← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 80

Sashe 50

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki ne ya kama shi ganin maganin mura da na zazzaɓin da ya aiko mata ɗazu, hannunsa ya kai ya ɗaki kwalar maganin muran dake kan coffee table, idanuwansa a waje yake kallonta daga kwancen da take, ganin abun da ke cikin kwalbar saura rabi.

Kenan duka ita ta shanye?, tab, ai dole ta yi bacci, rabin kwalba fa?, dariya ta kama shi, hannunsa ya kai ya ɗan taɓa fuskarta, amma kamar wanda ya taɓa gawa.

Hannunsa ya kai ya kamota ya na zaunar da ita, hakan ya sa ta buɗe idonta a wahalce, ta kuma lumshe idon sannan ta buɗe.

“K... kai... ka...”
Abun da take faɗi kenan, Kuliya bai san sanda ya fashe da dariya ba, maye take tuburan a fili, yau in ba shirme irin na Mishal ba, kusan rabin kwalba fa ta sha?, gaba ɗaya ta kasa zama gu ɗaya, sai layi take tana daga zaunen, ga idonta da take buɗewa ya na lumshewa da kansa.

“Tashi mu je na kaiki ɗaki...”
Ya faɗi ya na gimtse dariyarsa, a lokaci guda kuma ya na kama kafaɗunta, amma sai ta sa ragowar ƙarfinta ta ture shi.

“Kai...

Ka...

Ka rabu da ni...

Ba...

Ba ka san...

S...

San wa.. cece Mi...

Mishal ba ko?...”
Sai ta nuna kanta da ɗan yatsa.

“Ni ce...

Ce Hafsat...

Haf...

Hafsatun Aliyuu... hhhhhh!”
Sai ta ƙarashe da dariya, ta guntule dariyar tana nuna shi.

“Kai kuma...

Wa...

Waye kai?”
Kuliya na murmushi yace.

“Aliyun Hafsat”
Sai ta ƙyasta hannunta.

“Ka... ka ga mun yi ma...

Match kenan...

Amma me...

Ne kake a nan?”
Zama ya yi a kujerar yayin da take kallonsa da lumsassun idanuwanta.

“Wata na zo nema...”
Bai ko ƙarashe ba ta fashe da dariya.

“Haka...

Haka wani ma yace min a...

A...

A makarantarmu, wai...

Wai shi ya na neman wani, amma kuma ni na san ni yake nema...

Ni fa Cele...

Cele ce a makarantar nan...

Ko...

Kowa ni yake san gani...

Kai ma ka na san gani na ko ?”
Ya gyaɗa mata kai, sai ita ma ta gyaɗa nata kan.

“Amma kai...

Be kamata ka...

Ka ce kana so na ba”
Kuliya na ɗora hannunsa na dama a kan bakinsa yace.

“Amma me ya sa?”
“Saboda ni matar aure ce, mijina sunansa Kuliya...

Kuliya...

Yaro idan ka shiga hannun Kuliya ko, hmmmm”
Ya ƙara fashewa da wata dariyar.

“Me ya sa kake....

Kake dariya irin haka?”
“Ba dariya nake ba....

Kuka ne”
Sai kuma ita ma ta fashe da kuka harda hawaye.

“Yau ma yayata ba ta zo makaranta ba, ya...

Yayata ta de...

Dena sona, ba ta so...

Sona...

Kuliya ne kawai yake...

Yake sona...

Ka san...

Ka san me ya min yau da safe?”
Ta tambaya tana share hawayen fuskarta, kansa ya girgiza mata ya na murmushi.

“A nan”
Ta nuna masa lips ɗinta.

“Annan ya sumbace ne, kamar haka; ummmuah!”
Ta ƙarashe tana furta masa sautin sumbatar da bakinta.

Sai kuma ta fashe da dariya.

“Wai jiya cewa ya yi ya ba ni zuwa yau da...

Yau da safe na...

Na yanke shawara a kan soyayyarsa...”
Sai kuma ta ƙara fashewa da wata dariyar.

