Sashe 52
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wannan file ɗin ya na ƙunshe da bayanan kaf marasa lafiyar da aka karɓesu a asibitin nan, a tsakankanin sati uku da suka wuce, ku duba, wata ƙila za ku iya samun wadda kuke nema”
Ya ƙarashe ya na musu bayani kan abinda ya sa suka biyoshi, amma sam Raja bai fahimci zancen nasa na biyu ba, wannan maganartasa ta farko ita ce ta sa hankalinsa a kwalba ta kulle, don zuciyarsa ce ta hango masa dacewar bayanen da aka basu, da kuma wanda shi Huzaifan yake faɗa, to ko de ita ce?, amma ta ya za ayi ta kasance ita?.
“Ina ne ɗakin mara lafiyar?”
Rajan ya tambaya ya na kallonsa, har Huzaifa zai ce wani abu, sai kuma hoton fuskar yarinyar ya haska a cikin kansa, rannan da ya shiga ɗakin don dubata ya kalli fuskarta, a lokacin ya ga kamar ya san fuskar tata a wani wuri, duk da ɗinkin da aka mata a gefen fuskarta, amma ta masa kama da wani wanda ya sani, a yanzu da Raja yake zaune a gabansa, sai fuskarta ta haska a cikin kansa, haɗi da tasa fuskar.
“Nan ne!”
Huzaifa ya faɗi ya na nuna musu ƙofar ɗakin, Raja ya juyo ya kalli Rhoda, zuciyarsa na dokawa a kunnuwansa, ƙafafunsa suka masa nauyi, don ji yake kamar abun da yake zargi shi ne zai tabbata.
Kamar mara lafiya haka ya kai hannunsa ya kama ƙofar ɗakin ya murɗa, tura ƙofar ciki ya yi, sannan ya shiga.
Idonsa ƙyam a kan yarinyar dake kwance a kan gadon marasa lafiya, wasu na'urori ne ɗaure a jikinta, kuma babu sautin dake tashi a ɗakin sai na na'urorin.
Duk da wani irin fari da ta yi, duk da wani ƙaton yanka da ya gani a gefen fuskarta, duk da gashin kanta da ya yi alamar kamar an yanke, duk da yanda fuskarta ta yi wani irin fayau kamar wadda ta mutu, duk da yanda idanuwanta ke a rufe kamar gawa, bai hana shi gane taba.
Kuma ƙwaƙwalwarsa na ganeta, ta hankaɗo masa bayanan Huzaifa na ɗazu.
_“Wata mara lafiya ce aka kawota asibitin nan, sati uku baya, Wallahi abun tausayi, wasu ne suka mata fyaɗe sannan suka cillar da ita a hanya, mutanen kusa da mu ne suka kawota nan, sati uku kenan amma babu wani nata da ya bayyana...”_
Nan take ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta tashin bomb, a sanda kalaman suka tsaya, a lokacin ne ƙafafunsa suka ɗauki rawa, haka ma hannayensa, hatta da bakinsa rawa yake, duniyar ta masa.
Wani irin shiru, sannan duhu ya mamaye injinan ganinsa.
Fyaɗe!?, fyaɗe!?, fyaɗe!?, Ita ma?, kenan ita ma sai da aka samu wani ya aikata mata wannan zalincin?, me ya sa haka?, me ya sa ƙaddararsa take zuwa a haka?, me ya sa tarihi yake shirin maimaita kansa?, me ya sa?, me ya sa?, me ya sa?!...
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters
•••••••••••
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*19*
~~~
*Love is; when you hug someone and they feels like home...*
***
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja.*
A fusace Jadda ta shigo cikin gidan tana famar bambami, kamar wadda ta zauce.
Hajjara na zaune a kan kujera tana taunar chewing gum, haɗi da latsa wayarta, wani ɗan iskan kallo ta bi Jaddan da shi, kafin ta ci gaba da kallon wayarta, daga gefen ta kuma Fahima ce zaune ta na wasa, yayin da Hammad ke zaune a kan dinning ya na cin abinci.
