← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 101

Sashe 81

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranan an barni da mamaki don sai gashi anty ummi ta aiko aje mata da anty safiya itama wai akwai wash da zasu tafi kawaiyenta da zasu tafi a ranan nason su ganta da kayanta. Na fada mata ta shirya za azo a dauketa zuwa gidan hjyn nan na jiya nan anty safiya ta fara rawan jikin had a kaya ba,a jima ba saiga driver yazo daukata din suka tafi . Wanan yasa koda anty Basira matar yaya Habib tazo anty safiya din ta fita a lokacin amma haka ta zauna zaman jiranta saida ta dawo wajajen karfe dayan rana. Nikan ina mamaki a raina me sukeji a wanan kayan shiriritan na anty safiyane wai suke rawan jiki saya haka ? Tunda suka shige daki sun jima a dakin sai dai dariyansu akeji jefi jefi Ina nan kwance naji sako ya shigo min wayata . Daga classrep din mune yana sanar min da Monday zamuyi resuming school naji dadin jin wanan sakon don zaman gida ya isheni a lokacin har yana son juya min rayuwata a yanzu. Don haka tun a lokacin na fara jawo takarduna Ina hadawa a waje daya Aimana dake kwance tana charting ta dan dago tana fadin ya akayi don jin tsukin dana dan ja a lokacin. Ya akayine na juyo ina fadin kinga waifa takardana da zanyi submitting ashe na barshe hannun Joe kuma ita bata maida min dashi ba gashi dashi zamu tafi IT dashi. Wai kina nufin har zaku tafi IT ke nan nace to kinki karatun nan Aimana da yanzu dake za a tafi nina rasa dalilinki na dakatar da school dinki a yanzu tunda auren ba tashi yayi ba. Naga tayi min wani irin kallo kafin naci gaba da fadin kyawo ya kasance koda zaki shiga gidansa kina da iliminki ko kina kanyi kinga,,,,, Dakata don Allah Aeesha don me mace ke dagewa da karatu wani lokaci badon saboda ta karewa kanta matsalolin rayuwa na gidan miji dana yan uwa bane nan gaba ? Ehh kamar hakan ne dai amma ban dauka hakan bane kadai zaisa mace ta dage da karatu a sali a bangarena mace na karatune don abubuwa da dama na rayuwa fiye da wanda kika lissafa a yanzu. Toni a yanzu banda matsala a wanan tunda kinsan wanda zan aure yana iya tsare min komai na rayuwata dana iyayyena had yan uwa. To don me zan tsaya wani bata wa kaina lokaci da karatu can damage karatun nan don kawai neman na kai na shigesa kar ingani ga wani . Don haka barin karatuna matsalatace don ni ya shafa ni kadai kije Allah yabada sa,an karatu ke koke don kina da wanda ya tsaya makine ai kikake . Da badon hakan ba ba zaki kai wanan lokacin kina wanan wahalan banzan ba wai karatu kuma yanzu shima ya tafi kinga dole ki dage ai a yanzu tunda Abbu nason kiyi karatun aikya dage dashi. Ooh really haka zakice Aimana na dauka dani dake mun zama daya a yanzu ta yadda daya zai iya tsayawa ya fadawa dan uwa gaskiya kai tsaye. Amma tunda kin dauka haka Allah ya baki hakkuri tace amin tana wani fisge fisge kafin can inga ta mike tana shiri wai gida zata tafi a wanan lokacin samira ta shigo dakin ta sameta tana shiri. Tace a,a Aimana badai tafiya zakiyi ba a yanzu kin fasa zuwa gidan amaryam ne muga kwam nafasa ta fada a fusace . Samira ta kalloni tace wani abu ya farune kuma mummy nace ba komai daga dan magana tayi fushi haka dani wai zata tafi gida. Zakice dan magana mana Aeesha tunda ke naganeki baki son kowa yakai matsayin dake kika kai kinfi bukatan koda yaushe a gani a wajen ki ke kadai . Mu ko muna faman binki kamar wasu sakarkaru a kullum baki encourage dina akan auren nan da zanyi sai kin samu wani sukan da kikayi kan hakan . Dagani har Samira sororo mukayi muna kallonta na wani lokaci kafin Asmau ta fado dakin kamar an jefota taji kalaminta ta cabe zancen da fadin . Wanan magana kuma haka anty Aimana kamar dama kana jirace da mutum aiko bai kamata aji hakan ba a bakinki yadda mummy ta dauke a yar uwa. Dama aina fada maki mummy Aimana najin zafi akan ki tun kalamin da tayi shekaran jiya akanki ni naji ta zube min inbashi ba daga dan maganan fatan baki zata tsaya tana wanan maganganu haka ? Tsakaninsu ya koma da aimana din har Ammah taji ta shigo dakin tana tambaya duk su anty safiya suka task ake maida magana. Keko Aimana ai wanga magana bai kai na zafi ba fadin gaskiyane kawai tsakanin ku ai dake da Aeesha a yanzu fatan alheri mukewa kowan ku a rayuwa. Nan sai tayi mata fadan rashin kyautawa tunda banice na kawota gidan ba ai hakan yasa ta fasa tafiya a ranan da gamma suka kwasa zuwa gidan amarya anty fati ni dai banje ba tunda nasan abinda zai kaisu. Karfe goma agogon can nan ya nuna tara takwas