← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu Mishal ta shiga cikin ragar ta rungume Rabi suna dariya, ba tare da sun ankara ba suka hautsina suka faɗi ƙasa, Mishal ta sauƙa daga kan Rabi ta kwanta a ƙasa suna dariya, ba ƙaramin burge Mishal Rabi ta yi ba.

Ita kuma Rabi tana farin ciki ne don samun damar buga ƙwallo bayan tsawon lokaci, ita kanta ba ta zaci cewa za ta iya buga wasan da kyau irin haka ba, bayan shuɗewar wani dogon lokaci, yau ita ce take dariya sosai, wadda take fitowa tun daga ƙasan ruhinta, har ta manta rabonta da ta yi irin wannan dariyar.

RAJA POV.

Tafe suke shi da Rabi a kan titin Joy Emodi CI, layin ya yi shiru, kasancewar babu kai kawon mutane, tun bayan da ya ganta yau, ya lura da wani irin farin ciki kwance a fuskarta.

“Akwai wani abu na mussaman ne?”
Ya yi tambayar da ba tare da ya kalli fuskarta ba, ita ma kuma ba tare da ta kalle shi ba, ta sunkuyar da kanta tana murmushi.

“Bayan shuɗewar tsawon lokaci, yau na buga ball, shi yasa nake cikin farin ciki...”
Ya na ɗaga ƙafaɗarsa ta dama, ya juyo ya kalleta, Kyakkyawan murmushinta shi ne yake ƙara bayyana masa kammaninta da Mommansa, zuwa yanzu yasan da cewa akwai sabo tsakaninsa da ita, kuma a yanzun ne ya kamata a ce ya tambayeta wani abu game da kanta.

“Ammata a gidan ku da wa kike kama?”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta yi murmushi.

“Kana san sanin dangantakar ka da ni?”
Cak, Raja ya tsaya, hakan ya sa ita ma Rabin tsayawa tana kallonsa.

“Na san kana tunanin na haɗa alaƙa da kai.

Ban sani ba ko kai ɗin jinina ne, amma dai a cikin familynmu babu wanda ya ɓata, da ace akwai wani wanda na san ya taɓa ɓata, ko ya bar gida, da sai na ce wata ƙila kai ne, ko kuma ka fito daga wajensa ne!”
Ta zaɓi da ya ɓoye masa ne don har zuwa yanzu ba ta gama sanin waye shi ba, ta na buƙatar fara sanin waye shi, kafin ta bayyana masa cewar ta san shi da ɗan uwansa 'ya'yan abokiyar tagwaitakar Ummanta ne!.

“Da Ummana nake kama, dan haka ko da zan yi zaton cewa kai ɗan uwanmu ne.

Zan ce ka fito daga tsatson Umma ne!”
Da ƙyar Raja ya haɗiye yawu, jin cewa Rabi'a ba 'yar uwarsa ba ce kamar yanda ta faɗa, sai dai kuma shi ya jita ne kawai, amma ya riga da yasan cewa ita 'yar uwarsa ce, alaƙar tsakaninsu ce bai sani ba, amma tabbas ita 'yar uwarsa ce!.

KULIYA POV.

A hankali ya turo ƙofar ɗakinta, a lokacin kusan ƙarfe goma na dare, wai a hakan ma ya dawo da wuri, don ya na so ya sameta ido biyu, amma cikin rashin sa'a sai ya tarar ta yi bacci kamar kullum, a jiya ya nema mata drivern da zai riƙa kaita makaranta yana dawo da ita, kuma kamar yanda ta buƙata ya sai mata kayan abinci da kuma kayan girki, don ita kaɗai za ta girka kayanta, shi ba zai iya cin jagwalgalen da za ta girka ba, yanzu haka shigowa ya yi don ya sanar mata da an kawo kayan girkin.

