Sashe 20
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ni ma na gode, ka bar shi kai...”
Maganar ta bi iska, sakamakon hannunta na dama da Rajan ya kamo, ya danƙa mata kuɗin...
*
Rabi'a ta shawo kwanar layinsu, dai-dai kwanar da masu kayan siyarwa kan taru.
Tsayawa ta yi a kusa da wani mai kifi dake soyawa.
A kullum idan ta zo wucewa ta wurin sai ta haɗiyi yawu, saboda, kwaɗayin kifin da ke ranta.
Ita fa da abata kaza gwamma an bata kifi.
Gabshi kuma gidansu ba kifin ake ci sosai ba, sun fi cin kaza akan kifin.
Hakan ya sa ba sosai take samun damar cin kifin ba.
Hannunta na hagu dake damƙe da kuɗaɗen da Raja ya bata ta ƙara damƙewa, hakan ya tuna mata da yanda suka kwashe da shi a ɗazu.
A ɗazun bayan da ya kamo hannunta, sai ya saka mata kuɗaɗen, sannan ya ninke hannunta kan kuɗin.
Yayin da ita kuma ta saki baki da hanci tana kallonsa, wani abu me kama da ruɗani na kai-komo a cikin kanta.
“Idan na faɗi abu ba'a mun musu...
Kin fahimta ?”
Ta shiga gyaɗa masa kai, kuma ba ta bar gyaɗa kan nata ba sai da ya saki hannunta.
Ita kuwa ta fahimta, ba ta jin akwai wani wanda zai kaita fahimtar yaren nasa.
A kan idonta ya ɗaga mata hannu, sannan ya bar wurin, ya barta da raunanniyar zuciya.
Ta haɗiye wani abu a fili, sannan ta juya zuwa wurin me kifin.
Magana ta masa kan ya bata na dubu ɗaya, sannan ta miƙa masa dubu ɗayan.
Me kifi ya saka mata soyyayar karfarsar a takarda, ya ninke ya danƙa mata.
Ta kamo hanyar gida ranta fes.
Tana kaiwa gidan ta faɗa ɗakinsu, sai da ta faki idon kowa, ta saka kifin a jakarta.
Sannan ta fito tai alwalar sallar la'asar.
Ta yi sallar, kafin ta fito ta shiga yin ayyukanta da ta saba a gidan.
Ta yi wanka ta saka kaya baya-baya.
Ta dawo ɗaki ta zauna, tana ta dube-dube.
Anti saratu dake kwance a kan katifarta, ta lura da abinda take hakan ya sa tace.
“Rabi lafiya ?”
“Hmm, ina Mama ?”
Anti saratu ta yi murmushi.
“Ta tafi gantalinta, Fatima da Mahmud su na gidan kawu Abubakar.
Umma kuma ina jin tana ɗakinta, faɗamin ta samu ne ?”
Ta tambaya ta na tashi zaune...
Ran Rabi ƙal, ta tashi daga kan carpet ɗin da take, ta dawo bakin katifar ta zauna.
“Ina mutumin da na faɗa miki cewa ya temakeni jiya ?”
Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana tuna zancen da suka yi jiya, sanda ta tambayeta a ina ta ji rauni.
“To ai na faɗa miki cewar ya cillar da wallet ɗinsa...
Na ganshi ɗazu, kuma na bashi kayarsa, shi ne ya fitar kuɗin ciki gaba ɗaya ya bani, ya ce na yi kuɗin mota...”
Ta ƙarshe tana miƙa mata kuɗin.
Bakin Anti Saratu buɗe ta karɓi kuɗin, ita da kanta ta shiga lissafawa.
“Rabi!...
Dubu hamsin da uku ne fa?”
Anti Saratun ta faɗa ido waje, ita kanta Rabin sai da ta yi mamaki, duk da dama tasan kuɗin ba kaɗan ba ne.
“To da huɗu ne ma, tun da kin ga har kifin dubu na siyo”
Ta faɗi ta na miƙewa tsaye, tare sa nufar jakarta, ta fiddo da kifin dake duƙunƙune cikin leda, ta dawo ta zauna kusa da Anti Saratun ta miƙa mata.