“Shashasha bai san cewa tun ba yau nake san sa ba....”
Ta kuma saka wata dariyar, sai kuma ta jingina da jikin kujera, a hankali idonta ya shiga lumshewa, bakinta na motsawa, ta na faɗar wasu kalamai da shi bai ma san ma'anarsu ba.

Ganin kamar shirmen nata ya ƙare ne ya sa shi miƙewa ya ɗauketa duka, sannan ya yi ɗakinta da ita, a kan gadonta ya kwantar da ita, sannan ya lulluɓeta ya fita.

Ɗakinsa ya koma ya yi wanka, ya sauya kayansa zuwa wanda ya saba sakawa na zaman gida a irin wannan lokacin, wato baƙin sweat trouser da kuma baƙar T-shirt.

Kitchen ya fara dubawa ko zai samu abinci, ya tarar da ta aje masa wanda zai iya ci, za ma ya yi ya na ci ya na murmushi a kai a kai, don shirmen nata ba ƙaramin nishaɗi ya bashi ba.

Bayan ya kammala cin abincin ya ɗan taɓa aiki a system ɗinsa, kafin ya fara jin bacci, system ɗin ya rufe, sannan ya nufi ɗakinsa dan ya kwanta, sai wata zuciyar ta raya masa da me zai hana ya je ya kwanta a ɗakinta, wata ƙila ta buƙace shi ko da cikin dare ne.

Ba tare da wani tunani ba ya nufi ɗakin nata, sai ya tarar da ta hargitsa kwanciyar da ya mata ɗazu, ba kamar.

Murmushi ya yi ya na gyara mata kwanciya, sannan ya kwanta a gefenta ya na kashe musu wuta.

Janta ya yi jikinsa, sannan ya lumshe idonsa don yin bacci, ba jimawa kuwa baccin ya ɗauke shi, don a gajiye yake, amma kuma baccin nasa bai yi minti goma ba ya farka, saboda wani duka da Mishal ta masa da ƙafarta, sam ya manta da ba ta iya kwanciya ba.

Ƙafafuwan nata ya gyara mata, amma da aka jima sai ta ƙara lafta masa ƙafarta, tun ta na yi ya na gyara mata, har ya gaji ya rabu da ita, haka daren ya ƙare ta na ta bugunsa da ƙafarta.

Da asuba ya farka, hakan ya sa ya tashi ya koma ɗakinsa, ya ɗan watsa ruwa kaɗan, sannan ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci, har ya dawo ba ta farka ba, hakan ya sa ya mata tashin duniyar nan amma ko motsi ba ta yi ba, har ruwa ya watsa mata amma kamar an mintsin kakkausa, sai ya ƙyaleta ya koma ya kwanta a gefenta.

Wajejen ƙarfe 09:00 dai-dai wayarsa ta yi ringing.

Cikin bacci ya ji ƙarar, hakan ya sa ya buɗe idonsa, hannunsa ya kai ya ɗauki wayar, sunan 'Sharon' ya ga ya na yawo a kan screen ɗin, sai ya ɗaga ya na wani cin magani kamar ta na gabansa.

“Lafiya yau ka makara?”
Sharon ta tambaya bayan sun gaisa, sai da ya juya ya kalli Mishal dake baccinta tsakani da Allah, hankalinta kwance, kamar tsumma a randa, sannan yace.

“Hafsat ce ba ta jin daɗi, zan kaita asibiti”
Sharon ta ƙunshe dariyarta sannan ta ce.

“Allah ya ba ta lafiya, sai yaushe kenan?”
“Gobe”
Ya bata amsa a taƙaice.

“Sai goben”
Ya na gama sauraren hakan ya katse kiran sannan ya aje wayar a inda ya ɗauketa.
*
“Yau Sir ya na more amarci...

Dan haka ba zai fito ba”
Cewar Sharon ta na kallon su Symon, wanɗan da suka zo suka sakata a gaba kan ta kira Kiloya ta ji me ya sa yau bai zo ba.

