Sashe 15
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammah naji tana gani haka ta tafi wanan sha,anin ta barni duk da bata so hakan ba amma ba yadda ta iya tunda na kafe akan ba zanje ba yasa Abbu yayi mata fada sosai akan matsa min din da tayi a lokacin. Taso zuwa dani din ne tayi kwanakin da take sonyi acan din sai naki zuwa dole yanzu in angama ta juyo don hankalinta ba zai kwanta ba a can din ni ina gida. Gashi a can din kuma yara da manya suna tambayanta ina Aeesha maman Aeesha saita labe da cewa bata zo dani bane don ana makaranta don hakane ta barni gida. Sai kuma bata samu kan ita uwar bukin ba a wanan karon don uwar bukin kowa yana complain din fuskanta a daure yake lokacin sha,anin yasa an gama buki washe gari karfe biyu sai ga Ammah din ta shigo gida dawowana ke nan daga school ina zaune ni kadai a tsakar gida nayi tagumi ina faman tunanen duniya ta shigo. Na mike da fara,ara ina taron ta itama fuska a sake da murnan ganina ta rugumeni yadda nayi mata na dauki kayan ta nasa daki kafin in firo in karbo mata ruwa na kawo mata tasha. Tun a nan ta fara bani labarin kan bukin tana fada min abubuwan da suka faru inda ta dora da fadin ai gara da bakije bama Aeesha . Saina koma ban ganin laifinki kuma na matsa makin da nayi sai muje tare don muma da mukaje din munyi dana sanin zuwan tunda damu da babu mu a wajen uwarsu daya. Ke bari yar nan hjy ta ban mamaki wallahi matuka don banyi zaton hakan a wajenta ba sai lokacin na bude baki nace Ammah kuma ke nan balle ni da duk da sun saba ganina amma haka zasu samin baki da ido suna tambaya a kaina wanan yasa ban son shiga mutane yanzu wallahi. Budan bakin Ammah din tace aiko sai ki zama kofin rijiya don ko mutane haka su a ko ina da saka ido kan abinda bai shafesu ba yanzu. An daiyi bidiri kan gaskiya an kumaci an sha gaskiya tubarkallah wallahi don buki yayi kyau amarya kuma sun iso tun jiya daga yola. Shima Allah mai tangaram ance nan da wata ukkune bukin yayansa anma so a hada da wanan gidan iyayyen ita wanan yarinyar suka matsa ayi don su sun shirya sukace. Na dago ina fadin gidan su anty mami ke nan tace aisu mami din nake jin za aiwa auren ko kuma dai bada ita ba amma dai cikinsune su ukkun . Allah sarki sun karasa karatun nasu ke nan nidai suna birgeni wallahi don babu ruwansu da daukan kai faran faran dasu ko wani lokaci. Amma ita wanan da akace yar matarsa na yanzun ce itakan saboda itace ma banson shiga gidan su wallahi. Keko ai dole tunda uwata ke mulki a gidan su uwarsu ta rasu tun suna kanana shine ya auro hjy Binta din itama ta dinga haihuwa kamar tururuwa masa. Dariya zancen ya bani har yasa na dan murmusa ina fadin kamar tururuwa kuma tace ehh mana kin san mu mata ai wani lokaci kan kishi kishi ma harda wanda bai duniya in aka hadu da marasa tsoron Allah sai kiga anyisa ai. Mun kai wani lokaci a wajen zaune muna hira saida akai sallah la,asar ne muka shiga daki bayan mun fito ne ina shirin islamiya tacigaba da min hiran. Don nice dai abokiyan hiran Ammah din a gidan don Abbu ba zama yakeyi ba ko yaushe kasuwarshi yake zuwa yaci sai yamma yake dawowa gida ko yadawo din kuma yana waje gun abokan hiransa suna rage dare a wajen. Ankai wasu yan kwanaki aikin ke nan bada wanan labarin bukin a bakin Ammah din duk da tace an masu wullakanci hjy ta nuna kamar bata sansu ba wanan karon amma kuma tana yaba kyau bukin. Jerabawan mu na karshe yazo haka muka zanashi cikin yardan Allah muka koma kuma zaman gida zaman jira jin sakamakon daga Allah don jerabawa dai irin wanan dacene sai wanda Allah yabawa sa,an cinyeta yake hayewa. Duk wanan zaman dakon kuma da mikeyi ban taba jin Abbu yayi min maganan makarantana ba da yaimin alkawarin karasawa gaba a lokacin. Niko zamcen yana a kasan raina don gaskiya ina sha,awar karatu nikan a rayuwanta duk da nasan iyayyena basu da halin hakan don karatu na masu karfine. Ga zaman gidan dana sawa kaina a yanzu ya fara isata nima banda wajen zuwa sai dan aiken daba,a rasa ba da nakan jewa Ammah a makwabta shine kadai zance yana sani fita. Gashi kamar kada ace na kare karatun nan wani irin girma yazo min a lokacin halittana na asali ya kara baiyana a fili sosai har yasa idan zan fita a yanzu na tsiro saka nikaf a fuskana don bat da kamana saboda ido akaina yake ko wani lokaci nake gani. Ranan na dawo daga islamiya wajen hadda na samu Abbu a gida nayi mamaki kwarai haka kuma a yadda na sameshi yana dauke tabarma