← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 80

Sashe 4

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubakar ya girgiza kansa, ya san duk yanda aka yi wani laifin ta aikata, ba yau ta saba kawo takardu irin wannan ɗin ba, hasalima suna nan tili guda yana ajewa, dan sun ma fi yawan report ɗin ta na makaranta da take kawowa.

Abu ɗaya ne yasa ba zai cireta daga makaranta ba kwata-kwata, hazaƙarta ce tasa hakan, dan ba ma shi ba, hatta da makarantar suna tinƙaho da ita, gashi de ba wasu shekaru ne da ita ba, amma girman jikinta ne zaisa ka zaci wata babbace.

“Me kuma kika yi ?”
Ya tambaya yana karɓar envelope ɗin, kanta ta sunkuyar, tana wasa da yatsunta.

Murmushi kawai ya yi a sanda ya buɗe ya karanta, dan bi da bi ya gama haddace kalaman da ke ciki, saboda a kullum abu iri ɗaya suke turo masa tun tana junior.

Ya rasa irin abunda ke damun ta.

“Hammad yace min yau baki yi azumi ba, bayan shi ma yau yana yi”
Ta ɗago da kanta ta kalli Hammad ɗin dake gefen uw*rsa, kamar yanda bata san uwa*r yaron shi ma haka ta tsaneshi, dan kaf halayen uw*rsa babu wanda bai ɗauko ba.

“Saboda makarantar da nake zuwa ne...”
“Makaranta sai ta hanaki azumi?”
Sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.

“Bari na je waje.....”
Bayanta ya bi da kallo yana mamakin halin yarinyar, du-du-du ba za ta wuce 17-16 ba, har yau yana tuna yanda ya ɗauketa da hannayensa ranar da aka haifeta, da kuma irin maganar da mahaifiyarsu ta masa a wancan lokacin.
_“Sadiq, ka kula da ita, nasan za ta tashi cikin maraici, bata da kowa sai kai, kada ka danƙa renonta a hannun kowa, ciki kuwa harda Amma (tana nufin mahaifiyarta), ka kula da ita, ka kula da ita......”_
Kuma kalamanta na ƙarshe kenan, a kan idonsa a ka shiga da ita ɗakin tiyata. sai kawai fito masa aka yi da jairiya, aka ce ta haihu, amma ta rasu sai dai babyn da ta haifa.

“Wai haka za'a zuba ido ana kallon yarinyar nan tana abinda take so?.....”
Hajjara ta faɗi a ƙufule, dan Allah ya sani ta gaji da halin yainyar, kuma da ma tun sanda ta ɗora idonta a kan yariyar ta washeta.

“Me ta yi ?”
Ya furta hakan cikin halin ko in kula, yana ninke takardar da Mishal ɗin ta bashi.

“Jiya fa na yi baƙi, baka ga rashin kunyar da ta min a gabansu ba”
“Yarinta ce take damunta, idan ta girma za ta dena”
Haushi kamar ya kashe Hajjara, dan dama abin da ya saba faɗa mata kenan, a duk sanda ta kawo masa ƙarar Mishal ɗin, yau ɗin ma tsautsayi ne yasa ta kawo ƙararta, a ranta ta yi ƙwafa, Allah ya kawo ranar da za ta ga bayan yarinyar nan.

Idonta ya sauƙa a kan Daala dake ta zubar yawu, ita ma yarinyar Hajjaran take kallo.

Tawarta ɗaya kenan a duniya, wannan yariyar da Allah yasa ta haifota a nakashe, kuma nakasar yariyar yasa ta gujeta, babu wani abu dake shiga tsakaninta da yariyar irin na uwa da 'yarta, Mishal da Naani ɗin da Abubakar ya ɗauko su ne ke kula da yarinyar har wa yau.

Mishal na fita daga falon gidan BQ ta wuce, dan bata da wurin zama a gidan da ya wuce BQ ɗin, in baka sameta a BQ ba zaka sameta tare da Daala suna wasa, dan Allah ya ɗora mata ƙauna da tausayin yarinyar.

