Sashe 17
Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba dan dariyar da ɗaya ya yi ba, da babu abun da zai hana tace duka mutum ɗaya ne, zaune suke a ƙasa, daya ya dafa ɗaya.
Yau ta fara ganinsa, amma duk da haka sai da ta gano shi a cikin su biyun, saboda rabin idanuwasa da suke a lumshe, sannan akwai tsotsiyar karen da ta ga a ƙasan haƙorinsa.
Iko sai Allah, kenan ba ma shi kaɗai ba ne, to amma umma ta faɗa mata cewar abokiyar tagwaitakar ta wato mai sunanta Rabi'a ta rasu, kuma ta rasu, bayan rasuwarta ma aka ce su ma yaran da ta haifa sun rasu.
To su waye waɗanan ?, me yasa suke kama da Ummanta da kuma ita, dan ganin ɗaya ɗan uwan nasa yasa ta ƙara ganin kamarta a cikin fuskokinsu, duk da a lokacin yarinta aka musu hoton.
A hankali hannunta ya ci gaba da buɗa wallet ɗin, akwai kuɗaɗe a ciki, sai atm cards.
Bakinta ta taɓe, sannan ta rufe wallet ɗin, wata ƙila Allah zai sa su ƙara haɗuwa, sai ta samu damar ba shi kayansa.
Aje wallet ɗin ta yi a gefe, sannan ta ci gaba da shirya kayan nata.
Kuma a cikin kayan ne, hannuta ya ɗauko wata jersey, jerseyn ta Bacerlona ce.
Kuma tata ce.
Nan take idanuwanta suka hango mata lokacin da aka samu rigar.
_“Yaya Baby, Umma ta dawo”_
_Muryarta ta faɗi, a sanda take kallon Umman tasu da ta dawo daga asibiti, sannan a lokaci guda ta faɗa jikin mamar tata ta rungumeta._
_“Umma sannu da dawowa”_
_Baby ta faɗi a sanda ta leƙo daga ɗakinta.
Umman tasu ta kalleta tana amsawa._
_“Yayar mamarta kin san me Umma ta kawo miki ?”_
_Umman ta faɗi a sanda take zama a kan sofa, cike da ɗauki Adawiyya ta girgiza mata kai alamun a'a._
_“Jersayn Becelona!...”_
_Umman ya faɗa tana fiddo da jersyn daga jakarta da ta saba fita da ita.
Adawiyya ta daka tsalle ta rungume Umman tana murmushi._
_“Thanks Umma”_
Jin wata ƙwalla na shirin taruwa mata a ido yasa ta yi saurin cilla rigar cikin kayanta, a mafiya yawan lokuta rayuwarta ta baya ba ta faɗo mata sai a sanda ta ga wasu kayanta na da.
A da ba ta da jerseyn sakawa da ta wuce wannan, dan Barcelona shi ne favourite team ɗinta.
Ba ta da burin da ya wuce idan ta girma ta fara biluga ball, har ta kai ga wata rana Barcelona su ce za su siyeta, ta tafi can ta je tana buga musu ball.
Jama'a da dama sun sha mata kallon banza a kan ball ɗin da take da burin yi, kuma ba kowa ba ne illa al'umarta, hausawa 'yan arewa, kamar dai sauran mata, ita ma haka ake fatan ta darƙushe baiwarta ta ja bakinta ta yi shiru.
Saboda ana ganin ba za ta iya ba, a matsayinta na mace, mutane na ganin zaman gida ne ya dace da ita, ita kanta ta san da hakan, amma kuma aure ba shi zai hanata cimma burinta ba, tana san ta zama wata aba a fannin buga ball.
Wata rana ita ma a saka sunanta a jerin ƙwararru, kuma duk wanda zai kira sunan nata dole sai ya kira arewa, domin nanne tushenta, nan ne asalinta.
An sha cewa ba ta da hankali, dan kawai tana san zama 'yar ball, a ganin mutanen arewa ball wasan maza ne, mace ba za ta iya ba.
