Sashe 55
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da ma duka maza halinki ɗaya, baku da kirki, kanku kawai kuka sani, kun fi san kanku a kan komai, in dai za ku samu abu to kowa ma ya rasa, kun fiya san kai da yawa, wani mugu ya lalata rayuwar me sunana, shi ne har ta samu cikinka...
Sannan kuma tsabar san kai irin na kakana, shi ne ya koreta daga gidansa, wai don ta ƙi yarda ta zubar da cikin jikinta ba...
Daga nan kuma sai babana...
Babana ya lalata rayuwar Ummana, yanzu kuma tawa rayuwar ce aka lalata, wasu mugaye ne suka lalata min rayuwa...
Me ya sa ma na sanka Raja?, eh?
Na ce me ya sa?!”
Ta tambaya tana nuna shi da ɗan yatsa, Raja da ya daskare a wurin dan tsabar mamaki ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, abubuwa da dama sun haɗu cikin maganar tata, na farko ta ambaci cewar zuciyarta tana sansa, na biyu kuma yau ita da bakinta take furta cewa shi jininta ne, ita da bakinta ta furta masa labarin mahaifiyarsu da shi kansa bai sani ba.
“Ka fita daga nan, idan zai iyu ka fita daga rayuwata!”
Ta faɗi tana nuna masa hanya cikin kuka, a memakon Rajan ya fita kamar yadda ta buƙata, sai ya ci gaba da takowa zuwa gabanta, kuma kafin ta yi wani yunƙuri ya haɗata da jikinsa, ya rungumeta sosai ya na sauƙe ajiyar zuciya.
Rabi'a ta saki wani sabon kuka, don da ma abun da take buƙata a irin wannan lokacin kenan, ta na buƙatar wani a kusa da ita, tana buƙatar jin ɗumin wani a jikinta, ta na san ta samu kafaɗar da za ta kwantar da kanta ta rera kukanta yanda take so.
Don haka ta ɗago da hannayenta ta kewayasu ta bayansa ta ƙara ƙanƙameshi tana sakin kukan cikin 'yancinsa.
Raja ya ja hancinsa ya na ɗaga kansa sama, tare da ƙara riƙe Rabi a cikin jikinsa da kyau.
Sai dai kuma cikin sakan ɗaya...
Biyu...
Uku...
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
A hankali motar Raja ta tsaya a bakin lungun su Rabi, daga cikin motar shi ne zaune a mazaunin driver, yayin da ita kuma Rabin ke zaune a gefensa.
Sanye take cikin wata blue abaya, wadda Rahoda ta kawo mata ɗazu, ta yafa mayafin abayar a kanta, har zuwa gefen fuskarta na hagu da ta ɗan rufe gun ya kan nan.
A jiya da take cikin jikin Raja tana kuka, ta manta ma da wa take tare, ta manta a cikin jikin wa take, sai a sakan na uku da aka turo ƙofar bayin, a lokacin kuma hankalinta ya dawo jikinta, ta yi saurin sakin Raja ta na tureshi baya, sannan ta zuba idonta a bakin ƙofar bayin, inda Rhoda ke tsaye ta na kallonsu.
Kuma bayan faruwar hakan Rajan bai ƙara minti ɗaya a wurin ba ya fice, da Rhodan suka zauna har ta temaka mata ta yi wanka, ta ɗauro alwala ta zo ta shiga biyan sallollin da ake binta, duk da babu yanda Rhodan ba ta yi da ita ba kan ta fara cin abincin da ta zo da shi, amma fir ta ƙi.
Haka ta yi ta jera sallollin bayan da Rhoda ta sanar da ita kwanakin da ta kwashe a asibitin.
Kuma duk da sallallin da ta ruƙa jerawa, ba ta samu ta idar duka ba, ta dai samu ta yi da yawa, haka ta zauna tana hutawa, kafin Rhodan ta bata abincin ta ci, sannan likita ya zo ya dubata, har ma yace zuwa gobe zai ba su sallama.
Kuma tare suka kwana da Rhodan har zuwa safiyar yau.
Abu na farko da ta fara yi bayan ta tashi shi ne ci gaba da biyan sallollinta, sai in ta gaji ne za ta zauna ta huta, duk da a zaune take sallahr, kuma likitan ma bai basu sallamar ba sai da yamma.
Shi ne Rhodan ta kira shi don ya zo ya dawo da ita gida.
Ƙofar motar ta buɗe da niyyar fita, har ta sa ƙafarta ɗaya a waje sai ta fasa fita ta juyo ta kalleshi.
Shi ma kuma ita ɗin yake kallo.
“Dan Allah, kada ka ƙara kusanta tata, kada ka ƙara nema na, kada ƙara bin ko da hanyar da kasan za mu haɗu ce, wannan roƙona ne gareka...”
Kuma ta na kaiwa nan ta fice daga motar.
Raja ya yi murmushi ya na ɗaga kafaɗarsa ta dama, wai kada ya ƙara nemanta, ai abun da ba ta sani ba shi ne; shi da ita kuwa yanzu suka fara haɗuwa, don ba zai rabu da ita haka ba, dole zai san yanda ya yi ya aureta.
Sai da ya gama shawaginsa a duniyar tunani, kafin ya tayar da motar ya juya ya bar unguwar.
Da sallama a bakinta, Rabi ta shiga gidansu, duk da akwai duhun dare, ta na iya ganin komai dake wakana a tsakar gidan, saboda hasken wutar lantarkin dake ci a tsakar gidan.
Zaune a kan babbar tabarma Habiba ce, Fatima, da kuma Mahmud, sai Babansu daga can gefe ya na sauraren radio, daga Habiban har Ɗan Lamin miƙewa su ka yi suna kallonta.