Ganin yanda Hajjara ke bagarar da lamarin yarinyar saboda nakasar dake tare da ita, ita kuma Allah ya hallici zuciyarta da wani irin tausayi, kuma tausayin ne ke sakawa bata da aminan hira a gidan sai masu aikin gidan.

A bakin ƙofar BQ ɗin ta tsaya, tana ƙare musu kallo.

Mutum biyar ne zaune a kan bujukura.

Ladi, wadda ita ce ke kula da Daala sai mijinta Malam Audu, wanda ke musu gadi, sannan Khalifa, ɗan Mama Ladin na farko, wanda shi ne yake musu sharar garden da ta compound da ma aike idan ya taso, sai Shatu 'yar Mama Ladin ta biyu, sai autar Mama Ladin wato Ummul.

A taƙaice de duka ahalin Mama Ladin ne, waɗan da suka kasance ahalinta ita ma, dan bata da wurin zuwa da ya wucenasu, Shatu kuma ita ce wadda zata iya kira da ƙawarta, Mama Ladi ta zame mata uwa.

“Ah-ah, Hafsatu, ƙaraso mana”
Sai ta yi murmushi har ƙarafunan braces dake saman haƙwaranta na bayyana, tana ci gaba da kallonsu, su ma sai hadaniyar haɗa kayan shan ruwansu suke, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka ci gaba da takawa har zuwa kan bujukurar.

Guri ta samu kusa da Shatu ta zauna.

“Yau kin yi azumi ?”
Mama Ladi ta tambaya, yayin da take juye tiyara a cikin wata doguwar roba, Mishal ta girgiza kanta.

“Ban yi ba”
“Haba uwata, sau nawa zan faɗa miki cewar kin isa azumi ?, bai kamata ace ki na shan azumu ba gaira ba dalili ba”
Cewar Malam Audu yana aje radion hannunsa.

“Rabu da ita Baba, ai kullum gaya muku nake cewar yarinyar nan raguwace, amma bakwa yarda” Cewar Khalifa.

Mishal ta turo baki gaba tana sosa kanta.

“Allah ni ba raguwa ba ce, a class ɗin Kungu fu ɗinmu fa kullum ni nake zuwa a farko, kuma watan da ya auce ma saida na karya wani malamin mu....”
Hannunta ta kai ta rufe bakinta, sakamakon suɓul da bakan da ta tuna cewar ta yi, dan tasan yanzu Mama Ladi za ta shiga mata faɗa.

“Kema kin san cewa ba dai-dai kika yi ba kenan, shi yasa kika rufe baki” Cewar Mama Ladin tana miƙawa Baba pure water.

Sai kuma ta sauƙe hannun nata.

“To ai shi ne ya min tsawa, kuma ya dake ni....”
“Ai haƙuri ake uwata, idan kika yi haƙuri sai labari, dan wata ƙila ma kina gama makarantar auren ki za ki yi”
Ido waje take duban Baba.

“Aure fa Baba ?, a'a ni ba wani aure da zan yi yanzu, nawa ma nake da har zan wani yi aure?”
Abinda bata sani ba shi ne, waɗanan kalaman nata zasu mai-maita kansa a cikin kanta kwanaki kaɗan masu zuwa, dan bata da masaniyar ƙaddarar da Allah ya hukunta za ta faru a 'yan kwanaki masu zuwan.

Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura, ta kuma zama silar ɓacin wasu.

A wurinsu ta zauna ta sha ruwa, har sanda su Baba suka fita Sallah, Sai da Mama Ladi ta mata jan ido a kan ta tashi ta je ta yi sallah, dan Allah ya sani, zuciya ɗaya take zaune da yarinyar, ganin ta ɗauketa kamar uwa, shi yasa ita ma ta ɗauketa kamar 'ya.

Saboda rayuwar yarinyar tana buƙatar kulawar uwa, gashi ita kuma bata taso ta samu hakan ba.

Ko da ta koma cikin gidan ɗakinta ta wuce.

