← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 80

Sashe 47

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai Mishal sai ƙunshe dariyarta take, duk da daga can ƙasan zuciyarta akwai wani abu ɗan ƙanƙani me kama da damuwa, kuma abun ya samo asali ne saboda rashin zuwan Adawiyya makaranta!, abu ne wanda tun bayan da suka ɗinke bai taɓa faruwa ba, ko a da can ba ta ganinta tana fashi bare yanzu, amma har can ƙasan zuciyarta take fatan kada Allah ya sa wani abu mara kyau ne ya faruwa da Adawiyyan.
*Washe gari...*
*Brickhall School, Kaura District, Game Village, Abuja.*
RAJA POV.

Cike da mamaki principal ɗin makarantar yake kallon mutumin dake zaune a tsallaken teburinsa, kamar ba shi ba ne jiya ya zo ya na tambaya a kan Rabi'a, yau kuma sai ga shi ya dawo da wani yanayi da ban, saɓanin wanda ya zo da shi jiya, stil kuma ya na sake tambayarsa a kan Rabi'an.

“Ka yi shiru, ko akwai matsala ne?”
Rajan ya tambaya, ganin yanda mutumin yake kallonsa, principal ya girgiza kansa.

“Ba haka ba ne, kawai dai yau kwana biyu kenan bat ta zo ba!”
Wani irin shiru ne ya ratsa office ɗin, kuma a cikin shirun, banda bugu cikin sauri babu abun da zuciyar Raja ke yi, wannan abun da yake ji a jikinsa ya fi ƙarfin tsoro, ji yake kamar ma ya haukace ne, me ya sa Rabi'an ba ta zuwa?, saboda shi ne?, amma me ya sa?, ko wani abu ne ya sameta?.

Da waɗanan tambayoyin fal a ransa ya bar office ɗin.

“Yayana!”
Ya ji an kira sunan a bayansa, amma bai tsaya ba, saboda halin da yake ciki ba zai barshi ya tantance da shi ake ko ba da shi ake ba.

“Ɗan uwa!”
Aka kuma kiran sunan, hakan ya sa ya tsaya sannan ya juyo, wannan yarinyar ce, wadda ta ce masa ya na kama da cousin ɗinta.

“Dama a nan kake ?”
Mishal ta tambaya a sanda take isowa gabansa, mamaki fal kanta, na son sanin me ya zo yi a makarantarsu.

“Na...

Na zo neman wani ne”
Sai ta gyaɗa kanta.

“Ka same shi?”
Ta tambaya, sai ya girgiza kansa.

“A'a, ban same shi ba”
Ya faɗi yabna ɗaga kafaɗarsa ta dama, Mishal ta jinjina girman Allah a cikin ranta, sak Kuliya,duk da akawai 'yan banbance banbancea tsakaninsu.

“Faɗamin sunansa, na san kowa a makarantar nan, zan nemo maka shi”
Duk da halin da yake ciki sai da ya ɗan murmusa.

“Ba lalle ki san shi ba.

Zan koma, na gode ƙanwata, ki kula da kanki!”
Haka kawai ya samu bakinsa da furta sunan, kuma bai jira cewarta ba, ya juya ya ci gaba da tafiya.

Mishal ta ci gaba da kallon bayansa, abubuwa da dama na mata kai kawo a cikin kai, tana son ta san me ya sa Anti Adawiyya ba ta zuwa, kuma ta na son sanin me ya sa Kuliya babya tare da ɗan uwansa, tabna son ta san me ya sa su duka suka zo makarantarsu, don ta san ko Kuliyan ma jiya ba wurinta ya zo ba.
*No.189, Radeemer Estate, Lugbe, Abuja.*
Siyama da Karima Yayarta da kuma yaran Kariman ne zaune a falo suna karin kummalo.

Kowacce a cikinsu jikinta ɗauke yake da rauni, raunin da suka samu a zuwansu gidan Kuliya.

