Sashe 71
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“I mean, menene burinki, ko wani fatanki, ko mafarkin da kike, na irin rayuwar da za ki gudanar da shi bayan kun yi aure?”
Ba ta yi mamakin sanin Yayan da ya yi ba, dan a yanda ta fahimci mutum me aiki irin nasa, idan da hali har yanda hanjin jikin mutum ke aiki zai iya bincikawa.
Wayarta ta aje a kan cikinsa tana ɗora hannunta kan ƙirjinsa.
Idonta na kallon sama ta shiga faɗin.
“Farko dai auren mu, sai kuma mu zauna a wani ɗan ƙaramin gida, ba fa dole sai babba ba, kullum da daddare idan ya dawo, ya riƙa kunna mana wasan ball muna kalla a tv, ko da ba mu da tv a gidan, sai mu kalla a waya, ko ma de ya kasance laptop ɗinsa da shago.
Idan wata rana kasuwa ta yi kyau, ya ɗauke ni a bayan mashin, mu shiga zaga gari ni da shi.
Ɗan ƙaramin burina kenan.
Amma cikin wattanni komai ya wargaje, na tsani Yaya Raj!”
Zaid na wasa da geshin kanta ya furta.
“Wai kekam tsana ba ta miki wahala ne?”
Kallonsa ta yi na wasu 'yan sakonni, kafin ta miƙe daga jikinsa tana zuro da ƙafafunta ƙasan kujerar.
Zaid ya kai hannunsa yana ɗaukan wayarta da ta aje masa a kan cikinsa ya miƙe zaune shi ma.
Kallon gefen fuskarta kawai yake, yana san sanin abun da take tunani.
Kamar Rabi ba za ta ƙara cewa komai ba, can sai tace.
“A sanda na taso ban san soyyayyar kowa ba sai ta Umma data Yaya Baby.
Bayan rasuwar Baby sai ya rage daga ni sai Umma, bayan rasuwar Umma kuma sai na haɗu da soyyayar dangi.
Bayan na bar wurin dangina na koma gidan mahaifina a nan ne aka fara koyarwa rayuwata wani sabon darasin da ko da wasa ban taɓa kawo shi a kaina ba.
Tsana!, Kar ka yi mamaki idan na ce maka a tasowata ban san tsana ba, dan babu wanda ke nuna min ƙi...
Kowa haba-haba yake da ni.
Amma daga sanda na dawo gidanmu komai ya sauya, mafarkaina suka durƙushe, komai nawa ya hargitse, babu wanda nake raɓa na ji sanyi sai Anti Saratu.
Kowa tsana yake nuna min.
Daga baya kuma sai na haɗu da Zara, ita ma ba laifi, tana nuna min tata soyyayar.
Bayan wani lokaci kuma sai ga Yaya.
Shi ne na miji na farko da ya fara koyar da ni yanda ake so...
Shi ne mutum na farko da ya fara buɗemin hanyar soyyaya.
A lokacin da muka fara soyyaya da Yaya, a lokacin na fara zuwa Makarantar Brickhall.
Daga malaman har ɗaliban makarantar babu wanda bai taka rawa wurin nuna min ƙi ba.
Sai mutum ɗaya, wata yarinya ɗaya kacal, ita ce ta nuna min soyyaya.
Daga lokacin kuma sai na haɗu da kai...”
Ta ƙarashe tana maida dubanta gareshi.
Shi ma kuma ita ɗin yake kallo da lumsassun idanuwansa.
Yana nazarin kalaman nata bi da bi.
“Rabin rayuwata ta a kan tsana take Raj, me ya sa ni ma ba zan koyi tsanar ba?, an nuna min cewa ba'a so na, me ya sa ni ma ba zan nuna cewar ba na san wanda ba ya so na ba?...”
“Shhhhhh!”
Zaid ya faɗi yana ɗora yatsansa a kan lips ɗinta.
Kusa da ita ya matsa.
Ya ɗora hannayensa a kan kafaɗarta.
