← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 80

Sashe 60

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wannan ba damuwa ba ne Dude, hatta da sunana sai na manta da shi indai a kanka ne, ballantana ma da na kusa dena saka irin waɗanan kayan, na kusa musulunta fa!”
Maganar tata ta tuna masa da zagayen halin da suke ciki gaba ɗaya, ta tuna masa da bincinken da suke kan waɗanda suka yi wa Rabi'a fyaɗe, ta sa ya tuna case ɗinsu da Alhaji Bala.

“So yanzu ka san address ɗin gidan da za mu je?”
Kansa ya gyaɗa ya na ɗaukewa jakar.

“Saratu have told me everything a kan gidan...

But a mota za mu tafi, babu jirgin da zai je kano a gobe da safe, shi ya sa zamu tafi da motar”
*Magic Land, Abuja.*
YUSHAL POV.

Ticket suka fara siya, kafin suka shiga ciki, ko wani kalar game Mishal ta ga ni sai ta ce sai sun buga, kuma idan sun buga ɗin ita take cinyewa, don shi bai iya ba, ita kuwa babu wanda bata sani ba.

Lilo ma babu kalar wanda bata hau ba, Kuliya kam guda ɗaya ya gwada hawa, bai sauƙo ba sai da hajijiya, hakan ta sa yace ba zai sake hawa ba.

Sai da ta buga wasanni sosai, kafin suka siyi ice-cream suka samu wasu kujeru can daga baya, suka zauna suna sha.

“Ki bi ice-cream ɗin nan a hankali fa Teddy Bear, saboda mura”
Kuliya ya faɗi ya na kallonta, ganin yanda take shan ice-cream ɗin kamar wani abinci.

“Babu fa abun da zai yi”
Ta faɗi da ice-cream ɗi a bakinta, Kuliya ya girgiza kansa ya na ɗaga wayarsa, saboda kiran da Sharon dake shigowa wayar.

Ya ɗan jima ya na wayar, kafin wayar tasa ta ƙare, juyowa ya yi ya kalli Mishal.

Wadda ta gama shan ice-cream ɗin tana ta kalle-kalle a wurin.

“Kin gama?”
Ya tambaya ya na miƙewa tsaye, tare da ɗaga kafaɗarsa ta dama.

Ita ma sai ta miƙe tana turo baki.

“ummm”
Hannunsa ya kai ya gyara mata zaman gyalen kanta, sannan ya saka hannunsa a aljihu ya zaro wani hanki, ya na faɗin.

“Ji bi yanda kika ɓata bakinki”
Ya faɗi ya na goge mata bakin.

Kafin ya jata suka bar wurin, asbitin da aka saba mata wankin haƙori suka je, aka mata wankin haƙorin, kafin suka wuce Jabi mall.

Siyyaya suka yi sosai, kuma duk kayan wasa sun fi yawa a ciki, don da ma tace ta bar nata a gida.

Kuma daga nan Gidan Anna suka wuce, nan ma sun jima,dan sai dare suka bar gidan.
*Anyone can tell you that they love you, but it takes an authentic soul to show you that they so*
***
RAJA POV.

Da misalin ƙarfe biyar na yamma suka isa cikin garin haɗejia, bayan doguwar tafiyar da suka kwashe a mota, kasancewar unguwar Jama'aren da aka musu kwatance, ta na a farkon gari ne, kuma su ta kano road suka shigo garin, ya sa ba tare da sun shiga cikin gari ba kai tsaye suka shiga cikin unguwar.

Bayan ɗan neman gidan da suka yi, Allah ya sa suka samu, a bakin ƙofar babban gate ɗin gidan suka yi parking, a tare suka fito shi da Rhoda, wadda ke sanye da wata purple abaya, ta tsefe wannan kalbar attachment ɗin kanta nata da ta saba yi, ta dawo musulma sak.

Sai de abub da ba'a rasa ba.

Don har zuwa yanzu akwai ɗan wannan guntun baƙin kafircin tare da ita.

