Sashe 37
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma ita kanta ba ta ce ga dalilin da yasa take ba shi labarin ba, wata ƙila don zuciyarta na faɗa mata cewar a yanzu shi ne gatanta, ba ta da wani gata nan duniya bayan shi, tun da ba ta da uwa, ba uba, ba ɗan uwa.
Tun da ta fara bawa Kuliya labarin wani abu me kama da mashin ɗin yankan katako yake dagargaza zuciyarsa, ji yake ina ma ya na da damar da zai iya ganin bayan wannan mutumin, ko a baki ya tsani kalmar, bare kuma a ce matarsa aka yi kokarin aikatawa hakan.
“Wani hukunci aka ɗauka a kansa?”
Ya zaɓi da ya tambayeta ko zai ji salama game da yanda zuciyarsa ke masa zugi, ji yake kamar ya kurma ihu, ko raɗaɗin tsagewar zuciyar tasa zai ragu.
Mishal ta share hawayenta da gefen gyalenta.
“Cewa suka yi ai abun na gida ne, dan haka sai dai ayi haƙuri.
Wani abun takaicin ma shi ne; kakarmu Jadda ita ce tace babu wani wanda ya isa ya taɓa mata jika, kamar ni ɗin ba 'ya ba ce, ko wata ƙila dan ba ni da iyaye a raye ne, kullum ba ta da abun faɗi da ya wuce tana sanmu, amma ni sam ba na ganin son!...”
Ta ƙarshe tana sakin kuka me sauti a hankali.
Ashe kallon kitse Kuliya yakewa rogo, wasu abubuwan idan ta yi sai ka ce 'yar shekara 10 ce, amma idan ta yi wani abun kuma sai ka zaci ta kai 20, wani lokacin yarinta ce fal a zancenta, wani lokacin kuma sai ta yi maganar hankali, kamar ba daga bakinta take fita ba, hannunsa yasa a cikin aljihunsa, ya zaro mata hanki, sannan ya miƙa mata.
Mishal ta karɓa tana share hawayenta.
“Wannan na ɗaya daga cikin matsalolin societynmu.
Sai ki ga mutum ya aikata laifi, amma a ƙi ɗaukar mataki a kai, saboda ana ganin me laifin na gida ne, idan aka ɗaga maganar zumunci zai iya rabuwa.
Wannan zai bawa me laifin damar ci gaba da aikata laifukansa yana fakewa da kasancewarsa na gida.
Haka abun zai ci gaba da ƙaruwa kamar wutar daji” Cewar Kuliya.
Mishal ta juyo ta kalleshi, ita kam yau ya na bata mamaki, bata taɓa ɗaukar cewar yana magana cikin sanyi irin haka ba, kuma ta ɗauka cewar maganganunsa basu da tsayi kamar yanda ta saba jinsu daga bakinsa, amma yau da banbanci.
*
“Maraba Lale!”
Cewar Anna a sanda suka iso gidanta, tsaye take daga cikin falonta tana ta zabga murmushi, ta kasa gaskata abun da idonta ke gane mata, wai yau ita ce take ganin matar Aliyunta?.
Suna ƙarasa shigowa cikin falon ta kama haannun Mishal ta zaunar da ita a kam kujera, sannan suka gaisa, fara'ar matar ya sa Mishal sakewa da ita.
“Ni ce surukar ki 'yata, fatan ba za ki riƙa min ɗanyen tuwo ba”
Anna ta faɗi tana dariya, hakan ya sa Mishal ma yin dariya, banda Kuliya da ya haɗa girar sama da ta ƙasa, kamar baƙin hadarin dake shirin zubar da ruwa, don shi bai ga wani abun dariya a maganar ba.
“Kenan ke ce mamarsa?”
Ta tamabaya tana kallon Kuliya.
Anna ta gyaɗa mata kai.
“Ni ce nan mamarsa”
Mishal na murmushi ta ci gaba da ƙarewa fuskar Anna kallo, wai ko za ta tsinto wani abu guda da ya haɗa kamarta da ta Kuliyan. amma har ta gama yawo da idonta a kan fuskar Annan ba ta gani ba.
“Sunana Anna.
Ke kuma ya faɗa min suna ki Hafsatu ko?”
Mishal na murmushi tace.
“Hafsat dai, amma Mishal ake cemin”
Anna ta yi dariya tana kallon Kuliya da ya maze yana kallon tv, kamar ma be san abun da suke ba.
Anna ta ƙwalawa Siyama kira.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba, sai ga Siyama ta bayyana a falon.
Kamar yanda dalar ƙanƙara ke zaftarewa ta faɗi a yayin da zafin rana ya bugeta, haka zuciyarta ta zaftare ta faɗi lokaci guda, sakamakon idonta da ta ɗora a kan wata kyakkyawar yarinya me kama da 'yartsana, zaune a gefen Anna.
Ganin Kuliya da ta yi a gefe guda ya sa ta ji ƙarar faɗowar wani abu a ƙirjinta, kenan wannan ita ce matar Kuliya?, in dai kuwa wannan ita ce matar da ake ce ya aura, to babu ta yadda za ayi Kuliya ya kalli inuwarta bare ita kanta.
Duk da ta san cewa ita ma tana da kyau dai-dai gwargwadon, kuma a shekaru ba za ta wuce 23 ba, amma tun da Kuliya ya riga ya samu wannan kyakkyawa kuma sabon jini irin wannan yarinyar babu abun da zai yi da ita.
Yanzu ita shi kenan ta rasa Kuliya?, to yanzu ina za ta sa kanta?, ba ta jin za ta iya rayuwa me kyau tare da wani namijin da ba shi ba, ko da da take faɗin ta haƙura da shi faɗa kawai take, don ba ta hangowa kanta rayuwar da babu Kuliya a cikinta.