“Ke abar so ce Adawiyya, kuma ko duniya za ta ƙiki, Adawiyya ni me sonki ne, ina ganin fuskar ɗan uwana a kan taki, haka kuma ina ganin fuskar Momma gwamitse da taki, above all Adawiyya ke ce 'yar favourite sistern Momma, so please ki dena faɗin haka, da ma rayuwa ba zata iyu ba tare da maƙiyi ba, hatta ɗan adam ɗin kansa ba zai cika ɗan adam ba tare da yana da maƙiyi ba”
Murmushi ta yi ta na kallon fuskarsa, ita kanta a wasu lokutan ba ta san wani kalar so takewa Zaid ba, ita dai kawai ta san tana sansa, tana sansa fiye da yadda za'a iya ƙirgawa.
Hannunta ta ɗago ta kai kan wannan chain ɗin na wuyansa, tare da maida shi cikin rigarsa, a duk sanda za ta ga chain ɗin a waje sai ta sa hannu ta mayar masa da shi cikin riga.
Jikinsa ya ƙara janta, hakan ya bata damar kwantar da kanta a kafaɗarsa.
“Zuwa gobe ki shirya zan kaiki islamiyyar nan”
Kai ta gyaɗa masa domin ta gane wace islamiyya ce, jiya yake faɗa mata cewar yana nema mata wurin karatu a wata isalamiyya nan kusa da su, tun da tace ita ba za ta ci gaba da karatun boko ba.
“Allah ya kaimu goben”
“Ameen”
Zaid ya amsa.
*Say i love you to your problems and maybe they will leave you one day too.*
***
*No.181, Guzape, Abuja...*
MISHAL POV.
“Zauna a hankali!”
Cewar Kuliya yana zaunar da ita a kan kujera.
“Did you feel better now?”
Kai ta gyaɗa masa.
Don tun jiya bakin tsiwa da na surutu ya mutu murus, saboda yanzu haka daga asibiti suka dawo, fuskar nan a koɗe, kuma ajeme, ta yi jajawur.
“Na kawo miki abinci?”
Kanta ta girgiza tana faɗin.
“Ni school zan je”
Kuliya ya girgiza mata kai.
“No way Teddy Bear.
Ki tambayi wani abun da ban, amma ban da zuwa school”
Daddafawa ta yi ta miƙe tsaye tana kallonsa.
“Ni school zan je to”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa yana ci gaba da kallonta.
“Ba ki ga halin da kike ciki ba ne Hafsat?...
Ba ki da lafiya fa!”
Kanta ta girgiza idonta na cika da ƙwalla.
Yau za su na da exams, kuma ita za ta iya wasa da komai a duniyar Allahn nan amma ban da exam, ko faɗuwa ta yi a exam har jinya take wani lokacin.
Bare a ce result ɗinta ya yi ƙasa da ta biyu, ai ranar kuwa za ta yini tana kuka.
“Ni na warke, kuma zan iya zuwa school ɗin”
Ta faɗi ƙwalla na mata zuba.
“Hafsat!
Ba ki ji me na ce ba ne?,babu zuwa school, faƙat!”
Cewar Kuliyan kusan a tsawace.
Nan take Mishal ta fashe masa da kuka tana zama a kan kujera.
“Da ma ai na son ba so na kake ba...
Da ma na san ka tsaneni, in ka san za ka hana ni zuwa school me ya sa ka min...
Ka min...”
Sai ta kasa ƙarasawa tana fashewa da wani sabon kukan.
Kuliya ya ɗaga kansa sama.
Shi kam Allah ya haɗashi da mata.
“Je ki shirya na kaiki!”
Ya faɗi ya na sauƙe kansa.
Ɗif, kukan da take ya tsaya, ta miƙe tsaye a daddafe tana share hawaye.
Bayanta ya bi da kallo har ta shige corridor.
Ban da rigima irin ta Mishal, me zai sa ta je school a irin wannan yanayin da take ciki?, hatta da tafiyarta ta sauya.
