← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Me ɗin?”
“Babyn mana.

An tabbatar kina ɗauke da shi?”
Nan take ta haɗe rai tana kai masa duka a damtsen hannunsa.

“Auuchhh!

Teddy Bear irin wannan duka haka?”
Ta turo baki gaba tana faɗin.

“To ba kai ka ce min na samu baby ba, kuma sai ka dawo kana min wani ƙauli da ba'adi”
Ta faɗi idonta na ciccikowa da ƙwalla, dan ita har ga Allah ta riga da ta yadda da cewar ta kusa samun babyn, ya riga da ya sa mata rai, kuma sai ya zo yace ba haka ba?.

“Wasa fa nake miki, amma idan kina so sai an ƙara!...”
Ta san me yake nufi da sai an ƙara ɗin, dan haka ta ƙara ɗaka masa wani dukan, wannan karon a cinyarsa, ya dafe wurin yana dariya.

“Ki yi haƙuri, kin ga fa ba ni da lafiya, ya kamata ace an raga min ai”
Mishal ta share ƙwallar da ta silalo mata, dan ita ta mamanta da ba shi da lafiyar.

“To ka yi haƙuri”
“Ke!”
Ta kalleshi.

“Me ya sa kika yi laushi ne?.

Abu kaɗan sai ki masa kuka, bayan na san da ba haka kike ba”
Ya tambaya jin a ɗazun da ta yi magana murmuyarta ya fito a raunane.

“To ba girma nake ba!”
“Iyeee, lalle girma, su Mishallyn Aliyu an fara girma”
Sai ta yi dariya tana rufe fuskarta da tafukan hannunta.

Shi ma sai ya yi dariyar.

A lokacin kuma aka turo ƙofar ɗakin.

Anna ta shigo, hakan ya sa su duka suka kalleta.

ZAID POV.

Yana fita da Rabi'a ba su tsaya a ko ina ba sai wani ɗaki dake kusa da wanda aka kwantar da Aliyu, kasancewar ɗakin babu kowa.

Suna shiga ɗakin, ya tura ƙofar ɗakin ya rufe, sannan ya jingina bayansa a jikin ƙofar.

Yana miƙawa Rabi dake tsaye hannunsa, kamawa ta yi, shi kuma ya jata ta faɗo kan jikinsa, ya saka hanyyensa duka biyu ya rungumeta.

Ita ta ɗago daga jikin nasa tana faɗin.

“Ka ji yanda kayan jikinka suke warin gumi?”
Jikin nasa ya shinshina yana faɗin.

“To ya zan yi da rayuwa, larura ta sa na koma ƙazami, kwana ɗaya ban yi wanka ba fa, ga mu yau a na biyu...”
Ta ɗan yi dariya tana mayar masa da chain ɗin wuyansa ƙasan rigar jikinsa.

“Rhoda tace na faɗa maka, ita ta wuce gida, za ta je ta shirya, wai ku haɗu a kotu”
“Uffff!

Kin ga Wallahi shaf na manta!”
Ya faɗi yana dafe kansa.

“Abubuwan nawa ne da yawa, kinga kuma ko su kawu Abdullahi ban kira ba, dan kin san ya kamata na sanar da su halin da ake ciki”
Ta gyaɗa kai.

“Haka ne...

Abun da ya fi kawai yanzu ka koma gida ka je ka yi wanka, ka sauya kaya, sai ka wuce kotun...

Kuma ga abinci nan ma na kawo maka”
Kansa ya girgiza.

“Ba na jin zan iya tafiya na bar Aliyu shi kaɗai”
“Wa ya faɗa maka cewar Aliyu shi kaɗai ne, akwai ni, ga kuma Mishal”
“Idan kuma wata buƙata ta taso wadda dole sai kun buƙace ni fa?”
“Da yardar Allah har ka dawo babu wata matsala da za ta faru”
“Kin tabbata?”
Ta gyaɗa masa kai.

Sai da ya ƙara janta jikinsa ya rungume, sannan suka fita a tare.

Ganin wata mata da ban a ɗakin zaune kusa da Aliyu ya basu mamaki.

“Ƙaraso Zaid.

