Sashe 41
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka ya yi applying wata University a nan cikin garin kano, don ba zai iya yin nisa da Rhoda ba.
Da haka rayuwa ta ci gaba da gangara musu, yau da daɗi gobe babu.
A lokacin da Zaid ya kammala karatunsa, sai ya shiga neman aikin DSS, aikin da ya sha burin yi tsawon rayuwarsa, aikin da yake kwana yake tashi da shi a zuciyarsa, aikin da suke da burin yinsa tun suna yara shi da ɗan uwansa.
Cikin ikon Allah ya samu, hakan tasa ya ɗauki Rhoda suka koma Abuja, kuma ita ma bayan ta gama makaranta sai ta ce tana san ta shiga aikin DSS ɗin, Zaid be hanata ba, sai ma shige mata gaba da ya yi har ta samu.
Shekerar Rhoda biyu da fara aiki, aka basu wani assignment me haɗari, wani assignment me ɗauke da sumatsi, wani assignment wanda ya shafi rayuwar ko wannensu, wani assignment wanda ya taho da guguwar ƙaddararsu, wani assignment wanda zai zama sanadiyyar faruwar wata ƙaddara, wadda za ta iya tarwatsa komai, sannan ta shirya wasu lamuran.
Assignment ne a kan wani me kuɗi wanda ake zarginsa da yin safarar makamai da kuma miyagun ƙwayoyi, Alhj Bala, wanda a lokacin yake zaune a garin Abuja.
Daga Zaid har Rhoda babu wanda ya yi musu wurin karɓar aikin, don za su jefi tsuntsaye biyu ne da dutsi ɗaya.
Dole ta sa suka dawo garin Kano, don suna buƙatar bi ta hannun Garuje, babban yaron Alhj Balan, ƙarfi da ya ji suka koma 'yan daba, shi Zaid har da sauya suna zuwa RAJA.
Sannan sun yi yarjejeniya da Rhoda kan idan sun kawo ƙarahen aikin za ta musulunta, babu yanda be yi da ita ba kan ta musulunta tun tana ƙarama, amma taƙi, sai yanzu ta yarda da hakan, shi ya sa Zaid ya zage damtse, don ya samu ya kawo karshen aikin ta ko wani hali, saboda ya na so ƙanwarsa ta samu rabauta, tun da Allah be sa Maman Rhoda ta samu rabon ba.
Kuma sun nemo wasu 'yan dabar kan titi guda uku, dan aikin nasu ya tafi dai-dai, Alandi, Zuzu da Jagwado, Zaid ya temaki rayuwarsu sosai, kafin ya ɗauke su aiki.
Kuma a lokacin ne suka haɗu da Uchechi.
____________________
_Salmanians!...
Ku ce kallon kitse mukewa rogo, ashe Raja ba ɗan ba ba ne, kai amma wanga bawan Allah an yi ɗan reni_
_Kada fa ku manta da sirrin zuciyar Zaid da ya bayyana ya fito fili, shin kuna ga Rabi za ta amince da shi?_
_Ku dai ku ci gaba da bi na sannu a hankali, dan ganin wata waina za mu toya a feji na gaba_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*14*
~~~
_-*The key element to happiness is; Knowing that you deserve to be loved correctly for the wild and beautiful soul that you are*-_
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
RABI'A POV.
Har ta kai gida ba ta cikin hayyacinta, ba ta sani ba ma ko ta haukace ne, haka ta riƙa yin abubuwa sukuku, har Anti Saratu ta lura da ita.
Tana zaune a ɗaki ta takure wuri ɗaya, Anti Saratun ta shigo ta zauna kusa da ita ta na taɓata.
Yanda ta zabura ya ankarar da Anti Saratun cewa tunani me zurfi ta faɗa.
“Rabi?!
Wai me yake damunki?”
Rabi ta sauƙe ajiyar zuciya tana sunkuyar da kanta ƙasa, to wai ita me za ta ce ne?, ta faɗa mata cewar wannan Zaid ɗin da ta take yawa bata labarin suna mutunci ne ya yi faɗa da arniyar budurwarsa kanta, kuma ya furta cewa ita ce matar da zai aura nan gaba?, yin soyyayar sa da arniya ba laifi ba ne, dom ba haramun ba ne, amma yanda ya mari budurwar tasa, da yanda ya furta 'His wife to be' ɗin nan shi ne abun da ya tsaye mata a rai.
“Ba za ki faɗa min ba ?”
Rabi ta ƙara yin ƙasa da kanta, don ba ta san me za ta faɗa matan ba.
“Rabi!
Kin san cewa ba ma ɓoyewa juna komai, duk damuwata ke nake faɗawa, me ya sa ke ba za ki faɗa min taki damuwar ba?
Idan har ba zan iya temeka miki ki fita daga cikin dakuwar ba, ni me iya tayaki baƙin ciki ce”
Jin hakan ya sa zuciyarta tsinkewa, ba shiri hawaye ya sauƙo mata, hawayen da ta yi ta riƙe shi tun ɗazu don kar ya zubo, sai kawai ta kwantar da kanta a kafaɗar Anti Saratu.
“Anti Saratu wai ina zan sa kai na ne?.Ya ake so na yi?.Yau Zaid ya yi faɗa da budurwarsa a kaina, kuma ya faɗa mata cewar ni zai aura ba ita ba.
Da ma ina da wannan muhummancin?”
Bisa ga mamakinta sai ta ji Anti Saratu na murmushi.
“Kowani ɗan adam ya na da daraja da muhummanci Rabi, kuma kowa ya na da tasa darajar.
Ina me miki albirishiri da kasancewarki ɗaya daga cikin masu wanna darajar, saboda kina da daraja fiye da lissafinki Rabi!”
