← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 80

Sashe 68

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana cikin farin ciki yau, dan sai da ya biya da ita gidan yayanta, suka gana da Daala da kuma su Baba Lami, duk da ba su tarar da matar gidan ba, a cewar Baba Lami wai ta fita unguwa ne.

Da sallama aka turo ƙofar falon, hakan ya sa ita da Anna kallon ƙofar.

Siyama ce ta shigo tana ɗan murmushi, sai de kuma cikin sakan ɗaya wannan murmushin ya ɓace daga fuskarta, sakamakon arba da Mishal da ta yi, saboda ba ta manta karonsa ba.

“Ah-ah, Siyam, ƙaraso mana”
Siyama ta haɗiyi miyau tana ƙarasowa cikin falon, gaba ɗaya yanayinta kaɗai zai fallasa sirrin zuciyarta.

A ɗarare ta zauna kusa da Annan tana satar kallon Mishal wadda ke jifanta da murmushin ƙeta.

“A...

Anna ina yini”
“Ke!

Lafiyarki kuwa?”
Siyama ta yi saurin girgiza kanta, sai kuma ta gyaɗa shi.

Har wata zufa take don tashin hankali.

“A'a Siyama, wannan yanayin naki ba lafiya ba, bari na samo miki wani abun sha”
Annan ta faɗi tana miƙewa, tare da nufar hanyar kitchen, da sauri Siyama ta bi bayanta, don zama da Mishal inuwa ɗaya ba nata ba ne, Mishal ta wuce tunaninta, saboda haka gwara ta bar mata falon, kafin ta laƙa mata sharri kan tana shaƙar iskar da ta furzar.

Mishal ta ƙara bajewa a kan kujera tana murmushi, saboda ta tuna abun da ya faru tsakaninta da su last time!.
***
“Me kuke nema?”
Muryar Mishal ta tambaya a waccan ranar, lokacin da Siyama da Karima suka shigo gidanta.

“Rayuwarki muke nema!”
Karima ta amsa mata a hassale tana shigowa cikin falon, duk da Mishal ta tsorota amma ba ta bayyana tsoronta ba, sai ta ɓoye kayanta a cikinta.

“Me ya sa kuke neman rayuwata?”
Ta tambaya tana sakin tsintaiyar hannunta.

“Saboda kin shiga tsakanina da Kuliya, kin raba ni da Kuliya.Ni kuma ina sansa, dan haka ba zan bari ina ji ina gani ki raba ni da shi ba”
Nan take wasu ƙofafi suka buɗe a ƙirjin Mishal, kishi ya soma kamata, wani abu me kama da wuta ya shiga ruruwa a cikin ranta.

“Mijina kike so?”
Ta tambaya ta na nuna kanta.

Cike da gadara Siyama tace.

“Ƙwarai kuwa, mijinki nake so, kuma tun kafin ya sanki nake sansa.

Dan haka na zo ɗaukar mataki”
Ta ƙarashe tana fitar da wuƙa daga jakarta, Mishal ta zabura ta finciko wayar tvnsu, ta hau dukan Karima da Siyama, abun su kansu ba ƙaramin mamaki ya basu ba, dan ba su taɓa zaton ƙaramar yarinya kamarta za ta iya aikata hakan ba.

Dukansu take kamar wadda Allah ya aikota, su kuma banda kururuwa da ihu babu abun da suke.

Jin sautin dirin motar Kuliya ne ya sa Mishal yada wayar, ta leƙa ta wundo ta ga tabbas shi ne, ta dawo da baya, ta buga kanta a jikin bango, tare da fasa ƙara, wanda ta karaɗe gidan baki ɗaya.
*You are not hard to love; You've just run into a few who didn't know how to...*
***
*No.86, Garki 2, Abuja...*
RABI'A POV.

Kwance take cikin style ɗin motsa jiki na plank, tana kan tabarmar motsa jiki ne, a cikin gym ɗin gidan.

A rannan da Zaid ya kaiya ganin likita ya shawarceta da yawaita motsa jiki, kuma hakan ne ya sa Zaid ɗin kawo mata mashinan motsa jiki.

