Sashe 2
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma yanzu fa ?, gashin nata ma ya fara raguwa saboda rashin gyara, kalabar da Saratun ke mata ita kaɗai kan nata ke samu.
Saratu ta gyaɗa kanta sannan ta ce.
“Allah kai mu goben”
Har Rabi zata fita da ga ɗakin sai ta juyo.
“Wani kala zan miki ?”
“Ɗan gama nake so”
Da ga haka bata ƙara cewa komai ba ta gyaɗa kanta, sannan ta fita da ga ɗakin, wanka ta je ta yi, ta fito bayan da ta gama wankan, saboda yanzu ana cikin azumi shi yasa ayyukanta suka ragu a gidan.
Dan idan baki buɗe ne, sai ta kai niƙan alkamar da Habiba ke yin finkason safe, idan kuwa a week end ne ita ce ma da kanta take suyar finkason.
Kuma ta hanyar kuɗin da take samu a finkason, da albashi da ake bawa Rabin a wurin aikinta, Habiban ke iya kula da gidan, dan komai na gidan ita ce ke yi.
Bayan ta shiga ɗakin, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki hijabin da ta fitar ta saka, ta yiwa Saratu sallama, ta fita.
“.....Kin ji matsalata da ke, dan Allah Habiba yanzu idan baki rufa min asiri ba waye zai rufa min?....”
Rabi ta ja ta tsaya a sanda ta ɗora idonta a kan mahaifinsu tsaye yana ƙanƙan da kansa a gaban Habiba,wadda ta wani ɗaga kai sama tana shirin zazzago buhun masifa.
“Wallahi Ɗan Lami baka isa ba, a kan me zan ɗauki kuɗi na baka?, bacin na san caca za ka je ka yi da su......”
Rabi bata tsaya ta gama jin abinda take faɗi ba ta sa kai ta fita.
Kuma abinda Habiban ta faɗi gaskiya ne, dan baban nasu babu wani aiki da yake face cacar, duk kuɗin da zai samu a caca suke ƙarewa.
Sai da ta ɗan tsaya a ƙofar gidansu, ta ɗan ɗaga kai saka, da ga nan inda take tana iya hango dutsen zuma rock, dubanta ya kai kan tarin bolar dake tsallaken ƙofar gidansu.
Bolar har tsiri take dan tsabar yawanta, da sauri ta ɗauke kanta da ga barin duban bolar, dan Allah ya sani idan ma takalleta zuciyarta har wani tashi take, dan ta tsani ƙazanta a rayuwarta.
Haka ta ci gaba da tafiya a cikin ƙazamin layin nasu, wanda kwatanni da datti suka masa ƙawa.
Akasarin mazauna unguwar ta Madalla masu magana da harshen gwari da baagi ne, sannan akwai hausawa sai nufawa, da wasu sauran yarukan, sannan a cikinsu akwai musulmai da cristian.
“.....Rabi!”
Ta juyo saboda jin an kiran sunanta, gamin wanda ke kiran nata yasa ta yi murmushi tana juyowa gaba ɗaya, Zara ce, mutum ɗaya da za ta iya ɗagawa ta kira da ƙawarta.
“Aikin za'a je?”
“Eh mana, keda kika sani”
Suka ɗan yi dariya.
“Kunu kika siyo ?”
Rabi ta tambaya yayin da idonta ya sauƙa kan jug ɗin dake hannun Zaran.
“Eh wallahi, bari na wuce, kafin Umma ta soma faɗan na daɗe....”
Kuma daga haka suka yi sallama, bakin titi ta fita, a titin ma sai da ta yi wata doguwar tafiya a ƙafa, kafin ta iso Ɗan kogi motor park.
Inda ta saba hawa mota, ta biya kuɗin da ta saba biya a kullum, wanda Habiba ke bata dan yin kuɗin motar, saboda da ga gidan nasu zuwa makarantar da take aikin akwai nisa.
Tafiyar kusan minti 40 ce.
