Sashe 98
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zance in wanke in shanya ba ataba min shi ba a gidan haka kuma gugan su ma aiki zai zamo min. Kafin in kwanta saidana jawo computer dina nayi aiki a cikinsa da komai na gyara inda nake da kuskure banson inzo ranan friday ina inda inda gaban mutane. Lokacin basira ta lekoni tana fadin dazun naga an gyara muna kitchen fes akace kece kikayi aikin nace eeh kinsan mun saba da aiki a gida tace hakane . Nama kawai naci sai drinks dana sha na ajewa budurwan da bansan sunanta ba har lokacin sauran abincin na kwanta. Washe garima dai kamar jiyan na riga kowa tashi na wanken bayin da Izzal na kowa dettol na zuba sanan nayi wanka tare da alwala na fito. Ranan ma na danyi masu shara don kitchen din baiyi wani kazanta sosai ba na fito na shirya zuwa wajen aiki abina basira din ma bata ko fito ba a lokacin balle mijinta. Ranan alhamis daine koda naje security din ma,aikan sukace wai sai na kawo ID card dina sun gani na mika masu tun a nan na fara samun matsala. Duk inda nabi idone yasa na tsargu ina tunanen ko nayi wani shigan banzane kuma nidai nasan bujene da riga na lece a jikina sai dan gyale pink kalan fillawan lace dake jikina da wasu half cover masu kala daya da gyalen sai dan jakka karami shima pink mai sarka ba belt ba na dan rataya a kafadana. Hakana dana shigo office din mu na samu kowa yazo lokacin don na tsaya laundry na bayar da wankin uniform dina da kayan barcina a ranan hakan yasa na dan makara. Oga thomas yana duke yana faman aiki a computer office ya dan juyo yana amsa min ya mayar da kansa sai kuma naga ya sake juyowa da sauri ya sake kallona karo na biyu. Kansa a kasa yace miss Aisha is that you ? Nace yes sir na waw woo so is the uniform that hiding you before na kalli abokan aikina da suma kallon nawa sukeyi a lokacin . Sai kawai na tsargu na samu waje na zauna ina fito da laptop dina da ranan na fara zuwa dashi office din tunda na bude gaba daya hankalinsu ya dawo kaina. Enkechi ce farkon fadin ewwerr Ayasha na you get this laptop wanan fa bai shigo kasan ba tukun last month akai lunching dinsa. Hankalin mr Thomos din ya dawo a kaina yana fadin unbelievable you this Aisha you hinding something for us nifa na fara tsoron ki yau ? Tsoro kuma na fada yace duk zaman mu office din nan kusan kwana nawa sai yau din nan muka san kalar ki haka kuma kinzo muna da abin mamaki tare dake da yawa. Nan dai akai wasa da dariya na mika masa laptop din ya shiga ya fita yana mamakin akan kyawonsa. Tunda suka fita zuwa break nake ganin manyan mu suna shigowa suna fita office din nidai ina duke ina faman tura bayanaina a cikin computer din. Barka da aiki hjy aka fada a bayana hakan yasa na dago ina sawa da yauwa sannu don jin maishi yayi min hausa kai tsaye a lokacin. Idona ya sauka kan MD din wajen da sauri na tura computer din gaba kadan na mike tsaye ina sake gaidashi ya amsa tare da matsowa table din nawa yana fadin. Ba mamaki wani nakine a waje ya saya maki wanan simple din duk da bamuyi zaton ganin wani dashi ba nan kusa sai gashi yanzu nake jin angasa a hannuki kina amfani dashi. Kaina kasa nake fadin daga U S aka turo min shi da zanzo nan hannu yakai a hankali yana duba system din na dan lokaci ciki har baya kafin inji yace. Gaskiya hakan yayi kyau sosai wallahi saiki maida hankali ga koyon aikin yadda ya dace zamuyi alfahiri daku sosai don matan mu na arewa basa son yin course din nan amma ke gashi naga kin dauki abinda muhinmanci sosai Allah ya bada sa,a. Nagode Sir na fada yace ba matsala daga kano kike ko na amsa da ehh sir amma kamar ke ba ,,,,,,sai kuma yayi shiru ya dora da fadin anyway indan dai da matsala zaki iya samuna you are wellcome anytime . Nagode na kara fada yayin da lokacin mr Thomos ya dawo office din sai kuma ya tsaya wajenshi suna magana dashi kafin ya fice daga office din. Ajiyan zuciya na sauke ina kokarin kaiwa zaune naji mr Thomas din yace kiyi hakkuri fa bawai tsegumi na kai ba na fada masune ko za a samo muna irinsa a nan. Ba komai sir na fada naci gaba da abinda nakeyi sauran suka dawo mukaci gaba da abinda mukeyi akwai wata Meenat dake yawan shigowa office din mu daukan bayanai. Wata mai jiji da kai haka irin wayayyu din nan dai itace ta shigo a karshe take tambaya wacece kake zancenta dazun ? Ya nunani can karshe