Wani haɗɗaɗe kuma ƙawattacen ɗaki wanda aka cika shi da kayan buƙata irin na matasa dai-dai shekarunta.

Komai na cikin ɗakin peach color ne, sannan ga tarin teddies a ko wata kusurwa ta ɗakin.

Lokarta ta buɗe, da ƙyar ta samu hijabin da ta saka, dan ba saka hijabai take ba, hatta da kayanta yawancinsu ƙananu ne, bata sakka kayan hausawa sam, a cewarta takura mata suke.

Bayan ta yi sallar ta fita falo, a lokacin Daala ce kaɗai, zaune kan kujrarta tana ta gwalantunta, bakinta sai zubar da yawu yake.

Zama ta yi kusa da ita, ta kunna musu tashar mbc 3, sannan ta shiga bata labarin da ita kanta tasan cewa Daalan ba fahimta take ba.

Hammad ne ya shigo falon ta ƙofar ɗakinsa,byana shigowa ya ɗauki remote control ya sauya tasha.

A fusace Mishal ta yi kansa.

“Sh*ge ub*n baƙin hali, dan me zaka sauya mana tasha?, dan ka ga ban maka magana a kan munafurcin da ka min ɗazu ba ko?”
Ta ƙarashe tana ƙwace remote control ɗin tare da maida mbc 3n da suke kalla.

“Bar falon nan kafin na karya maka wuya”
Da gudu ya yi sama.

Kuma bai tsaya ko ina ba sai a ɗakin Hajjara, wadda ke kwantar da Fahima a kan gado, sakamakon baccin da ta yi.

Ƙarya da ƙarerayi ya sameta ya zayyana mata.

Kafin ita kuma ta bazamo ta sauƙo ƙasan ta samu Mishal ɗin tare da balbaleta da masifa, cikin ƙaraji da ɗaga murya take faɗan.

“Wai ke yarinyar nan me kike nufi ?, so kike mu fice mu bar miki gidan ko me ?, to wallahi baki isa ba, shi har gwara shi, tun da nan gidan ub*nsa ne, ke kuma fa ?, sakabu fa kike, to wallahi ki fita idon yarana!......”
Ba komai Mishal ke fahimta cikin kalaman nata ba, sakamakon ciwonta da ya shiga ƙoƙarin tashi, dishi-dishi take ganin komai, numfashinta ya shiga ƙoƙarin ɗaukewa daga ƙirjinta, waccan ranar ta soma dawowa cikin kanfa.
_“Yau daga ni sai ke, kuma babu me ƙwatarki a hannu na!....”_
Abinda ya biyo bayan kalaman nasa sune ya zama silar shigarta cikin halin da take a yau.

Numfashinta ya ci gaba da yin sama, da ƙyar take iya janyo shi.

Zuwa lokacin Hajjara ta tuna da ciwon nata, sai ta tsaya a gefe tana kallonta kawai, a ranta addu'a take, kan Allah yasa idan nunfashin nata ya yi sama kada ya dawo.

Mishal ta kai ƙasa tana dafe da wuyanta, sai neman iskar da za ta shaƙa ta ke, duk da sanyin acn dake falon sai gumi take, tuni idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, har hawaye ya fara sulalowa ta gefnsu, sai jan nunfashi take kamar me asthma.

Fatan Hajjara bai karɓu ba, dan a dai-dai lokacin da ta faɗi ƙasa gaba ɗaya, a lokacin ne ƙofar falon ta iyo ciki, alamun wani ne zai shigo, kuma bai fi tazarar sakan ɗaya ba, siffar Abubakar ta bayyana a cikin falon.

RABI POV.

Zaune take daga gefe a kan dakalin ƙofar ɗakinsu, yayin da Habiba da sauran yaranta ke zaune a kan tabarma suna kiciniyar shan ruwa.

Ba yau aka saba haka ba, kusan kullum hakan ake, a duk sanda za su taru irin haka, to ita za ka ganta daga can gefe tana kallonsu.
Chapter 4 · 0% Book details