da buta da kofin ruwa yasa nagane yayi bako a lokacin. Don gaskiya ba lokacin dawowanshi bane a lokaci haka kuma dana shiga gidan na samu yanayin Ammah acikin damuwa zan ma iya fadin har kuka tayi a lokacin haka kuma gata saye da hijjabi a jikinta yasa gabana kara faduwa. Saidai banyi magana ba bayan gaisheta daki na nashiga na aje jakata na dan jima ban fito daga dakin ba sai can naji Abbu ya shigo daga baya sun shiga daki suna zance kus kus kus a tsakaninsu. Duk da kasa kunnen da nayi don in fahunci kome ke faruwa ban gane komai ba cikin zancesu hakan yasa nima na koma sukuku a ranan. Ban taba kawo zancen Nana ba araina lokacin yo ina zan kawota ma kusa matarda ba wanda yasan ina ta shiga ko a saudiyan zanyi zaton daga wurinta hakan ya fito. Wai asheko itace tayowa su Abbu sakon kudi masu yawa a lokacin kuma mai sakon yazo da albishir din cewa tana nan lafiya a wani gari tana aure har ta haifi yara biyu a lokacin shi shedan hakane don sun jima dasu a cikin masallaci a madina a nan suka hadu dashi har ta yaba da hankalinshi mutumin ta yarda ta bashi sako zuwa wajen iyayyen nawa na yanzu. Wanan yasaka Ammah kuka a lokacin don jin labarin yar uwarta da kuma tarin sakon data bashi yazo muna dashi abin mamaki kuma shine. Ita tana da labarinsu su daine basu da nata a yanzu amma har inda suka koma ta sani don itace tayowa mutumin ma kwatancen gidan namu yazo. A yadda mutumin ke fadi ita nana din a yanzu tayi karfi a can itama don tana business dinta tana samun kudi sosai yadda ta bashi labari har ya bukaci ya ganeni akace dashi ina islamiya. Bayan fitan Abbu gidan kawai ina bakin murhu ina hasa wuta naji Ammah ta saki wani irin kuka daya tayar min da hankali lokaci guda har bansan sanda na fada dakin ba a razane cikin tashin hankali. Wurin Ammah din dake durkushe ta zubawa wasu kaya idanu na nufa ina tambayanta a gigice da Ammah waya mutu meya faru anyi wani abune ? Duk lokaci daya nake wanan babatun cikin tashin hankali a gareta kafin idona yakai ga kayan dake gabanta a take zuciyana yayi wani irin ras ras a wajen . Hakan yasa nakai durkushe a hankali ina bin kayan da kallo da ido abinda ya fito bakina lokacin shine Nanace ko Ammah ? Wani irin kallo Ammah din ta watso min a lokacin sai kawai na mike na fice daga dakin lokaci guda cikin karfin hali na nufi wajen aikin dana soma naci gaba ba tare dana sake waigen dakin Ammah din ba kuma. Fitowanta cikin mamaki yayi daidai da shigowan Abbu gidan dauke da kayan cefanen daya sawo muna na dago da idanuna da sukai ja ina masa sannu ya amsa da fadin dama nasan haka Nana ina sauri da Allah Allah karkiyi talge kafin na karaso. Kayan da Ammah ta karba a hannunsa nabi da kallo da dan buhun daya nuna abincine a cikinsa daya aje gefe daya sai kuma na kawar da idona da sauri akan kayan na juya zuwa aikina ina jin Ammah na fadin malam zo nan ya bita zuwa daki. Abbu bai karasa shiga dakin ba Ammah din ke fadin yau naji abin mamaki a bakin yarinyar nan da sauri ya juya ya kalleni yaga ina gyaran wuta ya juyo gareta yana fadin meya faru kuma ? Tayi ajiyan zuciya mai nauyi ta sake kafin tace sunan uwarta naji ta ambato min a bakin ta kamar a mafalki fa malam da cewa Nana ko ? Dan murmushi yayi kafin yace kin dauka duk tsayin nan bata san komai bane ta sani tasan komai game da uwarta don har hotonta ta gani a dakin nan ai ranan. Kirji ta dafe tana fadin na shiga uku malam garin yaya haka ya faru yace ban san ya akayi ba amma ta gani ta kuma san komai zaune takai saman dan gadonsu na katako lokaci guda tana dafe kai. Wai meye hakan data sani tayi wanin abin asshane a gareki ki natsu kibi yarinyar nan a yadda ta bimu ban son tashin tashin da zai kawo bacin rai a yanzu kuma. Hakan bai sa Ammah shiru ba sai bayan sallah insha,i Abbu ya dawo daga sallah ya fita ta zauna a inda muke zama nan tasa min kira daga daki na amsa na fito zuwa gareta. Tana zaune a cikin damuwa har lokacin nafito ina fadin gani Ammah ta dago tana fadin barci zakiyi bakici abinci bane Aeesha ? Na koshi na fada a razane ta dago kai tana sauke min wani kallo tare da fadin me kikaci kika koshi dashi ba komai na fada ciki ciki a wani irin yanayi na damuwa. Waime ke damun rayuwankine haka kika sakawa kanki wanan damuwa haka to ki jini da kyau wallahi Allahma shedanane Aeesha dani da bawan Allah nan don bamu rageki da komai ba a rayuwan ki . Yau abinda bawan Allah nan ke dauka a kanki kodashi ya haifeki ya tsaya a