“Wallahi wannan yaron da aka aurawa Hafsat ya ɓatata, yo in ba haka ba ta ya za ayi na je na ce ta taho mu tafi, amma ta ce ba za ta zo ba?, wata ƙila ma shanyeta ya yi!...”
Haka ta dinga sambatu, har ta kai ɗakin da ke a mazaunin nata, ta riga ta yanke shawarar barin garin a yau, don babu abun da za ta zauna ta yi a Abuja, tun da wadda take zaune don itan ta ƙi yarda ta biyota, duk da wahalar da ta sha kafin ta samu adireshin gidan nata.
Kuma ta riga da ta yamie shawarar datse ko wace alaƙa dake tsakaninta da Mishal ɗin, tun da ita ba ta da mutunci, wai ita 'yar daɗi miji, tun da ta zaɓi zama da shi ga fili ga me doki, sukuwa kawai ta rage, kuma Allah ya bata sa'a, amma ita da Mishal kam ko a lahira!.
*No.181, Guzape, Abuja...*
*07:55 PM.*
YUSHAL POV.(ALIYU & MISHAL)
“Ga shi”
Muryar Kuliya ta faɗi, a sanda yake miƙawa Mishal wani ɗan ƙaramin bowl dake ɗauke da yankakkakiyar albasa.
Rai a cunkune Mishal ta kai hannu ta karɓa, sannan ta juya kan stove, ta buɗe murfin tukunyar da take dafa jallof ɗin shinkafa, ta zuba albasar, sannan ta rufe murfin tukunyar.
Ta ajiye bowl ɗin ta shiga wanke hannunta a sink.
Kuliya ya ci gaba da kallonta, ya na nazarin yanayinta, tun bayan da suka yi wannan faɗan da Jadda bata dawo dai-dai ba, kuma saboda ya san ta na cikin yanayin damuwar ne ya sa shi dawowa gida da wuri.
Amma duk da haka sai ya isketa cikin damuwar.
Ko bayan da ta gama wankewa hannunta, sai ta ci gaba da tsayuwa a jikin sink ɗin, ta shiga karanta wasiƙar jakin da ba ta da ranar ƙarewa.
A hankali Kuliya ya isa bayanta, sannan ya saka hannaynesa ya kewaye waist ɗinta, ya janyota baya, tare da mannata da jikinsa.
Mishal ta rintse idonta, saboda da wannan sanyin da ya fara shiga kowace ƙofa ta gashi a cikin jikinta.
“Me yake damunki?”
Sai ta buɗe idonta, ta soma kallon garden ɗin gidan ta windown dake kusa da sink ɗin, amma bata ce masa komai ba.
A hankali Kuliya ya sunkuyo da kansa zuwa kafaɗarta, sannan ya manna mata peck a wuya, wanda ya sa ba shiri ta damƙe bakin sink ɗin.
“Me yake damunki?”
Ya tambaya wannan karon a cikin kunnuwanta, kuma murya ƙasa-ƙasa, wadda ta sa Mishal saurin juyawa a cikin hannayensa tana kallonsa.
Hannayenta a kan kafaɗunsa, idonta a kan kyakkyawar fuskarsa.
Peck ya mata a goshinta, hakan ya sa ta lumshe idonta.
“Me yake damunki?”
Ya kuma tambaya a karo na uku, yayin da goshinsa ke kare da nata, hancinsa a kan nata.
Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta fara hawaye, da sauri ya zare hannayensa daga jikinta ya dawo da su kan fuskarta ya na share mata su.
“Ba ki yarda da ni ba ne ?”
Da sauri ta girgiza kanta.
“Na yarda da kai sosai, wata ƙila ma sama da yanda na yarda da kaina, ina cikin damuwa saboda rashin ganin Yayata, yau ma fa ba ta zo ba, jikina na bani cewar ta na cikin matsala”
Kuliya ya girgiza mata kai ya na cije laɓensa na ƙa.