da rabi yasan lokacin fitan kakanshi bai ba hakan yasa ya danna masa kira a lokacin akai sa,a ya shiga kuma har yaji an daga. Sallaman da yayine ya sheda muryan jikin nasa don shi kadai ke masa hakan saida yai murmushi ya amsa masa tare da fadin aina zata tunda naja auren kane zuwa wani lokaci kake fushi dani kaki kirana ? Aure kuma ya tambaya cikin mamaki kakan nasa yace ba ka turo min da zancen ka yarda a hadaka da yar gidan Amina ba a yanzu har na yarda na turo ayi komai. Ni kuma grandfather yaushe na turo idan zan fada aida kaina zan sameka da zancen in baka zabina ba wani zan turo ma ba wait waima wana turo wajen kane ? Gaskiya ban sanda wanan zacen ba grandpa saidai idan tsufa ya fara kama ka magaji yaji tsohon ya ambaci sunan sa ya amsa da yes grandpa . Kada kace min baka da masaniya akan zancen nan kakan ka iya yazo min da maganan har nan falona da dare saidai nayi mamaki don yadda mukayi dakai a baya. Ke nan hakan na nufin shirine hakan kai baka da masaniya akan hakan so suke sujawa kansu tonon asiri kome da ba zasu hakkura da wanan zance ba wai ? Grandfather nasan shirin matarkace wanan amma badon kai ba da nayi maganin duk mai baki a ciki zan turo a kwashe min su baki daya in kaisu human right abi min hakkin bata min suna da suke son yi. Kai dakata nan ba turai bane don Allah aiba kai akaiwa laifi ba yanzu nida suka zo min da zancen banza a gabana na tara mutane aka shede hakan ? Yace what I am telling you grandpa zanyi maganin matar nan very soon ya kashe wayarshi yayi kiransa hakan bai samu ba yasa ya hakkura dashi din. Gudun kada ya jawo masu abin kunya yasa akaiwa kowa daya dace kiran gagawa a cikinsu sam basu dauka wanan zance bane saida suka tarune ya fito masu da zancen da basu zata ba ya fara da. Iya ya amsa da rankaidade yana daga mai hannu cikin ban girma saida ya ja iska irin na sarakuna yace ban dauka har dakai za a iya tukarana da zancen banza ba irin wanan. Tuba nake ranka ya dade a yafe min idan munyi ba daidai ba yace rufa min baki mutumin banza kawai . Hakan da sukaji duk wanda ke wajen ya shiga hankalinsa don sun san koma meye ba zancen wasa bane don mai martaba baya irin hakan da kowa. Yallabai a gafarceni iya ya kara fada cikin ban girma ya dan motsa hakan yasa da sauri bafaden dake kusa dashi yayi sauri gyara masa kimtsin shi. Ina zancen auren yaron nan magaji ya fito ka sameni dashi da sauri suka fara kallon kallo a tsakaninsu a take ya gano bakin zaren inda zancen ya fito a lokacin. Hauwa na fahinci kuna son ku mayar damu kananun mutane a idon duniya yanzu lokacin ya juya zamani yazo da wani sauyi an bar wancan akidan hadin na baya a yanzu. Lokaci muke ciki na yancin kai dakai koda kuwa baka son abin nan kamar me dole kasa ido hakan ya faru ga maishi. Naja kunnenki a falon nan ki sakawa yaron nan ido a lamarinsa wayewansa da akidunsa ba data bane da namu a yanzu da yake ganuwan wanan shekarun nasa kinki. Yau gashi kina son ki kaini ga abin kunya mutuncina ya zube a sanadin jikana Dan da Dana ya haifa da cikinsa like son zubar muna da kimarmu dan ra,ayin kanki. Shi magaji yafi kowa be yallabai ina haihuwansa akayi kamar kowa don haka dole a juyasa kuma yadda akeso tsawa ya daka mata abinda ya jima bai mata ba yana fadin duo abinda suka aikata su kuka da kansu ayanzu bayan ya gama masu fada son ransa. Yayi gyaran murya ya mike don shirin fita fada duk da ya makara a ranan amma saida ya fita don sauraren matsalan al,ummanshi. An tashi fada karfe daya aka cafke iya a hanyasa ta komawa gida wasu Jami,ai da ba,ansan ko suwaye ba. Wanan yasa na tare dashi sukayi saurin sanar da maimartaba halinda iya ke ciki gashi ba a san inda suka nufa dashi ba a lokacin. Maimartaba yasan aikin hatsabibin jikansane don haka ya fara neman layinsa baya shiga a lokacin hakan yasa aka kira masa mahaifinsa dagashi sai shi suka tatauna zancen nan ma shima din yayi trying layinsa bai shiga ba a lokacin. Damuwana shine bansan iya wa yanda zaisa akama masa ba a wanan zancen hakance yasa nake son a dakatar dashi ga komai. An kira masa mai babban daki hjy hauwa ya sanar da ita duo wanda ke cikin zancen nan ta sanar dashi yayi gagawan kawo kansa nan gidan sarauta don mafaka saboda yanzu iya yana hannun wa yanda ba asan ko suwaye ba. Yaron nan ashe yaron banzane daga ana son yi masa gata zai fitowa mutane da haukansa a fili shine matsalan da run farko na guda gashi kuwa. Ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba yallabai ba zancen yanzu bane
Chapter 81 · 0% Book details