Sai ya samu kansa da ƙare mata kallo daga nan inda yake, yanayin kwanciyarta kaɗai zai sa ka gane cewa mummunar kwanciya gareta, kanta a wani gefe da ban, haka ƙafafunta ma sun yi wata duniyar, blanket ɗin da ta rufe jikinta da shi ya yaye daga jikinta, ya yi wani wurin.

A zuciyarsa ya yi murmushi ya na shigowa cikin ɗakin, tsayawa ya yi a jikin gadon yana kallonta, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, kafin ya kai hannunsa ya na gyara mata kwanciyar, har ya ɗora kanta a kan pillow ba ta farka ba, ya gyara mata ƙafafuwan na ta duk shiru kake ji, kamar wata gawa, ya janyo blanket ɗin ya rufa mata, sannan ya mata addu'ar da yake da tabbacin ba yinta take ba, ya miƙe ya na kashe wutar ɗakin, sannan ya fita.

Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka, ya sauya kayansa, a sanda ya fito daga closet ɗinsa ya iske Ayra zaune a kan gadonsa, ya kamota ya ajete a inda ya saba kwantar da ita, shi kuma ya shiga ƙarasa aikin da bai samu ya ƙarasa a office ba.

Allah ya sani a kwanakin nan ayyuka sun sha masa kai, ko lokacin kansa ba ya iya samu, don a yanzu haka ma ko abincin dare be samu ya ci ba, amma babu yanda zai yi, yana bawa aikinsa muhimmanci fiye da komai.

RABI'A POV.

Yini ta yi tana bawa Anti Saratu da Zara labarin ball ɗin da ta buga, haka ta kwana da wannan farin cikin fal ranta, da ga ta yi juyi za ta tuna da yanda ta buga wasa me kyau, sai wani kalar farin ciki wanda ba ta san daga inda yake ba ya lilliɓeta har ka.

Washe gari weekend, don haka gidan kawai ta gyara, sannan ta shiga kiciniyar haɗa kayan suyar funkaso, kuma har washe garin wannan farin cikin bai bar ranta ba.

RAJA POV.

“Su kenan?”
Ya tambaya a dake, yayinda yake kallon mutumin da ya kawo musu makaman da suka yi oder, mutumin ya zuƙi karan sigarin dake hannunsa sannan ya furzar yana gyaɗa kansa.

“Su kenan”
Sai shi ma Rajan ya gyaɗa kansa, ya na ɗaga kafaɗarsa.

“Na fahimta”
sannan ya waiga yana bawa su Zuzu umarni da su kwashi makaman su zuba a booth ɗin motarsu, har ya juya zai koma cikin motarsu mutumin ya katse shi ta hanyar faɗin.

“Ɗan uwa wannan cikar fa?, Idan ba damuwa ina buƙata!...”
Mutmin ya ƙarashe yana wa Rhoda wani irin shegen kallo, babu shiri Raja ya juyo ya na watsa masa wani masiffafen kallo, idanuwansa da suke a lumshe da sune ya buɗesu tar a kan mutumin, kuma ba jimawa da buɗesun, farin cikinsu ya rikiɗa zuwa ja, jijuyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa, yau shi akewa magana kan ya bada ƙanwarsa a matsayin karuwa?, me wannan mutumin ya ɗauki kansa ne.

A fusace ya yi kan mutumin, shi kuma ya riga da ya tsorata har ya shiga ƙoƙarin guduwa, Raja ya ci kwalar rigarsa da hannunsa na dama, sannan ya shiga naushin fuskarsa da hannunsa na hagu.

Cikin su Zuzu da Jagwado da Rhoda babu wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi, dukansa yake yana ƙarawa, kunnuwansa sun toshe, babu abun da yake ji sai maganar mutumin da ya yi a ɗazu, sai da ya farfasa masa fuska tukkuna Alandi ya ga kamar kashe mutumin Raja ke ƙoƙarin yi, don haka ya ƙarasa kusa da shi ya riƙe shi, amma bisa ga mamakin Alandin sai Raja ya ha kaɗashi shi baya.

