
Kansa ya girgiza yana ɗaga kafaɗarsa.

“A'a, da yarar Allah mun kusa haɗuwa dai”
“To Allah ya yarda...

Yanzu ka je ka yi wanka, na tanadar maka abincin da ka fi so”
Peck ya mata a kumatu yana sakinta.

“Ok bari na yi sauri”
Mishal ta bi bayansa da kallo tana murmushi.
*No.86, Garki 2, Abuja...*
*10:30pm*
RABI POV.

Tana daga zaune a falo tana warewa Zaid kayan bikin da Umma ta bata ta kawo masa, dubulan da alkaki ne, cikin wata farar roba guda ta bata tace ta kawowa Zaid.

Ta kasa misalta kalar farin cikin da take ciki a yau, dan sai a yanzu take ganin rayuwarta ta dawo dai-dai, rayuwarta ta hau seti, wani irin setin da a da ma bata dedetu kamar yanzu ba, Allah ya shirya Abbansu, Habiba ta gane kurenta, Mama ta yi nadama, Allah ya bata miji na gari, budu da ƙari yau an ɗaurawa Anti Saratu aure da mijin da take so, kuma a yau ita ma anti Saratun za ta kwanan gidan mijinta, menene ya fi wannan daɗi?.

Jin an banko ƙofa yasa ta miƙe da sauri tana kallon side ɗin ƙofar.

Ganin Zaid ya shigo cikin wani irin yanayi ya sa da sauri ta nufe shi tana faɗin.

“Raj!...

Me ya sameka?”
Tsayawa ta yi a gabansa tana dubansa, kallonta kawai yake da idanuwansa da suka kusan lumshewa duka.

Gaba ɗaya oxford shirt ɗin jikinsa ta jiƙe da gumi, tie ɗin ya warware a wuyansa, ga kuma suit ɗin riƙe a hannunsa.

Ba tare da ta ankata ba ta ga ya saki suit ɗin daga hannunsa, sannan ya fincikitota ta faɗo jikinsa, ƙanƙameta ya yi kamar me shirin tsaga ƙasusuwanta.

Wannan sanyi Rabi ta ji ya shiga bin jikinta, ga wata siriryar iska da ta ke bi ta saman kunenta.

A hankali ta ɗago da hannunta ɗaya ta ɗora shi a kan bayansa, ɗayan kuma ta ɗora shi a kansa.

“Menene ya faru?”
Ta tambaya da ƙyar.

Saboda shirin zamewa ta faɗi ƙasa da take.

Zaid ya ƙara matseta a jikinsa ya na faɗin.

“Na je Madallah, sai suka ce min wai kina gida”
Kanta ta gyaɗa tana shafa bayansa.

“Umm...
Chapter 69 · 0% Book details