← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 80

Sashe 54

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu shiri ta faɗi a ka gadon._
_Duk da idonta a lumshe yake, ta na jin sanda suke rabata da tufafin jikinta, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, sai dai hoton abun da take gani ya koma ja, saboda jinin da ya wanke mata fuska, ba sosai take cikin hayyacinta ba, amma ta na ji ta na gani haka suka shiga haike mata ɗaya bayan ɗaya._
_Duk da irin raɗaɗin azabar da take ji, ba ta da damar yin ihun neman agaji, ta na kwance ne a wurin kamar gawa, amma da ko wace azaba da suke mata jikinta ya na amsawa, ko wanne a cikinsu sai da ya haike mata sau biyu, tun tana buɗewa idonta fa lumshe har sai da komai na kanta ya ɗauke, ji da ganinta suka yi nisa, numfashinta ya yi sama._
_“Usee kamar yarinyar nan fa ta mutu”_
_Usman ya ɗan karkato da kansa kaɗan ya kalli kan gadon, inda Rabi ke kwance malale cikin jini, babu tufafi a jikinta.

Sai ya zuƙi sigarinsa, ya furzar ya na faɗin._
_“Ku ɗauketa ku cillar da ita, idan abun sha ya ƙare, me za ayi da kwalba?”_
_Ba tare da ɓata lokaci ba suka cika umarninsa, a cikin blanket ɗin dake kan gadon suka nannaɗe, sannan suka ɗauketa suka saka a mota, suka fita daga gidan.

Sun ɗan yi tafiya me tsayi daga gidan Usman ɗin, kafin suka samu gefen titi, suka faki ido, duk da dare ne ,babu kowa a layin, suka cillar da ita a wurin kafin suka ƙara mai._
(Ya Ilahi ya Allah!...).

A hankali wata siririyar ƙwalla ta zubo daga idon Rabi wada ke kwance a kan gadon marasa lafiya, tana nan kwance kamar gawa, kuma idanuwanta a lumshe.

Wata ƙwallar ce ta sake gangarowa daga idonta ta shiga kunnenta.

Sannan a hankali bakinta ya buɗe, cikin wata dasasshiyar murya ta fara faɗin;
“Da...

Dan...

Dan A...

Allah, kad...

Kada ku...

Kada ku min...

Ka...

Kar ku...

Cutar...

Cutar da ni...

Ni...”
Haka bakinta ya ci gaba da faɗi, kafin kuma jikinta ya fara jijjiga, da alama duk abun da ya faru a waccan ranar take gani a cikin mafarkinta.

Cikin abun da bai wuce daƙiƙa ɗaya ba, ta wangale idanuwanta tar, ta na maida numfashi kamar wadda ta yi wani aikin ƙarfi, idonta ta ƙara lumshewa, sannan ta buɗe su tar.

Kafin ta miƙe zaune, ta na ta dube-dube, sai kallon ɗakin take, kafin dubanta ya dawo jikinta, tabbas ta na asibiti ne, to duk yanda aka yi ɓacin ran da Raja ya saka mata ne ya sa ta suma, shi ne aka samu wani bawan Allahn ya kawota asibiti, har ta yi mafarkin an mata fyaɗe.

Wanna hasashen da zuciyarta ta yi ne ya sa ta sauƙe ajiyar zuciya, haka ne ma, haba!, da ma in ba haka ba ta ya za'a yi ace an mata fyaɗe?!.

Hannunta ta kai ta ciccire na'urorin da aka saka mata a jikinta, sannan ta shiga ƙoƙarin sauƙo da ƙafacunta ƙasa, ta daddafa har ta samu ta iya sauƙa daga kan gadon.

Sai de me?, miƙewar tata ke da wuya ta ji ƙasanta ya yi wata irin amsawa, ba wai amsawa ta zafi ba, a'a, ji ta yi kamar an saka wani abu an ɗaure wurin, duk da haka ba ta karaya ba, wannan hasashen da zuciyarta ta yi shi ne ya ba ta ƙwarin gwiwa da kuma na zuciya, haka ta tattaka cikin wani irin taku me kama da na 'yan koyon tafiya, ta nufi banɗaki.