Wanan ita ce Anna!”
Cewar Aliyun yana nuna masa matar dake sharar ƙwalla.

Anna ta juyo tana kallon me kama da ɗanta.

“Zo nan, ai kai ma ɗana ne”
Anna ta faɗi tana miƙa masa hannu.

Zaid ya ƙarasa kusa da ita ya zauna.

Suka sakata a tsakiya, idan ta juya ta kalli Zaid, sai ta juya ta kalli Aliyu, kafin idonta ya sauƙa a kan Rabi dake tsaye kusa da Mishal.

“Wannan ita ce matar taka kai ma?”
Zaid ya gyaɗa mata kai.

Zaid ya ɗan jima a ɗakin, kafin ya musu sallama, bayan ya faɗa musu uzurin da zai je.

Har yabkama hanyar barin ɗakin,maganar Aliyu ta dakatar da shi.

“A dawo lafiya Zaid”
Sai da ya juyo ya kalleshi, kafin ya gyaɗa kansa yana fita.

Rabi ta bi bayansa suka fita tare har zuwa jikin motarsa.

Shiga ya yi, kana ya buɗe ɗayar ƙofar dake side ɗin da Rabi ke tsaye, ya mata alama da ta shigo, shiga ta yi ta zauna.

“Ban sani ba ko zan jima ban dawo ba, saboda ana gama shari'ar, za mu wuce na kai Rhoda karɓar musulunci”
Sai ta gyaɗa kanta tana ci gaba da kallonsa.

“Me kike so na kawo miki yau?”
“Ba na buƙatar komai, kawai kai nake so?”
Sai ya ɗage mata gira ɗaya yana faɗin.

“Ni da kai na?”
Ta yi dariya tana gyaɗa masa kai.

“In dai ni ne kin samu 'yan matana, and zan kawo miki kifi, ko shi ɗin ma ba kya so?”
Ta girgiza kanta.

“Ina so”
Zaid ya ɗaga kafaɗa cikin faɗin “To sai na dawo?”
“Ummm”
“Kuma tafiya za ki yi ba tare da kin...”
Tureshi ta yi tana dariya.

“Zaid hoo, baka jin magana Wallahi!”
“To ni ki min”
Juyowa ta yi tana kama fuskarsa, kafin a hankali ta yi kissing ɗinsa.

“Shikenan?”
Ta faɗi tana ja baya.

Fita ta yi daga motar, tana rufo masa ƙofar.

“A je a yi wanka, a ƙazan-ƙazan”
Ta faɗi tana leƙo da kanta.

“Lalle kin ci tuwo a kaina Adawiyya, amma zan rama”
Ta bar wurin tana dariya.

Ya tayar da motar yana ƙara sinsinar jikinsa.

“Wanka daɗi, wani bai san daɗin wanka ba”
Ya yi waƙar yana juya kan motar.
*Believe in your dreams...*
Anna da Rabi ne suke tafe, bayan da suka dawo daga wani shago da suka je dan siyan ruwa, duk yanda Rabin ta so Anna ta zauna kan ita za ta je, fir Anma ta ƙi yarda, tace sai de su je tare.

Dan ita tausayin Rabin take.

A kallon farko da ta mata ta gane cewar tana ɗauke da ciki!, shi ya sa take tunanin kamar ba za ta iya ɗaukan ruwan ba.

Amma sai ga shi bayam da suka siyo ruwan ma ba ta bar Annan ta ɗauka ba.

Ba tare da Rabi ta ankara ba, ta ji juwa ta ɗebeta, ta yi baya luuu za ya faɗi, ledar robobin ruwan dake hannunta ta faɗi ƙasa.

Anna ce ta yi saurin kamota.

“Sannu!...

Kin ga ko?, shi ya sa na ce ki bari na ɗauka, macen dake cikin hali irin naki ba'a barinta ta ɗauki abu me nauyi!”
Cikin rashin fahimta Rabi'a tace.

“Babu komai fa Anna, wallahi ƙalau nake”
Anna ta ɗauki ledar tana dariya.

