← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 80

Sashe 51

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunsa na dama riƙe da wani littafi, da a jikin covernsa aka rubuta 'I was never yours'.

“Ina kwana”
Ta gaida shi kanta a ƙasa, kamar ba Mishal ba, don a duk sanda za ta ganshi sai ya ƙara girma a idonta.

Kuliya ya ci gaba da kallonta, sanye take da wani wide blue jeans, sai farar top da ta saka, wadda a jikinta aka rubuta 'Believe in your dreams' gashin kanta baje a bayanta, sai band da ta saka daga saman gashin, fuskarta fayau, babu ko da lip balm.

“Lafiya, ya jikin nake?”
Ya tambaya ya na aje book ɗin hannunsa.

Ita fa ta ma manta da ba ta da lafiya, yanda ta yi overdose na maganin nan ba dole ma murar ta gudu ba.

Sai ta gyaɗa masa kai.

“Na ji sauƙi...

Na gama abinci, kuma na ga har yanzu...

Ba ka fito ba”
Iko sai Allah, ita fa a rayuwarta ba ta ƙumbiya-ƙunbiya wurin faɗin abun da ke ranta, amma a karo na farko, sai ga ta tana inda-inda wurin faɗin wani abu.

“Aiki nake, shi yasa ban fito ba.

Amma na gama, mu je”
Ya ƙarshe ya na tsayawa a gabanta, sai ta gyaɗa masa kai sannan ta juya, shi kuma na biye da ita a baya har danning ɗin.

Abincin ta zuba masa, sannan ta zuba nata, suna ci ya na mata magana jifa-jifa, wani abu sabo, yau shi ne yake hira, ita kuma uwar 'yan surutun ta yi shiru, ta nutsu, kamar ba ita ba, saɓanin da da idan suna cin abinci ko in sun zauna irin haka ita ce ke masa surutai.

Bayan sun kammala cin abincin ya ƙara komawa ɗakinsa, ita kuma sai ta zauna a falo tana kallon tv, yayin da takewa Ayra susa.

Garam!, ta ji an bankaɗo ƙofar falon, ba shiri ta miƙe tsaye ta na kallon ƙofar, Jadda ce ta shigo ta na wani muzurai.

Hatta Kuliya dake ɗaki sai da ya ji ƙaran turo ƙofar, hakan ya sa ya fito, amma ko kafin ya isa falon ya hangi Jaddan ta na shigowa, hakan ya sa ya ja ya tsaya daga corridorn ya na kallonsu.

“Jadda!”
Mishal ta kira sunanta.

“Eh ni ce jikata.

Zuwa na yi na ɗaukeki na tafi da ke.

Dan na ga kamar shi kawun naki ba sanki yake ba.

Shi ya sa na zo na ɗauke ki...”
“Ki ɗauke ni mu je ina?”
Mishal ta tambaya a sanda Jaddan ta riƙo tsintiyar hannunta.

“Maiduguri nake so mu koma, gwara ki koma can cikin 'yan uwanki, ko karatun ne ma ai sai ki ci gaba da yi”
Mishal na girgiza mata kai ta kai hannunta da bata riƙe ba ta kama na Jaddan dake riƙe da nata ta ɓanɓare.

“Jadda yanzu fa ni matar aure ce....

Ina kike san na je ba tare da izinin mijina ba ?”
Jadda ta rafka salati ta na kama baki.

“Ke Hafsat!, wai ke nan daɗin aure kika sani?!

Wato ke gaki matar gida ko?, Ub*n me shi wancan matsiyacin ya baki da har kika manta da mu haka?”
“Jadda please, shi ɗin mijina ne a yanzu.

Ba ki san shi ba amma kina zanginsa, dan haka kada ki sake.Dan idan kika kuma ba zan yi shiru ba”
Salatin da Jaddan ta rafka a wannan karon ma ya fi na ɗazu.

“Hafsat wai ko bakya cikin hayyacinki ne?

Yo in ba haka ba ta ya za ki tsaya kina gaya min waɗanan maganganun kamar wata sa'ar ki?”
“Jadda ke ce ba ki riƙe girman ki ba.

Wani daɗi zan biki ki bani a Medugurin?, Babu wani abu da za ki iya bani a Meduguri face ki saka ido kina gani jikokinki su ƙarasa lalatamin rayuwar da suka so su lalata min tun farko.

Ke a ko da yaushe ba ki da abun faɗi da ya wuce cewa kina son jikokinki, kina san jikokinki, a haka ake san jikan?.

Ta wannan hanyar da kika ɗauka za ki iya riƙe ni, saboda sanin halinki ya sa 'yarki ta cikinki kafin ta bar duniya ta gargaɗi yayana da kada ya bari na tashi a wajenki.

Yanzu kuma da hankali na kike so na biki mu tafi can?, can ɗin da babu wani me iya bani kariya?”
Cike da mamaki Jadda take kallonta, wai yaushe ma Mishal ɗin ta yi hankali har haka?, Kamar ma ba ita ba, ko da yake ai an ce aure na gyara mutum, sannan yakan sa mutum ya nutsu.

“Ba za ki biyoni ba kenan?”
“Ba zan biki ba, ya fiye min alkairi na zauna a gidan nan, ko da Aliyu zai riƙa dukana ne, da de na biki mu tafi Meduguri, ballantana kuma babu wani abu da mijina ya rage ni da shi.

