Sashe 8
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ai har ke, tun da de ba za ki je makarantar ba har sai an koma”
Rabi dai bata sake cewa komai ba, dan tun da ta ambaci kalmar 'makaranta', tunaninta ya tafi ɗazu, ta shiga tuna abinda ya faru tsakaninta da sabuwar ƙanwarta a ɗazun.
“Jibi za mu tafi garinmu, a can za mu yi bikin sallah”
Muryar Mishal ɗin ta katseta a ɗazun.
Sai kawai ta yi murmushi.
“Ina ne garin ku ?”
“Maiduguri”
Mishal ta bata amsa tana firfita lallen hannunta da iskar bakinta.
Rabi'a ta gyaɗa kanta.
Tana ƙara tabbatarwa da kanta hasashen da take a kan Mishal ɗin, na kasancewarta shuwa arab.
“Shikenan, na san zuwa yanzu an koma break, bari naje na share inda aka ɓata, ki kula da kanki, Allah ya dawo da ku lafiya, sannan ki gaida Mamanki idan kin koma gida”
Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi, amma maganar Mishal ɗin ta gaba ita ce ta hanata tashin.
“Mamata bata raye, kuma tun a sanda zata haifeni ta rasu, ban san babana ba ma, lokacin da cikina ya rasu, tare da yayana kawai na taso.....”
Rabi'a ba za ta iya cewa ga abinda take tunanin ba a lokacin, tasan dai kawai ta tsirawa ƙaramar yarinyar ido ne, tana nazarin ya akayi ta rayu tsawon shekarunta babu iyaye.
Ita da ta rasa iyaka mahaifiya ma kawai rayuwarta ta hargitse bare ita da ta rasa duka biyun.
Kuma bama wannan ba, ba ma ta sansu ba, bata taɓa ganin ko ɗaya daga cikinsu ba.
“Ke Rabi?
Tashi ki zo ki soya mana doyar nan!”
Muryar Habiba ta dawo da ita zahiri, a hankali dubanta ya kai kan Habiban dake tsaye a kansu.
“Umma ki bari mana na ƙarasa mata, saura guda biyu fa....”
“Ban yi niyya ba, yanzu nake so ta tashi ta min aiki na....”
Ba tare da Rabi'a tace komai ba, ta shiga ƙoƙarin jan doguwar kalbar dake riƙe a hannun Saratu dan ta miƙe, amma sai Saratun ta mayar da ita ta zaunar.
“Gaskiya Umma ba kya kautawa, Wallahi wannan ba adalci ba ne, yarinyar nan ta je ta yini tana aikin bautar da ba ita take cin kuɗinta ba, dan ke take kawowa, sannan ta dawo ta yi aikin gidan nan, kuma yanzu ta samu ana ɗan mata kalbar da za ta yi adon salla sai ki ce baza'a mata ba ?!”
Habiba ta ɗan sunkuyo tana miƙowa Saratu bayanta.
“Da ke ni mama Saratu, na ce inji didim!, sai na tabbatar da ranki ya ɓaci....”
Ta miƙe tana ci gaba da faɗin.
“Na taɓo uw*r ki Rabi ko?, To baki isa ba, dole sai ta tashi ta soya doyar nan!....”
Kafin Saratu ta sake cewa wani abu, Rabi ta yi wuf ta miƙe tsaye, tana ƙoƙarin ɗaure kanta da ɗankwali.
Gashin kanta da tsayinsa ya ragu a yanzu ya kwanta luf a gadin bayanta, har yana reto.
“Gaskiya Umma na gaji!, Wallahi na gaji da abinda kikewa yarinyar nan a cikin gidan, ita ma fa 'ya ce, kuma ko baabaarta bata raye hakan ba ya nufin a cusguna mata.
Umma kema uwar 'ya'ya mata ce, wata rana gidan wani za muje.
Na tabbatar da idan uwar miji ko 'yan uwansa suka mana haka ba za ki ji daɗi ba.
To ita ma kamar haka ne, tana da dangi bayan mu.