Bayan ta shirya cikin uniform ta fito, ba dan ya so ba haka ya kaita makarantar ya sauƙeta.
*No.86, Garki 2, Abuja...*
RABI POV.
Zaune take daga bakin gadonta tana latsa wayarta.
Ta shirya tsaf dan zuwa islamiyyar da Zaid ya ambata mata, yanzu haka shi take jira.
Ji ta yi zuciyarta na tashi, hakan ya sa ta aje wayar hannunta.
Jin cikinta murɗawa ya sa ta miƙe tsaye, sai kuma ta ji amai, ba shiri ta nufi banɗaki da gudu.
Amai ta shiga yi kamar me shirin amayo hanjinta, duk abun da ta ci na safiyar tas ta zazzage shi.
Kuma bayan ta gama aman sai ta ji kasala ta kamata, ta ji jikinta duk ba daɗi.
Kafin ta fito daga banɗakin ma sai take jin juwa na ɗinbata.
Da ƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna a bakin gadonta, hannunta na dama dafe da cikinta.
A dai-dai lokacin Zaid ya shigo ɗakin yana kiranta, ba ta samu damar amsawa ba, face binsa da kallo kawai da take, ganin yanayinta ya ɗarsa masa wani zargi a ransa.
“Baki da lafiya ne?”
Kanta ta girgiza masa tana miƙewa.
“Lafiyata ƙalau”
Be yarda ba, amma ba ya so ya takura mata, sai kawai ya gyaɗa kansa ya na kama hannunta.
“Na fahimta...
Kin shirya?”
Kanta ta gyaɗa tana ɗan cije baki, saboda cikinta da take jinsa babu daɗi.
“Raj!...
Me muke a nan?”
Muryar Rabi ta tambaya, a sanda ta ga Zaid ya kawosu wata football academy, makarantar da ta yi ta lokacin tana yarinya, dan a sanda Ummanta ke da rai nan take kawota training ɗin ball.‘As Roma Football Academy’ haka sunan makarantar.
Zaid be amsa mata ba, sai fita da ya yi daga motar, sannan ya zagayo ta ɓangarenta, ya buɗe mata motar, mamaki ya ƙi barin kan Rabi, haka ta fito baki buɗe, sai bin wurin take da kallo, wurin da rabonta da shi kusan shekaru shida kenan.
“Zuwa yanzu ta girma...
Dan haka ba daga rukunin da ta tsaya za ta ci gaba ba, za mu turata cikin rukunin sa'o'inta”
Cewar shugaban makarantar, yayinda Zaid da Rabi ke zaune a tsallaken teburin office ɗinsa.
Zaid ya gyaɗa kansa, duk da ba yau ya fara faɗa masa hakan ba, tun ranar da ya fara zuwa makarantar shugaban ya sanar masa da wannan batun.
Kuma ya yarda da hakan, shi ya sa ma ya kaita aka mata gwaji a asibiti, kafin ta fara buga ƙwallon da ta kasance burin rayuwarta.
Juyowa ya yi ya kalleta.
A dai-dai lokacin da ita ma ta kalleshi, idonta ya ciko da ƙwalla, bakinta har rawa yake, ta ma rasa abun da za ta ce da shi, sai kawai ta kafe shi da ido tana kallo.
Da haka suka bar office ɗin, aka bata kayan da zata riƙa sakawa idan ta zo makarantar, wata jar jersy ce, da wandonta, shugaban ya sanar musu da cewar zuwa gobe za su dawo, domin za su mata gwaji, idan ta ci gwajin da za su mata, za ta iya fara karɓar horo tun daga ranar.
Suna tafe a mota ledar kayan na kan cinyar Rabi, hannunta ta kai ta fito da jersyn ta ɗagata sama tana kallo. ‘ADAWIYYA’ shi ne abun da aka rubuta a bayan rigar.
Ƙwallar da take ta shanyewa tun ɗazu ce ta gangaro kan kuncinta.