← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 80

Sashe 79

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Damm, gabanta ya buga, ganin Zaid tsaye a tsakiyar ɗakin, hannunsa riƙe da takardar da ta manta bata ɓoye ba, kuma ba ma wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, wani irin kallo da ta ga yana mata shi ya haɗe kayan cikinta waje guda.

Da ƙyar ta haɗiye yawu ta fara takawa tana nufarsa.

“Adawiyya miye wannan?”
Ya tambaya yana nuna mata takardar, sai da cikin Rabi ya yamutsa, jin yanda amon muryarsa ya fito a ƙasashe.

“Ba magana nake miki ba?!”
Ya faɗa cikin tsawa, yana ƙoƙarin saka ƙaton dutse, dan danne ɓacin ran dake taso masa.

Abun ya bala'in ɓata masa rai, a matsayinsa na uban ɗan cikinta, kamata ya yi ace ta sanar da shi, amma me ya sa za ta ɓoye masa?.

Sosai Rabi ta tsora, ganin yanda ya buɗe lumsassun idanuwansa a kanta.

Hakan wani abu ne da bata taɓa gani ba a tare da shi, nan take ta fara in'ina.

“Ko ba ni ne uban cikin jikinki ba ya kamata ace na sani, ballantana na san da cewa ni ne ubansa, me ya sa za ki ɓoye min?!”
A wannan karon kam ita ma Rabi ranta sai ya fara ɓaci.

Dan haka tace.

“Miye laifi na a nan?, ni kai na ban san cewa ina ɗauke da ciki ba, sai bayan da Anna ta ankarar da ni, hakan ya sa na je na yi gwaji a yau ɗin nan, kuma shi ma gwajin ya tabbatar da ina ɗauke da juna biyu.

Tun bayan dawowarka nake ta neman hanyar da zan bi na faɗa maka, amma na rasa, shi ne na yi laifi?...”
“A'a kam, ba ki yi laifi ba!.

Tun ɗazu na dawo gidan, me yasa da na dawo ba ji faɗa min ba?!”
“Ya isheni haka Zaid!”
Ta faɗi ita ma a tsawace tana kallon cikin idonsa.

“Wai akaina aka fara ciki?.

Na ce maka ƙoƙarin gano hanyar da ta dace na faɗa maka nake, amma sai ka hau ni da faɗa?, na ga dai ba wata tara cikin ya yi ba tare da na sanar maka ba!”
“Ya yi kyau Adawiyya, yau kanki tsaye kike kiran sunan, a kan wannan cikin kike gaya mun duk maganar da ta zo bakinki ko?, ki riƙe abunki na bar miki!”
Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya aje mata takardar ba.

Rabi ta zame ƙasa tana fashewa da kuka.

Me ya sa ma za ta bari har sheɗan ya shiga tsakaninsu?, kuma ai shi ma ya na da laifi, mi ye na saurin fusatar haka?, tun bayan aurensu ba su taɓa faɗa ba sai yau, hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, har ta kwanta bata dena kuka.

Bacci ma a ranar sai ya gagareta.

Ta rasa inda za ta sa kanta, musamman idan ta tuna da yanda ta ɗaga masa murya, abun sai ya soketa a zuciya.

Ganin zama cikin kukan ba zai finsheta ba ya sa ta miƙe salin'alin ta nufi ɗakinsa, ƙofar ta tura a hankali tana saka kai ciki.

A kunne ta samu wutar ɗakin, shi kuma ya na zaune daga kan gado, ya zuro da ƙafafaunsa ƙasan gadon.

Kuma duk da ya bawa ƙofar baya, tana iya ganin yanda ya yi tagumi.

Wani kuka me ƙarfi ya ƙwace mata, dan gani take kamar ita ce silar rashin kwanciya baccin nasa.

Da gudu ta hau kan gadon nasa, ta shiga rarrafe a kan gadon, har ta isa inda yake, tana isa dab da shi, ta zura hannayenta ta bayansa, suka kewayo ta gaba, kanta ta kwantar a bayansa tana fashewa da kuka.

