Sashe 33
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da Rhoda ya fara haɗuwa a bakin ƙofa, ta jingina da jikin ƙofar part ɗinsu tana kallonsa, fuskarta ɗauke da murmushi.
Ransa ya haɗe ya na ɗauke kai, ya yi kamar be ganta ba.
Sai da ya zo wucewa ta gefenta, sannan ta ɗaga hannunta tare da saka masa wani fito me ƙarfi, har da wani tafa hannu, hakan yasa ya tsaya yana kallonta.
“Idan na ce you fall in love, sai ka ce ba haka ba, amma ga shi nan kullum sai ka karakata har bakin titi, idan ana cikin weekend sai ka riƙa ɓata rai, dude ko ka yarda...
Ko kar ka yarda, ka...
Faɗa.. can cikin kogin soyyaya! ”
Raja ya kai hannunsa ya dunguri kanta yana kamo wuyanta.
Ya ɗaga kafaɗarsa yana faɗin.
“Cuzzie yaushe kika fara sa ido?”
“Sanda ka faɗa soyyayar gaskiya...
Ba irin wadda kake a da ba”
Maganarta ta tuno masa da ita, Uchechi!, Wani sashi na kansa ya ambato masa sunanta, a hankali ya saki wuyan Rhoda, yana tuno alaƙar dake tsakaninsa da ita, kenan da shi ba son Uchechi yake ba?, to kenan da me yake ji a kanta?, kuma me yake ji a kan Ammantasa?.
Tukkuna ma wani hali Uchechi ke ciki, tun bayan zuwansa Abuja ba su yi waya da ita ba.
Naushin da Rhoda ta sakar masa a ƙirji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa yana kallonta.
“Tunani ba?
Ai da ma sai da na faɗa maka cewar ba son Uchechi kake ba, kuma ita ma ba sanka take ba, kuɗinka take so, kai ne ka kasa banbancewa tsakanin son gaskiya da na yaudara!...”
Kallon ta ya yi na wasu 'yan sakkani, kafin ya kamo kunnenta.
“Thunder go fire your head Rhoda!
Ki ce har zarar zance kika koya?”
“Zaid...”
“Shiru!
Ba na san wata magana!”
Sai ta yi shiru tana sosa kunnenta da ya saki, tare da turo masa baki gaba.
“Sorry”
Ta faɗi tana sinne kai ƙasa, janyota ya yi ya mata side hug, kafin ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama yace.
“Ke ɗin ce bakya jin magan Cuzzie...
Maza mu je akwai aiki a gaban mu”
Nan da nan Rhoda ta dawo serious, tunawa da ta yi da aikin dake jiransu a gaba, aikin shigo da makaman da Alhaji Bala ya ɗorasu a kai.
*Hotoro, Ring Road, Kano...*
Uchechi ce zaune a ɗakinta, ta sa gabanta yamma tana kallon mirror, yayin da take zaune a kan stool, kallon fuskarta take a mirrorn, yayinda take neman wani abu a fuskarta da wata ƙila shi ya sa Raja yake mata abun da ya so, wata ƙila ba ta da kyau yanda ya kamata, ko kuma akwai wani tabo a fuskarta da ya sa Rajan ba ya san kusantarta.
Ƙofar ɗakin aka turo, kuma ba tare da ta juya ta kalli ƙofar ba, ta hango wanda ta shigo ɗikin, Mesoma ce, yayarta wadda take riƙe da ita.
Ba ta juya ba har Mesoman ta zauna a bakin gadon dake bayanta, ta na ci gaba da kallonta.
“Wai Uchechi ba za ki manta da wannan Rajan ba?...
Tun da har ba za ki iya sato zuciyarsa ba, kuma ba za ki iya samawa kan ki ruwan da zai kashe miki ƙishin ruwar ki a kansa ba, zai fi kyau ki manta da shi”
Juyowa ta yi ta kalleta.
“Mesoma ina san Raja...
Ba na jin zan iya rabuwa da shi, duk munin abun da zai min kuwa, batun samun Raja kuwa zan daure na yi haƙuri har zuwa lokacin da ya tsara mana dan mu yi aure, tun da yace ba zan taɓa samunsa ba idan har ba aure muka yi ba”
Mesoma ta rage girman idonta tana kallon ƙanwarta.
“Hanyoyi nawa na tsara miki na yanda za ki samu kuɗi a hannunsa ?, Da na tsara mikin ba ki samu ba ?”
Uchechi ta girgiza kanta.
“Na samu, na samu abun da ban yi zanton samu ba”
“To me yasa da na tsara miki hanyar da za ki samu kansa ba ki bi ba?”
“Mesoma ba zan iya bin hanyar da kika tsara min ba, waɗannan hanyoyin naki sun yi tsauri da yawa”
Mesoma ta miƙe tsaye.
“So...
That was the only way that i have, tun da kin ga ba za ki iya bi ba, sai ki yi ta zama cikin ƙunci”
Da sauri Uchechi ta miƙe tana kamo hannunta.
“Ki temaka ki nemo min wata hanyar”
“Ba ni da wata hanya bayan wadda na riga ma baki, idan kin ga za ki iya binta, fine, if not sai ki sa haƙuri a zuciyarki”
Mesoma ta kama hanya ta fice daga ɗakin, cike da neman mafita Uchechi ta koma ta zauna a kan stool, ta furzar da iska daga bakinta.
Cike da takaici ta yi fatali da kayan dake kan mirrorn.
To wai ita ya za ta yi ne?, me ya kamata ta yi dan samun kan Raja?, wata hanya ya kamata ta bi don ta mallakeshi?!.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
“Wallahi Musa tun muna shaida juna ka kira wannan yaron da kuka aurawa jikata, ya faɗa mana ina ya kaita!