Ko me na buƙata cikin gaggawa yake samar min da shi, bayan haka kuma ina san mijina, to me zai sa na biki?”
“Kin yi da 'yar halak”
Jadda na faɗin haka ta juya a fusace ta bar gidan, wasu hawaye masu ɗumi suka shiga sauƙowa Mishal a kan kumatu, wai yaushe rayuwarta za ta setu ne?, yaushe ne ita ma za ta samu dawwamammen farin ciki kamar kowa.

Hannu ta ji ya kewayeta daga baya, sannan ta ji sauƙar haɓarsa a tsakiyar kanta, kafin ya ƙara janta jikinsa, ba shiri wani kuka me ƙarfi ya kufce mata, ta sake shi kuwa.

Kuma cikin gaggawa ta juya ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannayenta suka kewaya ta bayansa, sannan ta ci gaba da yin kukanta me sauti.

Kuliya ya ɗora haɓarsa a kanta, sannan ya shiga shafa kanta da hannunsa na dama, hanunusa na hagu kuma ya na shafa bayanta.

“Shhhhh!

Teddy Bear, komai zai wuce, komai zai wuce....”
Haka ya ci gaba da nanata mata a kunnenta, yayin da ita kuma ta ci gaba da rera kukanta a cikin jikinsa, dan kuka ne irin wanda ta jima ba ta yi ba, ba ma za ta iya tuna rabonta da yin irin kukan ba, ko a lokacin rasuwar Abubakar hawaye kawai ta yi, amma kuka irin wannan ba ta saba yinsa ba.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
RAJA POV.

Kamar kullum ya nazaune daga balconym ƙofar shiga gidan, ya saka ƙofar gate a gaba ya na ta kallo, ya tsinduma cikin kogin tunani da ya saba shiga, ya na ta linƙaya a ciki, ba tare da sanin madafa ko kuma gaɓar da igiyar kogin za ta kaishi ba.

“Zaid!”
Muryar Rhoda ta kira shi, hakan ya sa ya juya ya kalleta.

“Na samo address ɗin asibitin!”.

Be san meke faruwa a kansa ba a lokacin, amma shi dai kawai ya yi fatan ina ma zai lumshe idonsa ya buɗe ya tsinci kansa a cikin asibitin.

Wani irin gudu yake da motar, wanda ya wuce na hankali, shi da Rhoda ne, wadda ta saka ido ta na kallonsa kawai, yanda yake gudu da motar kai kace ce masa aka yi idan ya tafi a hankali duniyar ce za ta tashi ba tare da ya je ya cimmawa abun da yake san gani ba.

Cikin wasu 'yan muntuna sai ga su sun iso 'Vinca Hospital'.

“Sunanta Rabi'a!”
Raja ya faɗi cike da ƙaguwa, yayin da suke tsaye a reception, sai kai kawo yake, Rhoda ta dafa kafaɗarsa cikin san kwantar masa da hankali ya fi a ƙirga, amma sam ba ya fahimtar me take shirin faɗi.

“Zaid Aliyu!”
Da sauri suka juya daga shi har Rhoda, don ganin mahaluƙin da ya kira shi da wannan sunan, bisa ga mamakinsu, sai ya ga wani abokinsa ne da su ka yi jami'a tare, ba course ɗaya suke offering ba, amma sukan haɗu a cikin makaranta.

Duk da ya na cikin wani hali sai da ya yi wa abokin nasa murmushi, haɗi da miƙa masa hanu su gaisa.

“Me ya kawoka asibitinmu?”
Abokin me suna Huzaifa ya faɗa, Raja ya ɗan sosa kansa.

“Wata mara lafiya muke nema...”
Bai ko rufe bakinsa ba, receptionist ɗin tace.

“Ku yi haƙuri ranka ya daɗe, amma babu mu da mara lafiya me wannan sunan...”
Raja ya girgiza kansa.

“Kuma an tabbatar muku da ta na nan?”
Huzaifa ya tambayi Raja, Raja ya gyaɗa kansa a sanyaye.

“Da ga masaniya me ƙarfi muka samu labarin, kuma an tabbatar mana da tana cikin asibitin nan”
“Muje office ɗina, wata ƙila akwai wani temako da zan iya maka”
Daga haka kuma suka ɗunguma zuwa office ɗin Dr.

Huzaifa.

Wuri ya nuna musu suka zauna, sannan shi ma ya zauna ya na tambayarsu.

“Kamar yaushe kuke ganin an kawota nan?”
“Sati uku baya haka...”
Rhoda ta bashi amsa,sai ya gyaɗa kansa ya na ɗaukan wayarsa, kira ya yi, kuma bayan wani lokaci sai ga wata nurse ta shigo hannunta riƙe da files.

Dr.

Huzaifa ya karɓi fle ɗin ya na kallon fuskarta.

“Ɗakin nan kika shiga ba?”
Ya tambayeta saboda ganin yanda idonta ya yi jajir, alamun dai ta yi kuka, sai nurse ɗin ta sinkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsunta.

“Sakina!”
Ya kira sunanta, hakan ya sa ta ɗago da kanta ta kalleshi.

“Sau nawa zan faɗa miki ki dena shiga ɗakin nan, in har za ki riƙa shiga damuwa irin wannan, me nene amfani zuwa ganinta?”
“Na kasa iya hana kai na Dr., a duk sanda zan shiga na dubata sai na zubar da ƙwalla...”
Huzaifa ya miƙawa Raja file ɗin, wanda ya kafesu da kallo.

“Ki je kawai za mu yi magana daga baya”
Kanta ta gyaɗa sannan ta fita daga office ɗin.

“Akan wa kuke magana?”
Raja ya tambaya hannunsa riƙe da file ɗin da Huzaifan ya miƙa masa.

“Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana...
Chapter 51 · 0% Book details