Zaid ya rintse idonsa, zuciyarsa na masa zugi, yanzu haka zaman da ya yi na nadama ne, sai bayan da ya zo kwanciya ya ga rashin kyautawarsa kan abun da ya mata, be kamata ace ya ɗaga mata murya haka ba, kuma be kanata a ce ya fusata daga ganin takarda ba.

Zaman da ya yi anan yana ta tsara yanda za ayi ya bata haƙuri ne gobe da safe, sai ga shi kuma ita ta zo da kanta dan ta ba shi haƙurin.

“Ka yi haƙuri Raj, na tuba!”
Da ƙarfi ya sauƙe ajiyar zuciyar, sannan ya saka hannayensa a kan nata yana rabasu daga ruƙon da ta masa, sannan a hankali ya sauƙo da ido daga kan gadon, ta dawo gabansa ta tsaya.

Ya ɗan ɗaga kansa ya kalleta, fuskar nan sharkaf da hawaye.

Sai ya raba cinyarsa biyu, ya zaunar da ita akan ta dama.

Tana zama a kan cinyar tasa ta ƙara shigewa cikin jikinsa, tana nanata masa kalaman ban haƙuri.

Shi ma rungumeta ya yi, ninkun ƙauna da santa na ƙara shiga cikin zuciyarsa.

“Ya isa haka Adawiyya, ko tsakanin harshe da haƙuri ana samun saɓani.

Wannan karon sheɗan ya yi nasara a kanmu, dan haka sai mu kiyaye nan gaba”
Kanta ta gyaɗa masa tana shanye kukan nata.

“I'm sorry too, na faɗa miki maganganu masu zafi”
Kanta ta girgiza tana ɗagowa daga jikinsa.

Hannunsa ya kai kan cikinta, yana jin santa da kuma na abun da ke cikinta na ƙara kama shi.

“Ina sonki Ammatana.

Wannan babbar kyautar taki ta fi min komai a yanzu”
Ƙara kwanciya ta yi a jikinsa tana lumshe ido.

“Allah alhamdulillah”
Ya faɗi yana ƙara matseta a jikinsa.

“Ina sanki 'yan matan Zaid”
“Ina sanka Kayali! (Arabic:My choice)”
Sai ya ɗan kalleta kaɗan.

“Da ma ke kika zaɓeni?.

Ca nake ai ƙaddara ta zaɓa miki ni”
Da sauri ta miƙe daga jikinsa tana shirin saka masa kuka, sai ya yi dariya yana ƙara kwantar da ita.

“Ki yi haƙuri.

Gaskiya ni me sa'a ne Ammata, a karon farko?”
Kanta ta ƙara cusawa a ƙirjinsa dan tsabar kunya.

“Diary baka da kunya”
Muryarta ta fito daga ƙasan ƙirjinsa.

Ya yi dariya.

“Wallahi ji na nake kamar wani sabon mutum, ji nake kamar yau aka haifo ni, duka burikana ɗaya bayan ɗaya suna cika...”
Ya faɗi a setin kunnenta.

Sai ta ƙara narkewa a jikinsa tana lumshe ido. dan wani bacci da take ji na shirin kamata.

KULIYA POV.

Kwance yake a kan gadon marasa lafiya na asibti, yayin da Mishal ke kwance a gefensa, kallon fuskarta kawai yake, yana tuna yadda ta yi mirƙisisi kan ita ba za ta tafi gida ba, don ita tare da shi za ta kwana.

Baccinta take hankali kwance, kamar tsimma a cikin randa.

Juyawa ya yi yana kallon window, saboda wata iska me daɗi dake shigowa ta windown.

A yanzu komai na rayuwarsa ya hau seti, ba ya jin akwai wani buri nasa da rage bai cika ba, komai ya setu, komai ya hau kan hanya, ya samu dangi, ɗan uwa, uwa, mata ga shi har da suruka, shi ko me zai yi in ba godewa Allahnsa ba.

