← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 80

Sashe 44

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ganin mutumin ba komai ya sani a kan cutar ba, amma shi a ganinsa wannan abun da ya faɗa masa shi ne komai, don ko da likita zai samu sai de haka.

Fitowa ya yi daga cikin motarsa a sanda ya yi parking a parking lot, da gudu me gadinsa ya taso yana gaisheshi, ciki-ciki ya amsa ya na kama hanyar shiga gidan, amma sai me gadin ya dakatar da shi.

“Ranka ya daɗe kamar akwai matsala a cikin gidan fa...”
Da sauri ya juyo gaba ɗayansa ya kalleshi.

“Me ya faru?!”
“Eh to, ɗazu ina zaune wasu mata biyu suka zo, suka ce su 'yan uwan hajjiya ne, hakan ya sa na bar su suka shiga, ba jimawa da shigarsu kuma sai na fara jin iface-iface da koke-koke na fitowa daga cikin gidan, ban de yi gangancin shiga ba don ban san me ke aukuwa ba!...”
Be ƙarasa maganar ba saboda wani uban ƙara da suka ji an kwaɗa a cikin gidan, kuma ƙarar ta fito cikin muryar Mishal ne, hakan ya sa Kuliya shiga cikin gidan a ɗari uku da sittin.

Abun da idonsa ya gane masa shi ne, Mishal yashe a ƙasa, kanta ya fashe ya na zubar da jini, sautin kukanta ya cika falon, ga Anti Karima yayar Siyama tsaye a kanta, ga kuma Siyaman tsaye a bayanta, tashin hankali ne ya sa sam bai lura da irin yanayin da su suke ciki ba, ya yi maza ya isa gaban Mishal ya tsugunna ya na tallafo ta jikinsa, hankali tashe yake dudduba jikinta.

A fusace ya ɗauketa a hannunsa yana miƙewa, sannan ya juya ya kalli Karima da Siyama dake tsaye hankali tashe.

“Ku fice ku bar min gidana!”
Cikin tsawa ya yi maganar, kemar me shirin tsaga gidan, Anti Karima ta fashe da kuka ta na fita daga gidan, Siyama kuwa da ma tuni ta fara hawaye, haka ita ma ta bi bayan yayarta, shi ma kuma sai ya fice daga falon, ya saka Mishal a mota , kai tsaye ya wuce asibiti da ita.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger state*
*09:30 PM.*
Anti Saratu ce ke kai kawo a ɗakinsu cikin tashin hankali, tashin hankalin rashin sanin inda Rabi ta shiga, tun ƙarfe biyar na yamma hankalinta ya fara tashi, ganin ta haura lokacin dawowarta, ga shi har 9 ta yi amma babu Rabi bare labarinta, tsoronta ɗaya; shi ne kada Rabin ta je ta iallata kanta, ga shi ta na cikin matsanan ciyar damuwa.

Ganin zaman cikin gidan ba zai mata ba ya sa ta figi hijabinta ta fito.

A tsakar gida ta samu Habiba, Mahmud da Fatima suna cin abinci hankalinsu kwance, kamar ba Habiban ba ce ta aika Rabin aikatau, kamar ba ita ce uwar 'yar dake can England ta na aikata saɓon Allah ba, shinkafa da miya har da kaza suke ci, don a cikin kuɗin da Mama ta aiko mata ta ɗauka ta siya musu.

Cike da takaici Saratu tace.

“Umma Rabi fa ba ta dawo ba har yanzu”
Habiba ta juyo ta kalleta tana taune ƙashin dake bakinta ta furta.

“To sai me?!

Ai da ma ta saba tafiya gantalinta irin wannan, ba wani sabon abu ba ne don ba ta dawo ba!”
Saratu ta girgiza kanta cikin faɗin.

“A'a Umma, Wallahi Rabi ba ta haka, sanin kanki ne a ta makara da yawa ta dawo ƙarfe huɗu ko huɗu da Rabi, amma yau gashi har tara babu alamarta”
“Mtswww!