Sun yi doguwar tafiya a motar, kafin suka isa Joy Emodi CI inda za'a sauƙeta, daga nan ta soma tafiya a ƙafa, wadda ta ɗauketa tsawon lokaci, kafin ta iso makarantar da take zuwa aikin shara.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja*
A hankali wata farar mota ƙirar Corolla hybrid ta yi parking a harabar makarantar. ko minti ɗaya ba ta yi da parking ba, ƙofar gidan baya na motar ta buɗe.
Wata matashiya ta fito,sanye cikin wata baƙar pleate skirt, da kaɗan skirt ɗin ta sauƙo gwiwarta, sai farar oxford shirt, wadda ta ɗora maroon suit a kai, daga gefenta suit ɗin na dama an manna symbol ɗin makarantar, wuyanta saƙale da tie, kanta babu ko ɗankwali, sai gashin kanta wanda ya ji gyara, an ɗaureshi cikin pony rail, jelar sai reto take a bayanta.
Bayanta goye da backpack ɗinta me kyau, ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers.
Kuma ba ita kaɗai ce ke sanye da irin kayan ba, dan gaba ɗaya ɗaliban dake kai kawo a harabar makarantar sanye suke da irin kayan jikin nata, maza ne kaɗai ke saka wando, kuma shi ne abinda ya banbantasu, hakan ke nuna cewa kayan shi ne uniform ɗin makarantar.
Tafiya ta fara cikin takunta na wanda ƙuriciya bata gama saki ba.
“MISHAL!, kin manta abincin ki....”
Muryar drivernta malam Ali ta faɗi da ga cikin motar.Tsayawa ta yi da tafiyar, sannan ta juyo ta kalli motar, kafin ta fara takowa zuwa wurin motar.
Ba tare da ta ce masa komai ba, ta buɗe gidan baya ta ɗauki lunchbox ɗin nata, ta rufe ƙofar motar, kana ta ɗaga masa hannu alamun bye, sannan ta yi gaba.
Malam Ali ya girgiza kai yana murmushi, a cikin ransa ya na wa Mishal ɗin fatan shiryuwa, ita duk gari ana azumi amma banda ita, zai iya cewa tun da aka fara azumin ma bai fi guda goma ta yi ba, da ya mata magana ma sai tace masa wai akwai wahala haɗa azumi da zuwa makaranta.
Duk inda ta wuce sai an bita da kallo, amma ita ko a jikinta, dan bata damu ba, saboda wannan ba shi ne karo na farko da aka saba bintada kallon ba, wasu kallonta suke cikin tsoro saboda sanin halinta, wasu kuma cike da burgewa saboda sanin jarumtarta, wasu kuma suna kallonta ne cikin jin haushi, wata ƙila saboda faɗa ya taɓaa haɗasu.
Bata ko kalli kowa ba, duk da tasan cewa kowa kallonta yake.
Har ta kai ƙofar class ɗinsu, ta saka ƙafarta a cikin ajin, sai kuma ta dawo da baya, ta gyara tsaiwarta tana kallon wannan yarinyar.
Yarinyar da ke aikin shara a makarantar tasu, ba yau ne karo na farko da ta fara ganin yarinyar ba, hasalima tafi wata shida tana ganin gilmawarta a makaranta.
Ba wannan ne yasa take kallonta ba, kawai rayuwar yarinyar ce ke bata tausayi, dan da alama yarinyar na cikin halin ƙuncin rayuwa, ita kuma haka Allah ya yi ta, duk da baƙin halinta da rashin jin maganarta da wasu ke gani, Allah ya hallici zuciyarta da tausayin wanda bashi da shi, haka Allah ya saka mata tausayin yarinyar.
Duk da ba za ta iya kiranta da yarinya ba, saboda da alama ta girmeta, saide bata kai sa'ar Akinta(Yayanta) ba.
Da alama ma ita yarinyar bata lura da ita ba, dan moping ɗin floor take bil haƙƙi da gaskiya.
Ba tare da ta yi komai ba, ta juya ta shiga ajin nasu.