Tare da share mata wata ƙwallar dake bin fuskarta, ashe kenan hasashensa bai zama gaskiya ba, ba abun da suka yi da Jadda ba ne a ranta, damuwar Rabi ce a ran nata.
“Insha-Allah ta na cikin hali me kyau, ki kyautata mata zato, da yardar Allah zan nemo miki ita, wannan alƙawari na ne”
“Ka min alƙawari?”
Ta tambaya muryarta a raunane.
Kuliya ya gyaɗa mata kai ya na ci gaba da share mata hawayen, kwanciya ta yi a jikinsa tana sakin wani kukan, Kuliya ya gyara mata riƙo a cikin jikinsa.
“Ki na so mu yi faɗa?”
Ta girgiza kanta, hakan ya sa jikinsa motsawa, saboda kanta dake kwance a ƙirjinsa.
Ya ɗaga kafaɗa yana faɗin.
“To ki dena kuka...
Ke fa kina da ƙarfin zuciya, you are so strong Teddy Bear, so don't cry!”
Sai ta gyaɗa masa kai.
Sautin tafasar tukunya ne ya ankarar da su girkin da suke, don dukansu sun ma manta da girkin.
Hakan ya sa da sauri Mishal ta fice daga jikinsa ta koma jikin stove ɗin.
Shi kuma ya koma ya zauna a kan kujera ya na kallonta.
*Vinca Hospital, No.12, Remkom street, Kubwa, Abuja*
RAJA POV.
Zaune yake a kan kujerar dake kallon gadon marasa lafiya na ɗakin da aka kwantar da Rabi'a.
Bayansa jingine da jikin kujerar, yayin da ƙarfen da aka saƙala drip ɗin da aka saka masa yake aje a gefensa, hannunsa na dama juma saƙale da allurar dake aika drip ɗin zuwa cikin jikinsa, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Rabi'ar dake kwance akan gadon.
A ɗazun suma ya yi, har sai da aka ƙaramasa ruwa, kuma ya na farkawa ya fito daga ɗakin da aka kwantar da shi, ya dawo nan ya zauna.
A hankali wata ƙwalla ta gangaro daga idonsa, bayan da ya tuna irin gararin rayuwar da take ciki, yanzu kuma ga wani baƙin tabo me matuƙar muni ta ƙara samu.
Amma alƙawari ya yi wa kansa, na babu abun da zai hana shi aurenta, ko da sama da ƙasa za su haɗe, ko da duniyar ce za ta tashi, ko da kuwa aurenta shi ne abu na ƙarshe da zai yi a duniyar nan, ba fyaɗ...
Kasa ƙarasa kalmar ya yi a ransa, don haka kawai ya tsalleketa ya tafi tunaninsa na gaba; ko da cuta me karya garkuwar jiki ce tare da ita, ba zata hanashi aurenta ba, wani kalar so yake mata da ya wuce soyyaya kawai, sai dai soyyayar haɗuwar jini, kasancewarta ɗaya daga cikin ahalinsa shi ne ya ƙara ninka soyyayarta a ransa.
Ganin ruwan da aka saka masa ya ƙare yasa ya kai hannunsa ya cire allurar, sannan ya manne wurin da plaster, saboda kada jini ya zubo, miƙewa ya yi, duk da ya na jin jikinsa babu ƙwari, amma haka ya taka a daddafe har ya isa jikin gadon da Rabi'a ke kwance kamar gawa.
Zama ya yi a gefen gadon ya na kallon fuskarta, sannan ya kamo hannunta na dama, wanda ke saƙale da clip na wata na'ura dake jikinta, hannunsa ya saka cikin nata ya damƙe, dubansa ya dawo kan fuskarta.
Wadda a yanzu ta sauya suffa daga tata ta da, sakamakon wani yanka dake gefen fuskarta na hagu.
Ɗinkin da ya ga an yiwa raunin ya sa ya fahimci girmansa, ga kuma yanda fuskarta ta ɗan tattare daga gefen hagun, saboda yankan da aka mata, amma duk da haka kammanin fuskarta ba su sauya ba.