Sashe 18
Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana na dauka ilimin ki da wayaun ki tare da tarbiyan ki zai saki natsuwa ki fahinci gabar da muke son dora rayuwan ki a yanzu ? Sai gashi kuma na hango ba hakaba a wajen ki don nayi zaton yadda ake zuzuta ilimin da kwazo a yanzu zaisa ki hango matakin da muke shirin doraki. Idan kinyi tunane da babu dan dana taba bari yai zurfin ilimi a gidan nan kamar yadda ke muka barki a yanzu kina samun ilimi shin azaton ki yanzu nayi hakan ne saboda ban haifeki ba ko me ? Da sauri na dago kai ina kallonsa cikin hawaye ina girgirza kaina a gareshi da nufin ba hakan bane yace kamar hakane Nana a ganina. Bari kiji dalili a yanzu na hango ilimin nan shine tsanin takawa a duniya shine matakalan cinma burin rayuwa ga dan adam yanzu. Inkai manomine sai da ilimin nan na zamani yake bunkasa haka in kai malamine saida ilimi kake samun cigaba a rayuwa ke komai yanzu da zakayi hatta kasuwanci yau ya koma idan baka da ilimi hakan bai bunkasa yadda ya kamata ga bawa. Hakan yasa nayi amfani da wanan daman na ke kokarin ganin mun inganta rayuwanki don gabarki ki samu makoma mai kyau a cikin rayuwa. Alhamdullahi kuma donke din yarinyace mai natsuwa yare da tarbiya yasa muke maki hangen hakan a kanki a yanzu don ba zanso mu tauyeki ba mu durkusheki nan gaba ba zaki fahinci mun maki rikon tsakani da Allah ba. Amma da ilimin nan na zamani zaki fahinci komai a rayuwa a yadda muke fata haka kuma keda kanki zaki warware ma rayuwanki dana iyayyen ki hukunci in muna da rai da lafiya. Idona na runtse cikin dacin rai daga inda nake zaune ina maijin yadda zuciyana yake tafarfasa lokaci guda don ambatosu da yayi a zancensa. Ya dora da fadin to don hakane nake son in baki dama daman da ban taba ba wani yaro ba a gidan nan don ki samu ilimi mai inganci da zaki taka kafarki dashi har hakan ya zamo maki bangon dafawa a rayuwan don akwai rai akwai mutuwa ga bawa in mune yau ba mune gobe ba a duniyan nan. Amma fa duk wanan dole saina saka daga wanan arzikin da ita mahaifiyarki take turo muna hakan zai yuyu don ke shedace banda halin wanan hasashen da nake maki a yanzu. Don haka zancen ace kince ba zakiyi amfani da dukiyar da mahaifiyarki ta turo ba baiko taso a garemu ba yanzu wajen ki nana. Don koda rantsuwa nayi a wajen ban kaffara ta turo munane don inganta rayuwanki a gaba don ba Ammamatan bane kadai ta bari ai nan najeriya suna da yawa meyasa bata turawa sauran yan uwa kudina idan sun mata yawa ne kike gani. Don haka banso ki zalunci kanki da kanki nana in ma wani abu kike tunane a yadda nasan Nana Asma,u sai naga ya girgiza kai ya kare da fadin nana tafi wayau da dabara a duk wajen nan. Don tasan inda ta fito tasan darajan iyayyenta dana yan uwa ba zata bari wani abin asha ya shigo rayuwanta ba a can wanan yasa ina cikin wa yanda suka yarda da abindata fada dari bisa dari da wanan kaddaran rabonki ya gittamata a lokacin. Nasan ko waye nana a lokacin don a wajen mu ta fara zama kafin a kulla karbanta daga hannun mu abawa hajiya Naito rikon da ya zamo sanadin komai a yanzu daga baya kuma kowa ya dare ya koma gefe yana gulman hakan. Ki godewa Allah Nana kina cikin gatanki da rufin asiri akwai dubunki da hakan ya rutsa dasu nana basu san kowa nasu ba a duniya sunan nan suna walagigi da tangaririya a cikin duniya. Ke ko uwarki tayi maki gata bata barki ba sai da ta tabbatar da ta barki a hannun yar uwarta daba zaki taba kukan tanshita a kusa dake ba. Don haka in dai har na isa dake ina kuma da kima a idanunki daga yau din nan na kawar da zancen Nana As,mau a gareki har zuwa dawowanta haka kuma duk abinda ta turo da sunan naki ki dauka kiyi amfani dashi Aeesha. Ke kuma Ammamatan daga yau din nan bason a kara tayar da zancen nan don Allah har hakan yaba wani daman shigowa ya dauki sirin da muke faman dannewa shekara da shekuru a zukatan mu. Akwai sarka guda biyu da nana ta bari a lokacin suna wajen mu har yanzu mun masu boyon da ba mahalunki da zaisan dashi a gidan nan bayan mu. Don haka zan fito dashi a yanzu akai kasuwa a auna a tabbatar da kudinsa albashin in yaso idan sayarwa zamuyi sai a sayar a fara shirin karatunki da kudin ni nawa shawaran ke nan a yanzu . Sai naji Ammah ta nisa a hankali tana fadin to amma malam sai naga zancen karatun nan nidai gaskiya bai kwanta min kawai a sayar ta fito da miji anyi mata aure kawai shiyafi a daina wanan zance ko zata samu natsuwa itama. Dan murmushi Abbu ya sauke tare da fadin kaiya