← Book details Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 80

Sashe 65

Labarinsu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

I love all of you!”
Kalamansa ba ƙaramin tasiri suka yi a zuciyar Rabi ba, don tsabar tasirin da suka yi, Rabi'a ba ta san sanda ta ɗago da hannyenta ta ɗora su a kan bayan Zaid ba, ta na ƙara ƙanƙameshi a cikin jikinta, tare da ƙarawa kukanta sauti.

Sai de kuma cikin sakan ɗaya...

Biyu...

Uku...

A cikin na ukun ta yi sauri ta tureshi, saboda wannan fuskar tasa da ta hango, fuskarsa a lokacin da ya harbi wani bawan Allah.

Da sauri ta miƙe da gudu ta bar kitchen ɗin.

Ɗakin da yake a matsayin nata ta faɗa tana bankowa ƙofar.

Tare da jingina a jikin ƙofa, ta silale ƙasa tana fashewa da kukan da ba ta san daga ina yake fitowa ba, ƙafafunta ta takure a jikinta tana sunkuyar da kanta cikin kuka.

Ita da Allah zai ɗau ranta ma da sai abun ya fi mata sauƙi, ƙaddarorinta suna da tsauri, ga su kuma a laye, wata kan wata.

Har ta bar kitchen ɗin kan Raja a sunkuye yake, da ƙyar ya samu ya ja da baya zuwa jikin cabinet, ya jingina da ita, sai sauƙe numfashi yake da sauri-sauri.

Zai iya cewa a karo na farko kenan a rayuwarsa da ya yi nadamar shiga aikin DSS, wai me ya sa?, me ya sa komai nasa akan soyyayar Adawiyya yake da wahala haka?, ya tabbatar ba dan wannan aikin ba, da ba za ta ganshi ya harbi wani ba, da ba za ta ƙishi tana masa kallon makashi kamar haka ba.

Duk sai ma ya ji ya tsani rayuwar, ji yake kamar kansa na tiriri.

Cike da fusata ya ɗaga hannunsa na dama ya na dukan cabinet din dake bayansa.

Ya gaji, dole ne ya ƙarƙare aikin nan cikin wannan satin, dole ya kawo ƙarshen komai.
*
Rabi'a na zaune a falo tana kallo.

Jin wani sauti me kama da ƙaran kiran waya ya sa ta juyo ta kalli ƙofar ɗakin Zaid.

Mamaki ne ya kamata a sanda ta fahimci cewa tabbas, sautin kiran waya ne ke tashi daga ɗakin, to be fita ba ne ko kuwa?, ita de ta san sassafe ya fice daga gidan, amma kuma yanzu ga ƙaran kiran waya ta na ji, duk yadda aka yi manta wayar ya yi.

Bakinta ta taɓe tare da juyowa ta ci gaba da kallonta, jin sautin kiran wayar na ƙara tashi ya sa ta ƙara waigowa ta kalli ƙofar ɗakin nasa.

Ko de wani abu ne yake faru?

Ta tambayi kanta a sanda take miƙewa.

Ɗakin ta nufa.

Sai de bisa ga mamakinta ba ta ga wani abu mekama da waya a ɗakin ba.

Har ta juya za ta fita, ƙaran kiran wayar ya ƙara dakatar da ita, hakan ya sa ta juyo ta shiga bin inda sautin ke fita.

Can cikin loka ta ji sautin, don haka ta buɗe lokar, sai ta yi arba da wata kalar waya da za ta ce bata taɓa ganin irin ta ba.

Har zuwa lokacin wayar na ringing, hannun ta kai ta ɗauki wayar, amma kuma babu lamba bare suna.

Gaba ɗaya ta riga ta gama shiga duniyar mamakious, wani irin abu ne haka?.