“Salamu Alaikum!”
Suka ji sallamar Anna, a yayin da take turo ƙofar falon, da sauri Karima ta miƙe tsaye, hakan ya sa Siyama ma ta miƙe, saboda sun san ba su da gaskiya.

Ɗaya bayan ɗaya yaran Kariman su uku suka riƙa gaida Anna, ta na amsa musu.

“Abdul ku je ɗakinku ku ƙarasa karin a can”
Babban ɗan nata ya amsata ya na haɗa kan ƙannensa wuri ɗaya, tare da ɗiban kayan abincin nasu suka yi ɗaki.

Kamar da Annan take jira, ta samu guri ta zauna tana musu kallon tuhuma, ganin yadda ko waccensu ta kafa inda-inda ne ya tabbatar mata da gaskiyar abun da suka aikata, duk kuwa da ta san Kuliya ba zai mata ƙarya ba.

“Yanzu ke Karima a matsayinki na babba, ya kamata a ce kin aikata abun da kika aikata?, Ko za'a kira abun da Siyama ta yi a matsayin yarinta naki ba za a ce yarinta ba ce, saboda kin fita shekaru da sanin ya kamata.

Amma saboda ke babbar kwabo ce, kika wanki ƙafa kuka je gidan matar mutane kuka rufa mata duka ko?!”
Da sauri Siyama ta girgiza kanta, hawaye na ciko mata ido, musamman da ta tuna abun da ya faru a wacan ranar.

“Anna Wallahi.

Wallahi ba mu...”
“Ƙarya kuke!, Idan ba ku ne kuka daketa ba za ta buga kanta da kanta a jikin bango ne, ta zo tace ku ne kuka mata dan kawai ta muku ƙazafi?”
Da sauri Karima ta gyaɗa kai.

“Wallahi Anna ba mu daketa ba, hasalima ita ce ta dake mu, duba ki gani...”
Ta ƙarashe tana nunnuna mata tabon raunikan jikinta.

Anna ta yi dariya, irin kun rena min hankalin nan.

“Karima ko ƙur'ani za ki dafa kan wannan maganar taki ba zan yarda ba, jibe ki fa, yadda kike rusheshiyar nan da ke sai na yarda waccan 'yar fingilar yarinyar ita tai miki wannan raunin?, saboda ga Annan mahaukata ko?, to ni ba ma wannan ne ya kawo ni ba, zuwa na yi na ja muku kunne, babu ku babu gidan Aliyu, sannan babu ruwanku da sabgar matarsa, idan kuma ba ku ji ba ku je ku yi, Wallahi ni da kai na zan sa Aliyun ya hukunta ko waccenku, har ke Karima, tun da ba wani fikon arziƙi kika masa ba, in kun ce bakwa ji sai ku gwada mu gani!”
Tana ƙarashewa ta miƙe ta fita, don da ma abin da ya kawota kenan, Siyama ta zube a kan kejera tana fashewa da kuka.

“Kin ga inda kika kai mu ko Anti, yanzu ga shi bayan dukan da muka sha Anna ma ta ƙara mana da nata kashedin”
Karima ta matse ƙwalla, tunawa da irin dukan da suka sha da ta yi.

“Da ma ni sam soyyayar Kuliya ba ta karɓeni ba, ban da wahala babu abun da nake sha”
Ta ƙarshe tana miƙewa, tare da nufar ɗakinta da gudu.

Karima ta yi tagumi tana jinjina sharri da kissa irin na wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar da suka rena, ko dan ai an ce ɗan hakin da ka rena.
____________________
_Gani nan na yi tagumi hannu bibbiyu_
_jama'a!, wai ina Rabi ta shige ne?, wani ya temaka ya nemo mana ita_
_Ku ni fa na kasa gano abun da ya faru tsakanin su Karima da kuma Mishal_
_Salmanians, shin kuna kusa?_
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••••••••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*16*
~~~
*Don't be afraid of falling apart.

Some of the must beautiful heart are built from tragedy.*
***
Follow my Wattpad account 👇
https://www.wattpad.com/user/Salma_Ahmad_Isah?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
~~~
*Bayan sati uku...*
*No.181, Guzape, Abuja...*
*09:30pm*
MISHAL POV.