Dariya suka kwashe da ita, daga nan kuma sai aka shiga hira a kan Kuliya da Mishal.
*
Ya kamata ace zuwa yanzu ta tashi, Kuliya ya faɗi a ransa, ya na kaiwa hannunsa tare da ɗan tattaɓa fuskarta.

“Ummmm!”
Ta faɗi cikin muryar bacci.

“Hafsat”
Ya kira sunan a hankali ya na kallonta, yayin da yake kwance a gefenta.

“Ummmmmm!”
“Ki tashi gari ya waye”
Idonta ta buɗe a kansa, sannan ta ƙara lumshewa, ta kuma buɗewa, kuma a lokacin ne ta gano abun da ke faruwa, Kuliya ne kwance a gefenta, sannan a kan gadonta.

Ba shiri ta tashi zaune ta na waige-waige, kamar me neman wani abun, ita dai tasan bayan ta yi sallar isha, ta zauna a falo ta ci abinci, sannan ta ɗora da magungunan da ya aiko mata a jiyan, maganin murar ma da yawa ta sha, wai duk don ya mata magani da wuri, saboda ita ba ta san murar nan, kasancewar idan ta na yi takura mata take yi.

Kuma bayan hakan ita ba ta tuna komai ba.

Kuliya ya miƙe zaune ya na kallonta, abun da ta yi jiya ya dawo masa sabo, hakan ya sa shi murmusawa a fili.

“Kin tashi lafiya?”
Kallonsa Mishl ta yi a firgice, ta na san ta tuna wani abu da ta yi a daren jiya, amma ta kasa, ta kasa tuna komai, dole akwai wani abu da yake ba dai-dai ba.

“Har rana ta take ba ki yi sallah ba, ki je ki yi sallah”
A hautsine Mishal ta sauƙa daga kan gadon ta faɗa banɗaki da gudu, Kuliya ya yi murmushi ya na sauƙa daga kan gadon ya fita daga ɗakin.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*18*
~~~
*It's not hard to make someone feel loved.*
***
*No.181, Guzape, Abuja*
MISHAL POV.

A gurguje take aikin haɗa breakfast, don tasan yau ba ƙaramar makara ta yi ba, saboda ta na da tabbacin ma ko makaranta ba zuwa za ta yi ba, sai dai kuma akwai abun da ke ɗaure mata kai, me Kuliya yake ɗazu a shimfiɗarta, kuma ita da ta kwanta a falo me ya kaita ɗaki?, sannan shi ma me ya sa bai fita aiki ba yau?, abubuwan sun ɗaure mata kai.

Ga kuma kan nata dake mata ɗan banzan ciwo, sai jikinta da take ji a mace, haka ta yi sauri ta gama haɗa sandwich da kuma jallof ɗin indomie, tare da hot chocolate.

Ta kwashe komai ta jera a kan danning, sannan ta koma kitchen ɗin ta shiga wanke kayan da ta ɓata.

Har ta gama ba ta ga Kuliya ya fito ba, sai ta shiga gyara gidan, kuma gyaran gidan ma har ta kammala bai fito ba, abun ya so ba ta mamaki, ta san ko a da da ba ta girki da shi ya na fitowa da wuri ya ci abinci, kuma ta hakan ne ta gane cewa ba shi da jimirin yunwa, amma ga shi yau bai fito ba, to ko de tunani yake ba ta yi girki ba?.

Da wannan tunani ta nufi ƙofar ɗakinsa, sau ɗaya ta ƙwanƙwasa, ta ji muryarsa ta yi gyaran murya a cikin ɗakin, tunaninta ya ba ta cewar wata ƙila wani uzurin yake yi da ba ya so ta shiga ta gani a lokacin, sai ta ci gaba da tsayiwa a bakin ƙofar, har kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta ƙara bugawa.

A wannan karon magana ya yi.

“Shigo!”
Ta murɗa handle ɗin a hakankali, sannan ta shiga, tsaye ta ganshi jikin wani shelf ya na duba takardu, a karo na farko kenan da ta fara shiga ɗakinsa.

Kallonta yake kamar yanda take kallonsa.
Chapter 50 · 0% Book details