Rabi tasaki kuka me sauti.
“Yanzu ya zan yi da Yaya?, idan na rabu da shi ban masa adalci ba”
Wannan maganar tata ta tabbatarwa da Anti Saratu zarginta a kan Rabin tun lokacin da Zaid ɗin da take ba ta labarinsa ya fara ɗorata a taxi, daga Rabin har shi Zaid ɗin suna san junansu ne ba tare da sun sani ba.
“Rabi ki na son Zaid?!”
Tambayar ta saka Rabi fashewa da matsanancin kuka, ita ba ta san ya za ta yi da rayuwarta ba, ba ta ma san inda za ta sa kanta ba, ina za ta kai kanta da hakkin Yaya?, A gaskiya ta cuci kanta da har ta bari soyyayar Raja ta shiga ranta, haɗuwarta da shi kuskure ce, fara kula shi da ta yi ma kuskure ne, maganar da suka yi kuakure ce, komai ma tsakaninta da shi kuskure ne, a she da da take cewa tana son Yaya faɗi kawai take a baki, yanzu ta fara soyyaya, sai a yanzu ne ta faɗa ramin soyyaya, sai a yanzu ne ta saka ƙafarta a soyyayar, sai a yanzu ne ta fara jin shauƙin soyyaya, amma me ya sa ?, Me ya sa ƙaddarorinta suke zuwa a haka?, Me ya sa duk wani abu me kyau da ta samu sai ya guje mata, don kuwa ba za ta iya auren Raja ba, ko ta na son Yaya ko babta sonsa dole ne ta zauna da shi, don babu yanda za ayi ta kalli tsabar idonsa ta faɗa masa ba ta sonsa.
“Ina sansa Anti Saratu.
I LOVE ZAID!, i... i...
Love him, i feel like The word 'love' is not enough for me to explain the way i love him!”
Ta fito ta faɗi duk abun da ta san ta na ji a ciki zuciyarta, ba so kawai takewa Raja ba, har da ƙauna ma tana masa, don soyyayar tasu ta jini ce, su jinin mutum ɗaya ne, shi da mijin Mishal 'ya'yan yayar Umma wadda take yawan basu labarinta ne, su ne 'ya'yan me sunanta, su ne 'ya'yan da kakansu ya basu labari kan an sha nemansu amma ba'a same su ba.
Cike da tausayawa Anti Saratu ta ɗagota daga jikinta.
“Haƙiƙa Rabi kin gamu da jarabawa, amma babu yan da za mu yi, addu'a ita ce mafita, don haka sai ki dage da addu'a!”
*No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja*
“To yanzu Anti miye abun yi?”
Cewar Siyama cikin kuka, tun da ta dawo gidan Anti Kariman ma ba ta samu sukuni ba, don ji ta yi hankalinta ma ya fi tashi a nan ɗin.
Anti Karima ta kalleta na wasu 'yan sakkani, gaba ɗaya ta sauya, kamar ba Siyamanta ba, ta rame ta ƙara baƙi, kamar kazar mayu.
“Ba de kin ce yarinya ba ce?”
Siyama ta gyaɗamata kai tana share hawaye.
Anti Karima ta gyaɗa kai.
“To ai cikin sauƙi za mu yi maganinta, ba tare da kin ɗaga hankalinki ko kin tayar da nawa ba...
Zo ki ji”
Siyama ta miƙa mata kunnenta, ido waje take kallon Anti Karima, bayan da ta faɗa mata abinda za su yi.
“Kuka ki na ganin babu matsala?”
Ta faɗa cikin karyewar murya.
“Mtswwww!, Wata matsalar kuma za'a samu, hakan kawai za mu yi”
Siyama ta gyaɗa kanta cike da gamsuwa, duk da ta na jin ɗar-ɗar a cikin ranta, amma sai ta dake ta miƙe ta shige ɗakinta.
Anti Karima ta bi bayanta da kallo cike da tausayawa, idan de har Kuliya ya shigo hannunsa ba za ta masa da sauƙi ba, dan sai ta rama abun da ya yiwa ƙanwarta.
Ta yi ƙwafa a bayyane tana jan wani littafi dake aje kan coffee table.
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
Zaune take a falo ta na rubutu a cikin littattafanta, ta baje takardu da littatafi a ko ina, don wani assignment ɗin math aka basu me wahalar tsiya, duk da ita ba sosai take yin assignment ɗin math ba, wannan ɗin ma don malamin yace shi ne makin C.A ɗinsu.
Shi ya sa ta dage take yi.
Ƙofar falon aka turo, Kuliya ya shigo ba tare da ya ko kalleta ba ya kama hanyar corridor, ita ma ba ta takura da sai ta masa magana ba, don ta lura da ba ƙaramin miskili ba ne, ta taɓe baki ta ci gaba da aikinta.
Bayan shuɗewar kusan muntina ashirin sai ga shi ya fito, sanye cikin wata baƙar T-shirt da baƙin sweat trouser.
Fuskarsa kawai ta kalla ta ganta a haɗe, babu alamun rahama ko fara'a, da alama dai yau ransa a ɓace yake sosai.
A falon ya zauna ba tare da ya mata magana ba, sai wani cin magani yake, ɗagowa da kanta ta yi ta kalleshi, sannan ta ci gaba da rubutunta tana faɗin.
“Sannu da zuwa”
Ƙin kulata ya yi, don ransa a matuƙar ɓace yake, for the very first time a rayuwarsa ya yi falling assignment, wani abu da kaf tsawon fara aikinsa a wurin bai taɓa faruwa da shi ba, a ko da yauashe shi me nasara ne, kuma ba faɗuwar tasa ce kaɗai ta ɓata masa rai ba, sakin me laifin da aka yi ne ya fi ɓata masa rai.