Ɗaga kiran ta yi, tare da kara wayar a kunnenta, shiru ta yi ba tare da tace komai ba, kuma daga ɗayan ɓangaren ma sai ta ji shirun, hakan ya sa ta yi ƙoƙarin sauƙe wayar, sai kuma ta tsinto wani ɓangare na Zaid, wani ɓangare na gaskiyar sa da take tutiyar ta sani, wani ɓangarensa da ɗai-ɗaiku ne cikin mutane kawai suka sani.

“...Lion, umarni ya zo daga sama, duk yanda za ka yi ka yi don ka kawo ƙarshen wannan aikin, oga yace ba zai iya jira sama da haka ba, saboda haka sai ka san yadda za ka yi dan ka miƙo duka hujjojjin da ka haɗa!...”
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
ZAID POV.

Zaune yake a kan kujera ya na facing Rhoda, wadda ke daddana system ɗin dake kan cinyarta, hankalinsa rabi na kanta rabi kuma na ga wayar da yake ta jira, dan kuwa a jiya ya aikawa da office ɗinsu saƙon yana san magana da ogansu, ya san da cewa a yau ɗinnan za su kira, amma kuma ba zai iya jure zaman gidan suna cikin wannan halin shi da Adawiyya ba, ba zai iya zama a gidan ta na gudunsa ba, gwara ya ba ta space, ko ta samu damar sararawa a gidan, ina yado bayan ya koma sai ya amsa kiran.

“Dude!...

Zo ka gani!”
Cewar Rhoda, mamaki mamaye da fuskarta, idonta kyar a kan system ɗin gabanta.

Da sauri Raja ya miƙe ya dawo gefenta ya na kallon system ɗin.

A jiya suka samo putage na CCTV camera ɗin dake layin da aka cillar da Adawiyya bayan da aka haike mata, ba ƙaramar wahala suka sha ba kafin suka samu putage ɗin, sannan kuma suna da tabbacin putage din shi ne zai kaisu ga karshen binciken da suka fara.

A tare suka juyo suna kallon juna shi da Rhoda, bayan da vedion ya kai ƙarshe.

“Usman?!”
Rhoda ta tambaya tana dubansa.

Nan take idon Raja ya kaɗa ya yi ja, babu abun da Rhoda ke iya hangowa sai wutar masifa da tashin hankalin dake ci a cikinsu.

“Ba zan barsu ba!...”
Ya faɗi ya na miƙewa, da sauri Rhoda ta kamo hannunsa tana maida shi inda ya miƙe.

Kai ta shiga girgiza masa alamin a'a.

“Zuwa yanzu case ɗin ya zama biyu Zaid...

Ka fara miƙa hujjojji game da Alhaji Bala tukunna, idan an bamu izinin kamu, sai mu haɗa mu kamasu su duka!”
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga ya na cije leɓensa na ƙasa.

“Kin tabbatar da haka ya kamata a yi?”
Rhoda ta gyaɗa masa kai cike da tabbatarwa.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State.*
Habiba ce zaune a tsakar gida ta na dunduma jikinta da ruwan ɗumi, kwana uku kenan da aka sakota daga hannun 'yan sanda, kuma dukan da ta ci a hannunsa ne har yanzu be bar jikinta ba, dan ta doku ba ƙarya.

Ita ta yi ma mamaki da suka sakota da wuri haka, duk da shi Ɗan Lami ma ko kwana be yi a wurinsu ba.

Sallamar Saratu ta ji daga bakin ƙofa, hakan ya sa ta juya ta na kallonta.

“Sannu Umma... jikin ne?”
Habiba ta gyaɗa kai tana matsa ƙafarta.

“Amarsu kenan, daga ina kike ne?”
Habiban ta tambaya kamar ba ita ba, a sanda Saratun ta karɓi ƙyallen hannunta ta shiga dunduma mata jikin nata.

Saratu ta yi murmushi.