Daɗewar da ƙafafunta suka yi ba su yi tafiya ba ya sa suke amsawa idan ta na taku, ƙofar bayin ta tura, sannan ta shiga, kai tsaye jikin mirror ta isa, kuma abun da ta gani shi ne ya rikirkito da duniyarta ƙasa.

Wata tsawa da walƙiya suka haska a cikin kanta, wani irin tashin hankali da ba ta san akwai irinsa a duniya ba ya ziyarceta.

Wannan yankan da aka mata a gefen fuska, ya na nan, har da ɗinki an yi wa wurin, dan har ya warke an cire zaren.

Sannan ga gashin kanta da aka yanke mata, gashinta da a da yake sauƙowa har gadon bayanta, shi ne yanzu yake iyaka kafaɗunta, ga kuma tabon dukan da aka mata a kanta.

Sannan wannan raunin fuskar tata shi ne ya ɗan sauya kammanin fuskarta, duk da ba du ba, amma yanayin fuskar tata ya sauya.

Waɗanan alamomin su ne suka ƙaryata hasahsen zuciyarta, waɗanan alamomin su ne suka murmushe fatanta har garinsa, wanan alamomi su ne suka tabbatar mata da duk abin da ya faru a waccan ranar ba mafarki ba ne, gaskiya ne, da gaske ne cewar waɗanan mugayen samarin guda biyar, sun haike mata, da gaske ne cewar yanzu ita ba ta da wata martaba kamar ta sauran mata, kuma da gaske ne cewar ita yanzu ba budurwa ba ce, yanzu ita ba ta da wata kima da daraja wadda jama'a za su kalleta da ita, ba ta da wani abu da za ta nunawa mijin da za ta aura.

A lokacin da ƙwaƙwalwarta ta kai ƙarshe wurin zayyano mata waɗanan kalaman, a dai-dai lokacin ne ta ɗago da hannunta ta shafa fuskarta, ta taɓa kanta.

Nan take ta ji wani kukan ɓacin rai da na tashin hankali sun haɗe wuri guda sun tsaga haƙwaranta, sun raba laɓanta, sun fito cikin 'yancinsu.

Wani kalar kuka take me sauti, jikinta har rawa yake.

“Me ya sa ni ba ni da ƙaddara me kyau?!, me ya sa komai nawa yake rugujewa?!

Me ya sa ni ba zan yi farin ciki kamar kowa ba?!, Me ya sa za'a zaɓi da a lalata min rayuwa?!, Me na yi haka?!

Wani kalar zunubi gareni?!, Allah na tuba ka yafemin, Allah na roƙeka da kada ka ƙara ɗoramin wata jarrabawa bayan wannan, ya Allah na cutu, an cutar da ni, kai ne me girma, kai ne sama da kowa, kai ne sarkin da babu wani me milki irin nasa, Allah kana gani ya Allah!

Ya Allah ka bi min haƙƙina!”
Cikin gunjin kuka da ƙaraji take furta hakan, ta na yi tana kallon sama, can kuma da takaici ya ciwota ta sa hannunta ta ture kayan da suke kan mirrorn.

Sannan ta saki wani ƙaran takaici, ta riƙe kanta tana faɗin.

“Me ya sa komai sai ni?, me yasaaaa!”
Kuma a dai-dai lokacin aka turo ƙofar banɗakin.

RAJA POV.

Kamar Kullum, yau ma ya na zaune a gaban gadon Rabi ya na kallonta, yau kwanansa biyar kenan ya na jinyarta, kuma in har ya zauna a wurin nan ba ya tashi sai lokacin sallah, haka Rhoda za ta zo ta yi ta masa mitar ba ya san cin abinci, ko kuma ta kawo masa abincin, amma ba zai ci ba.