Sanye take da wani baƙin leggings, sai wata yar siririyar tanktop da ta saka.

Daga gefenta kuma ruwan da ta tanada ne dan sha a sa'ilin da ta gaji.

Ba ta yi tsammani ba kawai ta ga ya shigo, hakan ya sa ta kusa tuntsirawa daga yanda take, ba shiri ta tashi daga kwanciyat plank ɗin ta zauna a kan tabarmar tana kallonsa.

Sweat pants da wata singlet ne a jikinsa, hannunsa na hagu riƙe da mug.

“Kai kuma me ka shigo yi a nan?”
Kamar wani me neman wanda zai ba shi amsa haka ya juya ya kalli bayansa sannan ya juyo ya kalleta.

“Motsa jiki mana” ya amsa matavikin ɗage gira, na shi bai ga lefin abun da ya yi ba.

“Motsa jiki?”
“Ƙwarai....

Ko da an ƙa'ide cewar maza ba sa yi, mata ne kawai ke yi”
Rabi'a ta girgiza kanta, dan ta ga alamar ba motsa jikin ya zo ba, neman magana ne kawai irin nasa.

Dan haka ta juya abunta tana sauya salon motsa jikin nata zuwa cat cow pose.

A duk sanda za ta sunkuya cikin motsa jikin sai ta kalli Zaid dake bayanta.

Zaid ya yi murmushi ya na aje mug ɗin hannunsa a kan wata chest drawer, sannan ya tsaya yana kallon kansa ta cikin mirrors ɗin dake zagaye da gym ɗin.

Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana wani jujjuyawa.

Kafin ya ɗaga hannayensa ya na auna girman muscle ɗinsa.

Duk abun da yake Rabi na leƙensa ta ƙasan ƙafafunta.

Kamar da aka ce ya kalleta ta cikin mirrorn, karaf suka haɗa ido, da sauri Rabi ta waske ta ci gaba da cat cow pose ɗinta.

Zaid ya kuma yin wani murmushin yana kama rigarsa ta ƙasa, sannan a hankali ya cireta.

Tsabar gulma Rabi ba ta san sanda ta dungura ta ka ba, saboda wasu tabbubbuna da ta ga a bayansa, ga kuma tsayawar da ya yi babu riga a jikinsa, wani abu da sam bata so, shi kuma ga shi kamar wanda aka yiwa asirin rashin zama da riga, kwata-kwata bay a san zama da riga a jikinsa in dai yana gida.

“Wai dan Allah Raj me ya sa ba ka da kunya ne?”
Rabi ta tambaya tana rufe idonta da hannunta, yayin da ta yi zaman cin tuwo bayan da ta dungura.

Zaid ya juyo ya kalleta.

“Me kuma na yi?”
“Dan Allah ka sa rigarka?”
Ta faɗi tana ƙara rufe idon nata.

Dariya ya yi mara sauti ya na cillar da rigar gefe, sannan a hankali cikin takun sanɗa ya isa inda take ya zauna a gabanta, har gwiwowunsu na gogar na juna.

“To na meda, buɗe ido naki”
“Ka ta babbatar?”
Yana ƙunshe dariya yace.

“Dubu bisa ɗari”
Kamar me tsoron ganin aljanu haka ta sauƙe hannunta, ai kuwa ta yi kyakkyawan gani, dan shi ɗin ne zaune a gabanta, babu riga a jikinsa, ga wannan chain ɗin sarƙar da ta saba gani a wuyansa ya kwanta a ƙirjinsa, waɗanan tabbubbuna na jikinsa suka mata maraba lale!.

Zabura ta yi za ta miƙe, kuma kafin ta miƙe ɗin ya sa hannunsa ya janyota, bata faɗa ko ina ba sai kansa, hannayenta naɗe a ƙirjinsa, yayin da shi kuma ya saka hannunsa ɗaya ta bayansa.

Ta zazzaro idanunwata tana kallonsa, kamar wadda aka tunawa yadda jikinsa yake a lokacin ta yi saurin kulle idonta.