Da ga nan kuma sai ya shiga tsara abubuwan da zai yi idan ya bar asibtin, dan ba zai yi shiru a kan abun da aka masa ba, kuma ya san ko suwa suka masa hakan, dan case ɗinsu shi ne aiki na ƙarshe da ya yi.
***
Haka Aliyu ya ci gaba da samun kulawar likitoci a asibitin, har zuwa lokacin da ya samu sauƙi, a cikin jinyar da ya yi, 'yan uwansu na haɗejia duka sun zo sun duba shi, ba ƙaramin daɗi suka ji ba a sanda suka ganshi, kuma shi ma ya ji daɗin ganinsu sosai.

Bayan ya warke ne suka ɗunguma zuwa Hadejia su duka, domin bikin Rhoda, wadda ta zaɓi sunan Rauda a yanzu, dan bayan ta karɓi musulunci aka tambayeta sunan da take so a sa mata, sai tace Zaid ya zaɓa mata, shi da kansa yace ta karɓi sunan Rauda, dan yana kama da sunanta na da, kuma ma'anar sunan ma me kyau ce.

Haka aka sha bikin amarya Rauda da angonta Zakar.

Wanda suka ci gaba da zama a haɗejia, kasancewar shi Zakar ɗin a nan haɗejian yake aiki.
*BAYAN SHEKARU BIYAR...*
*No.275, Asokoro, Abuja...*
Anna ce zaune a kan kujerar daning, su na magana da Aliyu dake zaune a kan kujerar dake facing ɗinta.

Mishal ce ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da tray, wanda ta ciko shi da wasu warmers, ga tulelen cikinta tana turashi gaba.

“Sannu Hafsat.

Kai Aliyu ka tashi ka temaka mata mana” cewar Anna.

Kuliya ya miƙe tsaye yana nufarta, trayn hannun nata ya karɓa, sannan ya ƙaraso ya aje shi a kan danning, ya koma inda Mishal take, ya kamo hannunta, tana takawa a hankali har suka iso danning ɗin, ya zaunar da ita a kusa da Anna ya na jera mata sannu, ita kuma ban da gyaɗa musu kai babu abun da take.

“Sai da na ce miki ki bar girkin nan, amma kika ƙi”
Anna ta faɗi tana dubanta, ita dai ba ta iya cewa komai, don tun bayan samun cikin nata ta koma muiskila, sam ba ta son yawan magana.

Ƙofar falon aka turo, Zaid da ya je ɗaukan Rabi'a a NFF (Nigerian Football Federation) centre ya shigo, sannan ita ma Rabin ta shigo tana biye da shi, sanye take da wata kimonoh, wadda ta saka jersyn Super Falcons a ƙasanta.

Kasancewar yanzu haka suna training a kan gasar WACON (Women's African Cup of Nation) da za'a buga nan da sati me zuwa.

Dan zuwa yanzu Rabi ta zama ɗaya daga cikin 'yan ƙwallon da ake ji da su a Nigeria, a taƙaicen-taƙaicewa ma a halun yanzu ita ce kw riƙe da wannan kambun na (Best African Women player).

Duk yanda ƙungiyoyi da dama suke son siyanta ta ƙi, don ta ce ba za ta taɓa barin ƙasarta ta koma wata ƙasar ba, saboda mijinta da kuma ɗanta.

“Maman Junior har an dawo?”
Cewar Kuliya dake zubawa Mishal ruwa a cup.

“Wallahi na dawo Papi.

Wai Mishal ke kika yi girkin nan?”
Rabin ta ƙarashe tana kallon kayan abincin dake zube a kan danning.

“Sai da na hanata, amma haka ta sulale ta shiga kitchen ɗin ba tare da na sani ba”
Cewar Anna, Mishal ta karɓi ruwan da Kuliya ke miƙa mata ba tare da ta ce musu komai ba.

“Ina Junior?”
Rabi ta tambaya, sakamakon rashin ganinsa a wurin.

“Junior!

Junior!...”
Haka ta shuga ƙwala masa kira tana baza idonta, don ganin ta inda zai ɓillo.
Chapter 79 · 0% Book details