“Haba 'yanan, ai mace me ciki ba a rabata da laulayi!...”
Wani shaftareren yanki na zuciyar Rabi'a ne ya yanke ya faɗo ƙasa, wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan bomb ya fashe a ƙirjinta, ta sandare a wurin, ta kasa motsa ko da ƙafarta, sai idanuwanta da ta zaro suna duban Anna.

Ciki fa?, wai ita ?, ita Rabi'a take da ciki?.

Ganin haka ya sa Anna fahimtar cewa ba ta ma san cewa tana da cikin ba.
”Baki sani ba kenan?”
Kamar wata sokuwa haka ta gyaɗa kanta.
*
Zaune take a kan ɗaya daga cikin kujerun dake wani corridor, har zuwa yanzu ta kasa yarda da abun da ta ji, wai ita ce take da ciki, to garin yaya, daga sau ɗay!...

Kunyar kanta da ta kamata ce ta sa ta kasa ƙarasawa.

Ta yi jigum-jigum, tana jiran fitowar result ɗin gwajin da aka mata.

Wata nurse ce ta fito daga ɗakin da take fuskanta, ta shiga kiran sunayen mutanen dake zaune a wurin, da haka har aka iso kanta, ta karɓi nata result ɗin tana komawa baya, tare da zama a inda ta tashi.

Hannunta har rawa yake wurin buɗe takardar.

Tar manyan rubutun da takardar ke ƙunshe da su ke sanar mata cewar tana ɗauke da ciki na sati huɗu.

Kanta ta sunkuyar ƙasa tana shafa cikinta.

A lokacin kuma ƙwalla ta zubo mata.

Yanzu kenan ciki gareta?, cikin ma kuma ba na kowa ba sai na Zaid!.

ZAID POV.

Bayan hujjojji da aka gabatar a gaban kotu, kotu ta yankewa Alhj Bala hukuncin ɗaurin rai da rai, sauran abokan harƙallarsa kuma, ciki har da Garuje, an yanke musu hukuncin dai-dai da nasa, Usman da sauran abokansa kuma, an yanke musu shekare ashirin-ashirin a gidan kaso.

Kuma da haka shari'ar ta zo ƙarshe.

Bayan shuɗewar tsawon shekaru, sai a yau ne Rhoda ta samu adalci kan abun da aka aikata mata, ba ma ita kaɗai ba, hatta da Rabi a yau ne aka sama mata 'yanci.

Daga kotun kai tsaye Zaid ya wuce da Rhoda masallacin da ya yi magana da limaminsa, dan shi yake so ya bawa Rhoda kalimatu shahadah.
*No.86, Garki 2, Abuja...*
*08:00*
Rabi da Zaid ne zaune a falo suna kallo a tv.

Rhoda kuma na ɗakin da Rabi ta ware mata, dan yau a gidan zata kwana.

“Mts!

Ammata na manta da kifinki a mota, bari na je na kawo miki”
Cewar Zaid yana miƙewa tare da barin falon.

Rabi ta sunkuyar da kanta ta kalli cikinta.

Tun bayan dawowarta gidan take ta neman hanyar da za ta faɗawa Zaid wannan kyakkyawan labarin, amma ta rasa ta inda zata fara.

Kallo ta ci gaba da binsa da shi, har ya dawo hannunsa riƙe da leda, ya buɗe ledar, ƙamshin kayan haɗin da aka yi amfani da su wurin haɗa kifin ya bugi hancints, hakan ya sa ta ji amai ya zo mata.

Ba shiri ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinta.

Baki sake Zaid ya bi bayanta da kallo, kafin shi ma ya miƙe ya nufi ɗakinta da ya ga ta shiga.

Ko da ya isa ɗakin sai ya tarar da har ta faɗa bayi, ta kuma kulle kofar bayin.

Maganar duniya mata amma ta ƙi amsa shi hakan ya sa ya juyo, ya na shirin barin ɗakin, idonsa ya sauƙa kan wata takarda aje a kan hijabinta.

Don haka sai fasa fitar, ya dawo ya ɗauki takardar ya shiga karantawa.

Sai da Rabi ta gama aman nata, ta wanke bakinta, sannan ta fito.
Chapter 78 · 0% Book details