Dan tsabar san zuciya irin naki yau shekarar yarinyar nan biyar a gidan nan, amma kin hanata ta je ta ga dangin mahaifiyarta, dan kar ta je ta faɗi irin azabar da ake bata a cikin gidan nan su hanata dawowa ki rasa baiwa.
Wallahi Umma wannan ba adalci ba ne, ke ba kya tunanin wata ƙila wannan abun da kike shi ne ya zama sannadiyyar tagayyarar mu?, Ita 'yar taki ta fari, bata jin daɗin aurenta, sannan ni, shekaruna 27, amma na rasa mijin aure, ko sau ɗaya saurayi bai taɓa zuwa ƙofar gidanan yace yana sallama da ni ba, ga kuma Mama, wadda ta lalace da bin maza!.....”
“Ya ishe ni haka Saratu, ki rufa min baki ko na make ki a wurin!”
Saratu ta share guntuwar ƙwallar da ta zubo mata ta buɗe labulen ɗakinsu ta shige ciki.
Rabi'a da ke kiciniyar hura wuta ma ta share tata ƙwallar, saboda tunawa da ta yi da dangin Ummanta, ta tuna yanda suke matuƙarsanta da 'yar uwarta, sai kuma tunanin Anti Saratun, Allah ya sani kuma ita ma ta sani, ba ƙaramin cutuwa baiwar Allahn nan take da zaman gidan.
Kuma ta san cewa Anti Saratun na matuƙar san aure, dan tasha kamata tana kuka, kan abun da ke damun rayuwarta, sai dai ta zauna ta bata baki har ta samu ta yi shiru.
*DSS Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
*10:30am*
KULIYA POV.
“Aliyu Zaid Bichi!”
Cewar shubansa, yayin da yake tsaye a gaban shugaban, ya ƙame cike da girmamawa.
Wani murmushi kwance a fuskar ogan.
Kuma cikin abinda bai wuce sakan biyu ba, wannan murmushin ya sauya zuwa ɓacin rai ma bayyani.
“Kai wai me yasa ba zaka taɓa sauyawa ba?, yanzu saboda shashancin da ka yi, ɗaya daha cikin criminal ɗin ya mutu, kai kwata-kwata baka iya controlling fishinka ne ?!”
Kuliya ya ƙara ƙamewa yana kallon wani wurin da ban, dan da ma yasan hakan sai ta faru, ba ma yasan ya kalli fuskar ogan, dan idan har ya kalleta, zai iya hasaso kansa yana marin shugaban nasa, kuma wata ƙika ma hasashen ya zama gaskiya.
Dan baya san a ɗaga masa murya, daga an ɗaga masa murya yake kai hannu, shi kansa yasan cewa zuciyarsa a kusa da take, abu kaɗan ne ke tunzura shi.
Ya ɗaga kafaɗarasa yana ci gaba da kallon wani hoto dake aje a bayan ogan nasa.
“A haka kake san zama kamar Lion ɗin ?......
Shi Lion ɗin da kake san zama sam ba haka yake ba, cikin basira da taka tsan-tsan yake gudanar da aikinsa, ba shi da saurin fusata kamar kai, ba shi da saurin kai hannu kamar kai!....”
Lion?!, wani suna guda ɗaya da yake ƙwarara masa gwiwa a kan aikinsa, wani sunan da ko jinsa ya yi sai ya ji jinin jikinsa na tafasa.
Kuma ba shi kaɗai ne sunan Lion ke bawa ƙwarin gwiwa ba.
Kusan duka ma'aikatan DSS sun san sunan Lion, dan abu ne mayuwaci, ka je training ɗin DSS ba tare da an baka maka tarihi da kuma sunan Lion ba.
Duk wani jarumi da mai hazaƙa a hukumar burinsa kawai ya zama kamar Lion.
Sai dai kuma duk da wannan nasara da kuma jarumta irin ta Lion ɗin, in ka ɗauke manyan hukumar tasu, babu wanda yasan kammanin fuskarsa, sunan nasa kawai ake ji, sai kuma ƙwazon da yake a aikin nasa, sunan nasa ma ba na ainahin kowa ya sani ba.
Code name ɗinsa kawai suka sani.