A da Ummanta ta saka mata a ranta cewa za ta iya, ta ba ta duk wani goyon baya kan ta yi, amma kuma yanzu komai ya tsaya, komai ya wargaje tare da rasuwar Umman.
*DSS (Department of State Service) Headquarter, Maitama Evenue, Abuja*
KULIYA POV.
Cikin takunsa mai ƙarfi yake tafiya, kansa a sama, babu ruwansa da kallon kowa, ciki kuwa harda waɗanda ke gaida shi, kuma suma da alama basu damu ba, don idan da sabo sun saba.
Shi kullum haka yake rayuwarsa, babu ruwansa da kowa a wurin, idan har kai ba a tawagarsa kake ba, to fa shi babu ruwansa da kai.
Elevator ya shiga, wadda ta kai shi zuwa floor ɗin office ɗinsa.
Ya fita daga ciki, kafin ya shiga office ɗinsa, kujerarsa ya ja ya zauna, sannan ya kunna desktop, ya shiga danne-danne.
Kafin bayan shuɗewar wasu lokuta, ya ɗauki wayar land line ɗin dake kan table ɗinsa ya aika kira, kuma kalamai biyu kawai ya faɗi sannan ya katse kiran.
Bayan ɗan wani lokaci, aka ƙwanƙwasa ƙofar office ɗin, gyaran murya ya musu kamar kullum, kafin ƙofar ta buɗe.
Sharon, Abubakar da Symon suka shigo, nuni ya musu da kan set ɗin wasu sofa da ke tsakiyar office ɗin, alamin su zauna a can.
Zama suka yi, a sanda shi ma ya taso daga kan tasa kujerar, hannunsa riƙe da wasu takardu ya zauna a kusa da su. ya shi ga musu bayani akan abun da ya sa ya kirasu.
“Kamar yanda muka riga muka fara wannan binciken, tun farko na sanar muku da rukuni garesu...
Sunan ogansu Tomes, yana da yara shida, sannan akwai mace ɗaya a cikinsu...
Kuma ana zarginsu da fasaƙwaurin miyagun ƙwayoyi, kisa...”
Sai kuma ya yi shiru, yana tauna maganar da zai faɗa ta gaba, dan har wa yau kalmar na masa nauyi a bakinsa, musamman ma idan ya tuna cewa wannan hanyar ita ce silar samuwarsa, ita ce silar zuwansa duniya, ita ce silar raba mahaifiyarsu da farin cikinta.
Wannan hanyar ita ce ta sa bayan rasuwar mahaifiyarsu aka rasa wanda zai bawa rayuwarsu agaji, har ta kai ga ya rasa yayansa, ɗan uwansa, mafi soyuwa a ransa.
Kafaɗarsa ya ɗaga yana ci gaba.
“...Fyaɗe, sai kuma saye da siyarwar miyagun ƙwayoyin...
A halin yanzu na yi magana da Ram, ya na tricking location ɗinsu, kuma daga zarar ya gano inda suke, kai tsaye farmaki za mu kai...
Ko a mutu ko a yi rai!”
Abun da bai sani ba shi ne,wasu lokutan abubuwan da mukan furta su ne ke faruwa, wasu ƙaddarorin kan faru kamar yanda muka ayyana a zukatanmu.
Wannan kalaman nasa na da alaƙa da wata ƙaddara da Allah ya hukunta faruwar ta 'yan lukuta ƙalilan da za su zo.
Wata ƙaddara da za ta tarwatsa komai, sannan ta saita wasu lamura.
A yammacin wannan ranar, bayan lokacin tashinsa a aiki ya yi, yana tuƙi cikin baƙar motarsa ƙirar honda elevate.
Hannunsa na dama kan sitiyari, yayin da ɗayan kuma yake kan bakinsa.
A hankali ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, yana tsuga gudu a motar tasa, dan dama can shi haka tuƙinsa yake, ba ya tafiya a hankali, kuma hakan ne ke sawa suke raba gari idan za su yi tafiya shi da Anna, don haka take cewa; ita tabna san rayuwarta, ba ta shirya mutuwa ba.
