← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 80

Sashe 27

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safe, rana, dare, ba ya taɓa tsallakewa, har takai ga Zaid ɗin ya dawo hayyacinsa gaba ɗaya, amma yanayinsa da ɗabi'unsa duka sun sauya, ba ya son yawan magana, ba ya son fita, ba ya son shiga jama'a.

Ya koma rayuwar ƙunci.

Ƙarshe ma ya yanke shawarar barin gidan.

Rana tsaka Malam Ila ya shigo gidan kawo masa abinci amma ya nemeshi sama ko ƙasa babu alamarsa.

Ya ɓata ɓat!

Kamar almara.

Ranar da ya gudu cikin garin kano kawai ya bazama, ya kwana a titi, kafin da safe ya ci gaba da yawatawa.

Har Allah ya kawo shi rumfar wata inyamura me ƙosai, sunanta Ebere, tana da marainiyar yarinyarta Rhoda, da mijinta ya mutu ya bar mata.

Ganinta da Zaid na farko Allah ya saka mata tausayinsa, hakan yasa ta kira shi.

“Menene sunan ka ?”
Ta tambaya cikin gurɓattaciyar hausarta.

“Zaid”
Zaid ya amsa mata kansa a ƙasa.

“Kai maraya ne ?”
Sai ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.

“Ni maraya ne, ba ni da kowa”
Maman Rhoda ta waiga ta kalli 'yarta Rhoda dake zaune a raufar ta na wasa.

“Za ka zauna da mu?”
Zaid ya ɗago da kansa ya kalli matar, sannan ya kalli 'yarta, a take ya ga sun rikiɗa a idonsa sun koma masa Momma da Aliyu.

Ba jayyaya ta amince mata, a ranar tare suka wuni a rumfar saida ƙosan nata, bayan dare ya yi ta ɗauke shi da Rhoda 'yarta suka tafi gidanta.

Gidan ba wani babba ba ne, amma nata ne, kuma mallakinta, ɗaki ɗaya ta bashi tace masa ya yi zamansa, daga yau shi ma ɗanta ne, kuma ba ta hana shi yin addininsa ba, zai iya ci gaba.

Tun daga wannan ranar Zaid ya yi sabin ahali, ga su dai ba musulmai ba, amma sun nuna masa karamci da hallacin da ya kamata a ce 'yan uwansa musulmai ne suka nuna masa.

Maman Rhoda ta mayar da shi kamar babban ɗanta, Rhoda kuma ta ɗauke shi a matsayin wa, sai suka koma kamar 'yan biyu, duk da shi Zaid ɗin ya fita shekaru, amma hatta da kaya iri ɗaya suke.

Maman Rhoda ta saka Zaid a makaranatar su Rhoda, sannan ta biya masa kuɗin shekarun da zai yi har ya gama makaranatar kamar yadda ta yi wa Rhodan ita ma, don tace akwai mutuwa, ba ta son ta mutu ta barsu cikin wani hali.

Kullum da safe Maman Rhoda za ta haɗa kayan ƙosanta.

Kuma tare da su Zaid ɗin take tafiya, idan suka je suka aje mata kayanta a rumfar da ta saba yi, sai su wuce makaranta idan a cikin sati ne.

Bayan sun taso kuma kai tsaye can rumfar tata za su wuce, ba su suke dawowa ba sai rana, idan sun dawo da rana za su zauna su huta, idan suna da wani aikin yi su yi, idan kuma ba su da shi sai su hau aikin haɗa ƙosan yamma.

Yamma na yi za su ƙara komawa, ba sa dawowa sai wajajen sha ɗaya, wani lokacin ma Rhoda tun a can take fara bacci, sai dai Zaid ya goyota su dawo gida.

Zaid ya sake da su sosai, ya na rayuwa cikin farin ciki, dan Maman Rhoda ba ta rage shi da komai ba, ko azumi ne zai zo tana ta ya shi yin hidindumun azimin, kuma duk sallah sai ta masa sabon ɗinki.