Raja ya tsaya ya na kallon gate ɗin gidan, gidan da mahaifiyarsa ta barshi da cikinsu, gidan da aka kori mahaifiyarsu daga cikinsa, kuma gidan da muradin ransa ke ciki a yanzu.

Taku biyu kawai suka yi da niyyar nufar cikin gidan, cak suka tsaya, sakamakon ƙaton gate ɗin gidan da aka wangale, hakan yabsa suka tsaya suna kallon wanda zai fito, wasu magidanta ne guda biyu suke tafe a tare, ɗaya ne yake wa ɗaya magana, yayin da ɗayan kuma ya tsaya sauraronsa.

Raja ya daskare a wurin ya na kallon ɗaya daga cikinsu, wanda fuskarsa take sak, ta Momma, Mommansu dai.

Kuma suma magidantan sai a lokacin suka kula da su.

Sakan ɗaya...

Biyu...

Uku...
*
Durƙushe suke shi da Rhoda a gaban tarin manyan mazajen gidan, a ɗazun iyaka mutum biyu kawai ya gani, yanzu kuwa kusan su goma sha ne yake durƙushe gabansu, 'yan uwansa, 'yan uwan Momma, kuma ba ma su kaɗai ba, harda wani farin tsoho, wanda yake da tabbacin shi ne mahaifin Momma, shi ne mutumin da ya kori Momma saboda ƙaddarar samun cikinsu da ta faɗa mata.

Ɗaya daga cikin mutum viyun da suka ga a ɗqzu ne ya yi gyaran murya yana dubansu.

“Ɗan samari meke tafe da ku?”
Dammm, gaban Raja ya buga, amma sai ya kame kansa yan na ɗagowa da lumsassun idanuwansa tare da zuba su a kan mutanen falon baki ɗaya.

“Sunana Zaid, kuma ni ne manemin auren Rabi'a, a can garin Suleja!...”
Ya zaɓi da ya zaftara musu wannan kantamemiyar ƙaryar, ko ya samu abun da ke masa nauyi a ƙirji ya sauƙa, dan a tashin farko bai isa ya kallesu yace musu shi ne ɗan Rabi'ar da suka kora shekaru talatin da bakwai baya ba, gwara su je a hakan, idan su sun gano da kansu shi kuma sai ya musu bayani.

Alhaji Ali ya gyara zamansa ya na ci gaba da ƙarewa yaron kallo, tun a kallon farko da ya masa ya tabbatar da cewa shi jininsa ne, jinin nasa ma wanda ya fito daga tsatson Rabi'a 'yarsa, zarginsa ya ƙara tabbata ne a sanda ya furta sunansa 'Zaid!' haka aka ce musu shi ne sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan da Rabi'ar ta haifa.

Ya yi zaton yaron ya zo ne dan neman ahalinsa, sai kuma ya ji wani zance da ban, kenan ita Rabi'an har saurayi gareta a garin Sulejan?, amma kuma ya kamata ko ita Rabi'an da ta ganshi ta gane cewa shi jinin gidansu ne,domin kuwa ko ita kanta Rabi'an ta na kama da shi, amma to me yake faruwa haka?.

Kuma ba shi kaɗai ne wannan tunanin ke yawo a cikin kansa ba, kusan kowa na wurin irin tunani da mamakin da yake kenan.

“Yaro!”
Tsoho Alhaji Ali ya furta, hakan ya sa hankalin kowa ya dawo kansa.

Ciki kuwa har da Raja.

“Shin ita Rabi'an tana sanka?”
Kafin Alhaji yace komai Kawu Abdullahi ya riga shi furta hakan.

Raja ya haɗiye wani abu me ɗaci, duk da ya san abun da zai furta ɗin ba ƙarya ba ne, saboda ya san cewa Rabi'a tana sonsa, amma bai sani ba ko har yanzu akwai wannan son.

“Eh...

Muna son juna, kuma mun dai-daita junanmu, wannan tsautsayin da ya gifta ne ya sa ba ma tare, kuma ni sam ban sani yaushe ta dawo nan ba”
Wani irin shiru ya ƙara ratsa falon, kafin Tsoho Alhaji Ali ya samu damar furta abun da ke bakinsa.