ana baki kina roko amma na fahinci kina ganin wanan shawaran nawa baiyi ba akan yarki ke nan ko ? Yata kuma yau malam to Allah ya baka hakkuri in abin har yakai can amma ni bada wata manufa ai na fadi hakan ba don kace inda mai magana yayine yasa na tofa nima. Kayi hakkuri bana rainawa tsarinka bane a yanzu gaskiya don nasan kafimu tunane ai dagani har ita kawai dai ina ganin auren kamar shine mafita a yanzu. Ammah ina son karatu don Allah na fada cikin sanyin murya don jikina ya gama mutuwa a lokacin da zantukan Abbu din dayakeyi akaina don a kainane zance ita Ammah nata mai saukine ai. Nice dai bawan Allah keson ingatawa rayuwana a wanan zaman kuma iya abinda ya rage ke nan suyi min a yanzu din har incinwa burukana na duniya a yanzu. Yadda yace hakan ya faru don washegari da safe yai kirana da kansa ya mika min tulin kayan da nake gani kamar wani shara a lokacin a hannuna ya kuma kara min nasiha akan rayuwa. Don gaskiya Abbu ya fada ba wanda ya isa ya kaucewa kaddaransa sai in Allah yaso hakan ga bawa haka kuma ko wace kaddara tana da wata manufa ga bawa Allah kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan. Yadda nakai kayan daki na watsa ban dago na sake waiyayansu ba duk da zuciyata tayi laushi a lokacin amma nake ganin kayan wani mugun abu a gabana. Don haka zan iya cewa ban bude ko leda daya na duba inga yaya kayan suke bama balle insan kallarsu kayane kuma masu yawa da zasukai kala goma ko fiye da hakan ajiye. Saidai kamshinsu daya ciki min dakin don kamshi sukeyi irin na turaren yan nahiyar can ta larabawa hakan ya fara sa kaina yana dan sarawa a lokacin. A hankali har na kai kwance ban fadawa kowa banjin dadin jikina ba a gidan sai Abbune da zai fita yake kwala min kiran da nazo nagani . Wanan yasa na taso a dunkule cikin hijjab din islamiyata ina dan kaduwa na nufoshi a hankali ya fara walwale min sarkankokin a gabana inda nake tsugune yana fadin. Kinga wanan biyun tun barin nana kasan nan data tafi ta barmu dake suke boye a hannuna wanan kuma sune ta aiko daga bayan nan. Saidai gun Alh sani zani dasu don akwai shagon sarkoki a kusa da shagonsa su auna su fada muna nauyi su in yaso sai mu in dawo asan abinyi dasu din kamar yadda na fada a jiya. Kai kawai na dukar tunda nayiwa sarkokin kallo guda ban sake dago kai na kallesu ba kuma saida na amsa masa dakai kawai hakan yasa ya dago don ya kalleni anan ya fahinci yanayin da nake ciki lokacin. Da sauri yake furta subbahanallahi meke damun ki haka nanata nan hankalin Ammah dake kokarin kauda kayansu gefe daya ya dawo gareni. Tasowa tayi tana tamba jikina ta juya wurin Abbu tana fadin jikin gaba daya ya gashe kamar garwashin wuta kina ciwo Aeesh ba zaki fada kika kokarin halaka kanki haka ba gaira ba dalili saboda mugun abunda kikasawa zuciyar ki. Hannu Abbu ya daga mata ya mike da sauri yana fadin tashi muje chemist haka na daure naje chemist din tare dashi akai min allurori masu karfi na maleria tare da magani muka dawo gida lokacin idona ya gaba rufewa sai barci ya daukeni. Duk suna zaune sun tsureni da idanuwansu ganin na samu barci mai nauyi yasa Abbu fitowa daga dakin yanawa Ammah hannu da alaman ta biyushi. Batayi sanya ba ta mike ta biyoshi din zuwa wajen cikin tausa murya ya soma magana da fadin Ammamatan meyasa baki amfani da hankalinki ? Wani kallo ta watso masa yace kwarai ko so kike yarinyar nan ta bijere muna a yadda muka santa a baya ? Yanzun ne tafi bukatanki yanzunne kema zaki nuna mata kauna da kulawan ki a gareta don ga baki daya a yanzu bakin mu take gani a wanan gabar. Dole sai kin kara janta a ciki sosai fiyema da da can baya ki nuna mata itama yace kamar kowa tunda tana damu a duniya koba nana a kusa balle mahaifinta damuma ba mu sanshi ba. Wanan abin naki zai kara saka yarinyar a wani mugun yanayi da ba zamuso ba ki kwatanta a gareki yau ke haka ya sama a duniya ya zakiji zuciyar ki a lokacin da kika sanda haka ?. Nan dai ya lurar da ita halin da nake ciki kuma ta gane gaskiya Abbu ke fada hakan yada dana falko naga sauyi sosai a gun Ammah din duk da bada wani manufa take min hakan duk cikin tsawatawan su na manya ne a lokacin. A hankali na yaye hijjab din dana rufu dashi har kai ina kai dubana ga Ammah din dake zaune a gefena tana yankan kubewa. Sannu tayi min tana fadin sannu Aeesha kin falka ya jikin naki na dan juya dara daran idanuwana kafin in koma lumshesu ina fadin da sauki Ammah. Kokarin mikewa nakeyi zaune naga ta tashi da sauri tana kamani tare