Hakan ya ankarar da Rhoda cewar Rajan ba a hayyacinsa yake ba, saboda haka ita ta ƙarasa kusa da shi ta dafa kafaɗarsa ta dama.

“Zaid is okay!”
Cak, hannun da Raja ya ɗaga don dukan mutumin ya tsaya a iska, ban da hucin ɓacin rai babu abun da yake, har wani datse haƙwara yake, gaba ɗaya ilahirin jikinsa sai rawa yake.

Yakan shekara ransa bai ɓaci ba, amma idan ransa ya ɓaci abubuwa da dama za su ɓaci, sakin kwalar mutumin ya yi, hakan yasa ya zube a ƙasa ragwajab!, hannunsa na hagun da ya ɗaga ya daki iska da shi.

Har lokacin idanuwansa a buɗe suke gaba ɗaya, sai huci yake, kamar wani wanda ya yi wasan tsere, juyawa Rhoda baya ya yi yana rufe fuskarsa, duk da iskar dake kai kawo a wurin shi gumi yake, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana ɗaga kansa sama.

Kamar wanda aka tsikara kuma sai ya zabura ya faɗa cikin mota yana kwantar da kansa a kan dash-bot.

Sai sauƙe ajiyar zuciya yake, a hankali kuma girman idanuwansa suka shiga raguwa.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*80:40 AM*
MISHAL POV.

Tsaye take a kitchen tana girka jallof ɗin couscous, fuskarta kawai idan ka kalla za ka gano tsantsar farin cikin da take ciki, don yau da safe da ta tashi ta shiga kitchen ɗin ta tarar da tarin kayan abinci da kayan girki.

Allah ya sani, ita ba san wannan abincin restaurant ɗin take ba, shi yasa ba ta ci sosai, don har wata 'yar rama ta yi a kwanakin.

Daga ƙasan marbles ɗin kitchen ɗin kuma Ayra ce ke cin kifin da Mishal ɗin ta saka mata.

Mishal ta kwashe jallof ɗin tare da zubata a kan wani plate me kyau da ya fi burgeta cikin kayan kitchen ɗin, dai-dai da lokacin da aka turo ƙofar kitchen ɗin.

Kallon ƙofar ta yi, duk da ta san cewa shi ne, kamar kullum sanye cikin baƙar suit, yana kallonta a sanyaye, wani abu sabo game da shi.

“Ina kwana Abu Aswad!”
Ta faɗi a sanda yake shigowa cikin kitchen ɗin, cak Kuliya ya dakata da tafiyar da yake, sannan dubansa ya zarce zuwa kan fuskarta, yayin da take zama a kan kujerar island.

Abu Aswad?, shi ɗin ne Abu Aswad?, don kawai ya na saka baƙaƙen kaya, sai ua zama Abu Aswad?

Sai ya ƙi tanka mata, saboda wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarci hancinsa, kuma ƙamshin ba na turera ba ne, na girki ne, hakan yasa ya kalli plate ɗin dake gabanta.

Sai da ya baɗiyi wani kakkauran yawu a sanda kalolin jallof ɗin gaban nata suka shiga idonsa, kayan lambun da ta ƙawata girkin da shi yasa girkin ɗaukar ido, ga kuma kamshin da girkin ke yi, kenan dai ta iya girkin kamar yadda ta faɗa?, kai ina!, ta ya za ayi ace wannan ta iya girki?, ai sai dai jagwalgwalo, don wata ƙila kyan da ƙamshin ne kawai, a baki ba llale abincin ya yi ɗanɗano me daɗi ba, saboda haka ba zai yi kasadar cin abun da zai zo ya ɓata masa baki ba, ko ma ya ɓata masa ciki, shi da ko abincin daren jiya bai ci ba.

Sai ya ƙi amsata ya juya zuwa wajen da ya saba a je kayan haɗa coffeensa, sannan ya haɗa shi a coffee maker, kafin coffeen ya haɗu, ya zaro wayarsa yana daddanawa.

“Abu Aswad!
Chapter 38 · 0% Book details