Wayarsa ce ta yi ƙara, alamun shigowar kira, sai da ta yi ringing kusan sau uku, sannan ya ja dogon tsaki ya na saka hannunsa a aljihu ya zaro wayar.

'Huzaifa' ya gani rubuce kan screen ɗin, sai ya ɗaga kiran ya na dawowa da dubansa kan fuskarta.

Huzaifan ne ya masa magana kan ya zo office ya na san ganinsa, ba dan ya so ba haka ya tashi ya je office ɗin.

Kuma sun ɗan jima suna tattaunawa kan gwaje-gwajen da ya ce a yiwa Rabi'an, kuma an yi ɗin, sannan result ya yi kyau, babu wata matsala tare da ita, komai nata lafiya ƙalau, matsala ɗaya ce, ita ce wanan doguwar sumar da ta yi, kuma ga shi ba su san takamemen lokacin da za ta farfaɗo ba, duk da ya ji daɗin kyan result ɗin, sai kuma zuciyarsa ta cika fal da tsoron kada ya rasata, tun da sun ce ba su san lokacin da za ta tashi ba.

Da waɗanan saƙe-saƙen ya iso ƙofar ɗakin, sannan ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, wani irin bugu zuciyarsa ta yi, a sanda ya kalli kan gadon ya ga wayam, kuma kafin ya yi wani tunani, ya jiyo kukanta haɗe da maganarta a cikin bayi.

Tsabar kiɗima bai san sanda ya saki file ɗin hannunsa ba, sannan ya nufi banɗakin da gudu.

Kallonsa ta tsaya ta na yi da jajayen idanunwata, waɗanda bai hango komai a ciki ba face ɓacin rai da takaici, bai san me ya da ba, sai ya samu kansa da kasa ƙarasawa cikin bayin.

Nan take fuskar Rabi ta rikeɗe zuwa mamaki ma bayyani, wai me ya sa Raja ba zai rabu da ita ba ne, ta ya aka yi ya san inda take?, tukkunna ma ta ya aka yi ta zo asibiti?, kuma ma me yake a nan ɗin?.

“Me kake a nan?”
Ta tambaya tana ja da baya, a wannan karon da Raja ya saurari muryarta, sai hankalinsa ya dawo jikinsa, ta farka!, Rabi'a ta farka, sai ya shiga takowa cikin banɗakin fuskarsa ɗauke da murmushi, a gefe guda kuma ga hawaye na zubowa daga idonsa.

“Ka dakata daga inda kake!”
Ta faɗa cikin ƙaraji, ta na nuna shi da ɗan yatsa.

Cak, ƙafafun Raja suka tsaya, baki sake yake kallonta.

“Kada...

Ka ƙara ko da taku ɗaya ne”
Still bai ce komai ba, kawai ya tsaya ya na kallon fuskarta.

“Ka juya ka fita, ba na san ganinka”
Wata iriyar hautsinawa zuciyarsa ta yi a ma'ajinta, bakinsa da zuciyarsa suka shiga rawa a lokaci guda, da ƙyar ya iya faɗin.

“Ni...

Ni ne fa Ammata...”
“Kada ka ƙara kiran sunan!”
Ta faɗi a tsawace ta na nuna masa ɗan yatsa, idanunwata sun firfito waje, sannan ta ci gaba.

“Ba na san ganinka Zaid, ka fita daga nan, babu abin da ya haɗa hanyata da ta ɗan daba, me kashe mutane!

You are a goon Zaid!”
Wannan karon muryar tata a raunane ta fito, kuma har zuwa yanzu ƙafafunta rawa suke, ta kasa tsayawa a gu ɗaya, saboda jikinta babu ƙarfi, hatta da maganar da take ƙarfin hali kawai take.

“Na yi nadamar saninka da na yi, na yi nadamar barin zuciyata ta fara sanka, na yi nadamar haihuwata ma da aka yi, na yi na damar komai a duniyar nan....
Chapter 54 · 0% Book details