Amma duk da haka yana burge kowa, dan duk wanda zai gwada wata jarumta da kuma san nuna role model ɗinsa sunan Lion za ka ji ya kira.
“Sam shi Lion ɗin ba haka yake ba....”
Muryar Ogan nasa me amsa sunan Chidera Kingsly ta katse masa hanzari.
“Lion yana da basiri, he is so intelligent, amd smart, ya san aikinsa, baya komai cikin fushi, cikin nustuwa da tunani yake gudanar da aikinsa.....”
Kuliya ya sauƙe kansa ya ɗora manyan idanuwansa a kan fuskar shugaban nasa.
Kuma har zuwa lokacin bai ce komai ba, dan tun bayan gaida shi da ya yi a sanda ya shigo office ɗin, bai ƙara cewa komai ba.
Kuma shima Chideran yasan cewa ba lalle ya sake cewa komai ɗin ba, dan kowa yasan miskilancin bawan Allahn nan.
“Na san cewa yanzu haka ka rayawa ranka cewar; ka dalle min fuskata da mari!”
Wani abu me kama da murmushi ya faru a cikin zuciyar Kuliya, dan ya canka dai-dai, hasasowa kansa yake yayin da yake kashe sauraye a kan fuskar chideran, dan ba sauro ɗaya ba.
*
“Ehemm!”
Muryar Kuliya ta yi gyaran murya, alamun ya bawa wanda yake buga ƙofar izinin shiga, dan wannan ɗabi'arsa ce.
Kusan duk wanda yake headquarter ɗin yasan da hakan.
Shi a ganinsa magana ma wani kayan gabar ne, amma idan masifarsa ta tashi yafi ub*n kowa iya ɗaga murya.
Zaune yake a office ɗinsa, yayin da yake daddana system.
Kamar kullum; sanye yake da baƙaƙen kaya, wata baƙar suit ce a jikinsa.
Hatta da long sleeve oxford shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin baƙa ce.
Ƙofar office ɗin ta iyo ciki, alamun dai wanda yake bayan ƙofar yana shirin shigowa.
Suffar Abubakar ta bayyana a bayan ƙofar.
Kallo ɗaya Kuliya ya masa ya ɗauke kai, tare da ci gaba da danna laptop ɗin gabansa.
“Barka da safiya..... ni na gaida ka, tun da kai ba za ka iya ba gaisheni ba”
Abubakar ɗin ya faɗi yana ƙarasowa cikin office ɗin. har ya zauna a kujerar dake tsallaken teburin Kuliyan bai masa magana ba.
“Me yasa yau ka makara ?”
Muryar Kuliyan ta tambaya bayan wani lokaci, ba tare da ya kalli Abubakar ɗin ba. muryar tasa kamar da ga sama.
Sannan amonta ya fito kamar kullum, cikin ɗaci da alamun ɓacin rai.
Dan shi kullum ba'a rasa abinda yake ɓata masa rai.
Abubakar ya yi murmushi, to shi ya zai yi ne?, tun da Allah ya haɗa shi zama da mutane biyu masu murɗaɗɗen hali, tsakanin Kuliya da ƙanwarsa Misha!, Ya rasa wannene ya fi wani murɗewar hali.
“Ƙanwarka ce, ta yi rashin jin da ta saba a makaranta, sai da na biya ta can, sannan na ƙaraso nan”
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
Shi duka-duka sau ɗaya ya taɓa ganin ƙanwar Abubakar ɗin, ba ma sosai yake iya tuna lokacin ba, dan shekarun da ɗan dama.
“Dama autopsy results ɗin nan na zo karɓa, Kamis yace yana wurin ka”
Ba tare da Kuliyan ya kalle shi ba, ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan ya buɗe wata loka dake jikin teburin nasa, ya ɗauko file ɗin,ya miƙa masa.
Abubakar ya karɓa yana miƙewa tsaye.
“Na tafi...”
Ko kallonsa Kuliya bai yi ba, bare ya bashi amsa, kuma shi ma yasan ba lalle ya kalle shin ba.
Yasan halin Kuliyan sarai.
Har faɗi yake da bakinsa cewa; idan ba Abubakar ɗin ba babu me iya zama da shi a matsayin aboki.