Kamar yanda take tafiya da shi can Enugu garinsu idan Christmas ta zo, kuma hatta da 'yan uwanta na can ba sa nuna masa ƙyama, sannan ko da sau ɗaya ba ta taɓa masa tayin shiga addininsu ba, shi ma kuma bai taɓa musu ba, dan ya ga kamar idan ya musu ma bazasu karɓa ba.

Rayuwarsa ta ci gaba da wanzuwa a haka, cikin farin ciki da samun nasarori, kafin giftawar wata ƙaddara, wadda ta tarwatsa komai na rayuwarsu shi da Rhoda, ta yi fata-fata da jin daɗinsu!, Ƙaddarar ta hargitsa komai!.
*Present day...*
RABI'A POV.

Da sassafe ta farka kamar kullum, sai da ta yi sallah, sannan ta gyara alkama, ta kai niƙa, ta ɗauko niƙan, sannan ta haɗawa Habiba kayan suyar funkasonta kamar yanda ta saba.

Kana ta share gidan tas, sannan ta shiga wanka, a lokacin da ta fito har masu siyan funkaso sun fara taruwa a gidan, don Habiban da kanta take soyawa, tun da yau akwai makaranta.

Ɗakinsu ta shiga, ta saka kayanta, ta ɗan shafa mai, sannan ta yi wa Anti Saratu sallama, ta fita.

Yau ta yi mamaki sosai ganin har kusan kwana uku kenan ba ta ganin Mishal a makarantar, ita kuma ba ta santa da wata ƙawa ba bare ta tambayeta, wannan baturiyar ma da ta saba ganinsu tare ba ta san inda za ta sameta ba.

Hakan yasa tunanika sukai mata yawa, ta shiga saƙe-saƙe kala-kala, har zuwa lokacin da aka tashi.

Kuma kamar yanda zuciyarta ta raya mata, kamar yanda ta saba ganinsa.

Tana fita idanuwanta suka sauƙa a kansa, jingine jikin gate ɗin estate ɗinsu, sanye cikin wasu ash jogger set.

Hannayensa sanye cikin aljihun hoodie ɗin kayan, sai dai saɓanin kullum, yau ba shi kaɗai ba ne, shi da wannan budurwar ne, wadda ya kira da ƙanwarsa, sanye take ita ma cikin irin kayan jikinsa, hatta da takalmansu iri ɗaya ne.

Kamar yanda suka saba a kwannakin hannu ta ɗaga masa, hakan yasa Rhoda ta juya ta kalleshi, sannan ta kalli Rabi'an.

Bisa ga mamakinta sai ta ga Rajan ya sha mur, ya na bin bayan Rabi'a wadda ta fara tafiya, sai kawai ta yi murmushi ita ma ta bi bayansu.

“Me ya same ki yau ?”
Raja ya tambaya, ganin yanayinta ba kamar yanda ya saba ganin ba, Rabi'a ta ɗago ta kalleshi, sannan ta kalli Rhoda dake biye da su, ganin hakan yasa Rhodan ta ɗauke kanta sama tana fito, sannan ta ƙara da.

“Ni fa ba na jin komai...”
Raja ya tsaya, sannan ya waiga ya kalleta.

“Da ma biyoni kika yi ?”
Ta girgiza kanta.

“A'a fa, ni saƙo zan je na karɓo a nan bakin titi”
Raja ya finciko hannunta yana kama kanta ya matse, hakan yasa ta saki ƙara.

Duk abun da suke Rabi tsaye a gefe tana kallonsu.

Sai kuma ya dafa Rhodan, sannan ya yi wa Rabi alama da su ci gaba da tafiya.

Tafiyar suka ci gaba da yi, Raja na dafe da kafaɗar Rhoda.

Ya ɗaga kafaɗarsa sannan yace.

“Baki amsa ni ba Ammata”
Ko kafin ta ba shi amsar Rhoda ta yi wuf tace.

“Ammata?, What a wonderful name!”
Raja ya kama kunnenta ya murɗe, hakan yasa ta saka ƙarar azaba.

“Raja mana!”
Ta faɗi a shagwaɓe.

“Ammata manta da wannan yarinyar, neman magana take”
Sai faɗan nasu ya bawa Rabi dariya.