In ba haka ba Wallahi sai nai maka abun da kowa zai zo yana nadamarsa!”
Muryar Jadda ke faɗin hakan cike da masifa, yayin da wayarta ke kare a kunneta, daga gefenta kuma Hajjara ce zaune tana ƙunshe dariyar muguntar dake cinta, dan ita ta kunno wutar.
Suna zaune ne a falon gidan, yayin da Jaddan ke ta sirfawa Ammu Musa buhun bala'i.
“Wai dan Allah Jadda haka ake rayuwa?, Ta ya za ki ce na kira mutum na tambayeshi inda ya kai matarsa?”
Muryar Ammu Musa ta faɗi cike da gajiyawa da halin Jadda.
“Au haka ma ka ce?
To ka kyauta, Wallahi za ka ga abin da zan maka, shashasha, wanda bai san inda ke masa ciwo ba!”
Daga haka ta latse wayar ta cillar da ita gefe tana hucin bala'i.
“Gaskiya Jadda Ammu Musa bai kyauta ba, ta ya zai ɗauki 'yarmu ya bawa wani wanda ba musan shi ba?
Ba mu sani ba ma wata ƙila ɗan ya kan kai ne?”
Cike da san tittilawa wutar fetir Hajjara ke bayanin, dan har yau ba ta manta da abun da Mishal ɗin ta yi mata ba, gashi dai takaba take, amma baƙin cikin Mishal ɗin bai bar ruhinta ba.
Aiko fiterin da ta bilbila ɗin ya sauƙa a tsakiyar zuciyar wutar, don ta tashi sama ta ƙara ruruwa fiye da yanda take ci a da.
“Aiko ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ko ni ko Musa, dan Wallahi ba zan zauna ina gani ya sabautar min da jika ba, duk in da zai je dole ya dawo ya sameni, dan Wallahi ba zan bar garin Abuja ba sai na san gidan da ya kai min jika”
Nan take murnar da Hajjara ke ti ta koma ciki, don kuwa ita ba haka ta so ba, ta so a ce da zarar Jaddan ta gama abun da za ta yi ta kama hanya ta koma Maiduguri, ita kuma a bar mata gidanta ita ɗaya, tun da yanzu ɗayar abokiyar gabar tata ba ta nan, sai ta mulka gidan san ranta, duk da Ammu Musa ya ce idan an yi arba'in za'a raba gado, don akwai dukiyar Mishal da Abubakar ɗin ya ba shi riƙo.
Wutar da take ganin ta hura sai ta dawo kanta,sakamakon mantawa da ta yi ba ta janye hannunta daga saman wutar a sanda ta tittila fetirin ba, Zama da Jadda?, tashin hankali kenan.
_____________________
_Wayyo Allah cikina!🤣🤣_
_Kai jama'a, wai aka ce idan za ka haƙa ramin mugunta, ka gina shi gajere, kuma an ce mugunta sayin faƙo, idan baka iya ba ka ɓata jikinka_
_Ga Uchechi a kan layi..._
_Wani ya faɗamin abun da zai faru a aanda Uchechi ta san cewa Raja ya faɗa soyyaya da wata_
_Sannan ga kuma Jadda a nata ɓangaren, da alama ita ma za'a fafata da ita_
_Ga kuma Uncle Kuliya a gefe, kada fa kumanta da ya ga Rabi'a, wani ya faɗa min meke shirin faruwa..._
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*12*
~~~
_-*I think the most beautiful thing you could ever experienced is finding someone who wants your all, even if your all is a mess*-_
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
“Wannan shi ne file ɗin next assignment ɗinka!...”
Cewar Chidera, a sa'ilin da yake miƙa masa file ɗin aikin da ya kamata a ce ya aiwatar a gaba.
A karo na farko tun bayan fara aikinsa, Kuliya ya ji wani abu me kama da tsoro ya kama shi a kan aikin, tun da yake bai taɓa ja da baya a kan ko wani aikin da ya sa ƙafa ba, bai san tsoro ko koma ba ya kan aikinsa ba, amma a yau sai ga shi ya na jin ɗar-ɗar na karɓarsa sabon assignment.
A da shi da kansa yake neman assignment ko ba'a ba shi ba, ko ya karɓi na wani ya ƙarsa, amma a yau sai ya ke jin kamar ba zai iya ba, kuma tsoron da yake ba na komai ba ne, sai na gudun kada wani abu ya zo ya faru da makusantansa.
A da sam ba shi da kalar wannan tsoron, ko da rayuwarsa zai salwantar zai a kan aiki sai ya karɓa, bai damu da kowa ba dan ba shi da kowan da ya wuce Anna, tun da ya mallaki hankalinsa be san ya raɗaɗin zafin rasa makusanci yake ba, sai bayan da Abubakar ya mutu ta dalilinsa.
Kamar me shirin karɓar zunubansa haka ya kai hannu ya karɓi file ɗin, kafaɗarsa ta dama ya ɗaga sannan ya kalli Chideran da ya fara masa bayani a kan aikin.
“Case ne a kan kisa da kuma fyaɗen da aka ma wata yarinya a Life Camp”
_“Dama na san wata rana dole za ku so ku san waye mahaifinku...
A zahirin gaskiya Aliyu da Zaid ban san mahaifinku ba.
An gayyace ni zuwa wurin bikin wata ƙawarmu ne....
Kuma a wurin aka zuba min abun gusar da hayyaci a cikin abun shana.
Har aka samu wani ya haike min!.