← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 101

Sashe 100

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kasance jumma,a don haka na saka farar abaya a jikina normaly hakan dabi,antace ko a gida saka fararen tufafi a jikina ranan jumma,a don karrama ranan ga musulmi. Wanan kuma ya samo asaline daga Abbu da naga yana yawan fada idan har jumma,a tazo ba a tsabtace masa fararen tufafinsa da zai saka ya fita ba saina maida hakan dabi,ata nima. Abaya din farace sol daga bayanta sai ta gabatane aikai mata kwaliya har zuwa kasanta da hannayenta da silver din zare aka kuma dagwara mata wasu yan filawowi na farin kyalen rigan ta gaba zuwa dan kasanta kadan. Kayan aikina na dauko bayan na gyara kayana tsab har dakin don da yarinyar taga dana tashi abinda nakeyi ke nan itama saita fara tayani gyaran daki da gidan kafinsu fita. Sai dakin namu da muke kwana ya danyi space a yanzu ga kamshi ko yaushe a cikinsa ni dai banace na taba ganin wani a cikin su yana sallah ba gaskiya tun zuwana garin. Ahakan yasa na kara taka tsantsan da kayana dama kaina dasu tunda hakan ya nuna ba alkibilan mu daya dasu ba ke nan harko ita uwar gaiyar Basira bazance tun zuwana na risketa tana ibada ba gaskiya. Na fito cikin shirina suna zaune a falo da yan uwan nan nata magana sukeyi a cikin yare ganin na girshesu yasa nace a anty basira ashe kin tashi ko ina kwana ? Aisha har an fito na amsa da ehh ya kwanan Amira da yayan mu tace lafiya a takaice gidansu nazo na sameta da yan uwanta don haka na kallo sauran nace ina kwanan ku cikin jam,i garesu baki daya. Suka amsa min nikan nasa kai na fita abinda ba komai a zuciyana lokacin game dasu saidana fitane dayan namijin yace. Sister ke kinga wani abin daya nuna tana tare da mijinkine a yanzu tunda gata dai ba ruwanta da kowa har shi banga ta damu da zuwa wajenshi ba ai. Lukas nima nayi wanan tunanen kan hakan amma kuma madan Ladi tace dole saina saka ido sosai a kanta inson samune kuma in mayi sanadin barinta gidan nan kawai zaifi. Damani gaskiya ba wai son yan kano din nan nakeyi ba tunda gulma ke kawosu itama wanan abinda yasa na yarda don akwai mutunci a tsakanin mune yasa hakan aina fada maku. Jiya duk abin nan da kuka gani itace ta sayo muna wai tashiga kasuwa da kawarta ta gani ta sayo muna shi muyi amfani Amira kuma tayo mata sayayya dama mutumiyar tace. Sister nifa banga abin damuwa ba a nan tunda dan lokaci zatayi ta koma gida ba wai zama zatayi nan ba dindindin damu why not dai ki kara sa ido ki gani a tafiyan ta. Macen da komai bai hadani da ita tace a,a,a tabar gidan nan kawai mace mai kyau a waje hatsarine gaskiya ga brother da son mata balle wanan yadda take din nan. A sanyayye wace muke kwana da ita tace eyya sister sai naga kamar kunyi mata fahinta ba daidai ba bata komai sai karatu da duban computer dinta ko yaushe. Ban taba jin tana waya koda wata mace ba balle namiji tunda ten tayi barci suka kallota don abinda ta fada dayan tace kin sani ko yana binta can wajen aikin nasu ta dawo tana pretending basu hadu ba. Saida karamin namiji ya mike kafin yace wanan duk shirmene don Allah me wanan zata tsaya yi da mijinki yarinyar dake kyamar kowa bata da lokacin wanan ki dai bari ku rabu lafiya da ita is not good mutum bai maka komai ba tana kokarin kyautata maku kuma ku tsaneta. Dama kai haka kake ai don ka ganta haka kadai san ba ajinka bace kaje kaji da yan matanka masu warin gwajo can ita wanan dayan mai suna Bidi ta fada. Na isa wurin aikina ina sauka taxi motan wanan meenat din tazo ta shige ni tayi min horn hakan yasa na juya tayi min hannu na sake juyawa ina bawa mai taxi kudinsa kuma. Saiga wani mota mai kyau zai shiga ya danyi gaba kuma sai naga ya tsaya kadan bayan na tsalako na sameshi har zan wuce ya sauke glass yana fadin. A,ya akayi yau kika shigo taxi ko dama da ita kike zuwa shigo na karasa dake ciki jin hakan yasa na dan waiga don ban dauka dani meshi yake magana ba. MD din nan namu nagani ya sauke glass din motan yake min magana a lokacin kasan cewa ranan jumma,ace ya sawo shedashi mai kyau sai sheki takeyi ga kamshi na tashi har inda nake daga cikin motar nasa. Sorry sir ina kwana na fada tare da dan tsayawa nake fadin aiba nisa nagode zan karasa da kafa ma . No no shigo don Allah ko kina tsoro kada in sace kine ne ya fada a wajen yasa na danyi murmushi na zagaya na shiga gaban motan. Tare da gaidashi da kwana ya amsa min yana fadin lafiya wai dama da taxi kike zuwa