“Kwana biyu kenan wata ƙanwata ba ta zo ba shi yasani a damuwa!”
“Gidan ku ɗaya ?”
Rhoda ta tamabaya daga ɗayan ɓarin, Raja ya ranƙwashi kanta daga sama, kasancewar ya fita tsayi.

Ta dafe wurin tana turo baki.

Rabi'a kuwa sai murmushi take.

“Ki kwantar da hankalinki Ammata, lafiya ita ce ke ɓuya, da yardar Allah tana cikin ƙoshin lafiya”
“Kawai ki manta”
“Rhoda hoo!”
Raja ya faɗi yana ƙara dukan kanta, ta ƙwace kanta, sannan ta koma layin da gudu, tana faɗin:
“Kada ki dumu Ammata!

She dey fine oo!”
Daga Rajan har Rabi'a sai da suka yi dariya.

Tafiya sukaci gaba da yi suna 'yar hira, har suka iso bakin titi, kamar kullum haka y tsaidamata ta hau, har suka ƙulewa ganinsa ya na ɗaga mata hannu.

Kamar daga sama ya ji muryar Rhoda daga bayansa.

“Hooo!, Raja ya kwarewa soyyayar me kama da shi...”
Juyawa ya yi ya kalleta, tsaye take a bayansa, kenan dawowa ta yi?.

“Ki bari na zo na sameki a nan”
Ya yi maganar yana nufar inda take.

Rhoda ta fita da gudu tana dariya, shi ma ya bi bayanta yana dariyar, har ya cimmata, kafin ya riƙe kumatunta yana ja.

“Ke ba kya jin magana ko?”
Rhoda ta dafe wurin da ya ja mata tana kumburo baki.

“Ayya mana Zaid, wannan ai mugunta ce ”
“Ni ne mugun?”
Ya faɗi yana ƙoƙarin ƙara kamata.

Ta kuma saka gudu tana dariya.

“I'm sorryyyyy!”
Ta faɗi tana kama kunnuwanta, a sanda ya kuma cimmata, sai ya dafata kamar ƙawarsa, suka jera suna tafiya.

Har suka koma gidansu.
*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja.*
“Assalamu Alaikum...

Karima!”
Muryar Anna ta faɗi, yayin da wayarta ke kare a kunneta, bayan da ta aikawa Karima yayar Siyama kira.

Daga cikin wayar muryar Karima ta amsa da.

“Wa Alaikumu Salamu, Na'am Anna, ya kike, ya gidan ?”
“Lafiya ƙalau Karima, ya Siyama da yaran, da kuma me gidanki ?”
“Suna lafiya”
“To da ma so nake dan Allah ki kira mijin naki ki sanar masa da cewar ina son ganinki, idan xai iya miki lamuni”
Karima ta ɗan yi jim, kafin ta amsa da:
“Ba damuwa, Insha-Allah zai bari, amma Lafiya kike nemana Anna ?”
Anna ta ɗan shafo gefen fuskarta, sannan tace.

“Lafiya...

Ban faɗa muku ba ne, An ɗaurawa Kuliya aure, kuma yau za mu je mu ɗauko amaryar, su Laraba ma duk na kirasu, dan haka kema sai ko taho...”
Tsabar razanar da Karima ta yi sai da ta miƙe tsaye, hannunta kan ƙirjinta wanda ya shiga bugu da sauri.

“Aure kuma Anna!, Kuliyan ?!, Shi da wa ?!”
Sai da Anna ta ɗan yi shiru, kafin ta amsa mata da.

“Wannan ba huruminki ba ne, matar Aliyu kuma idan kin zo za ki ga ko wacece!...”
Daga haka ta sauƙe wayar.

Ɗazu da safe Kuliya ya zo yace mata kawun su Abubakar yace tun da jiya aka yi bakwai ya zo ya ɗauki matarsa yau.

Kuma su yake so su je su ɗaukota.

Shi yasa ya zo ya sanar da ita.

A lokacin kallonsa kawai ta ci gaba da yi, ganin yanda ya rame, ya yi wani irin baƙi, kamar wanda ya tashi daga jinya.

Kafin ta daure ta tambayeshi shirin da ya yi domin bikin.
Chapter 27 · 0% Book details