← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 80

Sashe 72

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta ga kamar tana rayuwa ne cikin mafarki, domin da ƙwallo a mafarki take ganinta, bayan hargitsin da ya ahigo rayuwarta sai ta manta da ƙwallon.

Ta haƙa wani wawaken rami a zuciyarta, ta cilla burikanta na rayuwa, ta binnesu, don a lokacin gani take rayuwar tata ta zo ƙarshe, labarinta ma ya ƙare, komai ma ya ƙare.

Shigowar Zaid rayuwata ya sauya komai, ya sauya yanda take kallon kanta, ya sauya yanda take ganin rayuwa, ya cika mata burikanta na rayuwa, duk abubuwan da take ganin ba masu iyuwa ba ne sun iyu, ta rasa me zata ce da shi, tace ta gode?, a'a, godiya ta yi kaɗan ta isar da shi, addu'a ita ce kawai abun da ya kamata ta masa, sannan ta ba shi ko wace kulawa, ƙauna da soyyaya.

Ganin ya nufi hanyar Kaura ya sa ta share hawayenta, don bayan wani lokaci me tsayi, yau Allah ya yi za ta haɗu da ƙanwarta.

Sai da suka fara zuwa suka ga Rhoda, kafin ta fice ita ɗaya, bayan ta da faɗa musu cewar za ta je ta ga ƙanwarta, Zaid be hanata ba, don shi ma ya na so su tattauna da Rhoda kan case ɗinsu, saboda suna kyatata zaton zuwa gobe za'a shiga kotu.

Kanta tsaye Rabi ta shiga makarantar, masu gadi sai tambayarta suke, kan dalilin dena zuwanta makarantar, ita kuma tana amsa musu da rashin lafiya ta yi, kuma su ma sai suka yarda, saboda ganin tabon dake kwance a gefen fuskarta.

Duk da sun ga sauyi sosai a tare da ita.

Kafin ta kai ss3 har ta fara hawaye, saboda ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, ta ƙagu ta haɗu da Mishal, don ta bata labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu.

Cikin wata irin sa'a, tana isa ƙofar ajin ana kaɗa ƙararrawar break, hakan ya sa ta tsaya cike da zumuɗi tana san ganin fitowar Mishal.

Sai da ko wani ɗalibi ya fice daga ajin, kafin Mishal ta miƙe tana muzurai, sai ciza baki take don tafiyar ma da ƙyar take, haka ta shiga taku cikin ƙarfin hali, har ta kai waje.

Ba tare da ta lura da wanda ke tsaye a bakin ƙofar ajinsu ba ta fara tafiya ta na nufar playground.

Rabi'a ta lura da yanayin tafiyarta, amma kuma ɗaukin ganinta ya sa ta ture komai tace.

“Mishal!”
Cak Mishal ta tsaya da tafiyar da take, sakamakon sauƙar sautin muryar yayarta da ta ji, yayarta mafi soyiwa a ranta, yayarta da take ji da ita, yayarta da take cikin halin damuwa na rashin ganinta.

“...

Kin ji abun da ya faru da ni!”
Cewar Rabi, a sa'ilin da ta ɗiga aya a ƙarashen labarin da take bawa Mishal, suna zaune ne kan kujerun da suka saba zama a da, Mishal wadda idonta ya cika da ƙwalla ta kalli yayarta.

Duk da Yazid bai samu damar ci mata zarafi ba, amma ta san yaya zafin abun yake, ta san irin baƙin ciki da ƙuncin da ake shiga, ta san zafi da tabon da abun kan barwa 'ya macen da ta fuskance shi.

Ita ba ta da wani wayo sosai, amma ta san irin ƙasƙancin da mata 'yan uwanta kan fuskanta, idan har basu kai budurcinsu ɗakin mazajensu ba.

Duk da ita Adawiyyan ta tsallake wannan ramin.

“Yaya ina so na faɗa miki wani abu”
Rabi ta share hawayenta tana kallon Mishal.

“Kina kama da Aliyu, kuma na san ke ma kin san hakan, kina da danganta da shi?”
Rabi ta yi murmushi tana ɗauke kai.