Tunanin hakan yasa shi yin murmushi a cikin ransa, a fili kuwa babu komai a kan fuskar tasa, ba fushi yake ba, ba fara'a yake ba, haka kuma ba ƙunci yake ba.
Duk ƙwaƙwaffin mutum ba zai iya tsintar abun da ke kwance a kan fuskar tasa ba.
Kamar daga sama wata motar ɗiban yashi, ta daki motar tasa daga gefe.
Motar tasa ta yi ta dungurawa tana sakewa a kan titin, hakan ya sa ta yi kwatsa-kwatsa tun kafin ta tsaya da dunguwarawar da take.
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
MISHAL POV.
Tsaye take a cikin kitchen, sanye cikin uniform, a hankali hannayenta ke jera kayan abincin da ta gama girkawa a cikin lunch box ɗinta.
Ƙofar kitchen ɗin ta buɗe, Hajjara ta shigo tana mata murmushi kamar wancan karon, kuma a yanzun ma sai da ta tsorata, dan ba ta san da me ta zo ba wannan karon.
Ƙarasowa ta yi gabanta ta tsaya tana mata wani irin kallo.
“Ya akabyi Tsaka?!”
Mishal ɗin ta tambaya, tana maida dubanta kan kayan da take jerawar.
Sunan ya daki gangar zuciyar Hajjara, amma da ta tuna abin da ya kawota sai kawai ta basar.
“Tsaka ba?, za kuwa ki ga ma'anar tsaka”
“Ai babu kalar tsakar da ban ga ba...
Me haɗa mutum da mutum ai tsaka ne Hajjara!... ko babu wanda ya taɓa baki labari cewar kaf tarihi babu wanda ya kai tsaka iya munafirci?”
Ta kira sunanta kai tsaye, kuma tana kallon cikin idonta.
Dan ba ta shakkarta ko tsoronta, tsoron sharrinta kawai take.
“Yaro man kaza...
Ke a tunanin ki za ki iya raba ni da mijina kuma na zauna ina kallonki ?”
Mishal ta ɗan yi murmushi tana harɗe hannayenta a ƙirji.
“Hajjara...
Ke ce kika ɗauke ni a matsayin kishiya, ko da wasa ba na kishi da ke, saboda ban ga dalilin yin hakan ba, na ga kamar jahilcinki na san taɓa miki ƙwaƙwalwa, babu aure tsakanina da mijinki...
Kuma kafin ya fara saninki ni ya fara sani...
Amma ba zan yi mamaki ba dan kina kishi da ni, tun da 'yar da kika haifa ma kin ƙita saboda tana da nakasa...
Me zai sa na ji haushi dan ni kin ƙini?”
A wasu lokutan duk da ƙarancin shekarun Mishal da kuma yarintarta tana da hankali, dan wani zubin takan yi magana ta hankali.
“Wata ƙila daga yau ba za ki ƙara ɗaga yatsarki a fuskata ba...”
Hajjara ta faɗa tana kallonta.
Mishal ba ta fahimci abin da take nufi ba, sai da ta ga ta shiga waige-waige a cikin kitchen ɗin, sannan ta gane me take nufi.
Kuma ba ta ƙara tabbatar da abin da kanta ke gaya mata ba, sai da ta ga Hajjaran ta rarumo wuƙa.
Abubakar na zaune a falo yanawa Daala wasa, sai ji ya yi an ƙwalla wata razannaniyar ƙara, wadda yake jin tana fitowa daga kitchen.
Tsabar tsoratar da ya yi, ya kasa gane ƙarar waye.
Ba shiri ya miƙe, ya nufi kitchen ɗin gadan-gadan.
Ba ƙaramin tashi hankalinsa ya yi ba, a sanda ya yi arba da abinda ke aukuwa a kitchen ɗin.
Mishal ce zaune a kan marbles, hannaunta na dama riƙe da na hagu.
Yayin da tsintsiyar hannunta na hagun ke zubar da jini, sai kuka take tana hawaye.
Dubansa ya kai kan Hajjara dake tsaye a kanta, hannunta riƙe da wuƙa.