“Rabi...
Ko dai ya na ciki ne ?”
Ta tambaya a sigar zolaya, Rabi ta yi murmushi tana hango rashin tabbatuwar hakan, don ko da wasa ba ta hango hakkan ba, babu ma ta yanda za ayi hakan ta faru, dan akwai banbanci tsakaninta da shi, wani irin banbancin da take ganin tazararsa kamar, ta Mutum da lokacin mutuwarsa, dan mutum bai san lokacin da zai mutu ba.
Haka ita ma ba ta san adadin tazarar dake tsakaninta da shi ba.
Kuma ita ta na ganin wata ƙila shi ma yana mata kallon wadda take kama da shi ne, ko kuma yarinyar dake buƙatar temako, ba ta san shi ba, ba ta san ya rayuwarsa take ba, amma tana da tabbaci kan shi ba sa'anta ba ne, akwai tazara me tarin yawa tsakaninta da shi.
Abun da ba ta sani ba shi ne, wannaan tazarar da take gani ta kusa zama kusa, wata iriyar kusa da za ta bata mugun mamaki.
Amma kuma kafin faruwar kusan, sai wasu ƙaddarori sun gifta a tskani.
Ita ta buɗe musu ledar kifin,suka ci tare, tana tambayar Anti Saratun; kan yaya za su yi da kuɗin?.
“Abun da zai faru kawai zan aje miki su a wurina, idan kina buƙata sai kimin magana, ni kuma na baki...”
Rabi ta yi dariya tana kai wani kifin bakinta, yau tana cikin farin ciki, wanda ba za ta iya cewa ga dalilinsa ba.
RAJA POV.
Tsaye yake a gaban mutumin da ke amsa sunan ALHAJI BALA.
Yayin da shi ma Alhaji Balan ke kallonsa.
Fuskar Alhaji Balan na ɗauke da murmushin alfahari, dan sosai yake alfahari da Raja, though wannan shi ne karo na farko da suka fara haɗuwa, amma ayyukan da yake dominsa suna isowa kunnuwansa.
Yayin da shi Rajan yake kallonsa da wani gutun murmushi, salihar fuskarsa na wani irin haske da ba ka ce na miye ba, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Alhaji Bala ƙasa-ƙasa.
Daga shi sai Rabbil izzati suka san abinda yake tsarawa a cikin kansa.
Suna tsaye ne a katafaren falon gidan Alhaji Balan, wanda ke ɗauke da maka-makan set ɗin kayan da kallo ɗaya za ka musu ka shaida tsadarsu.
Rajan na sanye cikin wani green khaki trouser, sai baƙar crew neck sweater, ƙafafunsa sanye cikin canvas baƙaƙe.
Alhj Bala ya ɗaga hannunsa na dama, tare da bubbuga kafaɗar Raja, yana ƙara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa.
“Zauna mana ZAKI!”
ZAKI?!, Bai yi ƙarya ba, dan ya na amsa wannan sunan a wata duniya, wata duniya can da ban, wanda ta zama sanadiyyar kasancewarsa a wannan rayuwar.
A hankali ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a bayansa, sanye cikin irin kayan dake jikinsa, kalabar attachment ɗin dake kanta ta sauƙo har kan kafaɗunta.
Da ido ya mata alama da ta zauna, zaman ta yi a kan kujerar dake kusa da ita, sannan shi ma ya zauna a kusa da ita, dan kujerar me ɗaukar mutum biyu ce.
Alhaji Bala ya kalli yaransa uku dake zaune a falon, sannan y ce.
“Ku ba mu wuri, za mu gana...”
Cike da girmamawa suka tashi suka fita, ya rage daga shi sai Raja da Rhoda.
“Ita ma wannan yarinyar taka ya kamata a ce ta fita ko?, Dan maganar da za mu yi sirri ce!”
Alhaji Bala ya faɗi yana kallon Rhoda, kamar me neman amsa a wurin Rhodan, ya juya ya kalleta, ita ma shi take kallo, kafin ya juya ya kalli Alhaji Bala.
Ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan wannan innocent voice ɗin nan nasa yace.
“Na fahimta, amma ba za ta iya fita ba, she is my other half, komai zan yi sai na sanar da iya, ba na taɓa yin wani abu ba tare da saninta ba...
So you can say what you want at her present”
Alhaji Bala ya gyaɗa kansa, sannan ya gyara zaman malum-malum ɗin jikinsa, alamun dai maganar da za ta fito daga bakinsa babbace...
Raja da Rhoda suka miƙe a tare, bayan da Alhaji Baka ya kawo ƙarshen maganarsa, hannu Alhj Bala ya miƙawa Raja suka gaisa.
Daga haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga falon.
Ƙofar falon ce ta buɗe, hakan yasa Raja da Rhoda tsayawa.
Wani mata shi ne ya shigo, yana binsu da kallon ɗai-ɗai, daga Rajan har Rhodan sun san waye, USMAN!, ɗan Alhaji Bala na fari.
Babu wanda ya kula shi, har suka raɓa shi suka fice.
“Ya aka yi yanzu kuma ?”
Alhaji Bala ya tambaya yana kallon Usman ɗin, Usman ya sosa ƙeyarsa yana kallon babansa.
“Kuɗi nake buƙata”
“Dama na sani, ka je, zan saka maka a account...”
Ba ko godiya, haka ya gyaɗa kansa sannan ya juya ya bar falon.
Ya na saka ƙafarsa a wajen ɓangaren mahaifinsa ya fiddo da wayarsa daga aljihu, ya aika wa abokinsa Bash kira.
“Usee boyyyy!...
So Sup? (To yaya ake ciki?)”
Muryar Bash ɗin ta faɗa ta cikin wayar.
Usman ya saki murmushi, har fuskarsa na haskawa ta cikin hasken fitulin dake haskawa a harabar gidan nasu, kasancewar lokacin dare ne.
“An samu kuɗaɗen nan, a tanadar mana babes ɗin kawai, dan gobe akwai chilling”
“Oboy!, that's my gee, kar ka damu, ka kwantar da hankalinka kamar kana jirgin sama mai ya ƙare, akwai zafafan 'yan mata, masu tafiya kyau na zuba, kai dai kawai sai na ganka goben”
Daga haka wayar ta katse, sannan ya jefa wayar aljihunsa.
Wannan shi ne halinsa, ainahin halinsa da kowa ya sanshi da shi, shaye-shaye, neman mata da kuma bin abokan banza, shi ya sa yake ɓarin kuɗi, kuma mahaifinsa ba ya hanashi kuɗin, a duk sanda zai tambaya sai an bashi.
KULIYA POV.
A hankali yake saka kayansa cikin ƙaramar jakarsa ta goyon baya.
Yau aka sallame shi daga asibiti, don haka ya shirya tsaf, don barin asibitin.
Ya riga ya tsara tarin abubuwan da zai gabatar a cikin kasan, ya riga ya tsara kaf, abubwan da zai gabatar bayan ya bar asibitin.
Ba zai sararaba sai ya ga ƙarshen aikin da ke gabansa, shi matsalarsa ɗaya, fushin da Anna ke yi da shi, don tun bayan da ya kwanta jinyar kusan kwana huɗu kenan, amma ba ta zo ta duba shi ba.
Tun ranar farko da ta zo ta gama masa wankin babban bargo ba ta ƙara dawowa ba.
Sai kuma ita, itan da kamanin fuskarta suka manne a cikin tunaninsa, dai-dai da sakan ɗaya idanuwanta sun kasa barinsa ya huta, tunani barkatai yake a kanta.
Ya kasa gane kan marsalar da ta samesa, yasan cewa shi bai taɓa samun kansa a cikin irin wannan halin ba.
Bai taɓa so ba, bai san ya yake ba, bai taɓa kusantar inda yake ba, bai taɓa budurwa ba ma, balle yace ya taɓa sanin kalar yanda so yake.
Amma a kallon farko da ya mata wani abu a kanta ya samu gu ya yi zaman darshan a zuciyarsa.