ne ko yaune nace ehh sir drop nake dauka zuwa nan. Naji yace kai daga wani unguwa kenan fa ? Na amsa da erea ten sir Yace ohh Garki ke nan ko na amsa da ehh sir naji yace ayya sorry amma ke ba yar nan bace ? Daga kano nazo sir na bashi amsa a gundure don tambayan yayi min yawa yace No wander you look different sai naji yayi shiru koya kula da irin hade fuskan da nayi a lokacin duk daba kallona yakeyi ba shima. Inda senior staff suke parker motarsu ya faka nayi masa godiya na fita zuwa hanyar da zai kaini office din mu. No ga hanya kibi mana ya fada kuma don haka a ranan ta kofan manya na shiga haraban ma,aikatan zuwa office din mu. Na samu senior staff din mu bai shigo ba tukun sai mutum biyu a office din namu na gaisa dasu na wuce wurin zamana don kowa yasan inda wajen zamansa yake. Banyi sanyi a gwiwa ba na fara jona system din aikina don binciken da nakeson yi kafin ogan mu ya iso sam bansan zan iya ba sai gashi da gwaji ina bin yadda mam bash ya taba fada min har na shiga wani na,uran wata kasa ina bincike akai. Inda na shagala sosai da abinda nakeyi har ogan namu ya shigo office din ba tare dana sani ba hakan yasa dayaga na shagala ya kewayo zuwa inda nake din a duke. Sai ji nayi an duka a bayana ya duko yana duba binken da nakeyi din a computer yabi da kallo kafin ya zaro ido yana kiran yan uwanna da sauri suka karaso wajen sit din nawa. How do you do these yake tambayana a cikin mamaki na dan tsorace na fara inda inda ina masa bayani sai kuma nayi nayi shiru ya tsurawa seching din nawa ido na dan lokaci kafin ya furzo iska daga bakinsa. Juyawa yayi ba tare da ya furta komai ba akaina yace kowa ya koma wajen zamansa kuma yanayin yadda ya zauna yasa na shiga tsarguwan kaina har na tashi naje gunshi ina fadin sir nayi wani abinda ba daidai bane ? Yake fadin yayi mamakin da yar traning ta iya kai hakan a bincike ba tare da jin komai ba wanan matakine da wasu manyansu suke amfani dashi na nuna don kosu basu san yadda zasu zakulo wanan hanyan ba a yanzu don,,,,,,,,, Shiru yayi yana fadin quit sure you are braved as you know these method now don sai wanda suka samu training din hakan a turaine suka san yadda ake wanan abin. Have you been there before ? No nace da sauri yace a,a abin yana da mamaki fa ace ke tun a yanzu kinsan wanan din ba matsala ki koma ki zauna ya fada tare da nuna mun wajen zaman nawa. Nabar computer yana loding dama karan da yakeyi kafin inkai na nuna bukata ya shiga yasa ya taso da sauri zuwaga computer nawa har ya rigani isa wajen . Saida ya gama dubawa ya juyo yana fadin miss how do you manage to do this serching please ya tsureni da idanuwan shi cikin dan daburcewa na bashi amsa da i just try it now. Yadda ya kalloni naga alaman kamar bai yarda ba nidai na share kawai nayi tsuru tsuru da idanuna kafin ya gama binciken shi ya mike da sauri ya fice daga office din. Zama nayi cikin karfin hali inda abokan aikina suka taru a kaina da tambaya na share kowa a wajen ba kawai saiga ogan mu ya shigo da manyan officers din mu ba. Sun taru suna ta magana kafin a dauki computer nawa gaba daya su fice dashi dama na ma,aikatane abinda na sani kawai shine yau najawa kaina sabuwar matsala kuma Allah kadai zai fitar dani wanan kuma . Shiru shiru ina jiran inji anzo an fitar dani sai naji shiru wanan yasa na dan samu sauki a zuciyana har time din zuwa mosque yayi musulmai suka fice zuwa ibada ya rage wa yanda basa sallah a wajen sai mu mata sai kuma wa yanda basu damu da ibada ba sosai tsirarunsu a ma,aikatan . Ogan office din mune ya tsure ni da tambaya ban yarda na fadi komai ba duk tsoratanin da yakeyi bance kala ba na kafe da gwadawa nayi kawai. A haka har muka tashi daga wajen aikin lokacin ina ji kamar na gudu in koma kano in fasa karatun ga baki daya don halin dana shiga ciki. Ashe bai kare min ba don ko zan samu wani a gidan yaya kuma dan kayan makulashe na soyowa Amira dake murna idan ta ganni. Ina jin nauyi da kunyan komawa ban rika mata komai ba don yanayin dana shiga a office yasa nake jin kasala na sauka min a lokacin. Da sallama na shigo gidan da muryana dake nuna gajiya a tare dani lokacin na hawowa samansu kuma da nayi a falonsu na samesu da kannenta . Kamar kullum ina sallama Amira tasheko tana tarona na rugumeta nima ina nuna mata jin dadin ganinta a lokacin yayin da uwarta ke faman waya a cikin yare. Tsaraban na mika mata sauran na mikawa dayan budurwa don yayiwa amira
Chapter 100 · 0% Book details