← Book details Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 101

Sashe 83

Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

a school din. Sai takai zaune tana bina da kallo kafin naji tana fadin gashi ko ba muyi abincin rana ba yau, don saura tuwon jiya ya rage da yawa jiya shi mukaci dazun da rana. Ba komai Asmau bana jin yunwa a yanzu tayi shiru na dan lokaci kafin can kuma tace dani mummy wani abu ya faru dake idon ki ya nuna kinyi kuka sosai wallahi ? Saida na juyo na dan dubeta kafin murmushi yake ya biyo baya ina fadin wani abune ya bata min rai Asmau amma ba komai akwai Allah . Sai naji tace dani kodai wani ya zageki inci ubanai wallahi yadda tayi maganan ya dan ban dariya nace ? Haba dai ba komai ai ya wuce ta zauna shiru kamar tana tunane kafin ta nisa tace ina mamakin mutane wallahi mummy yanzu.. Da basu da tunane sai ka dauki laifin wani ka dorawa wani ba zaka barshi yaji da abinda ke damunsa ba ka dauko wani ka dagwara masa kuma. Asmau ba hakana bane idan Allah ya hanemu da abu mu nisanci abin nan komai kankantar shi kuwa kada mu raina don fitinan yinsa yafi yinsa yawa . Mutane nada gaskiya wani lokaci saidai suna abin ne ba bisa ka,ida ba kamar yadda hadisi ya koyar ayi, kamata yayi su fuskanci mai laifin a lokaci da ya aikata abin amma ba daga baya ba ka dabawa mutun zafin laifin bayan ya aikata hakan. Nikin daure min kaina wallahi mummy ta fada nace ba zancen daure kai bane Asmau yau nima kaina din a daure yake wallahi. Don Salman ne ya ban mamaki matuka don ban taba zaton haka a gareshi ba wallahi sai gashi yayi min abinda ya daure min kaina? Salman dai da nake jin kina fada mummy nace shifa Asmau shidai dan uwan wanan matan da muka hadu shekaran jiya dasu a bukin nan. Mutumin da nake wa kallon daraja da yan uwan taka yau shi ya kalleni ya fada min maganan da ya daure min kai iya son ransa a gabana Asmau. Ni Salman yau zai fadawa Man Bash yayi amfani dani don cinwa manufarsa kuma ya biyani a fakaice yayi tafiyasa . Kada kuma in kara gigin nemansa ta hanyar shi mu matsalan mu ke nan mata idon mu a rufe da mutum ya nuna kulawansa akan mu sai mu dauka hakan sone ? Bamu la,akari da irin mutanen da level din mu ya dace muyi mu,amula dasu da farko duk wanda yazo gun mu sai mu dauka so ne a garemu Asmau ? Ni Man Bash bai taba nuna min wani abinda zan fada son shi ba yadda yake nufi haka kuma ya fada min da bakinsa kwarai don wani manufa yasa ya tsaya ya taimakawa rayuwata shi salman ya sani . Amma me zaisa yau ya fada min hakan kamar da wani manufa ko kuma na sani na yarda da plan dinshi aikin banza naji ta fada kai tsaye. Wai man bash dai wanan naki mai mutunci saukin abin cikin zancensa bai sa kinyi sha shanci da man bash din ba ai. Nace haba dai Asmau yace shine dai yau abin bakin ciki ko ba komai bane walle kishina nace kishin me kuma ? Rabu da kurman kishi mummy kurman kishi kamar mahauka yake saka mutum ai kada ki dada karki kara wata kila baiso zaman ki da wacan din bane. A shekarun Asmau da nake gani tayi kankanta da rike manyan magana a bakinta amma idan kinji ta zaro magana ko tsohuwa saita kaucewa Asmau kuma shigen duk haka da bi,ansu yake da manyan magana. Sam banyi wanan tunanen da tayi ba cikin dan lokaci guda haka don ba zan kawo wanan tunanen kan salman ba amma in har ba hakan bane data fada meya kawo wana maganan haka a bakinsa cikin hasala dani yau ? Kamar nayi masa laifi a baya kan mu,amulana da Bash ko kuma a sanadina wani abu ya taba faru tsakaninsu dama can ban sani ba ?
Chapter 83 · 0% Book details