“Wata ƙila idan na faɗa miki ba za ki yarda ba.

Amma mijinki cousin brother ɗina ne, sannan kuma shi ne ƙanin mijina.

Ɗan biyunsa ne, amma abun da ya shiga tsakaninsu ya rabasu ne... ban sani ba”
Wani irin shiru ya gifta a wurin, ba ka jin komai sai sautin wucewar iska.

A cikin wannan shirun, Mishal ta kunce ta kuma saƙa ya fi sau a ƙirga.

Kenan wannan wanda take gani a tsallaken makarantarsu shi ne Zaid ɗin da Adawiyya ta aura?.

“Da...

Da ma Raja shi ne Zaid ɗin?”
Mamaki ya kama Rabi.
”Kin san shi ne?”
Mishal ta gyaɗa kanta da sauri ta na share ƙwalla.

“Na sanshi...”
Rabi ta yi ajiyar zuciya tana ɗaga kanta sama.

“Ya kamata mu san abun da ke faruwa a tsakaninsu”
Rabi ta faɗi tana sauƙe kanta ƙasa.

Mishal ma kai ta gyaɗa mata cike da gamsuwa.

“Yau idan muka koma gida zan tambayi Aliyu”
Rabi ta yi murmushi.

“Ni kuma zan tambayi Zaid”
Sai kuma suka yi dariya a tare, ashe soyyayar da sukewa juna ba za ta faɗi ƙasa ba, ashe Allah ya hukunta zamowarsu facalolin juna.

Dariyar da Mishal ta yi ce ta sa jikinta jijjiga, hakan ya sa ta yi famu, sai ta ɗan cije lips ɗinta cikin jin zafi.

Sai a lokacin Rabi ta lura da abun da yake faruwa da ƙanwar tata.

“Me yake damunki Ƙanwata?”
Nan da nan ƙwalla ta cika idon Mishal, ta turo bakinta gaba tana shirin fashewa da kuka.

“Wallahi Anti Adawiyya Abu Aswad mugu ne, kuma zuciyarsa ma baƙa ce kamar kayansa, da ma ai na faɗa masa cewar sai na faɗa miki idan muka haɗu...”
Nan take Rabi ta gane inda zancen ya dosa, amma kuma sai sunan da ta kira mijin nata da shi ya bata dariya.

“Abu Aswad kuma Mishal?”
Mishal ta share ƙwallar da ta zubo mata.

“Abu Aswad mana, ba shi ne ba kullum cikin saka baƙaƙen kaya, shi ya sa na saka masa sunan...”
“Na ji kin ce kin gaya masa cewar za ki gayamin abun da ya miki, da ma ya sanni ne?”
Mishal ta kuma goge ƙwalla.

“Ya sanki mana.

Sanda kika ɓata shi na sa ya yi ta nemanki, kuma na san cewa shi ma ya gano cewar an saceki , amma shi ne ya ƙi faɗa min”
Haƙuri Rabi ta shiga bata, kafin ta ƙarashe da bata shawarwari kan yadda za ta kula da kanta, da kuma gyara jikinta.

Basu rabu ba sai da suka yiwa juna alƙawarin sanin dalilin rabuwar waɗanan 'yan uwan biyu.
*No.86, Garki 2, Abuja...*
*07:30pm*
ZAID POV.

Gama wayarsa da shugabansu ke da wuya, ya ji wayar ta sa na ringing.

Hakan ya sa ya duba screen ɗin wayar, don ganin me kiran.

Ganin Kawu Abdullahi ne ya sa shi yin murmushi, ya na ɗaga kiran.

Gaisawa suka yi cike da girmamawa, kafin dalilin kiran ya taso.

“Ɗazu muke jin wani zance a gida.

Wai ka kai Rabi'a makarantar ƙwallon ƙafa!”
Zaid dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya sosa kansa cikin jin nauyi, kafin yace.

“Eh haka ne”
“To tun wuri, ka yi gaggawar janye wannan ƙudirin naka...