ta dan kalleni tace wanan ne new product din da yake fada kafin in bata amsa khalid yace no gashi nan ta aje ya zagayo yana nuna mata ta jima tana kallo harda dauka hoto tayi tagama kaudinta ta fita. Lokacin sallah nayi na mike na fita zuwa mosque din mu inda na samu ba kowa a sashen matan hakan ya bani daman aje kayana don inyi alwala . Ina duke ina alwala suka shigo su biyu daidai ina shafan kai naji wace suke tare mai dan shekaru tace tubarkhalla masha Allah. Hakan yasa na juyo ina kallonsu ni dai suke kallo a lokacin ban fasa alwala naba na gama na mike don zuwa sallah lokacin suka shiga yin alwala su kuma. Hijjab dina na sallah na fitar na tayar da sallah koda na sallame na dan bude jaka na dauko mai ina shafawa kafana karya bushe. Naji wanan matar data idar ta kura min ido tace don Allah yar uwa in tambaye ki yasa nace tambaya mana anty a cikin hausa na bata amsa. Ke yar inace wai nace kano ikon Allah har da iyayyenki a kano suke nace ehh baba dan kano ne tace gaskiya da bake kika fada min ba sai ince ke balaraniyace. Kai na girgizs nayi murmushi ta sake fadin kunne wa yanda sukazo traning ko nace eeh ina kokarin mikewa don ina son biyawa in sai wani abinci nashiga dashi. To yar uwa baki fada muna sunanki ba zaki wuce nace Aisha amma da Aeesha ake kirana a gida nagode kada in makara na fada suka bini da kallo. Restaurant muka haduwa da Enkechi tare l muka jera muka koma department din mu muna hira take fada min tana son dress din mu na hausawa amma matsalan bata iya sakawa ta dade dashi a jiki. Amma baida matsala kafinta koma zatayi kokari ta dinka ko kala biyune ta gwada ta gani take fadin kayan sunyi min kyau sosai wallahi . Nadago ina mata godiya naga wasu tawagan manyan mu zsu shiga office din gagawa da sauri take fadin inama ace tana cikinsu nace ta roki Allah dai ya bamu sa,an karatub mu a yanzu. Mr Thomas baya office din hakan ya bamu daman zama yin hira na bude abincin na bada baya zakice bafulatan dajine yadda na juya daga garesu ina cin abincin. Ya jima baidawo da ya dawo kuma ya sallamemu take fadin in rakata kasuwa don Allah nima ina son zuwa don haka muka garzaya zuwa kasuwan . Abubuwa da dama nagani da nakeso saidai ba halin saya a yanzu don kona saya din zasu zamo min wahala don kayana ma a gidan yaya a rabe suke gefe daya. Don haka banyi sha,awan sayo wani abu don kaina ba nadai sayowa Amira kayan masu kyau da teddy na yara. Sai kayan kamshin gida dana sayo tare da kayansu fresh tomatoes daya ban shawa har nama da ice fish na kwaso donshi taje saya a wuse market. Saboda ita haya aka kama mata a wani side nan cikin girki mota daya muka shiga muka fara sauketa don motan gaba daya muka dauka sai ni yakai har kofa a karshe. Falo na samu madam Basir zaune da kawarta suna hira nashigo da sallamana Amira na ganina tasheko da gudu ta rungumeni . Gaidasu nayi da gida kadin na nufi kitchen dinsu na aje kayan dana sayo masu din don ganin bakuwar muka shige daki nida Amira da dayan ledan. Ina jin matar na tambayanta a cikin hausa da wanan fa tace sister din mijinane tazo pratical daga kano take zaune damu. Uwarsu dayane tace a,a not the same father ma kawai dai a family din take humm amma kina da sakaci maman Amira shine kika yarda ta zauna maki gida ? Meye halan iya abinda naji kenan muka shiga dakin ina fadi a raina wai gida gidan kazanta shine har ake tambaya ta yarda na zauna kome ? Har na sauya kaya Amira na dakin tare dani don kafin na dawo tayi barci idan zan fita kuma lokacin bata tashi a barci ba. Banyi na shiga na wanke kafin na fara sharan gidan lokacin matar tayi sallama ta fita sun dade a waje tare da matar kafin ta dawo cikin gidan. Sai lokacin naba Amira kayan dana sayo mata ita kuma nace madam yau kasuwa muka shiga nina rasa abinda zan sayo maki shina na kwaso maki wanan. Saiga Amira din da nata tana nuna mata tace wai,wai,wai ashe yau ba barci a gidan nan abinda takeso ke nan daddy ta ya hana a sayo mata. Ta karbi ledan yarinyar tana budewa taga riga maikyau ta bude na juya naci gaba da aikina saida nayiwa gidan fes kafin yan uwanta su dawo na saka kamshi ko ina. Sai can naji tana fadin ashe ke ba karamin sayaya kiyo muna ba to angode ta fada ta kara shigewa kitchen din nagama nayi alwalana kafinsu dawo su bata gidan nagama nashige daki ban kara fitowa ba kuma sai washegari.