Malamin geography ne a ciki, kuma tana shiga ajin ya yi tsit!, kallo ya dawo kanta kamar kullum.
Ba tare da ta damu ba ta nufi seat ɗinta.
“Ke Hafsat Muhammad Auwal!”
Uncle ɗin geographyn ya daka mata tsawa, ta juyo ta kalle shi da sauri, idonta babu ko da ƙwayar tsoro a ciki, dan bata saba jin tsoron kowa ba, kowa gani take kai kai ɗaya yake da ita.
A hasalle Uncle ɗin ya cillar da littafin da ke hannunsa, ya ɗauki wata cane ya yi kanta, yana ƙarasawa kusa da ita ya ɗaga bulalar sama zai zabga mata ta kai hannunta ta riƙe bulallar.
“Babban kuskuren da za ka yi shi ne duka na da wannan bulalar, dan Wallahil Azim ka kuskura ka dakeni sai na rama”
Ta ƙarashe tana wancakalar da bulalar, Uncle ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa, yana ci gaba da kallon yarinyar, Ba ƙaramin jajircewa ya yi ba da har ya iya yunƙurin dukan yarinyar, dan malamai da dama na yawan bada labarin yarinyar a staffroom, wasu da ga cikinsu ma kan ce wata ƙila aljana ce, dan normal ɗan adam ba zai iya abin da yarinyar nan ke yi ba.
Ta addabi kowa a makarantar, watan da ya wuce har wani malami ta mara, ɗalibai kuwa kullum sai an samu wanda zai kawo ƙararta.
Sai da ta aika masa harara, sannan ta aje jakaarta a kan desk, ta zauna tana baza ƙwayoyin idonta a cikin ajin, hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa.
Sai da ta yi ƙwafa sannan ta buɗe jakarta ta ɗauko littafi ta gyara zamata ta shiga kwafar note ɗin da uncle ɗi ya ci gaba da yi.
*
“Wai me yasa ke bakya azumi kamar 'yan uwanki musulmai”
Muryar Angelica yarinyar Mishal ta faɗi a sanda aka fito break, dan sai dai a kirata da yarinyarta, saboda duk wani aike ko bautar Mishal ɗin ita Angelican ce ke yi.
Kuma kaf makarantar Mishal bata da ƙawa ko ɗaya, ita ma Angelican ita ta cuso kanta gareta.
Mishal ta ture flask ɗin gabanta tana miƙe ƙafa.
“Saboda bana san wahala, bazan iya haɗa azumi da zuwa makaranta ba”
Ta bata amsa cikin harshen turanci, kamar yanda itama Angelican ta mata maganar cikin harshen turancin, kasancewarta baturiyar Engiland.
Aiki ne ya kawo mahaifinta zama a nigeria.
“Amma su Rashida su na yi”
“Baki ji me nace ba ?”
Sai Angelica ta girgiza kai, tana kai loma bakinta.
“Kai ka ga wata balarabiya”
Wani sabon ɗalibi da ya fara zuwa makarantar ya faɗi yana kallon Mishal da ga nesa, abokin nasa da ake nunawa Mishal ɗin ya juyo ya kalli wurin, kuma a lokaci guda idonsa ya zare cike da tsoro da kuma mamaki.
“Kai!!, karfa kace min santa kake!”
Sabon ɗalibin me suna Abdul ya yi murmushi.
“Ka jika da wani zance, waye zai ga wannan kyakyawar ya ce ba ya so, Allah da da na ganta na ɗauka balarabiyace”
Abokin ya haɗiye wani abu.
“Abdul da ka je ka ce kana san wannan, gwara ka samu Madam Joke (Malamarsu ta Math) ka ce kana santa”
Abdul ya ƙyaƙyale da dariya.
“Kai ana gabar kana yamma, me zan yi da wata Joke arniya kuma tsohuwa, ga kyakkyawar baby a nan”
“Idan za ka ka bar jirana, tun da na haneka baka ji ba, idan ka je ita zata maka bayani....”
Kuma yana kaiwa nan ya fita da gudu ya bar wurin zaman cin abincin nasu.