“Gidan su Farida na je, zuwa gobe za mu fara rabon cingam”
Habiba ta gyaɗa kanta, zuwa yanzu ta fara shiga hankalinta, ta fara gane gaskiya da akasinta, a jiya Saratu ke faɗa mata cewar wai Rabi ta yi aure, kuma wannan me kamar tata ne ya aureta, sai kuma ganin nutsuwar da Ɗan Lami ya fara yi, ita ma ta sa ta shiga taitayinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne, dan kuwa ga shi dai duk wannan abubuwan da ta yi ta yi, ba su hana Rabi auruwa ba, kuma duk wannan makirce-makircen da ta yi ta yi, ba su hana ikon Allah faruwa ba.

Wata sallamar suka ji cikin wata murya me kama da ta Mama, cikin sauri kuma a tare suka kalli ƙofar gidan.

Sannan cikin daƙiƙa ɗaya suka miƙe a zabure.

Kallonta suke suna san su gane wacece.

“Ni ce Umma, ni ce Mamanki!...”
Cikin kuka Mama take faɗin hakan, tare da sakin jakar hannunta, hannu na karkarwa Habiba ta nuna Maman dake tsaye a gabanta.

“Ma... mama...

Mama!”
Tsaye take a gabansu, jikinta ɗauke da cikin da ya fara fitowa, ga wasu ƙuraje da suka bai-baye mata jiki, ta wani kalar rame ta ƙwanjare, ta yi baƙi ƙirin da ita.

Allah kenan, za ka yi ta saɓa masa ya na ara maka dama, rana ɗaya kuma idon ya tashi kamaka, sai ka gwammaci ba a hallici me kamarka a duniyar nan ba.

Domin kuwa shi ya fi kowa iya kamu.
*Don't be afraid to lose people.

Be afraid of losing yourself by trying to please anyone around you*
***
*No.86, Garki 2, Abuja...*
RAJA POV.

A hankali ya turo ƙofar shiga falo, bakinsa ɗauke da sallama.

Cak ya tsaya, sakamakon ganin Rabi tsaye a tsakiyar falon, hannayenta harɗe a ƙirjinta, ta kafe shi da wani irin kallon tuhuma, duk wata ƙwarin gwiwa da ya zo da ita dan ya mata wasu tambayoyi game da abun da ya faru da ita sai ya ji ya gushe, kallon da take masa yana ƙarasawa ya ji ya muzanta, don ita ba ta kallonsa a matsayinsa miji gareta ko yaya, kallo take masa a matsayin ɗan daba, kuma makashi.

Wani yawu ya haɗiya, sannan ba tare da yace mata komai ba ya ɗauke idonsa a kanta ya shiga ƙoƙarin nufar ɗakinsa.

Sai de me?, tsulum ya ganta tsaye a gabansa, ta na ci gaba da kallonsa cike da tuhuma.

“Waye kai?”
Tambayar ta doka wata ƙatuwar ganga me amon gaske a cikin kan Zaid, ya kafeta da idonsa, amma ya kasa ce mata komai.

“Zaid!

Waye kai?”
Yawu ya haɗiya ya na faɗin.

“I'm a goon!”
Kanta ta girgiza tana sauƙe hannayenta daga ƙirjinta.

“I mean real you...

Waye kai!”
Ta kuma maimaita masa tambayar, hakan ya saka zuciyar Zaid cikin kokwanto, to me take nufi da waye shi?, ko de ta gano wani abu a kansa ne?, ina ba zata gano komai ba.

Dan haka ya haɗiye yawu yana faɗin.

“I am a killer and drug trafficker.

I'm goon”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga ta saka hannayenta ta kewayasu ta bayansa tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa, sosai rungumar ta ba shi mamaki, idonsa ya lumshe sannan ya buɗe, kusan shuɗewar muntuna biyar, kafin ta sake shi tana kallon fuskarsa.

“Akwai wani rubutu da na taɓa karantawa.

A rubutun an ce, idan har ka rungumi mutum na tsawon muntun biyar, to za ka fara yarda da duk abun da zai ce, amma har yanzu ni ban yarda da kai ba.

I will ask you for the very last time...
Chapter 65 · 0% Book details