Zaid ya yi dariya, a wannan karon me sauti ya yi, sannan ya mannata da jikinsa yana rungumewa, har zuwa lokacin idonta a rufe.

“To wai miye na jin kunyar?.

Na ga kin...”
Be ƙarashe ba saboda dukan da Rabi ta kaiwa bakinsa, dan ta san me yake shirin faɗa, shi ya sa a ko da yaushe take faɗin ba shi da kunya, bakin nasa ya dafe yana mata dariya.

Da sauri ta miƙe daga kansa ta fita da gudu ta bar masa gym ɗin.

Dan da ma kawai ta ɗan shigo dan ta motsa jikin nata ko kaɗan ne, saboda yau za'a ɗaura auren Anti Saratu, kasancewar babu wani shagali ya sa bata shirya da wuri ba, don Abbansu yace daga zarar an ɗaura za a kaita ɗakinta, babu wata bidi'a da za ayi.

Zaid na dariya ya miƙe zai bi bayanta, wayar dake cikin aljihunsa ce ta yi ƙara, hakan ya sa ya fasa binta ya zaro wayar ya ɗaga kira da sauri, ganin lambar abokan aikinsa, kuma wakilan da ya naɗa dan kamo Alhaji Bala da usman, dan tun daren jiya aka basu izinin kamu.

“Sir, mun kamosu, yanzu haka mun wuce headquarter da su!”
Abun da na cikin wayar ya fara faɗi kenan, hakan ya sa Zaid ya ɗaga kansa sama yana lasar lips ɗinsa.

“Na gane, anjima zan samu na leƙo”
“Ok sir”
Daga haka ya sauƙe wayar, shi kenan, duk wannan shekarun da ya kwashe cikin wannan aikin sun zo ƙarshe, assignment ya ƙare, komai ma ya ƙare, yanzu lokaci ne na fara sabuwar rayuwa tare da Adawiyyansa, lokaci ne da Rhoda za ta sake sabuwar rayuwa, lokaci ne da shi kansa zai huta, dan kuwa ba zai karɓi wani sabon aiki kwana kusa ba, zai ɗauki hutu ne dan ya kula da Ammatansa, zai ba ta lokacinsa duka, zai kuma zauna da ita na tsawon lokuta.

Zuwa yanzu abun da ya rage a aikin nasu kaɗan ne, abun da ya rage bai fi saura ba, dan tun da har an kama Alhaji Bala to an tsallake babban tudun, saura da me kuma?; Alhaji Bala ya amsa lefinsa, sannan ya bayyana sunayen abokan harƙallarsa da kansa, duk kuwa da su ma kansu sun san wasu daga ciki.

Usman da abokansa kuma shi ya san yanda zai yi da su, dan kuwa ɗaya bayan ɗaya ya sa aka kamo su, kuma shi ya san kalar hukuncin da zai musu.

Kafin su shiga kotu
“Sai yaushe kuma?”
Cewar Zaid, yayin da motarsa ta yi parking a farkon lungun gidan su Rabi.

Rabi da ta haɗe cikin wani kyakkyawan pink lace da bluen hijabinta ta juyo ta kalleshi.

“Sai ka zo ɗauka na mana. za ka je wurin ɗaurin auren ne?”
Ta tambaya tana ƙare masa kallo, dan kuwa yau ya fi mata kyau fiye da ko yaushe, sanye yake cikin wata brown color shadda, ga golden hular dake kansa, ya yi kyau kamar wani ango.

Zaid ya ɗaga kafaɗarsa ta dama ya na gyaɗa mata kai tare da faɗin.

“Insha-Allah.

Daga nan ma ai can zan wuce, sai de an jima kawai”
Ta gyaɗa masa kai tana shirin fita daga motar, caraf Zaid ya riƙo hannunta.

“Tafiya za ki yi ba tare da kin min...”
Dukan ta kai masa a baki, ya kaucewa ya na dariya.

“Wai ni ko me zan yi sai an dake ni?”
Rabi ta watsa masa harar wasa.

“Idan baka so ina dukanka ka dena rashin kunya”
Ya buɗe baki yana kama haɓa.
Chapter 68 · 0% Book details