Kwance take a falo, ta duƙunƙuna cikin blanket, idanuwanta sun yi ja saboda kukan da ta ci, ta kunna tv ta tsura mata ido amma ba kallon take ba.

Damuwa da ruɗani ne suka saka rayuwarta a gaba, yau kusan sati uku kenan, amma Antinta Adawiyya ba ta zuwa makaranta, tun ta na ganin abun kamar fashi ne, har fashin nata ya zo ya soma bata tsoro, dan zuwa yanzu ma an kawo wata sabuwar me yim shara a makarantar, kullum sai ta yi kukan rashin sanin halin da Adawiyyan ke ciki, ga kuma kaɗaici da yake damunta a yanzu, ga shi dai ba wani jimawa suka yi da Adawiyyan ba, amma haka kawai take jinta cikin kaɗaici, yanzu haka ta hana idonta bacci ne dan jiran dawowar Kuliya, tun da shi ɗan sanda ne wata ƙila zai iya yin wani abu akan case ɗin yayar tata.

Ta na kwance a wurin har goma ta wuce, kuma sai a lokacin Kuliya ya shigo gidan rai a ɓace, wanda ya samo asali daga wurin aikinsa, Mishal na jin shigowarsa ta miƙe da sauri ta sha gabansa, kallonta ya yi na 'yan wasu sakkani, sannan ya shiga ƙoƙarin raɓata ya wuce, amma sai ta ƙara tare masa hanya.

“Abu Aswad.Yayata ce ba ta zuwa makaranta.

Kuma ban san meke faruwa da ita ba, dan Allah ke nemo min ita” ta faɗi hawaye na mata zuba.

“Ke me ya sa baki san abinda ya kamata ba?, Yanzu na dawo gida da ɓacin rai, me makon ki bari na huce shi ne za ki tarbeni da wannan maganar?!”
Kamar de wancan karon haka ya mata magana cikin hargagi, Mishal ta fashe da kuka sannan ta naushi ƙirjinsa.

“I hate you Abu Aswad!”
Ta na kaiwa nan ta juya da gudu ta faɗa ɗakinta.

“Zan iya shigowa?”
Kuliya ya tamabaya ya na turo ƙofar ɗakin Mishal, wadda ke zaune a kan gado ta na kuka, sai bayan da ya je ya yi wanka sannan ya samu sauƙowa, shi ne ya taso ƙafa da ƙafa don ya nemi yafiya.

Saboda ya san ba laifinta ba ne, shi kansa yabna bincike a kan yarinyar me suna Rabi'a, amma har yanzu babu abun da ya samu.

Ya je makarantar Brickhall yafi sau biyar a cikin sati ukun, amma sam sun ƙi su ba shi adireshin Rabin, ga kuma wani renin hankali da suke masa na cewar ai jiya ma ya zo, bayan shi kuma ya san bai zo a ranar ba.

Zama ya yi a bakin gadon ta setinta, ya na kallon gefen fuskarta da ta kawar, fuskarta ta yi jajir, alamun dai ba ƙaramin kuka ta sha ba, shi ya rasa wannan wata iriyar ƙauna ce tsakaninta da wannan yarinyar.

“Hafsat”
Ya kira sunata a tausashe, sai ta ƙara haɗe rai ta na kumbura baki.

“Ki yi haƙuri ba zan sake ba!”
Juyowa ta yi suka haɗa ido, ta wurgar masa harara, ta ƙara kawar da kan nata, sai ta bashi dariya, hakan ya sa ya murmusa a ransa.

“Yanzu ba za ki yafemin ba?”
Ta kuma juyowa ta kalleshi.

Jin yanda ya yi maganar kamar maraya.
Chapter 47 · 0% Book details