Sai ki yi ai”
Ta ƙarashe tana fusrzar da ƙashin da ta gama taunewa.

Cikin ƙunar rai Saratu ta kama hanyar fita daga gidan don ta je ta yi magana da Yaya ko za ra iya jin wani abun daga gareshi.

“Gaskiya Anti Saratu ba mu yi wata magana da ita ba.

Ba ta faɗa min za ta je ko ina ba!”
Abun da Yayan ya faɗa mata kenan, Saratu ta dafe gashinta ta na karanto 'Innallillah wa inna ilaihi raji'un', kanta ya kulle gaba ɗaya, ta rasa madafa da abun yi, a take a gun kanta ya sara, haka ta bar shagon, duk kuwa da kiranta da yake.

Gida ta koma jiki a saɓule, a ɗakinsu ta zauna, sannan ta lalubo wayarta ta aikawa Fu'ad kira.

“Kin ga Sarah, ki kwantar da hankalinki dan Allah, Insha-Allah zan ga abin da za ayi!”
Kalaman Fu'ad ɗin kenan gareta, bayan da ta gama faɗa masa Abin da ke faruwa, kuma kalaman nasa su ne suka yi nasarar karya mata zuciya, ta fashe da kukan da take riƙe da shi tun ɗazu.

“Fu'ad ban san yanda zan yi ba, Wallahi jikina na bani cewar Rabi ta na cikin matsala, don Allah ka temaka, ka temake ni ka samo min ita.

Rabi marainiya ce!”
“Ki kwantar da hankali tukkuna, idan kina kuka irin haka hankalina ba zai yi kwanciyar da zan iya samo miki ita ba, please Habibty, dan Allah!...”
Da ƙyar ta iya shanye kukan nata, saboda lallashin da Fu'ad ɗin ke mata.

“Menene ma kika ce sunan makarantar?”
“Brickhall School, a nan Kaura District take, kusa da game Village”
“Inshaallah zan nemo miki Rabi'a, sai dai idan abun yafi ƙarfina”
Da haka suka yi salama, don yau babu wayar soyyayar da aka saba, saboda yanda take cikin tashin hankali.

Sallamar Babansu ta ji a tsakar gida, hakan ya sa ta fito da sauri, Ɗan Lami ya kalleta a lokacin da yake zama kan tabarmar da su Habiba suke kai, don shi ma ya samu a ɗan lasa masa abun da aka samu.

“Abba sannu da zuwa”
Ta faɗi cikin muryar wanda ya gama kuka.

Ɗan Lami ya ɗan kalleta kaɗan, sannan ya kauda kai, don haushinta yake ji, ba ƙaramin ɓaci ransa ya yi ba, a sanda ya ji labarin ta tura manemin aurenta wurin yayansa Habu, a inda ya ji labarin kuɗin yaron ya yi zaton wurinsa za ta turo shi, amma sai ba ta yi hakan ba, kuma haushi bai ƙara kama shi ba, sai da Kawu Habu ya ambata masa yawan kuɗaɗen da shi ma nemin auren nata ya kawo, kuma Kawu Habun ya yi mirƙi si-si ya hana shi ko asi a cikin kuɗin, yace wai da su za'a haɗa a yi wa yarinya kayan ɗaki.

Da ace kuɗaɗen hannunsa suka shi, ai da ya morewa rayuwa, don ko karuwarsa Vicky ba ta isa ta ƙara rena masa hankali ba.

“Abba har yanzu Rabi ba ta dawo ba”
Saratun ta kuma faɗi tana durƙusawa a gabansa, sai da ya juyo ta kalli idon Habiba, sannan ya furta.

“Ni na aiketa?