A dai-dai lokacin Saratu dake zaune a ɗaki ta fito da gudu, jin wata murya me kama da ta Rabi, hasken ƙwan lantarki nan, ya haska mata fuskar Rabi tar, kusan sati huɗu kenan rabon da ta saka 'yar uwar tata a idonta, kuma duk tsawon wannan lokacin ita kaɗai ce take cikin damuwa a gidan, daga Ɗan Lami har Habiba babu wanda ya damu.
Ta na iya ga wata kallar rama da Rabin ta yi, ga kuma wani rauni da take iya gani a gefen fuskar Rabin.
“Gantallaliya an dawo?”
Kalaman Habiba kenan, hakan ya sa da maɗaukakin mamaki Rabi ta kalleta, wato matar nan ba ta san Allah, ita take turata aikatau, kuma a hanyar dawowarta gida daga wurin aikatau ɗin aka saceta, har kusan sati huɗu ba ta gida, amma da abun da za ta fara tarbarta da shi kenan?.
“Gantali?, haka aka ce miki gantali na tafi?”
Ta tanbaya ƙwalla na ciko idonta.
“Yo in ba gantali kika tafi ba a gidan uw*r wa kike tsawon wannan lokacin?!”
“Gidan uw*r da kika aike ni na je, ko ba ki ji ba?, na ce gidan uw*r da kika aike ni na je!”
A wannan lokacin kam Rabi ta je ƙarshe, ba za ta iya jure ko wani cin kashi ba, a yanda take jinta ba za ta iya ɗaukar ko wani ciwon kai ba, bayan wanda take tare da shi, haba!, abun ai ya yi yawa, ya kamata ace an barta haka, ko ita ma ta huta.
Ba wulaƙancin Habiba kaɗai ba, na kowa ma ba za ta ƙara ɗauka ba.
Habiba ta shiga tafa hannuwa cikin sallallami.
“Rabi?
Ni kike zagi?
Ki ce dadiron naki rashin kunya ya koyar da ke?”
“Ni ba karuwa ba ce.
Wannan gantallaliyar 'yar taki da ta bar gidan ub*nta ta bi namiji ita ce karuwa!.
Ya isheki haka Habiba, na gaji, ba zan ƙara ɗaukan wani walaƙancinki ba, ya isheni haka!”
“Ɗan Lami ai ka na ji ko?, To ka koreta daga gidan nan, dan ba zan iya zama da ita ta na halin 'ya'yan akuya ba.
Ban da rashin kunyar da ta koyo kuma!”
Kamar da aka kunna inji haka Ɗan Lami ya hau zagin Rabi, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, Rabi kuwa ta na tsaye a gabansu ƙyam, babu wani alamar tsoro ko rauni tare da ita, to wani dare ne jemage bai gani ba?, ai na mutuwarsa ne kawai ya rage.
Abu da ya yi ƙamari Ɗan Lami ya rarumo muciya ya yi kan Rabi da ita.
“Kar ka soma Abba!”
Ta dakatar da shi a dake, hakan ya sa Ɗan Lamin ya tsaya daga shirin dukanta da yake, doj da ma duk borin kunya yake, ya na yi ne dan ya burge Habiba, saboda akwai maganar kuɗi tsakaninsu.
“Kar ka soma duka na.
Wani laifi ma na maka da na cancanci duka huh?, yau sati na uku ina kwance a asibiti, an samu wasu marasa imani sun haikemin, kuma ba komai ne ya ja min hakan ba face ayyukanka, ayyukanka marasa kyau da ka saba yi, zina da kake yi da 'ya'yan mutane ita ce yau ta faɗo kaina, bayan ta faɗa kan ɗaya 'yar taka, kai babu ruwanka da rayuwarmu, shagalinka kake san ranka...”
A take Ɗan Lami ya ji jikinsa ya yi sanyi, dan duk abin da ta faɗi gaskiya ne, babu abu ɗaya da ta faɗi wanda yake ba dai-dai ba, sai dai kuma waɗanan kuɗaɗen da yake hangowa ba za su su sa ya ji maganar tata ba.
“Ki fice ki bar min gidana, kada ki sake dawowa gidan nan!”
Zuciya ta ciyo Rabi, hakan ya sa ta juya ta fice daga gidan, da gudu Saratu ta bi bayanta tana kiranta, ko hijabi babu a jikinta haka ta fita.
Habiba ta samu wuri ta zauna, kamar ta tashi sama dan murna, dan kuwa duk abun da take so ya tabbata, rayuwar Rabi ta lalace, tun da har ta furta da bakinta cewar wasu sun mata fyaɗe, sai a yanzu ne burinta ya cika, sai a yanzu ne duk fafutukar da ta yi ta yi tun bayan auren Maryam ta kawo ƙarshe.
_“Wallahi sai na ga bayanki ke da yaranki, ba zan huta ba sai na ɗai-ɗaita rayuwarki Maryam!”_
Haka ta taɓa faɗawa Maryam ɗin, a wani lokaci can baya, kuma ga shi ta yi ɗin, ta aikata duk abun da ta ci buri, ita ce fa Habiba, babu wani wanda ya isa ya shiga gabanta.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*20*
~~~
*Let your wings be soft enough to carry her, until she remembers how to fly again...*
***
RABI'A POV.
“Rabi!...
Rabi!”
Kiran da Anti Saratu ke mata ne ya sa ta tsaya da tafiyar da take a fusace, ta juya tana kallon Anti Saratun, wadda fuskarta ta yi gaje-gaje da hawaye.