“Ba ki ga matar yayanki ba ne?
Ki gaisheta mana”
Muryar Annan ta dawo da ita zahiri, hakan yasa ta ɗauke idonta daga kan Kuliya da ta kafe da kallo, ta dawo da su kan 'yar ficilar yarinyar dake gefen Anna, duk da ba za ta kirata da yarinya can ba, don jikinta a murje yake, ta na da duk wata cikar sura irin ta 'ya mace, babu abun da Siyama za ta faɗa mata da ya wuce yawan shekaru.
“I'm the one that supposed to greet her...
Tun da ita ce babba”
Sassanyar Muryar yarinyar ta kuma katse mata tunani.
“A'a ita ya kamata a ce ta gaida ki”
Siyama ta haɗiye wani ƙullutun baƙin ciki a sanda take gaida yarinyar, cikin mutuntawa Mishal ta amsa ta, cikin san gano wani abu tsakaninta da Kuliya, don da ace ƙanwarsa ce kamar yanda Anna ta faɗa, ko kallonta ya yi, amma ji yanda ya hakimce ya na kallon tv abunsa kamar bai san akwai wasu hallitu a falon ba, kuma duk ta lura da irin kallon da Siyaman ke binsa da shi tun sanda ta shigo falon.
“Anna!
Na roƙi wani abu a wurinki?”
Mishal ta tambaya, bayan da Annan ta sa aka kawo mata abinci, zuwa lokacin Kuliya ba ya falon, don waya ce ta sameshi daga wani wai shi Symon, kuma bisa ga dukkan alamu maganar aiki ce, hakan yasa ya fice daga falon baki ɗaya, wannan Siyamar ma ba ta falon, saboda ba ta jima da shigewa ɗaya daga cikin ƙofofin dake falon ba.
“Ina jin ki 'yata, faɗi ko me kuke so, in dai bai gagara ba zan miki shi da yardar Allah!”
Mishal ta aje spoon ɗin hannunta tana sosa kai.
“Da ma so nake ki masa magana kan ya siyo min kaya girki, ina so na riƙa yin girki da kaina.
Abincin wajen nan ba ya min daɗi”
Anna ta yi 'yar dariya.
“'Yata kin iya girki ne?”
Da sauri ta gyaɗa kanta tana faɗin.
“Sosai ma kuwa, tun ina da shekara goma sha ɗaya na fara girki fa”
”Aaaa, ahse 'yar tawa babbar cooker ce”
Mishal har da dariya, irin an yabeta ɗin nan.
“To kada ki damu.
Da yardar Allah zan sa ya sai miki kayan girki, ta yadda za ki riƙa yin girkinki da kanki”
“Kai amma fa da na ji daɗi Sweet Anna”
Anna ta kwashe da dariya, da ma Rahila na ba ta bayanin yarintar Mishal ɗin, ba ta taɓa ɗaukar cewa haka take ba sai yau, amma ita yatinyar tata ta birgeta, don akwai nustuwa a ciki.
Siyama dake cikin ɗaki ta silale a kan gado tana danne bakinta da hannunta, gudun kada kukan da take riƙewa ya suɓuce mata, da ace ta na da ikon cire son Kuliya a ranta da ta yi ta huta da wannan azabar da take sha, ta gaji, Wallahi ta gaji har ranta, amma soyyayarsa ta hanata gannin gazawarta.
Ta riga ta yankewa kanta hukuncin gobe da sassafe za ta haɗa kayanta ta koma gidan Anti Karima, don su sake sabon lale.
___________________
_Salmanians, shin ba mu jawa Siyama kunne kan kada ta fara ba?_
_Godiya ta musamman zuwa ga dukan Salmanians na fili da na ɓoye, haƙiƙa kune ƙwarin gwiwata a ko da yaushe_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*13*
~~~
*Some people are your happy pill, no matter how sad you are...*
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
*Brickhall school, Kaura District, Abuja.*
RABI'A POV.
Za ta iya!, tabbas za ta iya.
Wannan shi ne abun da take faɗawa kanta, a dai-dai lokacin da take tsaye a filin ball ɗin makarantar, sanye take cikin kayan ball ɗin da Mishal ta ba ta jiya, a cikin filin kuma akwai wasu 'yan mata guda biyar, waɗanda su ma ke sanye cikin kalar nasu kayan wasan ball ɗin.
Daga can wajen ragar filin kuma, Mishal ce tsaye, ta yi ƙuri da idonta a kansu, yayin da take jiran ganin salon wasan Adawiyyan.
Rabi ta lumshe idonta na wasu 'yan sakkani, kafin ta buɗesu ta ɗora a kan ball ɗin dake tsakiyarsu, daɗewar da ta yi ba ta buga ball ba ba ya nufin cewa ta manta yanda ake buga ball ɗin, ko wani salo da ko wani taku na yin ball babu wanda ta mance, a da tasha dakun rana makamanciyar wannan, yau sai ga shi Allah ya cika mata fatanta, don haka za ta gwada, za ta gwada duk wata iyawa tata a kan wannan wasan.
Cike da ƙwarewa suka fara wasan, a tashin farko sai da suka ci Rabi sau biyu, duk da Mishal ta yaba da iya wasan nata sai da ta sare, amma kuma bayan tasu nasarar sai Rabin ta shiga yankasu, ba ta sarara ba sai da ta ci su uku.
Wani irin ihun murna da Mishal ta saki ne ya sa hankalin kowa ya dawo kanta, don zuwa lokacin hatta da ɗaliban dake kaikawo a wurin sai da suka tsaya kallon wasan, don wasan nasu akwai ban sha'awa.