Ita wadda ta aiketa ai ita ya kamata ta fita nemanta ba ni ba!”
Habiba ta taɓe baki, a zuciyarta kuwa murmushi take, don bisa ga dukkan alamu aikin wannan malamin ne ya ci, a rannan ta saurari gaba ɗaya zancen da Rabin suka yi iya da Saratu, kuma hakan ya sa ta kira yayarta Hajiya Inno a waya, aka haɗa musu wani laƙani da zai sa duk wani ɗa na mijin da zai kalleta ya yi sha'awarta, kuma a yau ɗin nan aka tura aikin, kuma bisa ga dukkan alamu aikin ya ci, tun da ga shi ba ta dawo ba, kuma shirinta na gaba shi ne; idan Rabin ta dawo, sai ta sa Ɗan Lami ya koreta daga gidan.

Jiki a saɓule Saratu ta miƙe ta koma ɗaki, ta na Allah wadarai da rayuwa irin ta gidansu.
____________________
_Suwanah!...

Salmaniansa, kuna jin abun da nake ji?_
_wai Rabi ta ɓata?_
_To sai ku ta ya ta da addu'ar Allah ya bayyana mana ita_
_Game da YUSHAL (ALIYU & MISHAL) kuma, sai de na ce Allah dai-daita tsakani_
_Godiya mara adadi_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*15*
~~~
_-*She doesn't need to be your whole world.

She just wants to know that she holds a special place in it.

That's all*-_
***
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
KULIYA POV.

“Babu zafi yanzu?”
Cewarsa ya na kallon Mishal, wadda idanuwanta suka yi jajir, saboda kukan da ta sha, kuma har zuwa lokacin ba ta dena hawaye ba, sai jan zuciya take.

Zaune take a kan wata kujera dake cikin permacyn da ya tsaya siya mata magani, bayan da suka dawo daga asibiti.

Shi kuma ya ɗan sunkuya a saitin fuskarta ya na kallonta, a hankali ta gyaɗa kanta tana jan hanci, sai shi ma ya gyaɗa nasa kan.

“Then tashi mu koma gida”
Ya faɗi yana miƙewa, tare da miƙa mata hannunsa, ta kalli hannun nasa, sannan ta kalli fuskarsa, ba ta taɓa zaton cewa son Kuliya take ba sai yau!

Yau ɗin da kishi ya rufe mata ido har ta aikata abun da ba ta taɓa zaton za ta iya ba.

Sai ta yi ƙoƙari ture wannan tunani, ta ɗago da nata hannun, ta ɗora a kan nasa, a hankali shi kuma ya naɗe natan cikin nasa.

Mishal ta lumshe idonta, ta buɗe, saboda wani ɗumi da ya ratsata, ɗumin hannunsa ne ya ratsa har tata fatar, a hankali Kuliya ya ɗagota daga zaunen da take, sannan ya riƙe hannunta da kyau ya na jawota jikinsa, hakan ya sa Mishal riƙewa wata iska a maƙoshinta, ta juyo ta kalleshi, a sanda shi ma yake kallonta.

Idanuwansa kaɗai sun isa su bayyanar da gajiyar da yake ɗauke da ita, kuma bayan gajiyar ma da alamun yunwa.

Ta haɗiye yawu, a lokacin da suka fara tafiya a tare, don rabin jikinta yana jikinsa.

Ko da suka shiga mota ma ba gida suka wuce kai tsaye ba, sai da ya tsaya a wani super market ya sai mata chocolate.

“Na gode!”
Ta faɗi cikin muryarta da ta gaji da kuka, a karo na farko tun bayan sanin Kuliya da ta yi, ta ga ya yi wani abu me kama da murmushi, dan wannan ba murmushi ba ne, kuma dai kamar murmushin.

Ita ta na mamakin halinsa, ɗan uwansa sam ba haka yake ba, su na tafiya a mota, Kuliya ya jefo mata tambayar da ke ci masa rai tun bayan ganinta tare da wannan me kama da shi ɗin.

“Hafsat!

Wacece wannan wadda na ganku tare da ita?”
Mishal ta yi murmushi tana ɓare ledar chocolate ɗinta.
Chapter 44 · 0% Book details