“Yaro kai jini na ne?!”
Ba Rajan da aka wurgowa tambayar kaɗai ba, tambayar ta doka wata uw*r ƙara a ƙirjin kowannensu, duk da kowa a cikinsu ya na zargin hakan.

Raja ya lumshe idonsa sannan ya buɗe.

“Ka ga...

Ka...

Ka yi haƙuri...

Ka san Halin tsufa”
Cewar Kawu Muktar cikin sigar bada haƙuri, ba don shi ma ba ya zargin hakan ba, sai dan ganin kamar yaron bai so tambayar ba.

A hankali Raja ya girgiza kansa.

“Ba kuskure ya yi ba....

Ni jininsa ne!”
Ido waje kowa yake kallonsa, ba don sun yi mamakin kasancerwasa jininsu ba, sai mamakin yanda ya amsa kansa tsaye.

Ƙwalla ta zubo daga idon tsoho Alhaji Ali.

“Yanzu kai jinin Rabi'a ne?”
Raja ya ɗago da kansa ya kalleshi.

“Eh...

Ni ɗanta ne”
“Amma an ce ku biyu ne...

Ina ɗan uwan naka?”
Wannan karon Kawu munzali ƙanin Alhaji Ali ne ya wurgo masa tambayar.

“Eh...

Mu biyu ne, kafin ƙaddara ta zo ta raba mu...”
Tun daga yanda suka yi rayuwa a gidansu su uku, zuwa lokacin rasuwar Rabi'a, zuwa lokacin da suka sha wahalar rayuwa su biyu, da yanda suka rabu da Aliyu, da kuma yanda ya koma wurin Maman Rhoda, har zuwa sanda ta rasu, da kuma yanda ya riƙe Rhodan har wa yau, da aikinsa bai ɓoye musu komai ba, ya sanar da su komai a kansa.

“Innallilahi wa inna ilaihi raji'un...

Yanzu jinina ne ya rayu irin haka?...

Jinin gidan nan ne ya yi bara a kan titi?...

Ka yi haƙuri yaro, ka yafemin...

Ni ma ina da hannu cikin lalacewar rayuwarku...

Da ban kori Rabi'a ba da duk hakan ba ta faru ba, na yi nadama.

Na yi nadama Wallahi.

Rasuwar Rabi'a da shekara ɗaya Allah ya ganar da ni gaskiya, sakamakon irin nasihar da yayansu ke min, hakan ta sa na tambayi ita kakar taku, ta sanar min da inda zan samu Rabi'a, na je, amma ban samu kowa ba, sai ce min aka yi wai ta rasu a gobara, sannan kuma an wayi gari babu wanda ya san inda kuke”
Raja ya girgiza kansa ya na kallo tsohon.

“Babu komai Baba, ƙaddarar mu ce a haka, Allah ne ya hukunta faruwar duka lamuran nan, ko da ka kori Momma ko ba ka koreta ba, idan har Allah ya hukunta za mu sha wahala dole mu sha”
Tsoho Alhaji Ali ya miƙawa Raja hannu ya na hawaye.

“Zo nan jikana, zo...

Ta ho gareni”
Raja ya miƙe daga inda yake, ya ƙarasa gabansa, Alhaji Ali ya rungume shi ya na kuka, duk taurin zuciya irin ta Raja sai da ta karye, shi ma ya yi hawaye, ɗaya bayan ɗaya ya Alhaji Ali ya shiga gabatar da shi ga mutanen dake falon, kafin Alhaji Alin yace.

“Yanzu kai da gaske kuna soyyaya da ita me sunan mamar taku?”
Raja ya ɗan yi murmushi ya na goge hawayensa, tare da gyaɗa kai.

“Eh, muna son junan mu”
“Allah me iko, Allah buwayi gagara misali, kun ga ƙaddara ko?.
Chapter 60 · 0% Book details