Ka bar ganin ita matarka ce, mu iyayenku ne, tun farko ya kamata ace ka shawarce mu kafin ka yanke hukunci a kanta.

Ko a sanda take yarinya da mahaifiyarta ta kaita makarantar ba so muke ba, dan de muna ga yarinya ce, shi ya sa muka yi shiru.

Amma a yanzu ta girma, tun da har mun mata aure, dan haka ba zamu ɗauki wannan shashancin ba.

Tana mace me ya haɗata da wata ƙwallo?, zaman gida da kula da tarbiyyar yara shi ne ya dace da ita, ba gudu da gajeren wando a kan idon tarin mutane ba!...”
Haka Zaid ya ja bakinsa ya yi shiru, har Kawun ya kai ƙarshe a faɗan nasa bai ce masa ƙala ba, sai da ya tabbatar da Kawun ya kai ƙarshe a wajen amayar da abun da ke bakinsa kafin ya seta kamillalliyar muryarsa, ya shiga koro bayani a natse, kuma cikin da girmamawa.

“Na fahimce ka Kawu, kuma duk abun da ka faɗi gaskiya ne.

Amma kuma ita ma Adawiyya tana da gaskiya.

Ka san a ina ta yi gaskiya?”
Kawu Abdullahi dake zaune a kusa da su Baba ya juya ya kallesu, dan kuwa suma suna jin duk maganar da Zaid ɗin yake, sai kuma ya girgiza kansa cikin faɗin.

“A'a, sai ka faɗa”
“Lokacin da ta farfaɗo a asbiti, ta kalli idona tace min maza ba su da adalci, kansu kawai suka sani; kuma kasan dalili?”
Ya tambaya ba dan ya na buƙatar amsa ba, dan kafin ya amsa masa ya ci gaba da cewa.

“Dalilin shi ne; mu maza a kullum gani muke mune a gaba, dan haka dole duk abun da muke so shi za'a ayi, hakan ba wai kuskure ba ne, saboda mu Allah ya bawa girma, amma kuma su ma suna da nasu 'yancin.

Domin ko addini ya basu 'yanci, daraja da kima, sai de ni kuma a yau ba ma duba hakan, sai namiji ya auri mace, ya zaunar da ita a gida, ya hanata rawar gaban hantsi, ya sa ƙafa ya take mata burinta da kuma 'yancinta, ga shi de ba ta son abun da yake mata, amma saboda ganin ita macace sai ta haƙura ta ja bakinta ta yi shiru.

Kawu a mafiya yawan lokuta muna dannewa mata hakkinsu, suna da baiwa kamar mu, suna da shauƙi kamar mu, suna da zuciya kamar mu, duk abun da zai fusata mu suma zai iya fusata su, banbanci mu da su shi ne, su sukan iya jurewa abun su shanye a cikinsu, wata dan 'ya'yanta, wata dan iyayenta, wata ma dan mijin shi kansa, haka za ta jure rintsi da wuya.

Kawu, Adawiyya ta shiga taskun rayuwa kala-kala, taga iftila'i da ban da ban, yanzu ne ya kamata ace ta samu jin daɗi da hutu, a yanzu ya kamata ace burukanta sun cika.

Ni kuma ina son ta yi farin ciki, kuma na yi alƙawarin sama mata duk wani abu da zai dawwamar da murmushi a fuskarta.

Ƙwallo mafarkinta ne, lefi ne dan na temaka wurin ganin ya zama gaskiya?!”
Shiruuu, har bayan shuɗewar wani lokaci, a cikin wannan shirun Baba dake kishingiɗe ya miƙe zaune da kyau, cikin alfaharin kasancewar Zaid jika a gareshi, Kawu Abdullahi kuma nadamar kiransa da masa wannan kashedin yake.

Kasa cewa komai ya yi, ya kashe wayar.

Jin wayar ta katse ya sa shi sauƙe wayar.

Sannan ya fita daga ɗakin, dan da ma niyyar fita yake, kiran shugaban nasa ya same shi.

Shi ya sa ya tsaya ya amsa saboda muhimmanci kiran.
Chapter 72 · 0% Book details